Jawabin Jagora A Yayin Ganawa da 'Yan Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran


  • Maudhu'i: Zagayowar Ranar 'Yan Majalisa ta Iran.
  • Wuri: Husainiyar Imam Khumaini (r.a); Tehran.
  • Rana: 26/Rabi'ul Awwal/1424 = 28/Mayu 2003.
  • Shimfida:A wannan rana ce Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Ayatullah al-Uzma Sayyid Ali Khamene'i (H) ya gana da Shugaba da 'yan majalisar shawarar Musulunci ta Iran, a zagayowar ranar 'Yan Majalisa ta Iran. A yayin wannan ganawa dai Jagoran ya gabatar da jawabi ga 'Yan Majalisar, abin da ke biye fassarar jawabin Jagoran ne. A sha karatu lafiya.

Jagora - Imam Khamene'i Tare Da 'Yan Majalisa

Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai

Ina wa dukkan 'yan uwa mata da maza da kuma wakilan Majalisar Shawarar Musulunci masu girma barka da zuwa. Hakika wannan taro ne da ke cike da kauna da son juna. Duk da kasantuwan kamarori da kuma 'yan rahotanni da suke gurin nan to amma duk da hakan ba za su tilasta mana kin nuna kaunar dake tsakaninmu ba, to amma dai duk da haka, mun gode wa Allah, taron dai cike yake da kauna da kuma son juna. Ina jinjinawa dukkan 'yan uwa saboda kokarin da suke yi a Majalisar Shawarar Musulunci da kuma nauyin da suka dauka na ayyukan majalisa, wadanda wasu daga cikin irin wadannan ayyuka, Sheikh Karroubi (shugaban majalisa) ya yi karin bayani kansu. Haka nan kuma ina jinjinawa shi kansa Malam Karroubi, saboda irin nauyin da ya dauka da kuma irin takura masa da wannan nauyi yake yi, lalle kan ina yabawa da kuma jinjina masa.

Ina ganin zan fara wannan jawabi nawa ne da wannan aya mai girma, da take cewa:

"Shi ne Wanda Ya saukar da natsuwa a cikin zukatan muminai domin su kara wani imani tare da imaninsu, alhali kuwa rundunonin sammai da kassai, na Allah kawai ne, kuma Allah Ya kasance Masani, Mai hikima". (Suratul Fat'h; 48:4)

Shakka babu irin abubuwan da suke faruwa a halin yanzu na irin farfagandoji da ayyukan siyasa akan Jamhuriyar Musulunci ta Iran, al'ummar Iran da kuma na sauran al'ummomin wannan yanki duk wani kokari ne na makirci da kuma ta'annuti; ta'annuti irin na siyasa da kuma na ruhi; duk dai da nufin haifar da damuwa da tsoro a cikin zukata- wanda hakan dai ita ce siyasar 'yan mulkin mallaka a yau din nan. Lalle hakan ba wani bakon abu ba ne a gare mu cikin wadannan shekaru ashirin da wani abu da suka gabata da kuma ma ga abubuwan da suka faru tsawon tarihin Musulunci, tun daga farko har zuwa yau din nan. Don haka idan kuka duba za ku ga cewa daya daga cikin abubuwan da Alkur'ani mai girma, yayi magana kansu a matsayin mummunan abu shi ne batun "Masu Tsegumi" wato mutanen da suke kokarin haifar da damuwa da kuma tsoro a cikin zukatan al'umma. Wata rana na taba karanta wa wasu 'yan'uwa da suka zo nan gurin wannan aya:

