Fassarar Jawabin Jagoran Juyin Juya Hali Imam Khamene'i
Kan Yarjejeniyar Iran da Turai Kan Batun Makamashin Nukiliya Na Iran
A Yayin Ganawa da Manyan Jami'an Gwamnatin Musulunci

A Birnin Tehran (02/11/2003)


Shimfida:A ranar 2 ga watan Nuwamba 2003 ne Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Ayatullah al-Uzma Sayyid Ali Khamene'i (H) ya gana da manyan jami'an gwamnatin Jamhuriyar Musulunci ta Iran don tattaunawa kan mas'aloli daban-daban da suka shafi al'amurran mulki musamman ma dai batun nan sanya hannu kan sabuwar yarjejeniya kan batun makamashin nukiliyya na Iran da aka yi kwanakin baya. A yayin wannan ganawa dai Jagoran ya yi karin bayani kan wannan lamari da kuma yadda yake ganinsa. Abin da ke biye fassara ce ta wani sashi na jawabin Jagoran da ya tabo wannan batu na makamashin nukiliyya:

Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai

......Dole ne mu aiwatar da takawa da tsoron Allah cikin dukkanin rayuwarmu. Hakika daya daga cikin hanyoyin da mu, jami'an gwamnati, za mu nuna da kuma aiwatar da takawa kuwa ita ce ta hanyar kula da iyakoki na shari'a a dukkan bangarori, dole ne mu guji saba wa doka da oda, don kuwa dokokinmu na kasa sun shata mana ayyukan da za mu aikata, don haka ba ya halatta wani ya saba wa wadannan dokoki. Saba wa wadannan dokoki shi ne ya ke kawo lalacewa, lalle kauce wa tafarki shi ne yake kawo hakan.

Har ila yau kuma wannan abu zai haifar da sabani da rashin jituwa tsakanin bangarorin gwamnati daban-daban, ya kan haifar da kace-nace maras amfani da zai haifar da lalacewa. Wannan dai na daga cikin abubuwan da ya zama wajibi mu kula da su a lokacin da muke magana kan tsoron Allah.

Akwai wani abu guda ko kuma wasu abubuwa guda biyu da nake son yin magana akansu (kafin in kawo karshen jawabina). Daya daga cikinsu kuwa shi ne abin da shugaban kasarmu mai girma Malam Khatami ya yi karin bayani akansa mai zurfi tun da farko (wato batun shirin makamashin nukiliyya na Iran da kuma yarjejeniyar da aka cimma da wasu kasashen Turai). Da farko dai ina so in ce wannan lamari dai a wannan kasa tamu, bai kamata ta kowani bangare, ya zamanto wani abin da zai haifar da rikici da sabani ba tsakanin jami'an gwamnati, al'umma da sauran kungiyoyi da jam'iyyu ba. Dole a guje wa hakan.

Kamar yadda shugaban kasa ya fada ne cewa babu laifi cikin fadin ra'ayi da kuma nuna rashin amincewa da wani abu, lalle abin da ya fadi gaskiya ne, babu laifin cikin hakan. Hakika irin damuwa da rashin jin dadin da wasu dalibai, al'umman gari da wasu 'yan jarida suka nuna kan wannan batu, abu ne mai kyau. Hakan yana nuni ne da cewa al'umma tana damuwa da mutumcin kasa da kuma 'yancinta ne. To sai dai hakan bai isa ya kai ga tashin hankali da daga jijiyoyin wuya ba, wannan lamari ne dake da muhimmanci a fahimce shi.

Manyan gari, jami'ai, musamman ma masu fadi a ji, 'yan majalisa ne, 'yan jarida ne ko kuma limaman juma'a da dai sauransu, duk sun taka gagarumar rawa wajen wannan lamari. Dole ne fa su san cewa a duk lokacin da kasa take fuskantar wani lamari, wanda yake kama da sauran lamurra da kasa take fuskanta, to babu abin da zai kasance mai cutarwa kamar wannan lamari ya kasance ummul aba'isin din rikici da ka-ce-na-ce tsakanin al'umma a cikin kasa. Wannan abu ne mai muni.

