Jawabin Jagora A Makon Hadin Kai (2 Mayu 2004)

 

 

 
Jawabin Jagora Ga Mahalarta Taron Makon Hadin Kai(1):
Daga:
Muhammad Awwal Bauchi
IRIB-Tehran - I.R.of Iran
awwalubauchi@yahoo.com

________________________

Jagora Imam Khamene'i - Yayin Da Yake Gabatar Da Jawabi

Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai

Yau rana ce ta haihuwar Manzon Musulunci Muhammad al-Mustafa (s.a.w.a) da kuma Imam Ja'afar al-Sadik (a.s), a hakikanin gaskiya rana ce mai girman gaske ga al'ummar musulmi.

Don haka da farko ina taya al'ummar musulmi, madaukakan al'ummar Iran, mahalarta wannan majalisi musamman bakin da suka zo daga waje murnar zagayowar wannan rana (mai albarka). Abu na biyu kuma, don girmama matsayin Manzon Allah (s.a.w.a), mu musulmi muna da abubuwan fadi ga junanmu, saboda shi Manzo a wajenmu malami ne na kyawawan dabi'u, adalci, 'yan'Adamataka da 'yan'uwantaka, kamala, ci gaban dan'Adam na har abada da dai sauransu. Shin akwai wani mutum da zai ce ba shi bukatar wadannan koyarwa? Musamman ma mutanen wannan zamani, muna bukatar wadannan koyarwa ta Manzon Musulunci.

Abin da nake son magana kansa a yau, shi ne batun hadin kai da kalma guda tsakanin al'ummar musulmi. Idan muka duba za mu ga cewa al'ummar musulmi suna fuskantar matsaloli da barazana masu girman gaske. Duk da yake a fili da dama daga cikin matsalolin suna tattare da mu ne; mu ne muka nuna gazawa; son kai da son duniyar da ke tattare da mu su ne suka kasance mana kafar ungulu wajen isa ga kamala da cika, don haka dole ne mu dawo cikin hankulanmu; dole ne mu motsa da tashi tsaye. Sai dai fa duk da hakan, bangare da dama na wadannan koma baya, matsaloli da bala'oin da muke fuskanta suna da alaka da gwamnatocin baba-kere na duniya da suka mulki duniya a da da kuma yanzu. Tsarin da ke gudana a duniya, tsari ne na zalunci, tsari ne da ya dogara kan amfani da karfi, ba tsari ne na gina al'umma ba, tsari ne na rayuwa irin ta dabbobi (mai karfi ya murkushe mai rauni).

Ku duba ku ga halin da duniyar musulmi ke ciki! (a matsayin misali) shekara da shekaru muke magana kan matsalar Palastinu a matsayin daya daga cikin lamurran masu sosa rai, (to ba ma kawai Palastinu ba) ga Iraki ma ta fada cikin irin wannan mummunan yanayi. Ku duba ku ga abin da wadannan ma'abuta karfi suke yi ko kuma yadda suke amfani da tursasawa ko. A yau, abin da ake amfani da shi su ne zantuka marasa tushe da amfani da karfin bindiga da kudi, su ne ababen da ake amfani da su. A fili ba tare da wani boye-boye ba suke aikata muggan ayyuka da laifuffuka da take hakkokin bil'Adama da suka saba wa dukkannin dokokin kasa da kasa a kan al'umma. A wasu lokuta kuwa sukan yi amfani da wasu sunaye wajen kare wadannan muggan ayyuka nasu duk da cewa sun san al'umma ba za su yarda da hakan ba; kai a wasu lokutan ma ko sunayen ba sa amfani da su. A matsayin misali a fili haramtacciyar kasar Isra'ila take cewa za mu kashe 'yan gwagwarmayar Palastinawa, ita kuma gwamnatin Amurka a fili take nuna goyon bayan ga hakan. Wannan dai shi ne yadda tsarin mulki yake a duniya a halin yanzu.