"Wadanda mutane suka ce musu: Lalle ne, mutane sun tara (rundunoni) saboda ku, don haka ku ji tsoronsu...". A wancan lokacin wasu mutane ne suke kokarin haifar da rikici da kuma tsoro a zukatan al'umma a birnin Madinan Manzon Allah (s), sun taru ne suna son su razanar da mutane da hana su aikata abin da ya dace. Anan sai aya ta sauko cewa a duk lokacin da irin wadannan makaryata, makirai masu raunin imani suke son share irin wannan fage na tsoro, suke son yada irin wadannan kwayoyin cuta masu hadari na tsoro da damuwa tsakanin muminai, to a wannan lokaci muminai su ne wadanda "Sai imaninsu ya karu", daga nan sai suka ce: "Sai suka ce Allah Ya ishe mu, kuma madalla da madogara".To wannan kalma ta "Allah Ya ishe mu, kuma madalla da madogara"ta ta'allaka da nan ne, wato wajen fuskantar makirce-makircen abokan gaba wadanda suke son cimma hakan ta hanyar farfagandojin da suke yadawa; suna da natsuwa. Wannan dai shi ne natsuwar da ake magana cikin wannan aya: "Shi ne Wanda Ya saukar da natsuwa a cikin zukatan muminai", a wannan lokaci Allah Madaukakin Sarki ya saukar da nutsuwa cikin zukatan muminai "domin su kara wani imani tare da imaninsu", wannan dai shi ne hakikanin al'amarin.

Hakika mutum ya kan rasa komai nasa hatta imani da natsuwar da yake da ita a lokacin da yake cikin halin damuwa da tsoro; lalle haka mutumin da ke cikin tsoro yake. Tsoro dai ya kan rikirkita hankali da azamar dan'Adam. Mutumin da ke cikin halin tsoro ba wai kawai ma ba zai iya amfani da hankalinsa yadda ya kamata ba ne, face ma dai ba zai iya amfani da azama da iradarsa yadda ya kamata ba. Sai ya yi gaba sai ya komo baya. Kamar yadda wata rana ne Manzon Allah (s.a.w.a) ya gaya wa Amirul Muminina Ali (a.s) ne cewa: "Kada ka shawarci matsoraci, don kuwa shi zai kuntata maka mafita ne". Don haka kada mutum ya kuskura ya yi shawara da mutum matsoraci mai raki cikin dukkan al'amurransa, don kuwa babu makawa zai toshe masa dukkan hanyoyi da tafarkin tsira. Hakika jarumin mutum, wanda ba matsoraci ba shi ne yake iya tunani yadda ya kamata, shi ne wanda zai iya daukar matsayar da ta dace, to amma lokacin da tsoro ya kama shi; to "zai kuntata maka mafita ne", don haka zai zamanto cikin damuwar ko in aikata haka ko kuma kada in aikata haka, daga nana kuma sai mika wuyan haka nan kawai hannun rabbana. Don haka natsuwa tana da matukar muhimmanci.

Lalle bayanin "natsuwa" da aka yi a cikin "Suratul Fat'h" "Lalle Mu, Mun yi maka budi, budi mabayyani" yana da ban mamaki kuma ya ta'allaka ne da wannan aya, kuma a cikin wannan aya an maimaita bayyanar da "saukar natsuwa" cikin zukatan muminai har marhala uku. Daya daga cikin jarrabawa mai daci mai wahala da musulmi suka fuskanta ta ta'allaka ne da wannan aya ta Inna Fatahna a lokacin da Manzon Allah (s.a.w.a) ya kuduri aniyar tafiya birnin Makka; garin Makkan da shekaru biyu kafin wannan lamari ya mamaye Madina da nufin takura wa mutanen garin; kuma yakin Ahzab ma cikin irin wannan yanayi mai wahala ne aka yi shi da nufin zubar da jinin Manzon Allah (s.a.w.a) da kuma sahabbansa. A wancan lokacin Manzon Allah (s.a.w.a) ya fada wa sahabbansa cewa muna son tafiya (Makka) don aikin Ummara, ya ce wa musulmi ku zo mu tafi gaba daya, to amma wasu daga cikin mabiyan nasa sun tsorata, suka ce Manzon Allah (s.a.w.a) ba zai dawo ba, za a gama da shi. To batun "saukar da natsuwa" anan ne yake aiki, lokacin da Allah Madaukakin Sarki ya saukar da natsuwa a zukatan muminai, kuma suka tafi suka fuskanci abokan gaba kuma suka yi nasara. Lalle abin da Manzon Allah (s.a.w.a) ya ke son tabbatarwa shi ne kuwa ya faru.


