Imam Khamene'i: Matukar Aka Kai Wa Iran Hari Zan Sanya Kakin Soji In Fito

 

 

 
Imam Khamene'i: Matukar Aka Kai Wa Iran Hari Zan Sanya Kakin Soji In Fito(1):
Daga:
Muhammad Awwal Bauchi
IRIB-Tehran - I.R.of Iran
awwalubauchi@yahoo.com

________________________

Jagora Imam Khamene'i - Yayin Da Yake Gabatar Da Jawabi A Masshad

Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai. Dukkan godiya ta tabbata ga Allah Madaukakin Sarki, tsira da amincin Allah su tabbata ga Shugabanmu kuma Annabinmu Abul Kasim al-Mustafa Muhammad, tare da tsarkakan Mutanen Gidansa zababbu musamman Hujjan Allah a bayan kasa.

Ina gode wa Allah Madaukakin Sarki da Ya ba ni wannan dama ta kasancewa tare da ku Ya ku 'yan'uwa maza da mata, muminai ma'abuta tsoron Allah da kaunar Ahlulbaiti (a.s) a ranar farko ta sabuwar shekara kuma a hubbaren Mai Girma Abul Hasan al-Ridha (a.s) mai tsarki. Kalmata ta farko ita ce ta girmama ga wannan Imami mai girma ce, ina fatan Allah Ya haskaka zukatanmu da hasken wannan waje mai tsarki Ya kuma biya mana bukatunmu.

A yayin wannan ganawa da zan yi da ku, Ya ku madaukakan al'umma birnin Masshad da sauran mutanen da suka zo wannan waje daga wajaje daban a wannan rana, zan yi magana kan wasu abubuwa biyu masu muhimmanci ga al'ummarmu, .daya dangane da batun zaben da ke zuwa ne sai kuma batun makirce-makircen makiya da barazanar da suke yi da kuma hanyoyin da za mu rusa su.

(Na tsallake batun da Jagora din ya yi kan zabe, da yake wannan ya shafi cikin gida ne, don haka na fassara kashi na biyu na jawabin nasa)

To amma dangane da batun fuskantar barazanar makiya da rusa shi ma dai yana daga cikin abin da hadin kan kasa zai iya samar da shi, don haka shi ma zan ce wani abu a kansa.

Yana da kyau dai a san cewa barazanar makiya, wani abu ne na tilasci sannan kuma da aka saba da shi, don kuwa duk wata al'ummar da take son ta rayu cikin 'yanci ba tare da mulkin mallaka kasashe ma'abuta girman kai ba, to babu makawa za ta fuskanci barazana kala-kala da kausasan maganganu. Don haka mu tuni al'ummarmu ta saba da irin wadannan barazana. Shekaru ashirin da shida kenan wadannan 'yan ba ni na iya ma'abuta girman kai na duniya musamman gwamnatin Amurka suke barazana ga al'ummar Iran da kuma fuskantarsu. Tuni kunnuwan mutanen Iran ya saba da jin irin wadannan barazana. Tuni al'ummar Iran sun yi kunnen uwan shegu da wadannan barazana, suka ci gaba da bin tafarkin da suka zaba wa kansu. A halin da ake ciki, banbancin ci gaban da Jamhuriyar Musulunci da gwamnatin Musulunci ta samu da lokacin da aka samar da ita tamkar sama da kasa ne. A yau din nan al'ummar Iran suna da karfin gaske, irin ci gaban da suka samu a fannonin ilmi, tattalin arziki, makamai a gaskiya yana da girman gaske, tattare da cewa wadannan barazana suna nan kuma ana ci gaba da ji da ganinsu.

