Shawarwarin Jagora (Imam Khamene'i) Ga Matasa Masu Shirin Aure(1):
Daga:
Muhammad Awwal Bauchi
IRIB-Tehran - I.R.of Iran
awwalubauchi@yahoo.com

________________________

Jagora Imam Khamene'i - A Daya Daga Cikin Ganawar Da Yake Yi Da Matasa

Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai

Kafin in daura muku aure a matsayin ma'aurata biyu, zan so in dan ce wani abu gare ku angwaye da amare da kuma iyalanku.

Da farko dai yana da kyau a fahimci cewa daura aure yana nufin kulla wata alaka ce da Ubangiji Madaukakin Sarki ya yi umarni da ita. Gaskiya ne cewa (aure) ya kasance daga cikin dabi'u na dan'Adam, to amma duk da hakan Allah Madaukakin Sarki ya tsarkake wannan alaka wacce daga karshe take haifar da abubuwa masu kyau. Don haka bai kamata a dauki wannan alaka a matsayin wani abu maras muhimmanci ba.

Daya daga cikin munanan ayyukan da kasashen yammaci suka yi shi ne rikon sakainar kashin da suke yi wa wannan alaka da rashin ba ta muhimmancin da ya kamace ta. Su dai turawa suna mu'amala ne da wannan muhimmin lamari, wannan karfaffiyar alaka tsakanin mace da namiji, mu'amala tamkar ta cire riga ko kuma shiga wani shago, wato a matsayin wani abu kawai mai sauki kana iya yinsa yanzu ka kuma canza shi duk lokacin da ka ga dama. Don haka wannan akida ta kan sanya shu'uri da dandanon mutum su kasance masu adawa da ci gaban wannan alaka ta auratayya. A duk lokacin da daya bangaren (macen ko namijin) ya ga wani abu ko kuma suka fuskanci wata matsala, to ba tare da hakuri da la'akari da wasu abubuwa ba akan kawo karshen wannan alaka (mai tsarki). Amma shi kuwa addinin Musulunci bai yarda da hakan ba, (wato baya kwadaitar da hakan) don kuwa a Musulunci an gina tushen iyali ne bisa karfafan tubalai. A koda yaushe Musulunci ya kan ja kunnen mabiyansa wajen yin taka-tsantsan a lokacin da suke kokarin zaben abokin zama ko kuwa abokiyar zama sannan da kuma yin duk abin da mutum zai iya wajen kiyaye wanzuwar wannan tsarkakakkiyar alaka. Dole ne ku yi iyakacin kokarinku wajen kare wannan sabuwar alaka, kamar yadda kuke kula da sabbin tsirran da kuka shuka don su girma su zama bishiyar da za ku amfana da 'ya'yanta.

(Yana da kyau a fahimci cewa) kula da wannan alaka ba ta damfaru ne da irin kudin shigan da mutum yake samu, ko kuma yawan ilminsa ko kuma irin aikin da yake yi kawai ba, don kuwa shu'urin dan'Adam kan aure da gina iyali kusan abu guda ne, babu wani (gagarumin) bambanci tsakanin masani, malami, dan wasa, ko kuma lebura da dai sauransu, hakan kuwa saboda shu'urin guda ne tsakankanin dukkan mutane, babu wani bambanci tsakanin talaka da mai kudi.

Babu shakka kowani guda daga cikin miji da mata suna son gidansu ya kasance wajen kwanciyar hankali da nitsuwa gare su bayan sun gama aikace-aikacensu na rana, wannan wata bukatuwa ce da ma'auratan suke bukatuwa da ita a rayuwarsu ta aure; suna bukatuwa da farin ciki da yanayin da yake samar da hakan. Mai yiyuwa ne (macen ko namijin) su kasance 'yan kasuwa, ko kuma 'yan siyasa ko kuma suna zama ne a gida don tarbiyyantar da yara, kai ko ma dai wani irin aiki suke yi, dukkansu sukan gaji, to a lokacin da suka dawo gida, suna bukatuwa da yanayin cikin gida mai faranta rai, wannan kuwa ba wata bukata ce ta wuce guri ba, a'a, a dabi'ance haka lamarin yake.