A farko-farkon kallafaffen yaki na kariyar kai mai tsarki (yakin da Iraki ta kallafa wa Iran na shekaru takwas), dukkan nauyin da suka hau kan kowa a fili suke kuma abin da ya kamata kowa ya aikata a fili yake. Munafukai ('yan kungiyar Mujahedin-e Khalk Organisation MKO) a lokacin sun kasance suna cikin karfinsu a birnin Tehran da sauran garuruwa, kamar yadda kuma suka kasance suna gudanar da tarurrukansu da jawabansu ba tare da tsangwama ba, amma duk da haka suna cewa an hana su 'yanci. Sun ci gaba da bayyanar da cewa ba su da 'yanci. A halin yanzu ma abin da yake gudana kenan. Akwai wasu mutane da suke fadin dukkan abin da suke son fadi da kuma aikata dukkan abin da suke son aikatawa, amma daya daga cikin taken da suke ta kan rerawa da nanatawa shi ne mu ba mu da 'yanci, an hana mu 'yanci. Sai dai ba su san cewa wannan abin da suke fadin zai sanya mutane su yi musu dariya da nuna su da yatsa ba. To irin haka ne dai ya faru a baya. Sun kasance a koda yaushe suna magana kan 'yanci!, 'yanci! 'yanci!. Sun kasance sukan tsaya a kan tituna suna rike da kwalaye, suna kokarin sanya shakku cikin zukatan al'umma kan asalin jigon wannan kariya ta kai (daga hare-haren abokan gaba).


(Ina so in sanar da ku cewa) babu wata yarjejeniya da aka cimma a wannan bangare don yi watsi da wannan abin da aka cimman, lalle mun kasance cikin kula da sanya ido kuma hakan ba zai taba faruwa ba ko da a nan gaba ne. Sanannen abu ne cewa matukar dai mutanen da suke tattaunawa da jami'an gwamnatinmu, suka ci gaba da neman karin bukatu da kuma dagewa kansu, to lalle babu makawa za a dakatar da duk wata tattaunawa da ake yi da su kuma ba za a biya musu bukatan ba.

A takaice dai abin da yake faruwa shi ne cewa yahudawan sahyoniya da jami'an gwamnatin Amurka masu ci yanzu, wadanda gaba da kiyayya da suke yi da Iran, Iraniyawa da kuma gwamnatin Musulunci ba ta da iyaka, a shirye suke su bi ta kowace hanya wajen ganin sun cimma bakar aniya da manufarsu. Wannan dai shi ne asalin yanayin jami'an gwamnatin Amurka na yanzu. Yahudawan sahyoniya wadanda suke zaune a Amurkan da kuma sauran yahudawan sahyoniyan da suka mamaye kasar Palastinu duk daya suke. Sun kirkiro wani take da suke rerawa a duniya, suna cewa wai Iran kokari take ta mallaki makaman kare dangi. Sun fara kokarin sayen hankula da tunanin al'umman duniya kai har ma da na wasu gwamnatoci.

A halin da ake ciki har ma sun kusan su cimma samun hadin kan kasashen duniya wajen cutar da gwamnatin Musulunci kan wannan batu na mallakan makaman kare dangi, wanda daman hakan shi ne buri da kuma manufarsu. Wannan shi ne abin da al'ummomin duniya suke jin tsoronsa, sun kusan cimma nasara kan hakan. Suna cewa irin karfin ilmi a bangaren ilimin kimiyya da makamashi da Iran take da shi duk hanya ce ta isa ga wannan manufa (ta kera makaman kare dangi). To anan abin tambaya shi ne me ya kamata mutum ya yi a irin wannan yanayi? Shin zai bar Amurka da yahudawan sahyoniya su kaddamar da farfagandan karya da kuma ci gaba da fadin wadannan maganganu ne? ko kuma a 'a mutum kamata ya yi ya fito fili ya yi bayani wa duniya da kuma fadin matsayarsa da nuna musu cewa lalle fa lamarin ba haka yake ba?

