Fassarar Hububar Sallar Juma'a ta Jagora Imam Khamene'i:
Juma'a 5 Nuwamba 2004
________________________

Shimfida: A ranar Juma'an da ta wuce (5/11/2004) ne Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Ayatullah al-Uzma Sayyid Aliyu Khamene'i ya jagoranci sallar Juma'an birnin Tehran, inda ya tabo batun Lailatul Kadri, shahadar Amirul Muminina (a.s), batun makamashin nukiliyyan Iran da kuma mas'alar Palastinu. Abin da ke biye fassarar hudubar da Jagoran ya gabatar ne a wannan rana, wanda Muhammad Awwal Bauchi ya fassara.


HUDUBA TA FARKO

Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai

Jagora Imam Khamene'i - Yayin Da Yake Jagorantar Sallar Juma'an

Dukkan godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai, muna gode maSa kuma muna neman taimako da shiriyarSa, mun yi imani da Shi kuma muna neman gafara da kuma dogaro da Shi. Tsira da amincin Allah su tabbata ga MasoyinSa kuma zababbe cikin halittunSa, Mai kiyaye sirrinSa kuma Mai isar da sakonSa shugabanmu kuma Annabinmu Abul Kasim al-Mustafa (s.a.w.a) tare da Alayensa tsarkaka masu shiryarwa musamman Bakiyatullah (Imam al-Mahdi). Amincin Allah ya tabbata ga shuwagabannin musulmi (A'imma) masu kare raunana masu shiryar da muminai.

Ina kiran 'yan'uwana maza da mata masallata da ni kaina zuwa ga tsoron Allah. A hudubar farko ta wannan sallar juma'a ina muku wasicci da tsoron Allah da nesantar abubuwan da Ya hana, ku yi kokarin amfanuwa da abubuwan da ake samu cikin wannan wata na Ramalana da kuma azumin da ake yi a cikinsa don zukatanmu su sami wannan babban matsayi na tsoron Allah, kuma mu zamanto masu takawa na hakika.

Yau dai 21 ga watan Ramalana ne, daga dukkan alamu rana ce ta 'al-Kadr' sannan kuma rana ce ta shahadar Amirul Muminina (a.s). Daren jiya ya kasance daya daga cikin darare uku na shekara masu muhimmanci, dararen da ake tsammanin su ne na 'Lailatul Kadr'. A cikin wannan dare ne Mala'ikun Ubangiji suke sauka, ko kuma Ruhi yake sauka, ko kuma a cikin daya daga cikin dararen nan biyu. Sun ji dadi (sun sami babban rabo) mutanen da suka sami raya ruhinsu da saukowan Mala'ikun Ubangiji. Saukowar Mala'ikun Allah kasa zuwa gare mu mu mutane kamar yadda Yake cewa: "Mala'iku da Ruhi suna sauka a cikinsa da izinin Ubangijinsu saboda kowani umarni", wanda hakan zai taimaka mana samun kusanci da Allah Madaukakin Sarki. Babu kokwanto akwai wasu daga cikin bayin Allah da suka sami falalar daren jiya, sun riski hakikanin daren Lailatul Kadri, mai yiyuwa ne wasu sun ga Mala'ikun Allah. Lalle ku madaukakan al'umma a ko ina kuke kuna daukan dararen 21 da 19 da kuma Insha Allah daren 23 (mai zuwa) a matsayin lokaci mai muhimmanci, ana iya ganin al'ummarmu, matasanmu, mazaje da matayenmu suna da nufin tsarkake da tace zukatansu a wannan dare, (wannan dare) yana tausasa ruhi, azumi ma dai yana taimakawa. Don haka dole ne mu yi fata, mu yi addu'a da kuma kokarin ganin mun amfana da wadannan darare don daukaka kawukanmu da kuma yin salla wanda hakan abu ne mai daukaka mumini, haka nan addu'a ma, daren Lailatul Kadri na haka ne, don haka dole ne mu yi abin da zai daukaka mu. Mu yi kokarin nesanta kawukanmu daga sharan duniya wadanda suka kasance ala ka-kai ga mafiya yawan mutanen duniya. Munanan ayyuka da dabi'un da suka saba wa dabi'un dan'Adamtaka, wuce gona da iri, watsa fasadi da alfasha da kuma zalunci suna daga cikin irin wadannan shara na duniya, don haka ya kamata dararen Lailatul Kadri su nesanta mu daga wadannan abubuwa. Wannan dai dangane da daren Laikatul Kadri kenan.

To amma dangane da shahadar yau (shahadar Amirul Muminina Ali), (muna iya cewa) wannan shahada dai ba wata musiba ba ce da ta faru a wani zamani, to yanzu kuma sai mu dinga tunawa da ita ba, a'a wannan musiba ce ta dukkan lokuta, musibar shahadar Amirul Muminina (a.s), (wallahi an ruguza rukunan shiriya) ba wai hasara ce ta wannan zamani ba kawai, hasara ce ga 'yan'Adam duk tsawon tarihi. Hakan kuwa, saboda Amirul Muminina (a.s) kamar yadda Fatima al-Zahra (a.s) a kan gadon rashin lafiyarta shekara 25 da suka wuce kafin wannan lokacin take gaya wa matayen Madina ne cewa da a ce kun bar Ali ya zamanto halifa da kun ga abubuwan da duniyar musulmi za ta cimma. Abin da Nana Fatima al-Zahra (a.s) din take cewa shi ne: (لسار بهم سيرا سجحا ) daya bude wa jama'a hanyar rayuwa, hukuma ba za ta bari a cutar da al'ummar musulmi ba, babu wata cutarwa komai kashinta da za ta same su, al'amurra za su tafi yadda ake so, kuma za a hana faruwar duk wata cutarwa. Mafi kyaun yanayin hukuma shi ne kada ta cutar da al'umma, za ta kare da kula da rayuwar mutane ta duniya da ta ruhi, wadannan abubuwa dai Fatima al-Zahra (a.s) ce ta fadi a wancan lokaci, kuma yadda yanayi ya kasance kenan.

To yanzu bayan shekaru 25, daga karshe dai al'ummar musulmi sun taru suka dora Amirul Muminina (a.s) akan halifanci. Cikin dan wannan lokaci kuwa wato daga watan Zil'Ka'ada shekara ta 35 zuwa watan Ramalanan shekara ta 40 hijiriyya, kimanin shekaru 4 da watanni 10 kenan, Amirul Muminina (a.s) yayi ayyuka masu yawan gaske. Ya gina jiga-jigan abubuwa, idan ba don wannan takobi da ha'incin wasu ba, idan ba don wannan danyen aiki na Ibn Muljam da mutanen da suka share masa fage ba a boye, da Amirul Muminina ya ci gaba da wannan tafarki nasa, da kuma watakila duniyar musulmi ta lamunta na wasu karnoni. Don haka wannan musiba da aka haifar da ita a wannan rana, ta kasance babbar hasara ga duniyar musulmi da tarihin Musulunci. Haka nan kuma wannan lamari ya nesantar da abin da da zai kare musulmi da Musulunci daga cutar da su, don haka musibar ta kasance ta kowani zamani. Ana iya fadin irin wadannan ayyuka na Amirul Muminina cikin jumla guda, kuma a yau zan yi takaitaccen bayani kan hakan.