Yana da kyau dai a san cewa barazanar makiya, wani abu ne na tilasci sannan kuma da aka saba da shi, don kuwa duk wata al'ummar da take son ta rayu cikin 'yanci ba tare da mulkin mallaka kasashe ma'abuta girman kai ba, to babu makawa za ta fuskanci barazana kala-kala da kausasan maganganu. Don haka mu tuni al'ummarmu ta saba da irin wadannan barazana. Shekaru ashirin da shida kenan wadannan 'yan ba ni na iya ma'abuta girman kai na duniya musamman gwamnatin Amurka suke barazana ga al'ummar Iran da kuma fuskantarsu. Tuni kunnuwan mutanen Iran ya saba da jin irin wadannan barazana. Tuni al'ummar Iran sun yi kunnen uwan shegu da wadannan barazana, suka ci gaba da bin tafarkin da suka zaba wa kansu. A halin da ake ciki, banbancin ci gaban da Jamhuriyar Musulunci da gwamnatin Musulunci ta samu da lokacin da aka samar da ita tamkar sama da kasa ne. A yau din nan al'ummar Iran suna da karfin gaske, irin ci gaban da suka samu a fannonin ilmi, tattalin arziki, makamai a gaskiya yana da girman gaske, tattare da cewa wadannan barazana suna nan kuma ana ci gaba da ji da ganinsu. Wasiyyata ta farko ga jami'an gwamnati ita ce kada su kuskura su bari wadannan barazana ta makiya ta yi tasiri a kansu har su hana su gudanar da ayyukansu da kuma nauyin da suka hau kansu; a'a ko da wasa su ci gaba da ayyukansu. Dole ne kowace al'umma kowace kasa ta kasance cikin shiri; lalle bai kamata a kowani lokaci, cikin kowani irin hali su gafala daga makirce-makircen da suke fitowa daga waje ba; sai dai duk da hakan bai kamata suruce-surucen makiya ya hana jami'ai gudanar da ayyukansu ba. Don haka dole ne al'umma da gwamnati su ci gaba da kokarin wajen sauke nauyin da ya hau kansu.

A halin da ake ciki kusan dukkan barazanar da suruce-surucen da Amurka take yi akan Iran ya fi shafi batun makamashin nukiliyya ne da karyar makaman kare dangin da suke yi. Shugaban kasar Amurka da sauran jami'an kasa a lokuta daban-daban maganarsu dai ita ce Iran tana kokarin mallakan makaman kare dangi, duk da cewa su da kansu sun san babu gaskiya cikin wannan ikirari da suke yi. Wani abu kawai suke son cimmawa; lamarin dai shi ne ba sa so Iran ta samu karfi da tsayawa da kafafunta; suna gaba ne da ci gaban kasar Iran; idan kuwa ba haka ai tuni daman sun san cewa mu ba ma neman makaman kare dangi. Abin da dai ba sa so shi ne a samu wata kasa a wannan yanki mai muhimmanci da ke da mafi yawan man fetur din duniya, wato wannan yanki na Gabas ta Tsakiya, wacce za ta daga tutan Musulunci da cewa karkashinta za ta rayu, baya ga haka kuma ta samu ci gaba. Hakikanin lamarin dai shi ne su wadannan kasashe na yammaci suna so ne kasashen wannan yanki - ciki har da Iran - su kasance karkashinsu da neman taimako daga wajensu; don haka ne ma suka yarda muna iya mallakan cibiyar makamashin nukiliyya amma mai din da cibiyar take bukata mu dinga saya daga wajensu (ba mu mu samar da kanmu ba).

Shekarun da suka gabata, a daya daga cikin jawaban sabuwar shekara da na yi a nan Masshad nake cewa idan da a ce wannan mai da a halin yanzu muke tonowa, da ake tono shi a wannan yanki na Gabas ta Tsakiya, da a ce a kasashen Turai da Yammaci a ke tono shi sannan mu mu saya daga wajensu, to da kudin kowace gangan ya ninninka yadda mu muke sayar musu a halin yanzu, ba a shirye suke su ba mu mai ba. A fili yake cewa wadannan mutane ba sa son ganin al'ummar wannan yanki sun sami wani abin da zai sa su wadatu daga gare su da kuma tsayawa da kafafunsu. Abin da suke so shi ne wannan yanki da ke cike da albarkatoci ya kasance karkashin ikonsu; don haka ne suke adawa da shirinmu na makamashin nukiliyya, suke adawa da ilmin da matasanmu suke samu, kai idan ma da za su iya da sun yi adawa da man fetur din da muke da shi, kamar yadda suke diban man fetur din yanki yadda suke so sakamakon rashin kishin kasa da ha'incin wasu shuwagabannin yankin. Shekaru masu yawa, man fetur din Iran ya kasance a hannun (turawan) Ingila, suna dibansa yadda suke so, daga baya kuma sai Amurkawa da sauransu suka shigo suka kame abubuwa; to wannan dai shi ne abin da suke so. Abin da ke kuna musu rai shi ne a sami wata kasa kamar Iran ta iya samun damar mallakan cibiyar makamashin nukiliyya da kuma man da ake bukata a cibiyar, sannan kuma taki mika kai gare su, wannan dai shi ne lamarin. Dimbin Jama'an Birnin Masshad Suna Sauraren Jagora