Don haka Jamhuriyar Musulunci da kuma madaukakan jami'anta suka yanke shawarar daukan mataki na yin bayani wa duniya da kuma barinsu su gane wa idanuwansu gaskiyar abin da ke gudana. Suna so ne su bayyana wa duniya cewa fa lamarin lalle ba haka yake ba, ku zo ku gane wa idanuwanku abubuwan da suke gudana don ku tabbatar. Wannan fa shi ne abin da ya faru. Ya zuwa yanzu fa wannan shi ne abin da jamhuriyar Musulunci ta dauka kuma ta yadda da shi. Ku zo da kanku ku gani, ku zo ku gani da idanuwanku kan yadda ake tace sinadarin (uranium) din. Sun zo kuma sun gane wa idanuwansu abubuwan da ke gudana da kansu. An ce musu su zo su ga duk inda suke tsammanin ana gudanar da irin wannan aiki don gane wa idanuwansu, don su tabbatar da farfagandar yahudawan sahyoniya ba komai ba ce face karya da zuki ta malle.

Hakika wannan dai ita ce hanya mafi sauki ta ruwan sanyi ta kare irin ilmi kimiyya da kuma nasarar da muka cimma, wannan kuwa ya biyo bayan cewa ba wani daga cikinmu da yake da hakkin yin watsi da wannan gagarumar nasara mai tsada da muka cimma ne ko mai za a bayar kuwa. Babu wani wanda yake da hakkin yin watsi da shi. Akwai wasu mutane da suke yada nasu farfagandan suna cewa wai, hakika babu wani abin a zo a gani da aka cimma. Lalle wannan ba gaskiya ba ne, dole ku san hakan. Hakika abin da aka cimma lalle yana da yawan gaske da kuma kima, an cimma abubuwa masu yawan gaske, idan kuwa da ba shi da yawa to lalle da abokan gabanmu ba su damu haka ba, don haka abin da aka cimma yana da yawa. Masana, kwararru da kuma wadanda suke bin lamurra sun cinka daidai, don kuwa mun cimma da kuma isa ga ilmi mai yawa a bangaren ilmin kimiyya, al'ummarmu ta samu wannan ilmi har ma ya zamanto kayanta, wannan kuwa shi ne ya ke da muhimmanci.

A halin da ake ciki, ko da abokan gabanmu za su samu damar lalata shi, to lalle ba za su iya ba. Ko da za su lalata dukkan cibiyoyin wannan ilmi da suke jamhuriyar Musulunci, to fa duk da haka ba za su iya lalata ilmin ba, don kuwa yana nan, don mun riga da mun mallaki ilmin ne da kanmu ba wai mun aro shi ne daga wajen wani ba, ba mun karbi bashinsa ne daga wajen wani ba. A'a masananmu ne suka ba da himmarsu suka aikata hakan, lalle sun cimma wannan manufar.

Babu shakka idan da a ce abin a hannun kasashen yammaci da wadannan helkwatoci na karfin duniya ne, to ba su so kuma da ba su bar jamhuriyar Musulunci ta cimma wannan nasara ba nan ma da shekaru dari masu zuwa ba. To amma ina hakan dai ya faru duk da kokarin da suka yi na hana faruwarsa na daga takunkumi da dai sauransu, to amma duk hakan dai sun gagara. Don haka abin da aka cimma dai yana da kima da girman gaske. A hakikanin gaskiya da gwamnati, jami'ai da hukumar makamashi ta kasa babu wani guda a cikin wannan kasa da yake da hakkin ya bari wannan babban abu ya kubuce ko kuma ya cimma yarjejeniya don lalata shi. (Ina so in sanar da ku cewa) babu wata yarjejeniya da aka cimma a wannan bangare don yi watsi da wannan abin da aka cimman, lalle mun kasance cikin kula da sanya ido kuma hakan ba zai taba faruwa ba ko da a nan gaba ne. Sanannen abu ne cewa matukar dai mutanen da suke tattaunawa da jami'an gwamnatinmu, suka ci gaba da neman karin bukatu da kuma dagewa kansu, to lalle babu makawa za a dakatar da duk wata tattaunawa da ake yi da su kuma ba za a biya musu bukatan ba. (jami'ai suka yi: Kabbara, Allahu Akbar)