Ku duba ku gani, hatta ayyukan ta'addancin da gwamnatin Amurka ke amfani da shi a matsayin hanyar cimma manufofinta da kuma amfani da karfi a kan al'umma, haramtacciyar kasar Isra'ila a fili tana amfani da su da aikata su (a kan Palastinawa). Hakan shi ne abin da ke faruwa a Iraki bayan mamayen da Amurka ta yi wa kasar da ci gaba da wulakanta wannan al'umma mai cikakken tarihi da kyawawan al'adu; suna masu amfani da kalmomi irinsu kare hakkokin bil'Adama da yada demokradiyya da 'yanci, duk da cewa babu wani mutum a duniyan nan da zai amince da maganarsu don kuwa ayyukansu a Iraki sun saba wa abin da suke ikirari, sannan kuma sun tabbatar da cewa babu ruwansu da wani batun kare hakkokin bil'Adama wajen cimma manufofinsu ( ku duba ku gani) su ne suke nadawa su ne suke saukewa, su suke nada shugaba, su ne suke tsara dokoki amma kuma su ne suke saba wa wadannan dokoki babu wanda zai hukumta su. Ku duba ku ga dai abubuwan da suke faruwa a Iraki mana. To wannan dai shi ne halin da duniyar musulmi take ciki.

Babban laifin al'ummar musulmi dai shi ne sun sami kansu a wani yanki da yafi ko ina arziki, suna wani yanki da ci gaba da kyawawan al'adun duniya suka dogara kan ababen da suke wajen, irin wadannan abubuwa su suke tsole musu idanuwa don haka a shirye suke su aikata duk wani ta'addanci a kan al'umma. Wannan dai shi ne halin da al'ummar musulmi suke ciki. To amma abin tambayar dai a nan shi ne shin kasashen musulmi ba za su iya kare kansu daga wadannan 'yan bani na iya ba ne? Amsar wannan tambaya dai ita ce, me zai hana, za mu iya mana, don kuwa muna da dukkan abubuwan da ake bukata wajen kare kai. (Misali) muna da yawan al'umma, muna da arziki mai yawa, muna da fitattun mutanen da za su iya kara wa al'ummarmu karfin gwuiwan yin tsayin daka, muna da kyawawan al'adu da dadaddun ci gaba da ba mu da na biyu a duniya (mun zama tilo), a takaice dai muna da abubuwa masu yawa. Don haka muna da karfin kare kanmu, sai dai abin tambayar shi ne me ya sa ba ma iya kare kanmu? Me ya sa ba a ganin wani abin a zo a gani a fagen aiki daga wajenmu? Amsar dai ita ce don kawukanmu ba a hade suke ba, saboda wasu abubuwa sun shiga tsakaninmu, wannan gagarumar al'umma tamu ta rarrabu gida-gida, muna fada da junanmu, a fili yake (idan aka samu haka) wannan runduna tamu ba abin da za ta iya yi.

A halin da ake ciki lokaci ya yi da al'ummar musulmi za su sake nazari cikin lamurransu, su yi tunani da sanya ido kan batun hadin kai. Idan muka duba za mu ga cewa barazanar Amurka a wannan yanki ba wai yana nufin kasa guda ne kawai ba, a'a, dukkan kasashe ne. A yau barazanan 'yan jari hujjan yahudawan sahyoniya bisa taimakon Amurka ba wai kawai za ta tsaya kan wani yanki ba ne, a'a, so suke su hadiye dukkan yankin nan, kai a yanzu kan ma a fili suke fadin hakan. Idan muka duba za mu ga cewa burinsu na shirin 'babban yankin Gabas ta Tsakiya' shi ne cimma wannan manufa. Kamar yadda manufa da niyyarsu guda ce, ita ce hadiye yankin tun shekaru hamsin da wani abin da suka wuce da kafa haramtacciyar kasarsu ko kuma tun shekaru darin da suka wuce da kafa Turai. Mutanen yankin nan dai ba su da wani muhimmanci a wajensu, ko ma mai zai same su ya same su. Abin da ya hau kanmu dai shi ne kowanenmu ya dawo cikin hayacinsa, mu hada hannuwa waje guda.

Kamar yadda na fadi ne a baya, bai kamata a dauka cewa ana iya samun so da kauna cikin ruwan sanyi ba ne, a'a dole ne a yi kokari kafin a same su. Idan kuka duba a kasashen yammaci, a wasu al'ummomi, za mu ga cewa matasa sukan tsoma kawukansu cikin harkokin zinace-zinace kafin aure, wannan shi ya kan sa ba sa yin aure da wuri idan aka kwatantasu da sauran al'ummomi. A irin wadannan kasashe maza da mata, musamman ma maza, sukan yi zinace-zinace kafin su yi aure, haka ne ya kan sanya auren da suka yi daga baya ba ya zama musu wani bakon abu, kuma ba wani lamari ne mai muhimmanci ba. Don haka ya ya za a iya kwatanta su da wani matashi musulmin da ya nesanci irin wadannan muggan dabi'u, wanda ya rayu rayuwa ta tsarkaka da mutumci? Shin mahangar wadannan nau'i biyu na mutane kan aure zai iya kasancewa guda? Shin girmamawarsu ga aure zai kasance guda? Koda wasa.