Wai shin ina ne haddin matsin lambar Amurka yake; ku tantance shi, don idan mun kai wannan iyaka mun san cewa mun kai haddin da Amurka ba za ta sake matsa mana lamba ba. Ni ina son sanin ina ne wannan haddi yake? Wannan haddi dai shi ne - duk da cewa ni da ku ba mu da wannan hakkin - da yawun al'umma Iran ku ce mu ba ma son Musulunci, Jamhuriyar Musulunci da kuma hukumar al'umma, duk wanda kuke so ya yi mulki a wannan kasa ya zo ya yi, wannan shi ne haddin da suke so; to wannan dai shi ne farkon sanya wannan al'umma cikin kangi. Shin za mu iya yin haka? Shin ni da ku za mu iya mika wannan al'umma ga hannun makiya? Shin muna da wannan hakki? Hakika al'umma ba su zabe mu don mu yi musu wannan danyen aiki ba
"Natsuwa" wacce ta samo asali daga dogaro da kyakkyawar zato ga Allah Madaukakin Sarki. Ku duba ku gani a lokacin da waninku ya zabi wata manufa da yake son cimmawa kuma ya ci gaba da ba da kokari wajen cimma ta, to fa ya san cewa Allah Madaukakin Sarki ya yi alkawarin ba da taimako da kuma nasara, babu shakku cikin hakan. Akwai wani lokaci da mutum ya kan iya zaban wata manufa da bata dace ba; wani lokaci kuma ya zabi wacce ta dace, to amma kuma babu wani abin da yake yi wajen cimma wannan manufa, to a irin wannan yanayi tsammanin taimakon Ubangiji aikin baban giwa ne. Babu shakka tun tun tuni musulmai suke da kyawawan manufofi; to amma saboda rashin kokarinsu wajen ganin sun cimma wadannan manufofi ya sa har yanzu suka gagara cimma su. A halin da ake ciki, duk inda kuka duba sai ku ga musulmai suna cikin halin wulakanci da matsin lamba, to ba komai ya jawo musu haka ba in ban da zaman dirshan da suka yi. Idan kuwa ba haka ba, to da lalle sun sami nasara, don kuwa a duk inda aka samu kyakkyawar manufa, kana kuma aka rufa mata baya da kokari da tashi tsaye, to lalle fa taimakon Allah da nasararSa babu shakka za su zo. To sai dai kuma yana da kyau a fahimci cewa nasara da taimakon Allah ba suna nufin mutum ba zai fuskanci jarrabawa masu wahala daga Ubangijin ba; a'a me ya sa, lalle akwai jarabawa: "Hakika kuma za mu jarraba ku da wani abin tsoro da yunwa da tawayar dukiyoyi da rayuka da 'ya'yan itatatuwa", to wannan dai shi ne lamarin kuma dukkan wadannan abubuwa suna nan akan wannan tafarki na gwagwarmaya; to sai dai kuma "Ka yi albishir ga masu hakuri", to hakuri anan yana nufin tsayin daka da dawwama akan tafarki, to anan albishirin Ubangiji yakan zo, ma'ana nasara za ta samu mutane.