Ina nufin, matukar dai wani mutum ya so ya wuce gona da iri kan jamhuriyar Musulunci kan wannan batu, to babu makawa jamhuriyar Musulunci za ta wurge su da abin da suke so a bakunansu. Shakka babu jamhuriyar Musulunci ba ta kuma ba za ta taba mika wuya kan wannan batu ba. Wannan dai lamari ne da kowa ya kamata ya mai da hankali kansa ya kuma fahimce shi. Dole ne mu kiyaye ci gaban da muka samu a wannan bangare na ilmi.

Wannan dai ba shi ne kawai ilmin da muke da shi ba, alhamdu lillah, muna iya ganin ci gaban ilmin kimiyya da fasaha da aka samu a dukkan bangarori a wannan kasa tamu, akwai gagarumin ci gaba da aka samu a bangarori daban-daban, duk da cewa har ya zuwa yanzu akwai dai tafiya mai nisa dake jiranmu kafin mu kai ga koluluwar wannan ilmi, hakan ya faru ne saboda mun fara ne tun daga kasa da sufuli, mutum ma dai ba zai ce wai daga sufuli ba.

Makiya dai sun aikata munanan abubuwa ga wannan kasa da nufin toshe ci gaban ilmin kimiyya da fasaha na wannan kasa, suna so ne su tabbatar da cewa al'umma sun fitar da burinsu kan wannan ilmi, hakan kuwa shi ne mataki na kasa da sufuli. Lalle ba mu fara da komai ba. Mun fara ne daga babu ga kuma rashin fatan cimma wani abin a zo a gani. Ta haka ne juyin juya halin Musulunci ya shigo fage. Amma, alhamdu lillahi, jamhuriyar Musulunci a yau ta ci gaba sosai, matasanmu suna da jini a jika kuma suna amfani da karfin da suke da shi, ta yadda ana iya kwatanta daga cikin manyan jami'oi 20 zuwa 30 namu da manyan jami'oin sauran kasashen duniya da suka ci gaba, ina nufin a bangaren irin ayyukan da ake gudanarwa da kuma irin kokari da kwakwalwar daliban da suke karatu a jami'oin. Alhamdu lillah, an cimma gagaruman nasarori.

Abin da dai ya faru shi ne abin da na gaya muku yanzu-yanzun nan. Wato wani mataki mai cike da hikima amma ba tare da mika wuya ba, ba tare da yarda da nuna fin karfi ba, don ruguza makircin Amurkawa da yahudawan sahyoniya akan jamhuriyar Musulunci. Wannan dai shi ne abin da wadannan jami'ai suka yi, kuma wannan abu da suka yi shi ne abin da ya dace a yi shi, duk da cewa dai hakan dai shi ne mataki na farko, don kowa ma ya sani. Ba wai an kawo karshen abin ba ne. matukar dai lamarin ya ci gaba kamar yadda aka faro to babu wata matsala dangane da hakan. To sai dai kuma a bangare guda matukar abokan gaban da kuma sauran ma'abuta karfin duniya suka so wuce gona da iri, suka ci gaba da kutsawa gaba dai gaba dai, to lalle hakan ba abu ne da za a amince da shi ba, don haka zai kasance tamkar mika wuya ne. To wannan ba abu ne da ya dace ba ta kowace hanya, kuma ba za amince da shi ba, kuma ba za a bar shi ya ci gaba ba.

Wani tunanin kuma shi ne a yi tunanin cewa - jaruman al'ummarmu za su yi tunanin - cewa, lalle gwamnati ta mika kai. Lalle lamarin ba haka ya ke ba, babu wani mika kai da aka yi, don kuwa wannan wata harka ce kawai ta siyasa, aiki ne na diplomasiyya, tattaunawa da kuma yarjejeniya. Babu wani mika wuya cikin hakan, ya zuwa yanzu.