Ana iya cewa cikin dan wannan lokaci dai, Amirul Muminina (a.s) ya tabbatar da cewa ana iya gudanar da dukkan koyarwa Musulunci cikin al'umma. Ku duba ku gani, wannan lamari ne mai muhimmancin gaske matukar muka yi dubi gare shi, kuma yana da alaka da rayuwarmu ta yau. (Idan muka duba) za mu ga cewa a lokacin Manzon Allah (s.a.w.a) ya zuwa yadda za a iya an yi aiki da koyarwar Musulunci, adalcin Musulunci, girmama dan'Adam, ruhin jihadi, gina Musulunci da kuma kyawawan dabi'u na Musulunci, to amma abin tambaya a nan shi ne al'ummar musulmi da garuruwansu guda nawa ne? Har zuwa shekara ta 10 dai gari guda ne, wani dan karamin gari mai 'yan dubban mutane. Kai hatta bayan bude garin Makka da Da'ifa ma wasu 'yan wurare ne da kuma arziki mahadudi. Mutane suna fama da talauci, abubuwan da ake da su kadan ne, da haka ne aka tsayar da koyarwa ta Musulunci.

To yanzu shekaru 25 kenan daga lokacin da Manzon Allah (s.a.w.a) ya rasu, kasar Musulunci ta ninnunku, ba wai kashi biyu ko uku ko goma ba, a'a sau darurruka, wato a wannan lokaci da Amirul Muminina (a.s) ya zama halifa tun daga tsakiyar Asiya zuwa arewacin Afirka wato Masar duk suna karkasin ikon Musulunci ne. A lokacin an ruguza manyan dauloli biyu da suke makwabtaka da musulmi wato Iran da Rum. Hukumar Iran da dukkan kasar suna karkashin ikon Musulunci ne, wani sashi mai yawa na Rum na karkashin ikon Musulunci ne. An samu fadaduwa, an samu dukiya mai yawa, talauci da rashi sun kawu. An samu zinariya da dukiya mai yawa, duniyar musulmi ta kasance mai arziki, mutane suna cikin jin dadi da walwala, wasu ma sun sami arziki fiye da bukatarsu.

Watakila wasu su ce lalle koyarwar Musulunci abu ne mai kyau amma fa a wancan lokaci na Manzon Allah (s.a.w.a) da duniyar musulmi ba ta da yawa, to amma bayan fadadar kasar Musulunci, bayan shigowar wasu al'adu na Iran da Rum da dai sauransu, al'ummomi daban-daban sun kasance karkashin lemar Musulunci, to fa wannan koyarwa ba za ta wadatar ba. Mai yiyuwa ne wasu su yi wannan tunani, cewa wannan koyarwa ba za ta iya gudanar da lamurran al'umma ba. To amma Amirul Muminina (a.s) cikin wadannan shekaru biyar, ta hanyar tafarki da ya dauka, ya tabbatar da cewa ana iya gudanar da irin wadannan koyarwa ta Musulunci, wato tauhidi, adalci, daidaitawa tsakanin al'umma, matukar dai aka samu tsayayye kana adalin halifa irin Amirul Muminina. Lalle Amirul Muminina ya tabbatar da hakan a aikace, kuma hakan tarihi ya tabbatar da shi, duk da cewa bayan Amirul Muminina ba a ci gaba da wannan tafarki nasa ba, wannan dai abu ne da yake a fili.

Amirul Muminina (a.s) ya tabbatar da cewar matukar shugaban musulmi, jami'an musulmi suka kuduri aniya suna iya aiwatar da wadannan koyarwa ta Musulunci a aikace komai yawan duniyar musulmi, kuma musulman su amfana da su. Lamarin dai haka yake ko a yau din nan ma.

Wadansu suna riya cewar irin taken Juyin Juya Halin Musulunci da ake rerawa, taken adalci, taken jihadi, taken addini, taken 'yanci, taken dogaro da kai da su ne suka kawo karshen gwamnatin dagutu (a Iran), taken da suka taimaka a kallafaffen yakin shekaru 8 a halin yanzu sun tsufa, abubuwa ne da ba za a iya aikata su a aikace ba. Lalle ba haka ba ne, me yiyuwa ne mu mu tsufa, me yiyuwa ne mu mu rasa irin tsayin dakan da muke da ita, amma wadannan koyarwa suna nan tsaye kyam. Matukar dai muka fuskanci bakar siyasar makiya da farfagandojinsu da imanin da ake bukata, da cikakken jagoranci, to wadannan koyarwa za su iya magance su. Sanannen abu ne cewa ba za a iya kwatanta gudanar da adalci cikin al'ummar da take da mutane dubu 10 zuwa 15 na Madina da adalci cikin al'ummar da ta kai miliyoyin mutane a lokacin Amirul Muminina (a.s) ba.

To yanzu ga wasu daga cikin maganganu da ayyukan Amirul Muminina (a.s) da na tsamo daga cikin dubban abubuwan da a halin yanzu muke karantawa kan rayuwar Amirul Muminina (a.s).

Misali a hudubar farko bayan ya zama halifa lokacin da jama'a suka so yi masa bai'a, amma ya ki amincewa da farko sai bayan matsin lamba daga manya da kanana da kuma manyan sahabbai wadanda suka bayyana cewa babu wanda ya dace da wannan matsayi in ba Aliyu bn Abi Talib ba. A lokacin Amirul Muminina yace musu to mu tafi masallaci, inda suka tafi, ya hau kan mimbari su kuma suka zo suka yi masa bai'a; a wannan waje Amirul Muminina (a.s) ya gabatar da wata huduba inda yayi bayanin matsayinsa (kan halifanci da yadda zai gudanar da shi), daga cikin abin da yake cewa dai shi ne duk wata dukiyar da aka ba wa wani da bai cancance ta ba idan har ya samu dama zai dawo da ita baitul mali. A wancan lokacin dai akwai wasu mutane da suka debi dukiyar al'umma suka ba wa kawukansu (da na kusa da su), to umarninsa dai shi ne wadannan mutane su dawo da wannan dukiya (ga baitul mali) ko da kuwa (لو وجدته قد تزوج بها النساء ) ko da kuwa kun yi aure ne da ita, to zan karbe ta, ko mai kuka yi da ita zan dawo da ita (ورددته) zan dawo da ita zuwa ga baitul mali. Wannan dai shi ne bayanin da ya fara yi kenan. (Kamar yana cewa ne) Ya ku jama'a, Ya ku manyan gari, wannan dai ita ce hanya ta idan kuna so to bisimillah. To amma ina bayan wani dan lokaci (bayan sun amince da hakan) sai wasu suka fara haifar da rikici. Lalle kan dole ne su haifar da rikicin don sun san sun aikata wadannan abubuwan (cin dukiyar al'umma) suka kirkiri tarurruka (suna cewa) a'a me Ali kuma yake yi ne, wato suka fara guna-guni. Daya daga cikin wadannan mutane shi ne Walid bn Ukuba, wanda shi ne gwamnan Kufa a lokacin mulkin Usman. Shi wannan mutumi ya taso ya zo wajen Amirul Muminina (a.s) ya ce: Ya Ali! Akwai fa sharadi cikin bai'ar da muka maka, sharadin kuwa shi ne: ka janye hannayenka daga dukiyar da muka tara lokacin Usman, kar ka sanya ido kan abin da muka tara kafinka, wannan dai shi ne sharadinmu.