Hakika lamarin ba shi da alaka da abin hannun da mutum ya ke da shi, don kuwa akwai da dama daga cikin masu abin hannun da ba su dandani dadin zamantakewar aure ba; rayuwarsu ta kasance cikin kunci, cike take da hassada da haramtattun bukatu da fata. Babu shakka mutumin da ke da wani mukami, wanda yake ba da umarni, ya kan iya fuskantar matsaloli daban-daban a gida, me yiyuwa ne shi wannan mutum ko kuma wannan matan ya/ta samu abokin zama mai saurin fushi, maras hakuri ko kuma malalaci. Don haka dukiya, mukami, zaman birni ko kauye ba za su canza yanayin zamantakewar iyalai ba matukar dai babu fahimtar juna da yafewa tsakanin ma'auratan biyu. Don haka ne ma Allah Madaukakin Sarki cikin Alkur'ani mai girma yake cewa: "Shi ne Wanda Ya halicce ku daga rai guda, Ya kuma halicci matarsa daga jikinsa don ya sami nitsuwa da ita…" (Suratul A'araf 7:189). Abin da Alkur'ani yake nufi shi ne "mu'amala da juna cikin kauna da kuma samun kwanciyar hankali da juna'. Lalle ya kamata mata da miji su kasance hanyar zaman lafiya, kwanciyar hankali da kauna tsakanin junansu, don haka dole ne ya ku matasa maza da mata ku sanya hakan cikin zukatanku, don kuwa aurenku zai kasance sanadiyyar haifar da iyali. Dole ne gidan da za ku zauna ya kasance waje ne na kwanciyar hankali da nitsuwa gare ku da kuma 'ya'yan da za ku haifa. Jagora Imam Khamene'i - A Daya Daga Cikin Ganawar Da Yake Yi Da Matasa

Abu na biyu da zan gaya muku shi ne yana da kyau ku fahimci cewa wadannan abubuwa ba a samunsu haka kawai, wato ba sa samun mutum haka kawai, dole ne ku yi kokari wajen samar da su. Hanyar samar da su kuwa ita ce dukkan ma'auratan su so junansu. Watakila ku tambaya ta ya ya? Kamar yadda ake cewa ne: "Ba a iya tabbatar da so da kauna ta hanyar karfi da tursasawa", lalle haka ne don kuwa so kamar karamar bishiya ce, dole ne a bata ruwa da kula da ita, don haka duk wani abin da za ku yi wajen kula da girman wannan bishiya dole ne ku yi hakan wa kaunarku. Hakan kuwa yana hannayenku ne Ya ku matasa. Hanyar da za ku bi wajen cimma wannan abu ita ce ta hanyar kauna da biyayya ga junanku da kuma nuna wa abokan zamanku hakikanin so da kula. Ku nuna wa juna cewa rayuwarku ta damfara ne ga junanku, dukkan wadannan abubuwa za su taimaka wajen karfafa shu'urin soyayya da ke zukatanku.

Babu makawa, kusan dukkan kiraye-kiraye da umarnin da Musulunci yake bayarwa dangane da sanya Hijabi yana yinsu ne saboda kare wannan alaka ta aure. Don haka idan har, a matsayinku na matasan da za su yi aure, ba ku kula da hakan ba (hijab) a lokacin da kuka fita waje, ko kuma kuka bari idanuwanku suka koma kan wasu matan ko kuma mazan, zukatanku suka koma ga wasu sabanin abokan zamanku na aure, idan kuka bari har kuka kulla alaka da wasu mata ko mazajen da ba naku ba wadanda kuke gamuwa da su a wajaje daban-daban, to babu makawa aurenku na iya shiga cikin mawuyacin hali. Da farko dai abokin zaman naku zai/zata fara rasa irin sha'awar da ke jawo hankalinsa/ta zuwa gare ka/ta da ke haifar da so da tausasawa. Don kuwa koda a ce mutum yana da irin kyaun da Annabi Yusuf (a.s) yake da shi, to babu makawa bayan wani lokaci zai kasance ba wani bakon abu ba ga daya abokin zaman. Don haka, kamar misalin wannan bishiya, dole ne a ba ta lokaci wajen kula da wannan so da kauna.