A bangare guda kuma, wasu mutane za su yi tunanin cewa: Kai malamai ku dai kada ku bata lokaci, ku ba su dukkan abin da suke so. Kada ku ba su wani fage na samun damar cimma manufofinsu, ka da ku ba da fagen kaza da kaza. To wannan ma dai kuskure ne, wannan shi ne tsoro.

Wasu makiyan Jamhuriyar Musulunci a waje suna tunanin cewa a halin yanzu fa jamhuriyar Musulunci ta hadiyi kugiya kuma kugiyar ta kame mata makogwaro, to lalle wannan din ma dai wauta ne kuma babu gaskiya cikinsa.

To koma dai mene ne, dukkan matakin da muka dauka, to fa a duk lokacin da muka ga hakan zai cutar da ka'idoji na addini da kuma jamhuriyar Musulunci, to babu makawa za mu dakatar da wannan lamari a daidai wannan lokaci. (mahalarta suka ta rera taken 'Allahu Akbar').

Don haka, za mu dau tafarki da matakai na zaman lafiya wajen kare wannan ci gaba da kuma kasa baki daya. To sai dai duk da haka akwai wuraren da ba za mu bari a tsallake ba, su ne kuwa: matukar bakin haure ('yan kasashen waje) suka kuduri aniyar tsoma baki cikin harkokinmu na cikin gida, to za mu bugi bakunansu. Idan kuma suna kara yawan bukatunsu da kuma son dankara mana wasu ka'idoji, to ba zamu yarda da hakan ba. Idan dai cewa suka yi suna son su sami nitsuwa da tabbaci ne, to mu ba za mu hana su ba, za su iya samun nitsuwa ta hanyar yin abin da suke yi.

Wannan dai zai ci gaba da faruwa daga yanzu har zuwa nan gaba. Babu shakka, kamar yadda doka ta tanada, matsaya ta karshe tana hannun majalisa ne. Ya zuwa yanzu dai gwamnati ba ta tsaida matsaya ba, wannan dai wani share fage ne da jami'ai suka yi, don kuwa bisa doka matakan karshe kan duk wata yarjejeniya tana hannun majalisa ne, babu wani wanda ya isa ya keta wannan tafarki. Daga baya kuma sai majalisar kare tsarin mulkin Musulunci su duba su ga da kuma tabbatar da cewa abin da aka cimma din bai saba wa shari'a ba.

Abin da dai jami'ai da dan'uwanmu mai daraja Dr. Ruhani (babban sakataren majalisar koli ta tsaron kasa kana kuma babban mai tattaunawa da kasashen Turai kan wannan batu na makamashin nukiliya na Iran) da abokansa, shugaban kasa da jami'an gwamnati suka aikata sun cimma su ta hanyar da ba ta saba wa ka'idojin (juyin juya hali) ba. Ina sane da abubuwan da suke faruwa, ina kuma sa idanuwa kan lamurra don ganin ba a kauce wa tafarki ba, don kuwa a duk lokacin da na ga cewa an yi wani abin da ya saba wa ka'ida, ya saba wa manufofi, mutumcin kasa da tsarin Musulunci, to ba makawa zan dakatar da shi. Har ya zuwa yanzu dai hakan bai faru ba, ina kuma fata za a ci gaba da hakan.

Abin da yake da muhimmanci, kan wannan lamari da ma sauran lamurra shi ne cewa 'yan kasashen waje su fahimci cewa jamhuriyar Musulunci fa ba wuri ne da za su iya yin abin da suke so su kwana lafiya ba kamar yadda da suke yi a lokacin mulkin mallaka. A halin yanzu dai lamarin ba haka yake ba kuma ya kamata kowa ya fahimci haka. A halin da ake ciki Iran ta mallaki makamin da yafi na kare dangi, wannan kuwa shi ne makamin karfin al'umma da imani. Lalle muna da wannan karfin.

