Fassarar Huduba Ta Biyu Ta Jagoran Juyin Juya Hali
Imam Khamene'i (H)
A Ranar Idin Karamar Salla
A Birnin Tehran (26/11/2003)


Shimfida:A ranar karamar sallan nan da ta wuce ne dai, Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Ayatullah Khamene'i (H) ya jagoranci sallar idi, inda ya gabatar da hudubobi guda biyu na salla. To saboda muhimmancin da huduba ta biyun take da shi ne ya sa na fassara ta. Abin da ke biye fassarar huduba ta biyun ne daga harshen Farisanci zuwa harshen Hausa. A sha karatu lafiya:

Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai

Dukkan godiya ta tabbata ga Allah, tsira da amincin Allah su tabbata ga Shugabanmu kuma Annabinmu Abul Kasim al-Mustafa Muhammad, tare da Aliyu Amirul Muminin da Fatima al-Zahra shugaban matayen talikai da Imam Hasan da Husain da Aliyu bn Husain da Muhammad bn Ali da Ja'afar bn Muhammad da Musa bn Ja'afar da Aliyu bn Musa da Muhammad bn Ali da Aliyu bn Muhammad da Hasan bn Ali da Imam al-Mahdi, hujjojiunKa akan bayinKa, aminci ya tabbata akan Imamai shuwagabanni masu kare raunana masu shiryar da muminai. Ina muku wasicci, Ya ku bayin Allah da tsoron Allah.

Da farko dai abin da na ga ya zama wajibi in yi magana akansa a huduba ta biyu, shi ne cewa a wannan karon ma al'ummarmu a ranar Kudus ta duniya sun sake nuna wa duniya irin karfin da suke da shi. Ranar Kudus dai ba wai kawai rana ce ta al'ummar Iran ba, rana ce ta duniyar musulmi, don haka ne a dukkan kasashen musulmi al'umma suka fito don nuna goyon bayansu ga 'yan'uwansu Palastinawa. A halin da ake ciki dai irada da karfin al'ummar musulmi wajen fuskantar wuce gona da irin Amurka da haramtacciyar kasar Isra'ila akan al'ummar Palastinu marasa kariya da dukkan karfinsu sai dada bayyana yake yi, sai dai a kullum al'ummarmu a sahun gaba suke a wannan bangaren, a wannan shekarar ma dai al'ummar Iran ta tabbatar da wucewarta kan gaba. A wannan shekarar ma dai al'ummarmu a ranar Kudus, take guda suka dinga rerawa wajen nuna goyon baya da kariyarsu ga al'ummar Palastinu raunana marasa kariya kamar yadda takensu guda ne wajen yin Allah wadai da kuma nuna kyamarsu ga Amurka, haramtacciyar kasar Isra'ila da kuma sahyoniyawa, wadanda duk da irin farfagandojinsu na karya kan batun kare hakkokin 'yan'Adam da demokradiyya suke aikata mafi munin ayyukan ta'addanci akan wata al'umma da ake zalunta (Palastinawa). Don haka ina mika sakon godiyata, a matsayina na karamin mai muku hidima, ga dukkan al'ummarmu madaukaka, lalle kun daukaka matsayin Iran, matsayin Jamhuriyar Musulunci a idanuwan al'ummomin duniya. A kowani lokaci kana a kowani guri, al'umma da dukkan karfi da iradarsu sun nuna wa al'umma matsayarsu. Mas'alar Palastinu dai mas'ala ce ta duniyar musulmi ta gaba-gaba, don haka dole ne mu yi dubi da idon basira cikin halin da Palastinawa suke ciki bugu da kari kan 'yan mamaya, azzalumai makiya al'ummar Palastinu.

Babu shakka, al'ummar Palastinu suna cikin mawuyacin hali sanadiyyar zalunci da ruguza gidajensu da ake yi. (yahudawan sahyoniya dai) sun kasance sukan lalata gonaki da lambunan Palastinawa, baya ga haka suna hana matasan (Palastinawa) yin aiki, mazaje kuma a jefa su gidajen yari, a wasu lokuta kuma sukan bude wuta akan al'umma da kuma kashe su kisan kiyashi, ciki kuwa har da jarirai da suke bayan iyayensu. A hakikanin gaskiya irin ayyukan da suke aikatawa kan Palastinawa na zalunci, aiki ne da da wuya ake samun irinsa tsawon tarihi. To sai dai kuma duk da haka wannan al'umma da aka mamaye ta, wannan al'umma da ake zalunta, ta yi tsayin daka da kuma fuskantar 'yan mamayan. Al'ummar Palastinu, da albarkan sunan Musulunci da kuma albarkan tutar Musulunci a Palastinu, sun tsaya da dukkan karfinsu wajen kare kansu da kuma fuskantar 'yan mamaya ma'abuta zalunci ba tare da tsoro ko ja da baya ba. (Takbirin masalllata)

Mu dai muna mika sakon gaisuwa da jinjinawarmu ga al'ummar Palastinu, daga wannan masallaci na Tehran, daga cikin Tehran, kai daga dukkan al'ummar Iran, muna isar da sakon gaisuwa da jinjinawa ga al'ummar Palastinu, ga matasa da samaruka, ga iyayensu da kuma wadannan zukata (nasu) masu imani da jaruntaka. Sun fuskanci makiya da dukkan karfinsu, sun yi tsayin daka da kuma sadaukar da rayuka da masoyansu a wannan tafarki.