Bayan Walid bn Ukuba, Talha da Zubairu ma sun zo, duk da cewa lamarin Walid bn Ukuba da na su Talha da Zubairu daban yake. Don shi Walid bn Ukuba yana daga cikin wadanda ba su jima sosai ba da musulunta, iyalansa dai sun kasance makiya Musulunci ne, sun yaki Musulunci, bayan Musulunci ya yi nasara sai suka zo, kamar sauran Bani Umayya, suka musulunta karshe-karshen rayuwar Manzon Allah (s.a.w.a), amma Talha da Zubairu suna daga cikin na farko-farkon musulunta, suna daga cikin sahabban Manzon Allah (s.a.w.a) na kurkusa.

To Talha da Zubairu, wadanda suna daga cikin manya-manyan Musulunci na wancan lokacin kuma daga cikin sauran sahabban da suka saura, su ma sun zo wajen Amirul Muminina (a.s) da kukansu. Daga cikin kukan su shi ne ka sanya mu martaba guda da sauran mutane wajen raba kudaden baitul mali, ka daidaita mu da sauran mutane (وسويت بيننا وبين من لا يماثلنا) ka daidaita tsakaninmu da mutanen da ba su kai mu ba wajen rabon baitul mali, wannan wani irin abu ne, me ya sa ba mu da wani bambanci, duk kuwa da cewa da takubanmu aka samo (wadannan dukiyoyi), mu ne muka ciyar da Musulunci gaba, mu ne muka wahala, mu ne muka yi kokari to amma yanzu kana daidaita mu da wadanda suka musulunta daga baya, ajamawa. Wannan dai shi ne kukansu, Amirul Muminina (a.s) ya amsa musu. Ni dai ban ga amsar da Amirul Muminina ya ba wa Walid bn Ukuba ba a wajen, tarihi bai nakalto ba, face dai ya je kan mimbari ne ya bayar da amsa mai tsanani. Dangane da Talha da Zubairu kuwa, wadanda sun kasance tsoffin musulmi, da ba za a taba zaton za su kawo irin wannan kuka ba, nan take ya ba su amsa. Daga cikin amsar da ya ba su shi ne cewa ai ba ni ne na kirkiro wanna tafarki (na daidaita tsakanin mutane) ba, ni da ku mun ga cewa haka Manzon Allah (s.a.w.a) yake aikatawa. Ni ban zo da wani sabon abu ba, ni abin da Annabi ya aikata ne na aikata.

Ku duba ku gani wannan ita ce hikimar Amirul Muminina (a.s), wato (kamar yana cewa ne) ni ina so in tabbatar da kafafun wannan akida ne da Manzo ya gina cikin al'umma, kuma hakan kuwa ya yi da a halin yanzu yake fuskantar wadannan matsaloli, wadannan matsaloli kuwa su ne yakukuwa guda uku da ya fuskanta. Amirul Muminina da bayan wafatin Manzon Allah (s.a.w.a), duk da cewa yana ganin halifanci a matsayin hakkinsa, ya yi shiru na shekaru 25, kai ya kan ma tsawata wa duk wanda yake son ta da kayar baya kan wannan batu, to amma a halin yanzu irin wadannan haruffa ne suke fitowa daga bakinsa. Shekaru 25 Amirul Muminina bai ta da kayar baya ba kan lamarin halifanci, to amma a halin yanzu kan wannan batu da bai kai halifanci ba (ya ki yin shiru) don ya sake gina tushen adalci tsakanin mutane, raya tushen koyarwa ta Annabi. A yayin gudanar da wannan koyarwa ne ya fuskanci yakukuwa har guda uku, su ne kuwa Yakin Jamal, Yakin Siffin da Yakin Nahrawan. Ku duba ku gani yadda wannan abu yake da muhimmanci a wajen Amirul Muminina (a.s). Wannan na daga cikin manyan ayyukan Amirul Muminina. Amirul Muminina yana cewa ne kiyaye hakkin mutumin da ya zama dole a kiyaye hakkinsa wajibi ne, (misali) mutum mumini ne, mujahidi ne, ya yi wahala da sadaukarwa, to a matsayinka na shugaba, jami'in gwamnati, wajibi ne ka kiyaye hakkokinsa, to amma idan har wannan mutumin ya yi wani kuskure, ya wuce gona da iri kan hakkokin wasu, to fa wadannan ayyukan alherin da ya aikata ba za su sanya a ki kwato hakkokin sauran mutane daga wajensa ba, wato a takaice wadannan abubuwa guda biyu ne da dole a raba tsakaninsu.

Ana iya samun wani mutumin kirki, wanda ya yi hidimar gaske wa Musulunci da kuma kasarsa, to babu matsala za a kiyaye masa hakkokinsa, to amma fa idan ya aikata wani abin da bai kamata ba, to kiyaye wancan hakki nasa bai kamata ya hana a zartar masa da hukumci akan kuskuren da ya yi ba. Wannan shi ne abin da Amirul Muminina yake nufi kuma ita ce hikimarsa.

Misali akwai wani mawaki mai suna Najashi wanda yana daga cikin mawakan Amirul Muminina, kuma yana daga cikin mawakan da suka taimaka wajen rera wakokin yaki da suka ba wa mabiya Amirul Muminina karfin gwuiwa a yakin Siffin, wato dai yana daga cikin mabiya Amirul Muminina (a.s). To wata rana cikin watan Ramalana sai aka kama shi ya sha giya, aka sanar da Amirul Muminina, nan take sai ya sa a zo da shi a tsayar masa da haddi. Hakan kuwa aka yi aka zo da shi Amirul Muminina ya tsayar masa da haddin shan giya a gaban jama'a. Sai iyalai da 'yan kabilarsa suka zo wajen Amirul Muminina suka ce Ya Amiral Muminina, lalle ka ci mana mutumci, ashe bai kasance daga cikin mabiyanka ba, ya kasance daga cikin 'yan kungiyarka, kamar yadda ake fadi a yau, to amma duk da haka ba zubar masa da mutumci (wato ka yi masa bulala).

