MAGANGANUN IMAM DANGANE DA KA'ID


Hakika idan muka yi la'akari da irin maganganun da Imam (r.a) yayi akan Ayatullahi Khamene'i, zamu iya fahimtan girma da daukakan da wannan madaukakin bawan Allah ya ke da shi.
Ga kadan daga cikin irin wadannan maganganu:

Idan kuna tunani cewa kuna iya samun, a duk duniya, mutum guda daga dukkan shuwagabannin kasashe, sarakuna da sauransu wajen sadaukar da kai ga Musulunci kamar Sayyid Khamene'i kuma wanda zuciyarsa take cike da shaukin hidima wa al'umma, lallai ba zaku iya samu ba.
Nine na raini Sayyid Khamene'i.
Hakika shi (Sayyid Khamene'i) ya kasance ni'ima ce daga Allah wanda Ya arzurta mu da ita.
Hakika Allah Ya arzurta mu da muka zabi shugaban kasa (Ayatullahi Khamene'i) mai kula da addini, mujahidi akan madaidaicin tafarkin musulunci kana masani kan al'amurran addini da kuma siyasa.
Ina rokon Allah da ya kara maka (Sayyid Khamene'i) lafiya don ci gaba da yin hidima wa musulunci da kuma musulmai.
Hakika ni na dauke ka a matsayin daya daga cikin jiga-jigan Jamhuriyar Musulunci, dan 'uwa masanin mas'alolin fikihu kana kuma mai kiyaye su, sannan kuma mai kiyaye rukkunan fikihu da ke da alaka da wilaya ta gaba daya ga malamin fikihu kana kuma daga cikin mutane mafiya karanci.
Shi (Ayatullahi Khamene'i) ya kasance kamar rana ce mai haskakawa
Muna rokon Allah da Ya kiyaye (mana) irinku wadanda basu da wani ra'ayi in banda hidima wa musulunci.