Da dama daga cikinku suna nan lokacin da ake gwagwarmayar (kafa tsarin Musulunci a Iran). A hakikanin gaskiya dai jami'an tsaron gwamnatin Dagutu (Shah) ba wai jami'an tsaro ne da za a iya fada da su cikin ruwan sanyi ba. A lokacin akwai da yawa daga cikin masu akidar markisanci da wasu 'yan boko da suke ta surutu, to amma lokacin da suka ga gidan yari da kuma irin azabtarwar da ake yi a ciki, kai wasu ma ba su gani ba face dai sun ji ne kawai, to sai suka juya baya a tsakiyar tafiya, suka mika wuya; to sai dai kuma duk da haka wasu da dama sun ci gaba da tafiya akan wannan tafarki. Albarka ta farko da ta samu wannan tsayin daka na wadannan mutane ita ce cewa Allah Madaukakin Sarki Ya bayyanar da gaskiyarsu ga mutane a fili; Ya kuma nuna tafarkinsu ga mutane su kuma suka yi riko da su. To lalle a lokacin da mutane suka yi riko da su, to komai zai yi kyau. Muhimmin abin dai shi ne cewa su wadannan 'yan gwagwarmaya wadanda suka kuduri aniya su nuna ainihin gaskiyan nasu da kuma riko da shi, su nuna cewa lalle da gaske suke yi suna son cimma wannan manufa; to a wannan lokaci Allah Madaukakin Sarki zai aiko da taimako da nasararSa. A cikin littafin Nahjul Balagah ya zo cewa: "Lokacin da Allah Madaukakin Sarki ya ga gaskiyarmu", a lokacin da Allah Ya ga gaskiyarmu; Ya ga cewa da gaske mu ke yi, ba don kudi ko son duniya mu ke yi ba; "Sai Allah Ya saukar mana da taimako kana kuma Ya saukar wa makiyanmu tsoro da razana".Allah zai ba mu nasara, ya kuma ruguza abokan gabanmu. Irin wannan lamari ma dai ya kasance a lokacin gwagwarmayarmu, kuma ma cikin wadannan shekaru talatin da uku zuwa da hudu duk hakan lamarin ya kasance, hakika babu wani lokaci da kasarmu ta kasance ba tare da irin wadannan matsin lamba ba.

Ya ku 'yan'uwa maza da mata! Ku 'yan majalisa ne kuma 'yan siyasa; me yiyuwa ne halin da ake ciki yanzu ya kasance a fili ga da dama daga cikinku, to amma dai abin da Amurka a yau - wacce take kan tafarkin kulla makirci ga Juyin Juya Halin Musulunci da kuma harkar Musulunci- take so daga al'ummar Iran, ba wai batun makaman kare dangi, ko kuma batun kare hakkokin 'yan'Adam ko kuma demokradiyya…..ba, face dai abin da suke so daga al'ummar Iran da kuma jami'an gwamnati, shi ne mika musu wuya kan dukkan abubuwan da suke so; bayan haka babu wani abin da suke so. Shin Amurka tana da wata alaka ce da demokradiyya? A yau wasu kasashe ne suke da irin wannan demokradiyya da Amurka take so? A halin da ake ciki duk wata gwamnatin da al'ummar kasar suka zaba a ko ina take a duniya, matukar dai ta dan kauce wa abin da sojojin Amurkan suke so komai kashinsa, to tuni wadannan sojojin kamar mahaukacin kare za su fada wa wannan kasa da kuma kokarin kawar da ita, shin ko ba haka lamarin ya ke ba? Ku duba kusa da ku ku gani, shin yaushe ne suka yi imani da demokradiyya? Su dai wadannan mutane a baki ne kawai suke bayyanar da batun demokradiyya, kuma su ma dai sun san cewa al'ummar duniya sun san hakan; sai dai kawai siyasar farfaganda ta duniya a halin yanzu ita ce nanata magana da kuma ci gaba da nanatawa, wannan dai yanayin farfagandar duniya kenan. Dole ne su fadi, su kuma nanata, su sake nanatawa, ko watakila daga karshe wasu mutane za su yarda da su. Alal akalla dai mutane sun riga da sun saba da jin hakan, to amma dai gaskiyar ita ce cewa wadannan mutane ba su imani da demokradiyya ba.

