Ci Gaban Jawabin Imam Khamene'i A Bukin Zagayowar Wafatin Imam Khumaini

Jagora Kenan Yayin Da Yake Gabatar Da Jawabinsa a Gaban Dubban Masoya Imam (r.a).
Jagora Yayin Jawabinsa

Ya ku jami'an Amurka - wadannan sabbin 'yan mazan jiya da suke tsammanin za su iya kaddamar da yaki akan duniyar musulmi - dole ne ku bude kunnuwanku, ku saurara ku ji: Ba za ku iya yin galaba akan Musulunci da al'ummar musulmi ba, kun rudu ne da abin da ya faru a Afghanistan da Iraki, hakan kuwa ya biyo bayan raunin fahimtarku ga al'amurra ne, wannan kuwa ya nuna cewa lalle ba kwa fahimta lamurra yadda ya kamata. A Afghanistan dai ba da al'ummar kasar kuka yi yaki ba; a Iraki ma dai ba da al'ummar Irakin kuka yi yaki ba. Al'ummar Iraki dai ba sa son kare gwamnati Saddam, kuma ba su kare ta ba ma, kamar yadda kuma al'ummar Afghanistan ba su so kare gwamnatin Taliban ba, kuma ma ba su kare ta ba. To amma yanzu da kuka shiga kasar Iraki, to fa kun sa kafafunku ne cikin ramin fada mai tsanani da al'ummar Irakin.

Wadannan 'yan mamaya dai suna matsa wa al'ummar Iraki lamba da kuma cin mutumcinsu - duk da irin abin da wannan al'umma ta mallaka na daga malamai da masana ga kuma tsohon tarihi da wayewa - suna cewa wai wasu Irakawa su taru su zamanto masu ba wa shugaban mulkin sojin Amurka a Iraki shawara! Shin mene ne aikin wannan shugaban sojin Amurka a Iraki? Wannan ai hakki ne na al'umman Iraki. Abokan gabanku dai a Iraki, al'ummar Iraki ne, shin me ya sa kuke tuhumar Jamhuriyar Musulunci?

A yau sun kasance masu buga gangunansu da karfin gaske, suna cewa mu dai muna cikin damuwa dangane da shigan da Iran take da shi a Iraki! A hakikanin gaskiya, kasantuwanku a Iraki ai shi ne abin damuwa gare mu.

Shin wani hakki Amurka da Birtaniyya suke da shi na tura sojojinsu Iraki? Da wata doka ce ko hakki suka dora wa al'ummar Iraki wani shugaba na soja? A halin yanzu dai abin da ke faruwa a Iraki da Afghanistan ya tabbatar da karyar Amurkawa na demokradiyya da kare hakkokin 'yan'Adam. Jama'a sun gane cewa (wadannan mutane dai) ba su yi imani da hakki da ra'ayoyin al'umma ba. Abin da kawai suka yi imani da shi, shi ne cika aljuhan kamfanonin da suke juya gwamnatin Amurka, wato kamfanonin mai, makamai da kuma cibiyoyin kudi da suke juya Amurkan da wasu gwamnatoci na daban.

Ina sanar da ku Ya ku al'ummar Iran! Wannan barazana ta Amurka ba wai abu ne na yau ba, kuma ba wai bakon abu ba ne. Tun daga farkon samun nasarar Juyin Juya Halin Musulunci, wadannan mutane suke mana barazana.


Imam, shekaru goma sha biyar ya yi yana gwagwarmaya, kuma saboda wannan imani nasa dake cike da wayewa ya samu damar fuskantar mulkin mallaka na cikin gida da kuma girman kai na kasa da kasa; lallai babu shakka a duk lokacin da al'umma suka yi tsayin daka (wajen fuskantar 'yan mulkin mallaka), to kuwa nasara tana tare da su.

Gaban da Amurka da 'yan korenta suke yi da tsarin Musulunci, ba wai bakon abu ba ne. Su kansu sun san cewa kai harin soji ga Iran, ga wannan al'umma mai girma, ga al'ummar da take da irin wannan adadi na matasa da suke tsaye kana jarumai, kisan kai ne gare su (wadanda suka kawo harin).

Ya kamata al'umman Iran su sani, kai yana ma da kyau abokan gaban al'ummar Iran su san cewa: Jami'an Jamhuriyar Musulunci, ba sa kokarin kai wannan kasa zuwa ga yaki da wani. Mu ba zamu sanya kasa da al'ummarmu cikin hatsarin yaki ba, kuma ba ma maraba da yaki, to amma (yana da kyau a gane) duk da cewa fa al'ummar Iran, jami'ani da gwamnati ba sa neman wani da fada, to sai dai fa matukar wani ya kawo mana hari, lalle zai dandana kudarsa a hannun al'ummarmu.

Shakka babu su kansu sun san cewa yaki da Iran dai zai jawo musu babbar hasara, sun san cewa yaki da Iran dai ba yaki ne da wata gwamnati guda ba, ba yaki ne da wata gwamnati da ta zo ta hanyar juyin mulki ba, kuma ba wai yaki ne da wata gwamnati ta soji ba, face dai yaki ne da wata al'umma! Don haka ne su kansu ba sa maraba da yakin, sai dai kawai ta hanyar bayyanar da zancen yakin da barazana suna so ne su razana al'umma musamman ma dai jami'an gwamnati, don su tilasta musu mika kai; su tabbatar musu da manufofinsu, sannan kuma su ha'inci al'ummar kasarsu. To amma ya kamata su san cewa babu wani jami'in gwamnati, a dukkan bangarorin gwamnatin nan guda uku da yake shirye ya mika wannan al'umma da manufofinta ga abokan gaba bakin haure. Kuma idan ma da wani (daga cikin jami'an) da zai yi wani kokari na mika al'umma da manufofinsu ga abokan gaba, to lalle cikin rashin tausayi da girmamawa al'umma za su yi waje da shi.

