Fassarar Jawabin Jagoran Juyin Juya Hali
Imam Khamene'i (H)
A Yayin Ganawa da Jami'ai A Ranar Idin Karamar Salla
A Birnin Tehran (26/11/2003)


Shimfida:A ranar karamar sallan nan da ta wuce ne dai, Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Ayatullah Khamene'i (H) ya gana da shugaban kasa da manyan jami'an gwamnatin Musulunci ta Iran, a lokacin da suka kai masa ziyarar ban girma da kuma barka da salla. Abin da ke biye fassarar jawabin da Jagoran ya yi wa jami'an ne daga harshen Farisanci zuwa harshen Hausa. A sha karatu lafiya:

Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai

Ina taya dukkan al'ummar musulmin duniya, madaukakan al'ummar Iran da kuma ku mahalarta wannan taro, jami'ai, ma'aikatan gwamnati da kuma baki 'yan kasashe daban-daban na musulmi murnar zagayowar ranar Karamar Salla.

Duk da cewa dai watan Ramalana, mai cike da albarka yana karewa ne da idin karamar salla, sai dai kuma a cikinsa (Ramalana) akwai madaukakan ma'anoni da darussa, wato azumi da tsayin dakan da mutane suka yi wajen fada da shaidan na ciki da na waje, wanda sakamakonsa shi ne idi (ranar farin ciki) da jama'a za su fito don nuna farin cikin da kuma kyautata alakarsu da Ubangiji Madaukakin Sarki. Duk da cewa Musulunci ya kasance yana kiran mutane zuwa ga ibada, gina kai da tsarkakewa, to amma hakan ba wai kawai yana nufin aiki ne na mutum guda wato ko wani mutum ya kyautata alakarsa da Ubangiji ba, face dai ya kamata ya dau wannan alaka, zikiri, kankan da kai, kusanci da a matsayin wata hanyar da zai bi wajen kula da al'amurran duniyarsa da kuma makomarsa. Kamar yadda wasu manyan masana suke cewa hadin kai da kalma guda wajibi ne wajen tabbatar da sa'ada da ci gaban al'ummar musulmi, hakan nan ma idin karamar salla, salla da kuma munajatinmu a wannan rana ma alama ce ta hadin kai da kalma guda; don kuwa hakan (gina) ruhi ne na imani, kaskantar da kai da kuma neman taimakon Allah, kamar yadda kuma karfafa zuciya ne ta hanyar imani da Allah da kuma samar da yanayi na sakina da kwanciyar hankali na rayuwa daban-daban. Ala kulli halin, idin karamar salla dai hada karfi da karfe ne na dukkan karfin da ake da shi waje guda don cimma manufofi na rayuwa. Don haka ne a yau din nan al'ummarmu da sauran al'ummomin kasashen musulmi suke da bukatuwa da wannan rukuni mai girma na Musulunci iyakacin bukata.

Hakika Juyin Juya Halin Musulunci ya mayar da zukatan al'umma zuwa ga Allah Madaukakin Sarki, kamar yadda kuma ya sanya su suka shiga fagen daga na kokari da gwagwarmaya wajen neman rayuwa mai kyau, sakamakon hakan ne ya sa al'ummar Iran suka kama tafarkin nasara kuma da iko da karfin Allah suka cimma wannan tafarki na ci gaba, don haka dole ne a kiyaye wannan tafarki da ya kasance tafarki ne na samun kusanci da Ubangiji da kuma kokari wajen samar da makoma mai kyau. Ku sani fa hadin kai da kalma guda dama ce ta nasara, don haka dole ne ku kiyaye wannan alama.

A wannan da'ira mai girma, alamar nasarar al'ummar musulmi dai ita ce hadin kai. Matukar dai al'ummar musulmi suna son ci gaba da nasara a fagen ilmi, ci gaban abin duniya, iko kan makoma, 'yantar da kai daga mulkin mallakan bakin haure da kuma sa'adar ciki da waje, to hanyar dai guda ce kawai, ita ce kuwa hadin kai da zance guda. A halin da ake ciki manyan kasashen duniya da cibiyoyin girman kai, wadanda suke amfani da dukkan karfinsu wajen tabbatar da mulkinsu, suna ba da kokari wajen ganin sun haifar da rikici, rarraba da rashin hadin kai tsakanin kasashen musulmi, to sai dai kuma abin bakin ciki shi ne cewa ya zuwa wani haddi dai sun ci nasara. (Ku duba ku gani) dukkan irin mummunan halin da al'umma Palastinu suke ciki a halin yanzu, haka nan idan har a yau jikkunan Palastinawa cike suke da jinni da ke sosa ran duk wani dan'Adam, to lalle dukkan wadannan abubuwa sun faru ne saboda rarrabuwa da rashin hadin kan musulmi, don kuwa da ce kan musulmi a hade suke to da hakan bai faru ba.

Idan har kasar Iraki tana karkashin mamayan 'yan mamaya, to hakan ya faru ne saboda rashin kalma guda. Haka nan idan har a yau Amurka da dukkan girman kanta tana barazana ga kasashen yankin Gabas ta Tsakiya, to dalilin dai shi ne rashin hadin kan musulmi. A hakikanin gaskiya, matukar dai al'ummar musulmi suna son fita daga wannan tsaka mai wuya, haka nan matukar suna son 'yantar da Palastinu, matukar suna son hana abokan gaba matsawa al'umma Afghanistan, Iraki da sauran kasashen musulmi lamba, to fa hanyar haka guda ce ita ce hadin kai tsakanin al'umma. Babu shakka ranar idi dai rana ce ta hadin kan al'umma.