A nan sai Amirul Muminina ya ce musu, to ai ni ban yi wani laifi ba, wani musulmi ne ya aikata ba daidai ba kuma haddi daga cikin haddodin Allah ya hau kansa ni kuma na zartar masa da wannan haddin. Daga karshe dai shi wannan Najashin, bayan ya sha wannan bulala (na haddi) sai ya ce to da yake lamarin ya zamanto haka, to yanzu zan koma wajen Mu'awiyya in dinga masa waka, hakan kuwa aka yi, ya bar sansanin Amirul Muminina ya koma wajen Mu'awiyya.

Amirul Muminina dai bai kori Najashi ba, to amma dai ya tafi wannan kuma ya rage masa, da dai ya zauna da ya fi. Ku duba ku gani hikimar dai ita ce wannan, wannan kuma shi ne tafarkin (abin da ya kamata a yi).

Irin wadannan kissosi dai suna da yawa, (misali) wasu mutane 'yan kabilar Banu Asad daga cikin mabiya Amirul Muminina sun zo wajen Amirul Muminina lokacin da wani haddi ya hau kan daya daga cikinsu, suka ce bari mu je wajen Amirul Muminina don a san yadda za a magance wannan matsala. Da farko dai sun fara zuwa wajen Imam Hasan al-Mujtaba (a.s) ne don su kama kafa da shi. Imam Hasan ya ce musu ai babu bukatan mu je tare da ku, ku je kawai ku da kanku. Sai suka tafi wajen Amirul Muminina suka ce Ya Amiral Muminina mu dai ga matsalarmu nan, ka yi duk abin da za ka iya wajen ganin ba a tsayar da wannan haddi ba. Sai Amirul Muminina (a.s) ya ce musu, to shi kenan zan aikata duk abin da ke bisa iko na, don haka sai wadannan mutane suka yi farin ciki suka fito waje. Da suka fito sai Imam Hasan (a.s) ya tambaye su yadda aka yi, sai suka ce alhamdu lillah Amirul Muminina ya yi mana alkawari, sai ya ce musu me Amirul Muminina ya ce, sai suka gaya masa abin da ya ce, sai Imam Hasan ya yi murmushi ya ce musu to shi kenan lalle duk abin da yake bisa ikonsa zai aikata, ku tafi. Bayan nan sai Amirul Muminina ya fito ya sa aka kira wannan mutumi ya tsayar masa da haddi. Sai wadannan mutane suka zo wajen Amirul Muminina suka ce masa Ya Amiral Muminin ya kuma muka ga haka, sai ya ce musu ai tsayar da haddi ba hannuna yake ba (ballantana in ki tsayarwa), haddi hukumcin Ubangiji ne. Ku gani fa Bani Asad suna daga cikin mabiya Amirul Muminina.

Wannan dai ita ce rayuwar Amirul Muminina, haka rayuwarsa take, haka abincinsa yake, haka yake sa kaya, haka 'ya'yansa suke. Wani mai ruwaya yana cewa wata rana na ga Imam Hasan da Husaini suna zaune suna cin abinci, abincin nasu kuwa biredi ne da ganyaye. Sai na ce musu: Ranku ya dade, ku dai yarimomi ne, ku 'ya'yan shugaban kasa ne, 'ya'yan Amirul Muminina ne, duk abincin da ke kasuwa din nan ba ku gani ba ku ka zo kuna cin irin wannan abincin? Sai Imam Hasan da Husaini suka dube shi suka ce: Lalle kan ba ka san wane ne Amirul Muminina ba, ka tafi ka ga irin rayuwarsa. Haka dai Amirul Muminina yake yi da iyalansa.

Na san dai kun san labarin Zainab al-Kubra (a.s) yayin da ta karbi aron wani abu a wajen Abu Rafi'. Irin wadannan labarurruka dai suna da yawan gaske. Haka nan ai kun taba jin lamarin Akil ma ko lokacin da ya zo wajen Amirul Muminina ya bukaci wani, ya bukaci a bashi wani adadi na alkama, inda Amirul Muminina ya dauki karfe mai zafin gaske ya mika masa amma ya ki karba. Haka nan labarin Abdullah bn Ja'afar dan wan Amirul Muminina kuma sirikinsa,wato mijin Zainab (a.s) lokacin da ya zo wajen Amirul Muminina ya ce: Ya Amiral Muminina! Rayuwa ta yi min kunci ta yadda har sai na sayar da kayayyaki na, don haka ina bukatan ka dan taimaka min da wani abu. Amma Amirul Muminina bai amince da hakan ba, inda ya ce masa: shin kana son baffanka ya saci dauki kudin baitul mali ya ba ka.

Wadannan hadisai dai suna nuni ne da kasantuwar Ali na tare da gaskiya a duk inda yake, don haka duk tafarkin da ya dauka, to tafarki ne na gaskiya, wanda kuma ya saba masa ya saba wa Allah da ManzonSa.

Amirul Muminina dai ya tsara tafarki, ya gina yadda hukumar wata al'umma da ta ci gaba, mai fadi, ma'abuciyar arziki za ta kasance. Haka dai al'amurra suka ci gaba da tafiya. A hakikanin gaskiya dai, ta hanyar wannan dabi'a, yana so ne ya tabbatar da cewa ana iya gudanar da wadannan koyarwa ta Musulunci a aikace, sannan kuma ana iya sake raya su cikin halin daake cikin, wannan dai na daga cikin manyan ayyukan Amirul Muminina. Rayuwar Amirul Muminina dai cike take da asalin lamurran ma'anawiyya (na ruhi), asalin adalci, jihadi, kyautata rayuwar al'umma, asalin kwarewa wajen gudanar da lamurran mulki; mun ji kuma muna ci gaba da ji. Dukkan wadannan abubuwa dai suna nuna mana manufar Amirul Muminina ne ta nuna wa duniya cewa ana iya aiwatar da wadannan koyarwa ta Musulunci a kowani irin yanayi. Wadannan koyarwa dai su ne adalic, tauhidi, daidaituwa tsakanin al'umma, kiyaye hakkokin mutane, kula da hakkokin raunana, fada da makiya Musulunci, kare gaskiya da fada da karya, wadannan dai su ne asasin koyarwar Musulunci da za a iya aiwatar da su a kowani lokaci.

To sai dai fa dukkan wadannan abubuwa da muka fadi a yau muna fadi ne, don kuwa wani mutum ne za a iya tunanin zai iya zama kamar Amirul Muminina, ina! Hakika babu wani mutum da zai zama kamar Amirul Muminina.