Babu shakka da dama daga cikin gwamnatocin da Amurkan take dasawa da su, ba su ma san ma'anar demokradiyya ba, kai hatta mutanen wadannan kasashe ba su ma san ma'anar zaben jami'an da za su jagorance su ba, amma duk da haka ba su taba nuna damuwarsu kan wadannan kasashe ba. Babu shakka a duk lokacin da suke tuhumar Jamhuriyar Musulunci (ta Iran) da mulkin kama karya, rashin demokradiyya da dai sauransu, -duk kuwa da irin zabubbukan da ake yi a Iran, duk da irin kasantuwan al'umma a fagen gudanar da mulki, duk da irin hukumomi da kungiyoyin tabbatar da 'yancin al'umma, wanda da wuya a samu kasar da take da irin hakan, duk da irin kyakkyawar alakar da take tsakanin al'umma da jami'an gwamnati, duk da irin yadda al'umma suke goyon baya da kuma kare jami'an-, to manufarsu a fili take. Manufarsu dai ba ita ce makaman kare dangi ko kuma demokradiyya ba, don kuwa su ne suka cika wannan yanki da irin wadannan muggan makamai.

A halin yanzu ku duba ku ga haramtacciyar kasar Isra'ila, haka nan akwai wasu guraren ma. Su suka taimaka wa hukumar Saddam, su suka taimaka masa da makamai masu linzami masu cin kilomita dubu ko kuma dubu da dari biyar da kuma makamai masu guba, ko kuma mu ce da taimakonsu ya samu daman kera irin wadannan makamai, duk kuwa da cewa sun riga da sun san cewa hukumar da take mulki a Irakin na kama karya ce.

Matsalar Amurka ita ce suna cewa ne: Ya ku al'ummar Iran! Ku saki hukuma da kuma abubuwa masu tsarkin da kuka yi imani da kuma girmama su, ku nisanci wadannan abubuwa. To babu makawa matukar muka saki wadannan abubuwa da kuma wannan hukuma wacce ta ginu akan dokokin kasa (na addini), wacce kuma cikin wadannan shekaru ashirin da wani abu ta aikata gagarumin abubuwa masu amfani ga al'umma, to ma'anar hakan shi ne cewa Amurkan za ta sami daman shigowa cikin Iran kamar yadda ta kasance lokacin mulkin Dagutu, wanda daman shi ne abin da suke so, duk wani abu kuma kasa da hakan ba za su amince da shi ba. Sai dai kuma idan abubuwa biyu suka hadu musu mai muni a mahangarsu da wanda yafi muni, to za su zabi mai munin ne; wani mutum a kan wani; wata kungiya akan wata; wata kalma akan wata; a yau dai komai ya fito fili ga al'ummomin duniya. A duk lokacin da wani abu ya saba wa ra'ayi da tunaninsu, daga ko ina kuma yake, to tuni za su fitar da maitarsu a fili.

A halin yanzu Amurkawa cikin gururi da ji-ji-da kai - wanda a ganina ji-ji-da-kan nasu ma na wauta da rashin hankali ne, wanda kuma nake ganin da sannu za su raina kansu - sukan fito da da dama daga cikin maganganunsu (abubuwan da ke cikin zukatansu). Bayan jawabin da shugaban kasarmu Sayyid Muhammad Khatami ya yi - inda ya bayyanar da hakikanin matsayarsa, wanda mu daman bai taba buya mana ba, kuma ba wani bakon abu ba ne, don kuwa tun tuni daman mun san shi kuma mun riga da mun san matsayarsa - inda ya bayyana tabbatuwarsa akan jiga-jigan addinin Musulunci da kuma kiyayyarsa ga irin halayen girman kai na Amurka - wanda kowa ya ji hakan- nan take dukkan kafafen farfagandansu suka yi ca a kan wannan jawabi nasa. Alhali kuwa su dai wadannan mutane ne dai a wasu lokuta suke goyon bayansa kan wasu maganganu da ya yi. Yana da kyau a fahimci cewa su matsalarsu ba wai wannan mutum ko wancan ba ne, ko kuma wannan kungiya ko waccan ba ne, face dai lamarin shi ne cewa dai a wannan kasa tamu dai an sami wata hukuma wacce jama'a suka zaba bisa kan radin kansu, kuma akidar su kansu mutanen ba bisa akidar Amurkawan ba.