Kamar yadda na fadi ne a baya, bai kamata a dauka cewa ana iya samun so da kauna cikin ruwan sanyi ba ne, a'a dole ne a yi kokari kafin a same su. Idan kuka duba a kasashen yammaci, a wasu al'ummomi, za mu ga cewa matasa sukan tsoma kawukansu cikin harkokin zinace-zinace kafin aure, wannan shi ya kan sa ba sa yin aure da wuri idan aka kwatantasu da sauran al'ummomi. A irin wadannan kasashe maza da mata, musamman ma maza, sukan yi zinace-zinace kafin su yi aure, haka ne ya kan sanya auren da suka yi daga baya ba ya zama musu wani bakon abu, kuma ba wani lamari ne mai muhimmanci ba. Don haka ya ya za a iya kwatanta su da wani matashi musulmin da ya nesanci irin wadannan muggan dabi'u, wanda ya rayu rayuwa ta tsarkaka da mutumci? Shin mahangar wadannan nau'i biyu na mutane kan aure zai iya kasancewa guda? Shin girmamawarsu ga aure zai kasance guda? Koda wasa.

Wani abu kuma da yake da muhimmanci ku fahimta shi ne cewa babu wani mutum, namiji ne ko mace, (in ba Ma'asumi ba), da ba shi da irin wadannan rauni da kura-kurai, babu wanda yake ya cika komai. Hakan ne ma ya sa za mu ga cewa dokokin Musulunci suna kokarin kiyaye alaka ne ta aure. Hijabi ma don haka aka yi umarni da shi, don kada mace ta bude jikinta ga wasu na daban, kada ta shigo cikin mutane ba tare da suturan da ta dace da mutumci da girma ba, don kada ta tada hankulan wasu na daban, dukkan wadannan abubuwan janyo hankula an kiyaye su ga abokin zamanta (mijinta).

Don haka ya zama dole, tun ranar farko na auren, ma'abutan biyu su yi kokari wajen kare wannan so da kauna da Allah Ya dasa cikin zukatansu. Ya kamata su yi kokari wajen kara wannan kauna da soyayya da kuma karfafa su. Hanyar cimma hakan kuwa, kamar yadda na fadi ne a baya, ita ce ta hanyar taimakon juna da kiyaye mutumci da manufofin juna. A matsayinsu na ma'aurata biyu, dole ne su kiyaye sirrin juna, kada su fade su ga wasu ko da kuwa dangi ko na kurkusa da su ne, dole ne ku kiyaye irin shigar da kuke yi. Idan har kuka kiyaye hakan, to babu makawa za ku ji dadin zaman aurenku.

Abu na uku da nake son nuni da shi, shi ne muhimmancin sassauci da yafe wa juna, duk da cewa sassauci ba abu ne dake da kyau a dukkan lokuta ba na rayuwa ba, to amma mafi kyaun sassauci da yafuwa akan yi shi ne a rayuwa ta aure. Don kuwa, a matsayinku na sabbin amare da angwaye, za su ci daba da fahimtar junanku da kuma dabi'un juna kusan kullum. To lalle kada irin wadannan sabbin abubuwa su kashe muku gwuiwa, don kuwa babu wani mutum a duniyan nan (a halin yanzu) da ya cika goma. Don haka dole ne ku yi hakuri a lokacin da kuka ga wani abin da ya bata muku rai, ko kuma wasu maganganu marasa dadi, don kuwa hakuri da kau da kai su ne kawai maganin wadannan abubuwa.