Imam Sajjad (a.s) wanda shi kansa Imami ne ma'asumi kuma jikan Amirul Muminina, lokacin da ake siffanta masa irin tsananin ibadun da yake yi yana cewa: Ai ba za a taba kwatanta ibada ta da ta Ali ba. To idan har Imam Sajjad duk da irin ibadan nan nasa yana cewa ba za a iya kwatanta ni da Ali ba (to mu fa). Babu shakka akwai dubban kilomitoci tsakanin Imam Sajjad (a.s) da mafi girman mai gudun duniya na cikinmu. Hakika Amirul Muminina ya tabbatar mana da abin koyi, ya nuna mana abin da ya kamata mu yi, ya nuna mana tafarki, don mu isa zuwa ga inda za mu iya.

Don haka tsarin Musulunci tsari ne na adalci, tsari ne na daidaitawa, tsari ne na biya wa al'umma bukatunsu, kuma tsari ne na girmama da kiyaye hakkokin bil'Adama. Kamar yadda kuma tsari ne na fada da zalunci da mai karfi yake wa mai rauni, wannan dai shi ne matsalar bil'Adama duk tsawon tarihi. Su ne dai abubuwan da suke damun mutane tun wancan lokaci har kuma zuwa yanzu. Ku duba ku gani a yau yadda manyan mahandaman duniya suke ikirarin komai nasu ne, suna cutar da al'ummomi saboda irin wannan zalunci da baba-kere, don haka hikimar Musulunci da kuma Amirul Muminina, hikimar gwamnatin Ali ita ce fada da wadannan abubuwa, shin tsakanin al'umma ne, wato wani karfi yana son hadiye maras shi, ko kuma a duniya da kasa da kasa. Wannan dai ita ce hikimar Amirul Muminina.

A karshen wannan huduba bari in sanar da ku wani abu, wannan kuwa shi ne cewa kada kowa ya zaci cewa Amirul Muminina wani muhalli ne na sabani tsakanin sunna da shi'a da dai sauran mazhabobin musulmi, a'a Amirul Muminina dai muhalli ne na hadin kan al'umma ba wai na rarraba su ba. A halin da ake ciki dai mun gano wadansu mutane da suke kokarin haifar da rarrabuwa tsakanin al'umma, wannan wani tabbataccen labari ne, Ya ku 'yan'uwana maza da mata, suna son haifar da sabani na mazhaba, sabani tsakanin shi'a da sunna. (Su kan) rubuta littafi na zagin shi'a, su rubuta littafi na zagin sunna, lokacin da muka bi sawun lamarin sai muka gano cewa daga waje ake shigo da kudaden da ake amfani da su wajen buga wadannan littattafa, daga wani waje na daban suka fito. Lamarin dai haka yake. Kowace mazhaba dai tana da akidarta da kuma dalilanta, a wajen kafa hujja duk wanda ya yi galaba shi kenan, to amma bai kamata a mayar da kasa wajen rikici da tada jijiyoyin wuya ba. Amirul Muminina dai muhalli ne na hadin kai, dukkan musulmi suna girmama Amirul Muminina, shi'a ko sunna. Wata 'yar kungiya karama ta nasibawa ce, wadanda suke kiyayya da Amirul Muminina (a.s) duk tsawon tarihin Musulunci, lokacin Umayyawa da Abbasiyawa, su ne (kawai suke kiyayya da Amirul Muminina), amma sauran al'ummar musulmi sunnansu da shi'ansu suna girmama Amirul Muminina (a.s). Ku duba ku gani za ku ga abubuwan da limaman mazhabobin Ahlulsunna suja fadi kan Amirul Muminina (a.s). Akwai wakokin yabo da aka ce an nakalto ne daga (Imam) Shafi'i ba wai kawai ga Amirul Muminina (a.s) face ga dukkan A'imma ko kuma a ce mafi yawan A'imma. To mu dai akidojinmu na shi'a akan wadannan manyan mutane a fili yake, sai dai su ('yan sunna) sun gagara ganewa. A lokacin da ake tattaunawa ta ilmi, wadannan abubuwa a fili suke kuma za a iya ganinsu. Dalilanmu suna da karfin gaske. Amma abin bakin ciki a halin da ake ciki wasu 'yan tsirarru a Iran da Iraki da sauran kasashen musulmi musamman ma a Iran kokarinsu shi ne haifar da fitina. Ma dai mun san daga inda wadannan mutane suke samun t allafinsu.

To ala kulli halin dai yau ranar shahadar Amirul Muminina (a.s) ne, don haka bari in fadi wasu 'yan jumloli (na juyayi) dangane da wannan musiba.

Sallallahu Alaika Ya Amiral Muminina (amincin Allah ya tabbata a gare ka Ya Amiral Muminina), hakika mutanen da suke (birnin) Najaf da suke kusa da hubbaren Amirul Muminina (a.s) sun ji dadinsu (sun sami babban rabo) don kuwa suna da daman su isar da gaisuwarsu ga Amirul Muminina (a.s) kusa-kusa, to duk da haka dai mu ma muna cewa amincin Allah ya tabbata a gare ka Ya Amiral Muminin, aminci ya tabbata a gare ka Ya shugaban masu tsoron Allah, amincin Allah ya tabbata a gare ka Ya shugaban wasiyyai.

Bayan faruwar wannan musiba (saran da Ibn Muljam da ya yi wa Amirul Muminina) da asubar ranar 19 ga watan Ramalana mutanen garin Kufa da sauran garuruwan da suke gefe wadanda wannan labari ya zo musu sun shiga cikin halin damuwa, don kuwa mutanen Kufa suna tsananin son Amirul Muminina (a.s) don haka suka shiga cikin damuwa, maza da mata, manya da yara musamman ma mafiya kusanci da shi daga cikin sahabbansa duk sun shiga cikin damuwa. Don haka mutane suka taru a kofar gidan Amirul Muminina (a.s). Kamar yadda wata ruwaya ta nuna Imam Hasan al-Mujtaba (a.s) ya fito ya ga jama'a cikin kauna suna son ganawa da Amirul Muminina (a.s), suna son su gaishe shi don haka sai yace musu: Ya 'yan'uwana, ku yi hakuri ba zai yiyu ku ga Amirul Muminina ba saboda halin da yake ciki, don haka ku yi hakuri ku tafi. Sai jama'a suka watse, sai kawai Asbak bn Nawata ne ya saura ya ki tafiya, yana mai cewa duk kokarin da na yi in tafi na gagara tafiya in bar gidan Amirul Muminina, don haka sai na saura. Bayan wani lokaci sai Imam Hasan (a.s) ya fito ya ganni ina tsaye sai ya ce min Asbak ashe ba ka ji na ce jama'a su watse ba, ba za a iya ganin Amirul Muminina (a.s) ba. Sai na ce masa Ya dan Manzon Allah (s.a.w.a), wallahi ba zan iya tafiya ba ne, ba zan iya daurewa in bar wajen nan ba, idan har zai yiyu a barni ko da na dan wani lokaci ne in gana da Amirul Muminina. Sai ya ci gaba da cewa sai aka min izini, sai na shiga na ga Amirul Muminina (a.s) a kwance akan gado cikin rashin lafiya an daure kansa mai albarka, wato an daure inda raunin yake. Ya ce na ga an daure kansa da wani kyalle ja, sai ya ce na gagara ganewa kyallen ne ya fi ja ko kuma fuskan Amirul Muminina (a.s). sai Asbak ya matsa kusa da gadon da Amirul Muminina (a.s) ya ke kwance, a daidai lokacin Amirul Muminina (a.s) ya kan suma ya kuma farfado. To a daya daga cikin lokutan da ya farfadon sai ya kama hannun Asbak ya gaya masa wani hadisi, hadisi ne mai tsawo, daga nan sai ya sake suma. Daga wannan ganawa, babu wani mutum ko shi Asbak din ko kuma wani daga cikin sahabban Amirul Muminina (a.s) da ya sake kai masa ziyara. A wannan dare ne dai wato daren 21 ga watan Ramalana, Amirul Muminina (a.s) ya yi ban kwana da duniya.