Makamashin nukiliyya dai wani abu ne mai darajar gaske, kuma sakamako ne na ci gaban ilmin da aka samu, sannan kuma wani abu ne da al'umma suke bukatuwa da shi a rayuwarsu ta yau da kullum. Da dama daga cikin kasashen da suka ci gaba suna amfani da irin wadannan cibiyoyi ne wajen samar da kansu karfin makamashin da suke bukata. Misali samar da wutan lantarki na daga cikin aikin irin wadannan cibiyoyi wanda hakan kuma ya kasance wani babban ci gaba da kowace kasar da ta iya samar da shi; don haka abin da suke so shi ne kada Iran ta samu wannan daukaka da ci gaban; dukkan rikice da kace-nace din kan wannan lamarin ne. Sai dai karya kawai suke yi su ce mu muna tsoron Iran tana iya kera makamin kare dangi, don kuwa sun riga da sun san cewa kera makamin nukiliyya ba ya daga cikin shirye-shiryenmu; dole ne al'ummar Iran su san wannan; matasanmu ma dole ne su san hakan.

Babu makawa, kusan dukkan kiraye-kiraye da umarnin da Musulunci yake bayarwa dangane da sanya Hijabi yana yinsu ne saboda kare wannan alaka ta aure. Don haka idan har, a matsayinku na matasan da za su yi aure, ba ku kula da hakan ba (hijab) a lokacin da kuka fita waje, ko kuma kuka bari idanuwanku suka koma kan wasu matan ko kuma mazan, zukatanku suka koma ga wasu sabanin abokan zamanku na aure, idan kuka bari har kuka kulla alaka da wasu mata ko mazajen da ba naku ba wadanda kuke gamuwa da su a wajaje daban-daban, to babu makawa aurenku na iya shiga cikin mawuyacin hali. Da farko dai abokin zaman naku zai/zata fara rasa irin sha'awar da ke jawo hankalinsa/ta zuwa gare ka/ta da ke haifar da so da tausasawa. Don kuwa koda a ce mutum yana da irin kyaun da Annabi Yusuf (a.s) yake da shi, to babu makawa bayan wani lokaci zai kasance ba wani bakon abu ba ga daya abokin zaman. Don haka, kamar misalin wannan bishiya, dole ne a ba ta lokaci wajen kula da wannan so da kauna.

Abin da a yau din nan kasashen yammaci suke ta yadawa - musamman ma Amurka - dangane da batun makamashin nukiliyyanmu, shi ne su hana al'ummar Iran mallakan wannan ilmi da ci gaba. To amma ai wannan hakki namu ne; don me za a hana mu mallakansa? Ina ai hakkin al'ummar Iran ne, wato ilminsa da kuma sinadarorin da ake bukata, don kuwa ai ci gaba ne na ilmi, harkokin kiwon lafiya da kuma ci gaban matasanmu, don haka a fili yake cewa babu yadda za a yi al'ummarmu su ja da baya daga hakan, wato su kauce daga wannan hakki nasu.

A kokarin da suke yi na boye haramtacciyar manufarsu, makaryata kana munafukan jami'an Amurka, suna tuhumar Iran da cewa tana kokarin kera hulunan makamin nukiliya, su dora su a kan makamai masu linzami su harba su. (abin tambaya a nan shi ne) mu harba su ina? Mu dai hatta ga abokan gabanmu ba za mu iya aikata haka ba. Irin wannan aikin Amurka ne (ba mu ba). Amurka ce kasa guda da ya zuwa yanzu ta aikata wannan danyen aiki. Kasashen yammaci ne suka kera makaman kare dangi, suka harba su kan al'umma, su ne suka ba wa Saddam irin wadannan makamai yayin yakin shekaru takwas da suka kallafa mana, sannan kuma suka yi shiru kan danyen aikin da ya aikata da su, suka ci gaba da taimakon Saddam. Mu dai Musulunci bai ba mu daman yin haka ba. Mu za mu yi amfani da shi wajen ci gaban ilmi, ihun da Amurka take yi ba don komai ba ne face sai don cimma manufarta.