Ni ba zan iya da'awar cewa gwamnati, ko majalisa, ko kuma sauran jami'an gwamnati, cikin wadannan shekaru sun aikata dukkan abubuwan da suka hau kansu ba, kuma sun sami nasara a dukkan bangarorin ba, a'a. To amma dai a dubi na gaba daya, tun daga majalisa, gwamnati, ma'aikatar shari'a da kuma sauran jami'an gwamnati, dukkansu dai suna kokari wajen tabbatar da wannan jigo ne (hidima wa al'umma da kuma tabbatar da tsarin Musulunci), lalle ba ni da shakka kan hakan. Hakika irin wadannan abubuwa ne Amurkawan ba sa so su gani. Irin wannan hukuma ce wacce ta ginu akan ra'ayin al'umma ne, ba sa so su gani ba wai kawai a wannan yankin ba, hatta ma dai a dukkan duniya, wanda yake gutsure mugun nufinsu da kuma hana su cimma manufofinsu. Kai ba wai kawai a nan ba, irin wannan lamari shi ne yake musu barazana a dukkan kasashen musulmi, wannan lamari dai a fili yake.

Bayan ziyarar da Malam Khatami ya kai kasar Labanon, na gaya masa cewa, duk wata kasar da ka je a duniya, al'ummar kasar irin wannan tarba da mutanen Labanon suka yi maka ita ce su ma za su yi maka, gaskiyar lamarin dai kenan. Shin wani shugaban kasa ne a wannan duniya zai kai ziyara wata kasa ta daban, amma al'ummar kasar su fito da dukkan kauna da shauki suna yi masa maraba? Wannan wani lamari ne kawai da ya kebantu ga Jamhuriyar Musulunci. A ziyarar da na kai kasar Pakistan lokacin ina shugaban kasa, duniya ta sha mamaki; haka nan ziyarar da Malam Hashimi Rafsanjani ya kai Sudan lokacin yana shugaban kasa, dukkanin duniya ta sha mamaki; hakika wannan lamari ne da ba a saba ganinsa ba a urufin kasa da kasa; ba a taba ganin irin hakan ba. Idan kuna iyawa ku nuna min ko da wani misali guda, babu irin wannan misali, wani shugaban kasa ya je wata kasar da ba tasa ba, amma jama'a su fito, suna sumbantar motarsa, su rufe motarsa, suna rera take, suna daddaga hannuwa, suna daddaga hotuna, hakika wannan ya saba wa tunani, wannan yana nuni da kasantuwanku a duniya.

Wasu suna raina kawukansu; wasu kuma suna kaskantar da karfin da suke da shi; wasu kuma suna raina irin gagarumin karfin da wannan al'umma da kuma jami'anta suke da shi, hakika hakan na daga cikin farfagandar abokan gaba. Hakan dai shi ne asalin manufar farfagandar abokan gaba; wannan ba karamin hasara da rashin nasara ba ce! (Idan har kuka fara tunanin haka), to fa shi kenan komai ya kare. Lalle irin wannan farfaganda ba wai kawai yau ne aka fara shi ba, a a tun da jimawa suke ta maimaita hakan; a halin da ake ciki ma dai zan iya tuna da dama daga cikin irin wadannan abubuwa, suna nan a cikin kwakwalwata, sai dai kawai ba na so ne in bata lokaci da wadannan abubuwa. Kuma babbar manufar dai ita ce su sanya ku mika wuya da kuma ja da baya, lalle wannan ba mas'ala ce bakuwa ba, ko kuma mai ban mamaki, lamari ne da ya yi daidai.