To sai dai kuma abin bakin cikin shi ne cewa, a duniyar musulmi akwai wadansu mutanen da don samun kusanci da Amurka da sauran cibiyoyin girman kai, a shirye suke su aikata duk wani abin da ya saba da kuma haifar da rikici tsakanin 'yan shi'a da 'yan sunna. A halin da ake ciki, ina ganin hannayen wasu daga cikin kasashen makwabtarnmu da da gangan suke kokarin haifar da sabani tsakanin 'yan shi'a da sunna da haifar da rikicin siyasa don su sami cimma haramtattun manufofinsu a kasashen musulmmi. Don haka dole ne mu yi hankali. Dole ne al'umma, gwamnatoci, dukkan musulmi, kungiyoyin siyasa da masana su yi hankali daga wannan makirci na makiya, ka da su bari makiya su yi nasara a wannan kokari na su na haifar da sabani. Irin wannan aike ne suke son aikatawa a kasar Iraki.


Idan har kasar Iraki tana karkashin mamayan 'yan mamaya, to hakan ya faru ne saboda rashin kalma guda. Haka nan idan har a yau Amurka da dukkan girman kanta tana barazana ga kasashen yankin Gabas ta Tsakiya, to dalilin dai shi ne rashin hadin kan musulmi. A hakikanin gaskiya, matukar dai al'ummar musulmi suna son fita daga wannan tsaka mai wuya, haka nan matukar suna son 'yantar da Palastinu, matukar suna son hana abokan gaba matsawa al'umma Afghanistan, Iraki da sauran kasashen musulmi lamba, to fa hanyar haka guda ce ita ce hadin kai tsakanin al'umma.

A yau din nan, halin da al'ummar kasar Iraki suke ciki lamari mai dacin gaske ga duniyar musulmi. Kasar Iraki dai kasa ce hadaddiya da ma'abuta girman kai suka yi kokarin rarrabawa kuma suke kai, don kuwa sun san cewa hakan ba aiki ne na lokaci guda ba, don haka ne suke yinsa a hankali a hankali. Don haka dole ne al'umma, al'ummar musulmi da gwamnatocin kasashen musulmi su yi hankali. Kokarin raba kasar Iraki, lamari ne mai tsananin hatsari ga ita kanta Irakin da kuma kasashen wannan yanki. Kasar Iraki dai ta Irakawa ce; don haka ne dole ne kasar ta kasance a hannunsu, su ne kuma ya zama wajibi su rubuta dokokin kasar. Babu shakka duk wata dokar da aka rubuta a Washington to babu wani amfanin da za ta yi wa al'ummar Iraki, ya kamata 'yan mamaya su san cewa idan har suka aikata hakan, wato suka ki mika al'amurra ga hannunsu, to fa ba za su iya kwace wuyansu daga hannayen Irakawa ba, kuma Irakawan ba za su taba mika musu kai ba.

'Yan mamayan Iraki dai suna so ne su maida Iraki kamar Palastinu. A halin yanzu dai yahudawan sahyoniya da Amurka suna cikin tsaka mai wuya a Palastinu, da babu abin da zai fitar da su daga ciki face su mika kai ga bukatan al'ummar Palastinu. Gaskiya ce cewar al'ummar Palastinu al'umma ce da ake zalunta, to amma fa jarumai ne don hakan ba laifi ba ne idan muka kira su da 'Jaruman Al'ummar Palastinu' (kowa dai yana gani) yadda suka yi tsayin daka hannu rabbana amma duk da haka ma'abuta karfin duniya sun gaza aikata komai a kansu duk kuwa da cewa ba sa jin kunyan amfani da duk wani makami da kashe al'umma. Ya kamata 'yan mamayan Iraki su san cewa matukar suna son aikata abin da yahudawan sahyoniya suke aikatawa a Palastinu, to su san cewa al'umma da dukkan karfinsu za su fito filin daga, don kuwa al'ummar musulmi a farke suke.

Al'ummarmu dai cikin shekaru ashirin da biyar din nan (na nasarar Juyin Juya Halin Musulunci) sun nuna wa al'ummar duniya cewa suna tare da Juyin Juya Halin Musulunci, tsarin Musulunci da kuma jami'ansu, kamar yadda suke riko da 'yancin da suka samo. (Ya kamata a fahimci cewa) ba mu samu wannan 'yanci cikin ruwan sanyi ba; ba mu samu wannan demokradiyya ta Musulunci cikin sauki ba; al'ummarmu dai sun yi tsayin daka da kokari, mun ba da rayukanmu ne da muke so; shin cikin sauki da ruwan sanyi za mu iya mika wannan ('yanci) na mu?

A hakikanin gaskiya dai abin da muka dogara da shi wajen fuskantar makirce-makircen makiya, shi ne imani da Allah da dogaro da alkawarin Ubangiji Madaukakin Sarki. Wannan alkawari na Ubangiji kuwa shi ne: ولينصرن الله من ينصره (Hakika Allah zai taimaki wanda ya taimake Shi), wato wadannan mutanen da suke taimakon addinin Allah, wadannan mutane da bisa umarnin Allah suke tura dukkan karfinsu wajen kyautatawa da neman tsira, to Allah Madaukakin Sarki ba zai taba barin wadannan mutane haka kawai ba, lalle zai taimaka musu da kuma ba su nasara, kuma lalle mu mun ga hakan.

Ina rokon Allah Madaukakin Sarki da ya daukaka al'ummarmu da dukkan al'ummar musulmi saboda albarkar wannan ranar ta Idi da kuma watan Ramalana mai albarka, kuma Ya taimaka musu akan abokan gabansu.

Wassalamu Alaikum Wa Rahmatullahi Ta'ala Wa Barakatuhu.