Duk da haka yana da kyau in sanar da ku, ya kamata al'ummar Iran ta san cewa, irin mutanen nan da suke komawa gefe suna surutun cewa me ya sa ake kokarin mallakan makamashin nukiliyya, su san cewa suna aiki ne wa makiya a gafale, su san cewa a yau batun makamashin nukiliyya wani abu ne kawai da Amurka take fakewa da shi don cimma manufarta. Wadannan mutane ma'abuta karfi ba abin da suka sani in banda barazana. Ta hanyar barazana da ruba suke ciyar da harkokinsu gaba, sai dai abin bakin cikin shi ne cewa wasu al'ummomi da gwamnatoci sun nuna gazawarsu wajen fuskantar irin wadannan barazana. Amma yana da kyau a san cewa wadannan mutane ba abin da suka iya in ba barazana ba. Don haka a yau abin da suke fakewa da shi shi ne makamashin nukiliyya, idan da a ce babu shi da wani abun kuma za su koma kansa. Su ne asalin 'yan ta'addan duniya, alhali kuwa suna tuhumar Iran da al'ummar musulmi da ayyukan ta'addanci. Mu duba mu ga irin ayyukan ta'addancin da jami'an tsaro da na leken asirin Amurka suke aikatawa a kasar Iraki da gidan yarin Abu Ghuraib, wanda hakan ma kadan ne daga cikin irin ayyukansu, don kuwa makamantan hakan suna nan da yawa. Suna cin mutumcin mutane, suna take hakkokin bil'Adama, shin a Irakin ne ko kuma a Afghanistan, ko kuma a cikin gidajen yarinsu (da ke cikin kasarsu) ko kuma wanda yake Guantanamo, amma suna bude baki suna tuhumar wasu mutane da take hakkokin bil'Adama. A iyakacin sanina dai, ban san wata kasa da take take hakkokin bil'Adama kamar Amurka ba. Yayin da nake duba kididdigan ababen da suka faru cikin 'yan shekarun baya-bayan nan - ababen da suka faru a kan idanuwanmu - na tabbatar da cewa babu wata kasa a wannan duniya da take take hakkokin bil'Adama kamar Amurka, hakan ma baya ga ayyukan da take aikatawa a sauran kasashen duniya, a cikin kasarsu ma (Amurka) suna aikata ayyukan ta'addanci da take hakkokin bil'Adama. A yau kamar sauran shekarun da suka gabata bakaken fatan Amurka suna fuskantar nuna banbancin launin fata da sauran nau'oi na bambanci. A lokacin mulkin uban wannan Bush din, an gudanar da wasu gagaruman bore da zanga-zangogi a wasu jihohin Amurka sakamakon irin zalunci na fili da ake nunawa bakaken fata, har sai da ya kai sojoji suka fito kan tituna saboda 'yan sanda sun gaza. A lokacin shugaban da ya biyo baya ma sama da 'yan Dawudiyya - wata kungiya ce ta kiristoci da ke adawa da siyasar gwamantin Amurka - tamanin ne aka kona su a gaba idon mutane, maza da mata yara da manya a lokacin da suke gudanar da wani taro nasu da kuma kin watsewa kamar yadda 'yan sanda suka bukace su. Wannan dai shi ne kare hakkokin bil'Adaman wadannan mutane. A lokacin wannan shugaban Amurkan ma, lokacin da suke kokarin mamaye kasar Afghanistan, baya ga rowan bama-baman da suka yi a kan al'ummar da ba su ci ba su sha ba, (kowa ya ga) yadda suka bude wuta kan wasu fursunonin da suke tsare da su, inda suka musu kisan kiyashi; an watsa wannan labari, sai dai kawai ba a bari sun yi wani tasiri a zukatan al'umma ba, cikin gaggawa aka yi yadda aka mance da su. A daidai wannan lokaci kuma suna bude baki suna cewa a waje kaza ko kuma a Iran an musguna wa wannan fursunan, misali su ce ba a bashi takalmi faden da ya dace ba. Ina, take hakkokin bil'Adaman da ake yi a Amurka ya fi na kowace kasa yawa, to amma suna bude baki da tuhumar wasu al'ummomin duniya ko kuma al'ummar Iran da gwamnatinsu ta Musulunci da cewa suna take hakkokin bil'Adama. (Abin bakin cikin shi ne cewa) mutanen da suka ba wa kansu tutar kare hakkokin bil'Adama su ne suka fi kowa take hakkokin bil'Adaman.