Hakika dai, suna kokarin su sanya mu mu ji cewa ba mu da wannan karfi (na al'umma da imani), sannan kuma al'umma sun kosa da addinin Musulunci, juyin juya hali da kuma tsarin siyasa (na Musulunci). Abin da suke so su ce kenan, to sai dai lalle hakan ba gaskiya ba ne, dukkanmu mun riga da mun san hakan. A yau dai jamhuriyar Musulunci tana da wannan makami mai karfin gaske, karfin imanin al'umma da kuma mubaya'arsu ga gwamnati da kuma jamhuriyar Musulunci.

A wasu lokuta turawa suna da tunani na mulkin mallaka a zukatansu, tun daga shekarun da suka gabata, to sai dai yana da kyau su fahimci cewa jamhuriyar Musulunci ba za ta taba amincewa da amfani da karfi da tilasci da kuma tsoma baki cikin harkoki da wasa da yarjejeniyar da aka cimma ba.....

Al'umma dai suna tare da Jamhuriyar Musulunci da kuma goyon bayanta, kuma su ne sojojinta, ya kamata wadannan mutane su fahimci hakan. Mutane dai suna son Musulunci da kuma 'yancinsu, kuma a shirye suke su kare su. To sai dai kuma duk da haka akwai wasu mutane da siyasa ta yi jifa da su, wadanda Imam (Khumaini) da kuma Juyin Juya Hali suka yi watsi da su da kuma mai she su saniyar ware, wadannan mutane dai a ko da yaushe suna farin ciki da duk wani sharri da zai faru ga Jamhuriyar Musulunci. Sukan nuna farin cikinsu kan hakan. Sun kasance masu cin gata da kuma amfanuwa da Jamhuriyar Musulunci, Juyin Juya Hali da kuma al'ummar musulmi, Jamhuriyar Musulunci ta ba su 'yanci da dama, to sai dai kuma sun ki su nuna godiyarsu ga Imam, Juyin Juya Halin da kuma al'umma. Su dai sun kasance ma'abuta butulci.

Sun kasance masu bijirewa duk kuwa da abubuwan da aka musu. A halin yanzu ba abin da suke yi in banda kulla kulle-kulle wajen ganin Amurka ta yi barazana wa Iran. A duk lokacin da suka ga Amurka tana barazana ga Iran, su kan yi farin ciki. A duk lokacin da Amurka da yahudawan sahyoniya suka ga wata gazawa, sukan yi farin ciki, kai tun ma kafin hakan ya tabbata. A matsayin misali, a halin yanzu ana tayar da batun hakkokin bil'Adama don sukan Jamhuriyar Musulunci gobe, hakan ya kan sa su yi farin ciki. To sai dai bai kamata su yi farin ciki da yaudarar 'yan siyasa ba musamman na Turai. Su dai ba komai ba ne kuma ba kowa ba ne. lalatattu ne kuma mujirimai a idon Jamhuriyar Musulunci. Mutane ne da suka juya wa al'umma baya, don haka al'umma ma suka juya musu baya, mutane koda wasa ba sa yarda da su.

Ko shakka babu, Jamhuriyar Musulunci ba ta bukatuwa da su, matukar dai suka ci gaba da mujirimancinsu, su kasance a can, wannan dai sabanin abin da suke fadi ne a yayin farfagandojinsu. Suna cewa wai ana adawa da su ne saboda yanayin ra'ayi da tunaninsu da ya saba. Sun kirkiri wata matsaya mai mutumci ga kawukansu, wato wadanda suke tunani da kuma ra'ayi na daban. Wata rana na taba cewa a ma kira su mutane masu ra'ayi na daban kuskure ne. To a cikin al'ummarmu dai, akwai mutane da dama da suke da ra'ayi na daban. Yin tunani da gina ra'ayi na daban ba yana mai da mutane abokan gabanmu ba ne.