Ya Allah! Don Muhammadu da Alayen Muhammadu, ka isar da aminci da rahamarKa ga ruhin Amirul Muminina mai tsarki. Ka sanya mu daga cikin mabiya kuma 'yan shi'ansa. Ya Allah! Ka kiyaye al'ummar musulmi da al'ummar Iran daga sharrin masharranta masu fada da gaskiya. Ka ba wa al'ummar Iran nasara a dukkan bangarori. Ka tada ruhin shahidanmu tare da Amirul Muminina (a.s). Ka tayar da ruhin Imaminmu mai girma (Imam Khumaini) tare da Amirul Muminina (a.s).

(A karshen wannan huduba Ayatullah Khamene'i ya karanta Suratul Ikhlas kafin ya je ga huduba ta biyu)

HUDUBA TA BIYU

Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai

Dukkan godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai, tsira da amincin Allah su tabbata ga shugabanmu kuma Annabinmu Abil Kasim al-Mustafa Muhammad (s.a.w.a) tare da tsarkakan mutanen gidansa musamman ma Aliyu Amirul Muminina da kuma Siddikatul Tahira (Fatima al-Zahra) da jikokin rahama al-Hasan da Husaini shuwagabannin matasan gidan aljanna da Aliyu bn al-Husain da Muhammad bn Ali da Ja'afar bn Muhammad da Musa bn Ja'afar da Aliyu bn Musa da Muhammad bn Ali da Ali bn Muhammad da Hasan bn Ali da Muhammad bn Hasan al-Mahdi (a.s) hujjojinKa akan bayinKa sannan amintattunKa cikin bayinKa. Amincin Allah ya tabbata a kan shuwagabannin musulmi masu kare raunana kuma masu shiryar da muminai. Ina neman gafara ga kaina da kuma gare ku.

A huduba ta biyu zan yi magana ne kan abubuwa biyu kuma zan yi kokari in ga na takaita gwargwado insha Allah kana daga baya kuma in isar da wani sako ga 'yan'uwana larabawa (cikin harshen larabci).

Wadannan abubuwa biyu kuwa, na farko ya shafi surutan da ake ta yi ne dangane da batun makamashin nukiliyya (na Iran), dayan kuwa kan Kudus ne, wato mas'alar Palastinu da kuma zanga-zangar da, da yardar Allah, za a yi ranar juma'a mai zuwa da al'ummar Iran da sauran al'ummomin duniya za su yi.

A hakikanin gaskiya wannan kace-kace na makamashin nukiliyya da 'yan adawa suka haifar da shi wani lamari ne da babu hankali cikinsa. A fili dai ana iya fahimtar manufar Amurka cikin wannan batu. A fili yake sauran wadanda su ma suka shigo cikin wannan kace-nace, imma dai wadanda suke karkashin ikon Amurka ne ko kuma sun tsoma kansu ne cikin damuwa. To koma dai mene ne manufar Amurka da sauran masu adawa da al'ummar Iran da kasarmu da kuma tsarin Musulunci a fili take. (To abin tambaya a nan) shi ne wai shin mece ce manufarsu, zan ba da wannan amsa ne cikin wata 'yar karamar jumla. Su dai wadannan mutane suna adawa ne da duk wani ci gaban da zai sanya wata al'umma ta samu 'yanci (na hakika) su samu dogaro da kansu, to wadannan kasashe masu karfi na duniya da suke son komai ya zama nasu suna gaba da shi. Haka dai 'yan mulkin mallaka suke. Su dai wadannan cibiyoyi (na zalunci) suna ma sauran duniya kallo ne na nufin zalunta da kuma mamaye su, dole ne komai ya kasance a karkashinsu. Tattalin arzikin duniya, kasuwancin duniya, karfin aiki na duniya dole ne su kasance karkashinsu. 'Yan mulkin mallaka dai wasu 'yan kasashe ne, 'yan wadansu ma'abuta karfi ne, su din ma wadansu 'yan kamfanoni ne suke jujjuya su, cibiyoyin tattalin arziki, su ne wadanda suke tsara siyasar da za a gudanar a duniya.

A matsayin misali, idan manyan kamfanonin da suke juya gwamnatin Amurka ta yanzu suna son su sake samun sabuwar hanyar shiga da mallake dukiyar yankin Gabas ta Tsakiya, ko kuma suna son su magance matsalar karyewar tattalin arzikin da suke fuskanta, ko kuma suna son tsoma baki cikin harkokin man fetur din Gabas ta Tsakiya, ko kuma suna son kare hannayen jarin yahudawan sahyoniya ko kuma haramtacciyar kasarsu, a takaice dai su sami bakin magana a yankin, me za su yi, sai su shirya kai wa kasar Iraki hari. Sai su kirkiro wani yaki ko mai hasarar da hakan zai janyo kuwa matukar da za su cimma manufarsu ta tattalin arziki da siyasa, lamarin dai haka yake. Don haka duk wani kokari, duk wani motsi da wata al'umma za ta yi wajen sama wa kanta 'yanci, wadannan 'yan mulkin mallaka suna gaba da shi.

