Jawabin Jagora Ga Mawakan Ahlulbaiti (a.s) A Bukin Ranar Haihuwar Fatima al-Zahra (a.s)


  • Maudhu'i: Ganawa da Mawaka a Bukin Ranar Haihuwar Fatima al-Zahra (a.s)
  • Wuri: Gidan Jagora -Tehran.
  • Rana: 20/Jimada al-Thani /1424 = 19/Augusta/ 2003.
  • Shimfida:A wannan rana ta 19 ga watan Augusta ne, da yayi dai dai da ranar haihuwar 'yar Manzon Allah, Fatima al-Zahra (a.s),Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Ayatullah al-Uzma Sayyid Ali Khamene'i (H) ya gana da kuma gabatar da jawabi ga mawakan Ahlulbaiti (a.s) da suka kai masa ziyarar taya shi murnar wannan rana. A cikin wannan Jawabi dai Jagoran ya yi tsokaci dangane da wajibcin da'a da biyayya ga Allah don samun daukaka ta duniya da lahira, da kuma ruguza akidar cewa son Ahlulbaiti (a.s) ya kan wadatar daga bautan Allah, kuma ba za a azabtar da mutumin da ya ke son Ahlulbaitin ba ko da kuwa ya sabi Allah. Abin da ke biye dai fassarar jawabin Jagoran ne:

Jagora - Imam Khamene'i Yayin Isowarsa Wajen Taron Ranar al-Zahra

Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai

Ina taya dukkan 'yan'uwa abin kauna wadanda suka zo wannan bukin haihuwa da idi mai girma na (haihuwar Fatima al-Zahra) murnar zagayowar wannan rana. Haka nan kuma ina mika sakon godiyata ga dukkan 'yan'uwan da suka ba da lokacinsu wajen shirya wannan taro mai albarka, musamman 'yan'uwan da suka zo daga wurare masu nisa, haka nan kuma 'yan'uwan da suka tsara da rera mana wadannan wakoki masu dadi da ma'ana.

Lalle yana da kyau mu fahimci girma da daukakan wannan alaka ta zuciya da ruhi; don kuwa ita ce garkuwar imaninmu; kuma abu mai kiman gaske da ke gina yanayinmu na dan'Adamtaka da kuma Musulunci. Lalle ya kamata mu ci gaba da karfafa alakarmu a kowace rana da wadannan iyalai tsarkaka na Iyalan gidan Manzon Allah (s.a.w.a) musamman ma dai Fatima al-Zahra (amincin Allah ya tabbata a gare ta), bugu da kari kuma kan kokarin kyautata alakarmu da Ubangiji Madaukakin Sarki da kuma yi masa da'a da biyayya.

Hakika wakar da dan'uwanmu ya rera yanzu ba daidai ba ne, mu ce wai don mu 'yan shi'a da masoya (Ahlulbaiti) ne, Allah ba zai mana azaba ba ko da kuwa mun aikata zunubi; lallai lamarin ba haka yake ba. Don kuwa "Wanda ya yi biyayya ga Allah shi ne masoyinmu, masoyinsu (Ahlulbaiti) dole ne ya yi biyayya ga Allah; don kuwa su kansu wadannan manyan mutane ta hanyar biyayya ga Allah ne suka sami wannan matsayi da daukakan da suke da su. An yi musu jarabawarsu ne tun kafin su zo wannan duniya; "Allah Ya jarraba ki tun kafin Ya halicce ki, sai ya same ki mai hakuri da juriya bisa abin da ya jarraba ki".Al'amurran Ubangiji dai ba haka kawai suke kara zube ba. Ya zo cikin wata ruwaya cewa Manzon Allah (s.a.w.a) ya gaya wa Fatima al-Zahra (a.s), duk da irin wannan matsayi da take da shi, cewa; wato (Ya Fatima) alaka da nasabar da kike da shi da ni ba za su amfanar da ke da komai ba a gaban Ubangiji. A'a ashe ba a samu a cikin 'ya'yan Annabawa da Imamai wadanda ba su da alaka da Ubangiji ba, kuma ba su samu amfanuwa da wadannan taurari masu haske ba?

Hakika abin da ya daga darajar masoya addini (waliyai), tun daga Manzon Allah (s.a.w.a), Amirul Muminina da sauran taurarin wannan zuriya mai tsarki - wadanda suka kasance abin koyin da ba su da na biyu cikin halittu - har zuwa sauran waliyan Allah, shi ne da'a da biyayyarsu ga Allah Madaukakin Sarki. Don haka ne ma a lokacin da ku ke son ambaton sunan Manzon Allah (s.a.w.a) cikin Tahiyar salla don girmama shi ku kan ce ne (Ashhadu Anna Muhammadan Abduhu) bauta ku ke fara ambato kafin ku ce (wa rusuluhu). Bautan (Ubangiji) ita ce take sama da sako, asasi da kuma kimar aiki, bautar Allah ce. Don haka dole ne ni da ku mu bi wannan tafarki, wannan dai abu ne mai girman gaske, lalle idan har idanuwanmu suka samu nasarar ganin wannan girma da daukaka, to fa dole ne mu gode wa Allah Madaukakin Sarki, dole ne dai mu kama wannan tafarki, don kuwa shi ne kawai tafarkin; dole ne mu bi wannan tafarki da dukkan karfi da iyawanmu, idan ma dai hakan bai samu ba dai to za mu amfana da abin da muka iya cimmawa.

Ina rokon Allah Madaukakin Sarki da a kullum Ya kara albarkarSa a gare ku; ina rokon Allah da Ya albarkaci wannan taro da ku da dukkan wadanda suka shirya wannan taro da tausayawa da kuma yardar Fatima al-Zahra (a.s); kuma Ya dubi wannan kauna da soyayya taku ga wannan madaukakiyar mace da idon rahama, tausayawa da kauna; a kowace rana kuma Ya kara mana sani da fahimtar matsayin wannan baiwar Allah Madaukakiya; zuciyar Waliyul Asr (rayukanmu su kasance fansa gare shi), wanda cikin ikon Allah wannan taro namu ya albarkatu da kamshinsa, kuma ta kasance tare da mu kana kuma Ya sanyamu cikin addu'oi da tausayawan wannan Madaukakin bawa.

Wassalamu Alaikum Wa Rahmatullahi Wa Barakatuhu.