Hakika ku dai al'umma ce kuma masu mulki ne bisa yardar al'umma, kuma kuna fadin albarkacin bakinku, kuma kuna bin tafarkinku, kuma kuna kula da abubuwan da suka yi daidai da akidarku, kuma sananne abu ne cewa duk wadanda suke da irin wannan abu, ba za su taba gushewa ba, ba za su taba yin rauni ba. Don haka ne (abokan gaban) suke adawa da irin wannan lamari naku. Wannan lamari ne da ke a fili ga kowa, kuma don hakan ne ya sa suke son ku mika musu wuya da kuma ja da baya.

Ya 'yan'uwana mata da maza madaukaka! Hakika akwai bambamci mai girman gaske tsakanin Majalisar Shawarar Musulunci (ta Iran) da sauran majalisun kasashen duniya, hakan kuwa shi ne Musulunci. Hakan ba abin wasa ba ne fa, yau din nan shekaru dari da hamsin kenan wasu gwarzayen siyasa da addini na al'ummarmu kana wandanda suka fi kowa fice da daukaka suka daga tuta da kuma hukumcin Musulunci sama da kuma wayar da kan musulmi. A saboda haka da dama daga cikin al'umma din sun sadaukar da rayukansu a kan wannan tafarki; mutane irin su Mudarris, Akhund Khorasani, Sayyid Jamal al-Din, lamarin dai haka yake.

Don haka batun cewa siyasa da addini abu guda ne ba bakon abu ba ne a tsakanin al'ummarmu. A daidai lokacin da wasu suke cewa lamarin guda ne wasu kuma cewa suke yi a'a ba haka ba ne. Don haka yana da kyau a fahimci cewa lamarin ba bakon abu ba ne tun shekaru dari da hamsin yake nan. Mahaifin mafi ficen furen wannan kasa ya rasa ransa ne wajen kare wannan tunani; dubban rayuka masu tsarki na wannan al'umma an rasa su ne a wannan tafarki. Ku duba ku gani duk da daukakan da Mudarris ya ke da shi, amma ya ba da rayuwarsa ne wajen kare wannan akida. A hakikanin gaskiya dokokin Iran akan wannan abubuwa suka ginu, duk da cewa wasu sun yi kokarin lalata hakan, wasu sun yi ayyukan da ba su dace ba; wasu kuma ta hanyar dogara da hukumomin kasashen waje sun yi wayon kwace hakan daga hannuwan al'umma. To sai dai kuma a lokacin da Imam mai girma ya zo, ya gina asalin harkar tasa ne akan wannan akida, hakan kuwa shi ne abin da al'ummar Iran suke kauna da kuma so.


Yau dai ba rana ce da in muka juya baya daga wannan nauyi na tabbatar da karfin cikin gida da kuma rikon sakainar kashi gare shi, Allah Madaukakin Sarki, al'umma da kuma tarihi ba za su taba yafe mana ba. Yau dai rana ce da bai kamata a yi rikon sakainar kashi wa wannan lamari ba, don haka ya kamata ku kasance cikin hankulanku.
Kai bari in gaya muku hatta al'ummar kasashen da suka fi sauran kasashe tsame hannayensu daga addini wadanda a halin yanzu suke kewaye da mu, haka suke - duk da cewa ba zan ambaci sunayen wadannan kasashe ba, ku da kanku ku sawwara hakan cikin zukatanku - da za su sami irin wannan dama, su sami mutum irin Imam da kuma fage irin na wancan lokacin a kasashen nasu, su daga tuta, to da kun ga cewa wadannan al'ummomin da kasashen nasu suke cewa babu ruwansu da addini sun juya musu baya, kuma duk wani mutumin da ya kawo batun rashin addini cikin siyasa ko kuma ya yi wani motsi da ke nuni da hakan, to nan take zai gane kurensa. Da kun ga wadannan al'ummomi sun taru karkashin tutan (Musulunci), Musulunci dai haka yake, kuma hakan daidai ne, kuma zai amfani al'ummomin ne, su kansu al'ummomin sun riga da sun san haka. Idan da a ce a yau din nan za mu gudanar da hukumce-hukumce na Musulunci; wato da a ce ni da ku za mu sami dacewar aiwatar da koyarwar Musulunci, to da duk wadannan matsaloli an magance su.