Wani abin da kuma ya kamata ku sani shi ne cewa mata sun fi maza ruhin hakuri da yafuwa. Mai yiyuwa ne wani ya yi tunanin cewa maza, saboda irin kirar da suke da shi, sun fi mata karfi. Lalle lamarin ba haka yake ba, wannan kawai alama ce ta zahiri. Mai yiyuwa ne a fili su kasance masu karfi (na jiki), to amma idan har ana maganan tausayi da yafuwa ne, to a nan fa mata sun fi maza, don kuwa sun mallaki karfi na hakuri da yafuwa kuma suna da hanyar da suke bi wajen tabbatar da wanzuwar iyali. A lokuta da dama dai mata sun fi maza gane wuraren rauni na abokin zamansu, sun fi sanin bangarorin karfi da rauni na mazajensu, don haka suna da gagarumar dama wajen kyautata yanayin rayuwar aure.

Abu na gaba kuma shi ne batun jin dadi, bukukuwa da sauran kashe kudade na gaira ba dalili (a lokacin aure). A lokuta da dama na sha magana kan kokarin takaita kudin sadaki, to sai dai hakan ba wai yana nufi cewa idan aka ba da sadaki mai yawa aure ya baci ba ne. A'a, abin da dai nake kokarin nunawa shi ne cewa aure dai wata alaka ce ta dan'Adam, wato wani alkawari ne tsakanin rai da zuciya, don haka idan har batun makudan kudade suka shigo cikin to zai tashi daga wannan ma'ana tasa ya koma zuwa ga ma'ana ta kasuwanci, wato saye da sayarwa a kasuwa. Baya ga haka kuma irin wannan yawan sadaki zai kara dora nauyi kan mazaje masu son yin aure. Misali wata mace tana iya cewa ai sadakin da aka ba wa wance kaza ne (kudi mai yawa) don haka ni ma dole ne sadaki na ya kasance kaza wato ya fi na wancen. Don haka ne nake shawartarku da kada ku sanya idanuwanku kan yawan sadaki. Ku yi kokari ku takaita shi daidai gwargwado ka da ku wuce hakan.

Abu na karshe da ya kamata ku sanya cikin zukatanku shi ne batun karfafa juna kan kyawawan dabi'u da kula da hukumce-hukumcen Musulunci. Ku yi kokarin ku ga kun kara karfafa imaninku ta hanyar aurenku da kuma wuraren da kuke, shin ofishi ne ko kuma wajen da kuke aiki, ko wajen wasanni da dai sauransu. Don kuwa ta hanyar dabi'unku za ku iya janyo hankulan wasu zuwa ga addini, ta hakan za ku iya sake rayar da koyarwar Musulunci a zukatan sauran mutane da kuma karfafa su. Ku kula da sallolinku na ranaku a kan lokaci a duk inda kuke. Mai yiyuwa ne wani ya zo ya ce muku kai ku bar sallar ai za ku iya yi daga baya, to lalle (ina shawartarku) da kada ku kula da wannan magana tasa, ku yi kokarin wajen kwadaitar da sauran mutane zuwa ga kula da kiyaye koyarwa ta Musulunci. Babu makawa wadannan abubuwa za su kasance masu amfani ne gare ku da kuma al'ummar da kuke ciki.

Ina fatan wadannan shawarwari nawa za su kasance muku tafarkin samun kyakkyawar rayuwa ta aure.

Wassalamu Alaikum Wa Rahmatullah.




____________
(1)- A kowace shekara musamman a lokacin bukukuwan Eid al-Ghadir ko kuma lokacin haihuwar Manzon Allah (s) Jagoran Juyin Juya Hali Imam Khamene'i ya kan daura wa wasu matasa musamman 'yan jami'a aure. A yayin wannan buki dai kafin ya daura auren ya kan ba su shawarwarin da za su amfane su a rayuwarsu ta auratayya a matsayinsa na Uba kana kuma masani kan wannan lamari. Don haka ne na fassara mana daya daga cikin irin wadannan shawarwari da yake bayarwa a lokacin daurin auren don su kasance mana hannunka mai sanda musamman ma dai ga matasanmu da suke shirin aure.