Wasiyya da kirata ga kasashe da al'ummar musulmi ita ce su yi tuntuni da aiwatar da wani abin a zo a gani a wannan bangare, duk da cewa hakan yana bukatuwa da gabatarwa da kuma aiki tukuru, da dole ne a kula da su. Sai dai yana da kyau a fahimci cewa su ma fa makiya ba zama kawai za su yi ba, ko da wasa, za su ci gaba da amfani da abubuwa irinsu kabilanci, mazhaba da 'yan garanci da sauran 'yan kananan abubuwa da Musulunci bai ba su wani muhimmanci ba wajen raba kan al'umma. Musulunci ba ya ganin kabila ko inda mutum ya fito a matsayin wani abu mai muhimmanci "Hakika wanda ya fi ku a wajen Allah shi ne wanda ya fi ku tsoronSa". Musulunci ya bukaci musulmi da su yi alaka da junansu a matsayin 'yan'uwa. Musulunci bai ce dan sunna ko dan shi'a ko kuma dan wata mazhaba ta daban ba, cewa ya yi "Hakika muminai 'yan'uwa juna ne", duk wani mutumin da ya yi imani da wannan Littafi, da wannan Alkur'ani da wannan addini da wannan Alkibla, to mumini ne, don haka su 'yan'uwan juna ne, wannan dai shi ne abin da Musulunci ya kiraye mu a kai. Amma abin bakin cikin shi ne cewa mu kan boye wukakenmu a baya don saran kirazan 'yan'uwanmu, a hakikanin gaskiya mu kan nuna gazawa a dukkan bangarori. Dole ne fa mu kawo karshen irin wannan yanayi.

A halin da ake ciki matukar dai al'ummar musulmi suna son rayuwa. daukaka, 'yanci da kuma daga tutar Musulunci, to suna bukatuwa ga hadin kai. Idan aka samu hakan, babu karfin da ya isa keta tsakaninsu ballantana ya haifar da rarrabuwa. Hadin kai lamari ne da ke da muhimmanci ga kowani guda daga cikinmu, to amma me ya sa ne ba ma fahimtar muhimmanci hakan tsakanin musulmi? (Ya kamata mu fahimci cewa) akwai babban nauyi a kanmu. Mu sani cewa matukar makiya suka yi nasarar kwace wannan yanki, to babu makawa duniyar musulmi za ta sake komawa baya na wasu shekaru dari kamar lokacin mulkin mallaka, hakan zai kara yawan banbancin da ke tsakanin kasashen musulmin da sauran kasashe. Don haka dole ne mu mike tsaye, don kuwa a halin da ake ciki muna da babban nauyin da ke kanmu, a yau gwamnatoci, masana da malamai suna da gagarumin nauyi a kansu, dukkanmu muna da babban nauyin da yake kanmu na tabbatar da hadin kai tsakanin musulmi. Abin da mai girma Imaminmu (Imam Khumaini), Allah Ya kara masa yarda, ya ke jaddadawa tun kafin nasarar juyin juya halin Musulunci har zuwa karshen rayuwarsa shi ne batun hadin kai tsakanin musulmi da a halin yanzu muke ganin fa'ida da hikimar da ke cikin wadannan wasiyoyi nasa.

Muna rokon Allah Madaukakin Sarki, don darajar ruhin wannan Manzon namu mai girma kuma cikamakin Annabawa, wannan mafificin 'ya'yan Adamu da kuma ruhin Imam Ja'afar al-Sadik (a.s) da kuma sadaukarwar da wadannan manyan bayin Allah suka yi, da Ya farkar da mu daga wannan gagarumin barci da muke ciki. Ya shiryar da mu zuwa ga tafarkin gaskiya; Ya sanya mu fahimci nauyin da ya hau kanmu da sauke shi kamar yadda ya dace, sannan kuma ya mayar da sharrin makiya gare su.


Wassalamu Alaikum Wa Rahmatullah.
____________
(1)- Jagoran Juyin Juya Hali Imam Khamene'i ya gabatar da wannan jawabi ne ga mahalarta taron makon Hadin Kan da suka kai masa ziyara gidansa a ranar 12 ga watan Rabiul Awwwal 1345 da ya yi daidai da 2 ga Mayun 2004, da ya yi dai dai da farko makon Hadin Kai.