A shirye suke su bude kofar masana'antu, amma ga wa ga, ga wanda zai bi su sau da kafa; a shirye suke su ba da jirgin sama amma ga kasar da ko bude injin jirgin ba za ta yi ballantana ta ga da me aka kera shi, sai dai kawai injiniyoyinsu su zo su bude su tafi da abin da ya baci zuwa kasashensu su gyara, kamar yadda suke yi wa tsohuwar gwamnatin dagutu ta nan Iran. A shirye suke su kafa cibiyar nukiliya ga gwamnatin da take binsu sau da kafa kamar gwamnatin dagutu ta gidan sarautar Pahlawi (ta Iran), don kuwa tana karkashin takalminsu ne, to amma lokacin da aka zo kan Jamhuriyar Musulunci, ina! Ko da wasa. Don sun san a Jamhuriyar Musulunci kan idan har ba a shirye suke su ba da man da ake bukata ba, matasanta, injiniyoyinta, masananta za su zauna dare da rana su kirkiro na'urar da za ta samar musu da mai don su yi amfani da shi (Kabbarorin masallata).

Haka dai yana kona musu rai, wannan ba shi ne abin da suke so ba, don haka suke gaba da hakan. Da kyau, ku duba ku gani, tun lokacin da aka samar da tsarin Musulunci (a wannan kasa) wadannan 'yan mulkin mallaka suka fahimci cewar Jamhuriyar Musulunci babbar barazana ce ga manufofinsu na mamaya. Sun fahimci hakan don haka ne tun ranar farko suke gaba da ita. Ba wai Iran dai ce barazanar ba face dai barazanar shi ne bakon abin da Jamhuriyar Musuluncin ta zo da shi, don kuwa za ta yi kafar ungulu wa da dama daga cikin manufofinsu. Duk da cewa sun san hakan, to amma suna riya cewa ai Jamhuriyar Musulunci ba za ta jima ba. A irin wannan duniya da ilmin kere-kere shi ne akan gaba, dukiya ma akan same ta ne ta wannan hanya, to ya ya za a yi wata kasa da ba ta da irin wannan ilmi da ci gaba, ga kuma takunkumi ko ta ina za ta iya rayuwa, (babu makawa) ita da kanta za ta fadi. Misali, bishiya ce aka hana ta ruwa, aka hana ta shakan iska, da sannu za ta bushe, ba a ma bukatan a sare ta, ita da kanta za ta fadi ta mutu. Wadannan (mutane) dai haka suke zato. Don haka ne tun farko-farkon samun nasarar juyi suke cewa mun ba su watanni biyu, wasu lokuta kuma suka ce shekara guda, wani lokaci kuma su ce shekara biyar, Jamhuriyar Musulunci za ta fadi kasa war-was. Amma ina, sun dankara takunkumin tattalin arziki, takunkumin ilmi da kere-kere, sun kirkiro yaki, sun goya wa abokan gabanmu a yakin baya da dukkan karfinsu don dai a kawar da Jamhuriyar Musulunci, to amma a halin yanzu bayan shekaru 25 sun ga Jamhuriyar Musulunci ta kunno kai ta fito fili daga wadannan abubuwa da suka dora mata, ta tsaya da kafafunta, ta dogara da kanta, tana mai ganin kyakkyawan fata wa kanta a nan gaba.

A bangaren ilmi mun ci gaba, a bangaren kere-kere ta ci gaba, wannan dai wani lamari ne da ba za a iya musanta shi ba, kuma wadannan mutane ma sun fahimci hakan. A wasu bangarori masu muhimmanci mun ciwo lambobin zinare. Idan kuka dubi wannan ilmi na nukiliyya akwai kasashe da dama da suke amfani da mansa, amma kasashen da suke iya samar da wannan mai, wanda akan hakan ne aka haifar da wannan kace-nace, kadan ne, misalin kasashe goma ne kuma Iran tana daga cikinsu. (Kabbarorin masallata)

Ku yi hakuri don babu lokaci. Haka nan dangane da mas'alar gina kasa, misali mas'alar gina madatsun ruwa (dam-dam) wadanda a halin yanzu suke da yawa (a Iran). A lokacin dagutu tun daga farkon lokacin da ilmin gina madatsun ruwa ya shigo wannan kasa har lokacin da aka kawar da gwamnatin dagutu a wannan kasa madatsun ruwan da aka gina ba su wuce goma zuwa sha biyu ba su din ma da taimakon 'yan kasashen waje wasu din ma suna da matsaloli na aiki. To amma bayan nasarar juyin juya halin Musulunci an gina mafi yawa daga cikin madatsun ruwa saba'in da aka tsara za a gina, sauran kuma ana kan hanyar gina su, nan gaba za a gama su a amfana da su. Kamar yadda rahotanni da aka aiko min suke nunawa an gina madatsun ruwa manya da kanana, kuma masanan cikin gida ne suka gina su, wannan ya sanya mu daya daga cikin kasashe biyar ko shida na duniya. A duk duniya kasashe 5 ko 6 ne suke da karfin gina irin wadannan madatsun ruwa da irin wannan shakali sannan kuma masu girma.

A bangaren sana'anta kayayyaki soji, a bangarorin masana'antu daban-daban (duk dai mun ci gaba), haka nan a bangaren al'adu, a yau duniya, duk da cewa akwai wadansu 'yan ku ci ku bamu da suke son yin zagon kasa wa kafafun jiga-jigan al'adunmu, asalin al'adun Musulunci da falsafar Musulunci da ilmummukansa sun watsu, sun amfanar da mutane masu yawan gaske.