Hakika yin hidima ga al'ummar Iran abin alfahari ne (a wajen jami'ai). Maganganu da ra'ayin jami'an gwamnati guda ne wajen kare hakkoki da 'yancin al'umma, wannan kuma wani abu ne da ya kamata kowa ya fahimta, duk da cewa dai sun riga da sun san hakan.

Kafafen watsa farfagandojin abokan gaba - duk da cewa abin bakin ciki suna samun 'yan kore a cikin gida - suna watsa farfagandan cewa akwai rashin fahimtar juna da fada tsakanin jami'an gwamnati. Suna rudin kansu da abokansu cewa wai wannan sabani zai sa jami'ai su gafala da abokan gaban. Ina sanar da ku Ya ku al'ummar (Iran), duk jami'an gwamnati na bangarorin gwamnati uku, kansu a hade yake wajen kare al'umma da akidun Musulunci da kuma fada da abokan gaba. Abokan gaba dai za su rudi kansu ne idan har suka yi tunanin su sami wani jami'i daga cikin rukunan gwamnatin wannan tsari na Musulunci wanda yake son ganin bayan wannan tafarki na marigayi Imam da kuma Juyin Juya Halin Musulunci.

Shekaru uku ko hudu da suka wuce a irin wannan rana na taba cewa kokarin abokan gaba dai shi ne samun damar sanya 'yan koransu cikin hukuma da kuma samun bakin magana. To abu ne mai yiyuwa abokan gaban su sami nasarar samun shiga cikin wasu jami'an gwamnati, ko kuma su sami nasarar jawo wasu raunana zuwa ga bangarensu, to amma ko da wasa wannan abu ba zai kasance mai amfani ga abokan gaban ba; don kuwa asasin tafarkin Imam da Juyin Juya Halin Musulunci abu ne da ya samu karbuwan dukkan jami'an gwamnati da na bangarori ukun nan manya na gwamnatin. Lalle matukar suka bi ta wannan hanya dai to za su sha kunya kuma ba za su yi nasara ba.

Alhamdu lillah har ya zuwa yanzu suna da kuma tunanin Imam yana nan cikin zukatan al'ummammu, sun kare shi, kuma kowace rana daukaka da mutumcin Imam mai girma sai dada karuwa suke yi. Kuma muna gode wa Allah cewa jami'an gwamnati mabiya Imam ne da tafarkinsa, kuma mun gode wa Allah cewa al'ummarmu a raye suke.


Mafi muhimmancin aikin da Imaminmu mai girma ya yi a duniyar Musulunci shi ne rayar da bangarori daban-daban na siyasa da zamantakewa na Musulunci. Daga lokacin da mulkin mallaka ya shigo kasashen musulmi, babban kokari da kuma aikin da suka fi ba shi muhimmanci shi ne shafe bangarorin siyasa da zamantakewa na Musulunci da kuma kira zuwa ga adalci da kuma 'yancin da Musulunci ya ke jaddadawa
Duk da cewa dai a lokuta da dama na sha gaya wa jami'an gwamnati, kuma a yau ma zan sake nanatawa: Hidima wa wannan al'umma shi ne babban fada da Amurka, duk wani wanda yake son ya yi fada da Amurka fada na asasi, to dole ne ya yi hidima ga wannan al'umma. Duk wani wanda yake son fada da abokan gaban wannan al'umma a aikace, to dole ne ya yi fada da fasadi.

Mataimakan abokan gaba da suke tare da mu su ne fasadi da nuna banbanci tsakanin al'umma; dole mu yi fada da wadannan abubuwa, hakan kuwa aiki ne na gwamnati, majalisa, ma'aikatar shari'a da dukkan manyan jami'an gwamnati. (Ina kiranku da) ku yi hidima ga al'umma, ka da ku sassauta wa lalatattun mutane, koda wasa kada ku taba amincewa da fasadi a cikin hukuma, hakan kuwa shi ne babban hidima (ga al'umma).

Matukar dai muka ji rauni da kokarin kauce wa hanya, to cikin gaggawa mu yi kokarin gyarawa; dole ne mu ba da himma wajen gyara tsare-tsarenmu, gyara ta hanyar wannan tafarki da Imam ya koyar da mu. Gyara dai na hakika shi ne fada da fasadi da nuna banbanci; dole ne kokarin tabbatar da adalci ya zamanto babban burin jami'ai, hidima wa al'umma dai wani asasi ne na addini da ya zama wajibi ya kasance tare da jami'ai. Wannan dai shi ne tafarkin Imam na hakika.

Ina rokon Allah da Ya sanya rayukan Annabawan Allah da waliyanSa masu tsarki, ruhin shahidai da Imaminmu mai girma su kasance tare da jami'an gwamnati da kuma al'umma wajen bin wannan tafarki, sannan kuma addu'oin Bakiyatullah, Imam Mahdi (rayukanmu su kasance fansa gare shi) su shafi wannan al'umma da jami'anta.

Wassalamu Alaikum Wa Rahmatullahi Wa Barakatuhu.