Jamhuriyar Musulunci dai ba ta taba yakan mutanen da suke da ra'ayin da ya saba mata ba. Yanzu ga ku nan kuna zaune a nan, akwai 'yan'uwa wadanda ma ba shi'a ba ne kai akwai ma wadanda ba musulmi ba ne. Riko da ra'ayin da ya saba ba yana nufin su zama abokan gaba ba ne. Dukkansu al'umma ne na kasar Musulunci, kuma dukkansu suna aiki ne don kasar Musulunci. Abin da dai yake zama abin ki shi ne gaba da kuma munanan ayyuka. Wannan dai shi ne abin da Jamhuriyar Musulunci take yaka, to sai dai babu makawa, duk wanda yake da mugun nufi ko kuma miyagun halaye, to fa Jamhuriyar Musulunci ba za ta yi la'akari da wani ba wajen yakansa, kuma ba za ta taba yin kasa a gwuiwa ba. (mahalarta suka daga murya Allahu Akbar).


To koma dai mene ne, dukkan matakin da muka dauka, to fa a duk lokacin da muka ga hakan zai cutar da ka'idoji na addini da kuma jamhuriyar Musulunci, to babu makawa za mu dakatar da wannan lamari a daidai wannan lokaci.

Daya daga cikin abubuwan da aka fadi cikin yarjejeniyar da aka cimma, za mu fade su ne don abokanmu su sani. Suna cewa ba su da wata adawa da kasantuwan makamashin nukiliya a Iran, Iran tana iya mallakan makamashin nukiliyya don amfani a tafarki na zaman lafiya, za mu zo mu gina muku cibiyar ma da kanmu da kuma baku man da ake bukata, (wadannan dai na daga cikin abubuwan da suke fadi). Wadansu daga cikin wadannan mutane sun fadi hakan, turawa ma da sauransu sun fadi hakan. A'a wannan dai ba abin yarda ba ne a gare mu, abin da 'yan yammanci da turawa suke son ginawa ba abu ne mai kyau ba ga Iran. Hakan na nufin su mai da Iran da iraniyawa bayi, don kuwa kawo man nasu zai ta'allaka ne da cika musu wasu darurrukan sharudda da bukatu. Kai wata rana na taba fadin haka kan batun mai.

Idan da a ce man fetur din da yake hannun kasashen da suke da shi yana hannun turawa ne sannan kuma ku mutanen Iran da sauran kasashe masu arzikin man fetur za ku saya ne daga wajensu, to lalle da sai kun ba da rayukanku kafin su ba ku kofi guda na man fetur. Ina nufin kafin su ba ku kowani kofi guda na mai. To amma a halin yanzu suna diban miliyoyin ganguna na man fetur cikin sauki da araha da kudaden da ba su taka kara sun karya ba, kai kamar ma dai kyauta suke diba. Wannan dai shi ne abin da za su yi, za su tilasta muku, ku ba da rayukanku don kawai kofi guda na mai, matukar suna da shi.

To a halin yanzu, suna so ne su zo nan su gina mana cibiyar makamashi da kuma ba mu mai suna cewa, za mu baku mai matukar dai kuka cika wadannan sharudda. Suna cewa me ya sa kuka ce haka? Me ya sa kuka fadi wannan kuka ce wancan? To ba za mu ba ku ba. Me ya sa ba za a ce haka ko haka ba? To lalle ba za mu ba ku ba. (To su san cewa) Jamhuriyar Musulunci ba za ta taba amincewa da haka ba. An riga da an gina cibiyarmu ta makamashi, lalle a da muna da kwangila, amma yanzu an gama, mu ne muke samar da mai ga injunan da suke aiki, wannan dai abu ne da dokokin kasa da kasa suka yarda da shi. Wannan dai shi ne abin da ake yi a kasar nan dangane da batun makamashin nukiliyya.

Wannan dai lamari ne mai muhimmancin gaske…..wannan dai shi ne abin da Jamhuriyar Musulunci take jaddadawa akansa. Wadansu dai suna cewa za su gina mana cibiya, to amma Jamhuriyar Musulunci ba ta bukatuwa da hakan....

Wassalamu Alaikum Wa Rahmatullahi Ta'ala wa Barakatuhu.