A duk lokacin da aka bar mu a baya, to lamarin dai shi ne cewa ko dai ba mu yi abin da ya dace ba a wannan bangaren, ko kuma ma dai ba mu yi komai ba. Wannan take dai tun shekaru dari da hamsin din da suka wuce musulmai suka bayyanar da shi. To shin yana yiyuwa a juya masa baya haka nan? To wani abu ne aka samu cikin wadannan shekaru dari da hamsin na zubar da jinin dubban mutane masu tsarki - wadannan mutane da suka yi shahada fa, ba mutane haka nan kamar sauran mutane ba, mutane ne masu jihadi, sadaukarwa, madaukaka da kuma jarumai, wadanda suka shigo filin daga kana suka sadaukar da rayukansu - ? To abin da dai aka haifar shi ne; Majalisar Shawarar Musulunci, gwamnatin Musulunci da kuma tsarin Musulunci. Wadannan abubuwa dai su ne abin da aka samar saboda wannan kokari. Bambancin Majalisar Shawarar Musulunci da sauran majalisu shi ne wannan, hakan kuma shi ne ma'anar cewa dole ne hukumci da kuma dokoki su kasance sun yi daidai da koyarwar Musulunci.

Asalin wannan tsari ya dogara ne kan tunanin irin na Musulunci da jiga-jigan Musuluncin; haka nan ma asalin Majalisa da kuma Jagoranci duk sun dogara ne akan wannan asasi. Wata rana Imam ya taba cewa da a ce zan juya baya ga Musulunci, to da al'umma sun yi waje da ni; to ai babu shakka gaskiya ya fadi. Don kuwa mutane sun san Imam ne da Musulunci, saboda irin sadaukarwarsa da kuma kokarinsa wajen tabbatar da tafarkin Musulunci ne ya sa al'umma suka bi shi; dukkanmu, ni da ku duk haka ne. Idan da za mu kauce wannan tafarki, to za mu cutar da kawukanmu ne, to amma dai wannan tafarki zai ci gaba kuma ba zai tsaya ba. Babu shakka (ci gaban) tsarin Musulunci bai ta'allaka da irina ko irinku ba. Wata rana mun ji Imam yana cewa tsarin Musulunci bai ta'allaka da ni ba, a hakikanin gaskiya mun sha mamakin jin wannan kalami na Imam, don kuwa Imam shi ne ya haifar da wannan juyi kuma shi ne wanda ya samar da wannan tsari, kuma lalle rarrabe tsakanin kasantuwan Imam da kuma wannan tsari lamari ne mai wahalar gaske a gare mu; to amma a fili Imam yana cewa kasantuwan wannan tsari na Musulunci bai ta'allaka da shi ba. To a dai dai lokacin da Imam, da dukkan irin wannan girma nasa, kasantuwansa ba ta kasance wajibi ba wajen tabbatar da wannan tsari, to mutum kama na wata magana kuma ya ke da ita kan cewa kasantuwa da kuma tabbatuwar wannan tsari da kuma Musulunci ya ta'allaka ne da ni! A'a lamarin ba haka ba ne, dole ne darurrukan mutane irinmu su kasance fansar wannan addini na Musulunci; mu ba da rayukanmu, dukiyoyi da mutumcinmu don Musulunci ya tsaya da kafafunsa. Wannan dai shi ne abin da makiya suke son ganin bayansa.