Idan muka duba za mu ga cewa barazanar da suke yi ba wai kawai ta takaita kan batun makamashin nukiliyya ba ne, wasiyyata ga jami'an gwamnati da al'ummar Iran ita ce kada su damu da barazanar makiya; su ci gaba da tafarkin da suka kama su ci gaba da ayyukan da suka sa a gaba. Sai dai yana da kyau su kasance cikin hankulansu, kada su gafala kan komai.

Har ila yau ma yana da kyau in sanar da ku cewa: mu dai, ba kamar jami'an Amurka ba, ba ma'abuta tsokanar fada ba ne, su ne ma'abuta tsokanar fada da kuma neman yaki, to amma yana da kyau a san cewa za mu sadaukar da dukkan abin da muka mallaka wajen kare martaba da mutumcin wannan kasa da wannan al'umma tamu. Mu (jami'ai) ba ma daukan sadaukarwa a matsayin aikin sauran al'umma ba, ko da wasa. Ku duba ku gani, bayan harin 11 ga watan Satumban da aka kai wa dogayen gine-ginen nan na birnin New York, babu wanda ya san inda shugaban Amurka, mataimakinsa da sauran manyan jami'an Amurka suke (sun buya), to mu fa ba haka muke ba. Idan, abin Allah Ya kiyaye, wata jarabawa mai daci ta samu wannan kasa tamu, to mu da al'ummarmu za su sanya tufafin soji, su fito don ba da gudummawa da kuma sadaukarwa.

Mafi girma da muhimmancin makamin wannan al'umma tamu na kashe wutan barazana shi ne hadin kan al'umma waje guda, al'ummar Iran ba ta bukatan makaman kare dangi wajen kawar da barazanar makiya. Hadin kanku Ya ku al'ummar Iran bisa taimakon Ubangiji da imani da addini shi ne babban makaminku; da wannan makami ne shekaru ashirin da shida da suka wuce tun daga lokacin samun nasarar juyin juya halin Musulunci zuwa yau kuka samu ci gaban da kuke da shi kuma kuka nuna wa duniya, kuma da shi ne za ku ci gaba da nuna musu.

Don haka ku kiyaye hadin kai tsakaninku. Wannan hadin kai naku shi ne abin da makiya suke son ganin bayansa, makiya suna so ne su sami shiga tsakankaninku, wannan dai shi ne tunani da mafarkinsu. A fili a halin yanzu Amurkawa suke bayanin manufofin da suke son cimmawa, wannan ma dai na daga cikin kamun Ubangiji ga ma'abuta girman kai. A fili suna fadin cewa za mu ba da taimakon kudi ga duk wanda ya taimaka wa Amurka cimma manufarta a Iran. Sai dai ina ba su san al'ummarmu ba, don haka ne suke fadin hakan a fili suke cewa muna son mu yi amfani da kudi wajen samar da 'yan adawa a cikin Iran. Don haka dole ne kowa da kowa ya sani; kamar yadda kuma ya kamata duk wani da yake son kudin Amurka don ya biya musu bukatarsu a cikin Iran da yin adawa, ya san cewa zai kasance abin kyaman da aka fi ki a idanuwan al'ummar Iran. Dole ne kowa da kowa, musamman manyan kasa, matasa, daliban jami'a da sauran jama'an da suke da tasiri, su san cewa babban maganin dukkannin matsalolin da ake fuskanta shi ne hadin kai da fahimtar juna.

Ku yi kokarin kusato da zukata waje guda; ku nemi taimakon Ubangiji wajen ci gaban wannan kasa da irin arziki da albarkatun da ya yi mana, lalle Allah Madaukaki Zai taimaka. Ina da tabbacin cewa goben wannan al'umma tamu zai fi shekarun da suka gabata, kuma da yardar Allah addu'an Mai Girma Bakiyatullah (Imam Mahdi) zai hada da wannan al'umma tamu.

Ina rokon Allah Madaukakin Sarki da Ya jikan wannan al'umma tamu saboda tsarkakakken ruhin madaukakan shahidanmu da kuma ruhin Imaminmu Mai Girma (Imam Khumaini), ya kuma lullube mu da rahamarSa da gafararSa.


Wassalamu Alaikum Wa Rahmatullah.
____________