Idan muka koma ga 'yan mamaya kuma, sahyoniyawa 'yan fashin kasa da masu goya musu baya wato azzaluman gwamnatin Amurka, (muna iya cewa) idan mutum ya yi dubi da idon basira kan lamarin Palastinu, to lalle zai ga cewa a halin yanzu fa Amurka da sahyoniyawa suna cikin mawuyacin hali a kasar Palastinu, suna cikin halin tsaka mai wuya, babu gaba babu baya, rashin nasara ce take fuskantarsu. Al'ummar Palastinu dai sun farka, sun fahimci cewa babu wani abin da zai tseratar da su daga hannun abokan gaba 'yan mamaya face gwagwarmaya, sun fahimci cewa halartar tarurrukan kasa da kasa kamar yadda 'yan mamaya da masu mara musu baya suke so ba zai fisshe su ba, sun fahimci cewa dole ne su sadaukar da kansu don cimma manufofinsu, dukkan wadannan abubuwa dai Palastinawan sun gansu ne da kuma fuskantarsu, don haka suke ci gaba da gwagwarmaya.

Irin wannan yanayi (gwagwarmaya) dai, idan har ta kasance ta samo asali ne daga mabubbuga ta addini da kuma akida ta tauhidi, wanda alhamdu lillahi haka lamarin yake a halin yanzu a kasar Palastinu, to babu makawa ba za a iya kawar da shi ba. Ina rokon Allah Madaukakin Sarki da Ya gaggauta kusanto da samun nasara ga al'ummar Palastinu.


Ko ina dai a duniyar musulmi aka gudanar da irin wannan zabe (zaben jin ra'ayin mutane kan Amurka), to sakamakon zaben dai shi ne abin da Amurkawan suke tsoro, shi ne kuwa samar da mutumin da zai yi kiyayya da Amurka ta kowani bangare. A ko ina ne cikin duniyar musulmi aka gudanar da irin wannan zabe, wannan dai shi ne sakamakon da za a samu, babu wani bambanci.

Wata matsala kuma da take fuskantar duniya musulmi, ita ce matsalar kasar Iraki. Amurka dai ta hanyar fakewa da demokradiyya, hakkokin bil'Adama ta kutsa kai kasar Iraki, sun shiga Irakin ne da sunan fada da makaman kare dangi, makamai masu guba da dai sauransu, suna cewa mu muna son tabbatar da 'yancin al'ummar Iraki ne, to amma a halin yanzu saboda irin abubuwan da suke yi wa Irakawa, ya sanya Irakawan suka ga ba abin da ya dace in banda su fuskanci Amurkawan da dukkan karfinsu kuma hakan ne ma suke yi. Kasantuwar Amurka a Iraki dai babban cin mutumci ne ga al'ummar Iraki ta yadda koda wasa Irakawa ba za su iya jure masa ba.

Ya kamata dai al'ummar Amurka su san cewa gwamnatinsu ta sanya su ne cikin tsaka mai wuya a kasar Iraki, gwargwadon yadda suka ci gaba da zama a Irakin kuwa gwargwadon irin matsalar da za su ci gaba da fuskanta. Ya kamata a san cewa fa tsaka mai wuyan da Amurka take ciki a Iraki ya kai matsayin da Amurkan tana ruwan bama-bamai daga sansanoninta da suke cikin ruwa, wanda hakan yana nuni da gazawarta wajen gudanar da ayyukanta a Irakin. Matukar dai suka ci gaba da zama to yanayinsu zai ci gaba da lalacewa da shiga halin kunci.

A halin yanzu kuma suna cewa mu muna so ne mu tabbatar da demokraradiyya a yankin Gabas ta Tsakiya, to shakka babu dai wannan karya ce tsagoronta, don kuwa su kansu ba su yi amanna da demokradiyyar ba, su dai sun san cewa da a ce za su binciki ra'ayin al'ummar Iraki, ko shakka babu mafi yawan Irakawan za su zabi wani mutum ne da ba zai bari Amurkawa su ci gaba da zama a Iraki ba ko da kuwa na kwana guda ne. (Takbirin masallata)

Ko ina dai a duniyar musulmi aka gudanar da irin wannan zabe, to sakamakon zaben dai shi ne abin da Amurkawan suke tsoro, shi ne kuwa samar da mutumin da zai yi kiyayya da Amurka ta kowani bangare. A ko ina ne cikin duniyar musulmi aka gudanar da irin wannan zabe, wannan dai shi ne sakamakon da za a samu, babu wani bambanci. A halin yanzu dai abin da wadannan mutane suke gudanarwa shi ne hana al'ummar Iraki zaben abin da ya dace da su, to sai dai ya kamata su san cewa duk wani kundin tsarin mulki da za a tilasta akan mutane, duk wata hukuma da za a tilastawa Irakawa, to lalle za ta fuskanci fushin al'ummar. Ba wai kasafin kudi na dala biliyan dari hudu ba da shugaban Amurka ya ware wa ma'aikatar tsaro, ko da biliyan dubu dari hudu ne aka ware ba zai sa kasashen wannan yanki na Gabas ta Tsakiya da al'ummar musulmi su mika musu wuya ba. (Takbirin masallata)

Gwamnatin Amurka dai duk da da'awar demokradiyya da take yi amma sai ga shi tana aikata nau'oi na ta'addanci daban-daban akan al'ummomin duniya da kuma demokradiyya, wannan gwamnati dai ta Amurka da ranar 28 ga watan Khordad ta kulla makirci ga Iran, ta shirya juyin mulki a kasar Chile akan gwamnatin da al'umma suka zaba, gwamnatin Amurka da ta sha shirya juyin mulki daban-daban akan halaltattun gwamnatoci a Latin Amurka, Afirka da dai sauran kasashe, gwamnatin Amurka da shekara da shekaru take goyon bayan manyan 'yan kama karya irinsu Muhammad Ridha Pahlawi na Iran, gwamnatin Amurkan da ko a yanzu takan amince da kowace gwamnati komai zaluncin da take yi kuwa matukar dai za ta biya musu bukatunsu, to wani mutum ne kuwa zai yarda da wannan gwamnatin. (Takbirin masallata)

Cikin 'yan kwanakin nan shugaban Amurka ya fasa musu kwai, ya bayyana wa duniya irin burin Amurka na girman kai da zalunci da suka jima suna boyewa ba sa so kowa ya sani, yana mai cewa su dai suna so ne su kame wadannan al'ummomi, su tabbatar da haramtattun manufofin Amurka akan manufofin kasashen wannan yankin. To amma ya kamata su gane cewa fa koda wasa wadannan al'ummomi ba za su taba mika musu wuya ba, al'ummar Iran madaukaka, al'ummar Iran ma'abuta jihadi, al'ummar Iran ma'abuta tushe, sun kasance abin koyi na tsayin daka tsakanin al'ummomi.

Al'ummarmu madaukaka, 'yan'uwana maza da mata a duk fadin Iran, kun nuna wa sauran al'ummomi cewa fa ku mutane ne ma'abuta daukaka, gwagwarmaya da kuma imani, kun yi kafar ungulu wa makiyanku wajen cimma burorinsu shekara da shekaru bayan nasarar Juyin Juya Halin Musulunci. Muhimmin abin da ya taimaka muku a wannan bangare kuwa shi ne imani da Allah da kuma hadin kai. Imani da Allah da kuma hadin kai shi ne ya daukaka matsayinku da kuma tsoratar da makiya.

A nan gaba dai muna da zabe a gabanmu, zabe dai na daga cikin hanyoyin da al'umma suke nuna karfinsu, to sai dai fa tun yanzu abokan gaba sun fara farfagan-dojin karya don ganin ba a gudanar da tabbataccen zabe na jama'a ba, wanda da yardar Allah cikin watanni uku zuwa hudu za a gudanar da shi, don haka ya zama wajibi al'umma su kasance cikin shirin ko ta kwana da zama cikin hankalinsu. Akwai maganganu da yawa na fadi dangane da zaben, amma har ya zuwa yanzu akwai lokaci, idan dai har muna raye zan yi karin bayani wa al'umma. To sai dai abin da nake so in jawo hankulan mutane a halin yanzu shi ne cewa lalle ne dukkan al'umma su dauki wannan zabe da muhimmanci, wanda ta hakan za su sami damar karfafa kasa....

A karo na biyu ina sake kira ga 'yan'uwana maza da mata da mu kula da takawa da komawa gaba daya zuwa ga Ubangiji, sannan kuma mu taimaka wa juna da kuma taimako wajen bunkasa kasa. Ina rokon Allah Madaukakin Sarki da Ya taimaka wa al'ummarmu da su sami nasara akan abokan gabansu da kuma samun nasara akan dukkan bangarori.

. . .

Wassalamu Alaikum Wa Rahmatullahi Ta'ala Wa Barakatuhu.