A halin yanzu muna iya ganin Jamhuriyar Musulunci ta taso da kuma fitowa daga abubuwan da aka jibga mata aka. A da dai (makiya) suna fatan wadannan abubuwa da suka dora mata za su danne ta amma ina sai suka samu tsayayyun al'umma da matasa masu sadaukarwa wadanda suka mike tsaye suka yi watsi da wadannan abubuwa, wannan abu ne ya bata wa makiya rai. A halin yanzu suna tuhuma da cewa suna su ne su kera makaman kare dangi. Ina, mu ba ma da wannan tunani. A lokuta da dama na sha fadi cewa makaman kare danginmu su ne wadannan al'umma tamu. Makaman kare danginmu shi ne wadannan matasa, don haka ba ma bukatan wani makamin kare dangi kuma. Al'ummar da take da irin wadannan matasa muminai, al'ummar da take da hadin kai da bakin magana guda, ai ba ta bukatuwa da makaman kare dangi. Makaman kare dangi, kera su, ajiye su da kuma amfani da su, kowani guda daga cikin wadannan abubuwa na da nasa matsalar. Tuni kuma mun riga da mun sanar da ra'ayin shari'armu dangane da wadannan makamai, wannan dai a fili yake kuma kowa ya san hakan. Babu wani abin ta da jijiyan wuya kan wannan lamari, kawai suna damun kansu ne su ma dai sun sani cewa Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta samu ci gaba, wannan shi ne ya sa suke bakin ciki, wannan dai shi ne yadda lamarin yake. Al'ummar Iran ta san hakan duk da cewa ya kamata ta sake sani. Makiya sukan yi fushi ne kan wani abu (na ci gaban kasarmu) don haka dole ne al'ummarmu ta kasance cikin hankalinta. Makiya dai suna bakin ciki da hadin kan dake tsakanin al'ummarmu don haka suke kokarin ganin bayan wannan hadin kai. Haka nan makiya suna bakin ciki ganin cewa manyan jami'an gwamnatin (Iran) ra'ayinsu guda ne kan jiga-jigan mas'aloli. A duk lokacin da suka ga shugaban kasa, shugaban majalisa, shugaban ma'aikatar shari'a da sauran manya-manyan jami'an gwamnati suna fadin kalma guda kan wata mas'ala (ba tare da sabani ba), zuciyarsu ta kan yi kuna, don kuwa abin da suke so shi ne samun rikici da sabani tsakaninsu. Cikin shekara guda zuwa biyun da suka wuce sun fara watsa taken samun gwamnatoci biyu (a cikin kasa) kuma wasu ma daga cikin gida su ma suna yada wannan take. Abin da suke nufi da hakan shi ne a samu rikici da ta da jijiyoyin wuya tsakanin manyan jami'ai kan jiga-jigan mas'alolin kasa. A fili sun bayyana haka, wannan dai shi ne abin da suke nufi, idan kuwa ba haka nan ne ba, ai daman babu yadda za a yi a samu cewar jami'an wata kasa suna da ra'ayi guda kan dukkan mas'aloli, wannan abu ne da ba zai yiyu ba. Wannan dai ba shi ne abin da suke so ba, abin da suke so shi ne a samu ta da jijiyoyin wuya tsakanin jami'ai kan manyan mas'alolin da suka shafi kasa. Abin da ke daga musu hankali shi ne samun muminan jami'ai wadanda suke son Musulunci da son yi hidima wa al'umma, wannan shi ne abin da ba sa so. Ransu na baci idan har suka ga al'umma suna goyon bayan jami'ansu. Suna bakin ciki saboda ganin matasanmu suna da ruhin jihadi, ko kuma kasantuwan matasanmu muminai ne, ko kuma don matasanmu suna halartar tarurrukan addini da wajajen ibadu, dukkan wadannan dai suna bata musu rai; ba sa jin dadin hakan. Ku duba ku ga yadda matasanmu suka fito kwansu da kwarkwatarsu don halartar ayyukan ibadu na daren Lailatul Kadri, cikin son juna da kaunar Ubangiji, to wannan shi ne abin da makiya ba sa son gani. Alhamdu lillah, al'ummarmu suna cikin hankalinsu, amma dai duk da haka su kara kaimi. Makiya suna so ne su haifar da fitina a cikin Iran, abin da suke so shi ne kada a samu zaman lafiya na siyasa a cikin Iran, abin da suke so shi ne wannan ya rike wuyan wannan, wancan ya rike wuyan wancan. Abin da suke so kenan kuma dukkan kokarinsu yana karewa ne wajen cimma wannan manufa. Don haka dole ne kowa da kowa ya zamanto cikin hankalinsa. Wannan dai dangane da mas'ala ta farko kenan.

Mas'ala ta biyu ita ce mas'alar Palastinu. Ku sani cewa zanga-zangar da za ku yi, da yadar Allah, ranar juma'a mai zuwa na da muhimmacin gaske, don haka kada ku yi masa rikon sakainar kashi. Akwai dai wasu abubuwa guda masu muhimmanci cikin wannan mas'ala ta Palastinu, wadanda zan yi ishara da su a bangaren hudubar larabci (don 'yan'uwanmu larabawa) da zan yi daga karshe. Wadannan abubuwa uku dai ba za su taba gushewa ba daga shafukan tarihi.

Abu na farko shi ne zalunci da kisan gillan rashin tausayi da sahyoniyawa suke wa Palastinawa. Wannan lamari zai ci gaba da zama cikin tarihi. Misali ku duba ku ga a duk lokacin da wani yaro Bapalastine, wanda daman yana cikin mawuyacin hali, ya kai harin kunar bakin wake kan yahudawa 'yan ka-ka gida, yadda sojojin yahudawa suke rusa gidan shi kansa wannan saurayi, da ya yi shahada, na iyayensa, duk su rusa su bayan sun azabtar da iyayensa (masallata suka rera taken la'antar haramtacciyar kasar Isra'ila)

Da karfin soji, ta hanyar amfani da tankunan yaki, sukan shiga garuruwa da sansanonin 'yan gudun hijira, sannan kuma sukan kai hare-hare kan gidajen mutane, su ruguza gidaje da gonaki, a wasu lokuta ma sukan kashe duk wanda suka samu. A halin da ake ciki ma kisan gilla, kashe yara da matasan Palastinwa, mata da tsoffi ya zama ruwan dare, wannan kuwa abu ne mai ban mamaki da ta da hankalin. Don haka babu kokwanto wannan abu zai ci gaba da zama cikin shafukan tarihi. Wannan dai shi ne abu na farko.

Abu na biyu kuma da zai ci gaba da zama cikin tarihi shi ne hakuri da tsayin dakan da Palastinawa suke yi, wannan ma zai ci gaba da zama cikin tarihi. (Ku duba ku gani fa) wata al'umma wacce aka ritsa da ita ta ko ina, makiya ne ta ko ina, amma duk da haka suka tsaya kyam, duk da wahalhalun da aka sa su a ciki, na yunwa, ruguza gidaje da gonaki, rashin aiki duk da haka suka tsaya kyam. Mu fa fahimci cewa al'ummar Palastinu ba wai 'yan jam'iyya ko kungiya guda ba ne, amma (idan ka dube su) mazansu da matansu, manya da yaransu sun zama daya kuma da dukkan karfinsu suke fuskantar makiya, Allah Ya ja zamaninku Palastinawa! Allah Ya ja zamaninku Palastinawa. Lalle kun tabbatar da cewa ku al'umma ne ma'abuta gwagwarmaya. Wannan ma dai zai ci gaba da zama cikin tarihi.

Abu na uku kuma, shi ne rikon sakainar kashin da duniya take wa wannan lamari. Mu dubi jami'an kasashen Turai (da suke nuna cewa) su ma'abuta kare hakkokin bil'adama ne, (wadanda suke nuna cewa) zukatansu suna tsananin kaunar kare hakkokin bil'Adama, amma a idanuwansu wadannan abubuwa suke faruwa, sai dai a mafiya yawan lokuta ba abin da suke cewa, a wasu lokuta ma sukan goyi bayan wadanda suka yi zaluncin ne, lalle wannan abu ne mai ta da hankali. Amurka kan ba'a ma magananta don ita ma tana da hannu cikin wannan zalunci. Hannayen gwamnatocin Amurka cike suke da jinin al'ummar Palastinu. Da dai a ce za a kafa wata kotun da za ta yi shari'ar zaluncin da ake wa Palastinawa, to wadanda za a tuhuma ba wai kawai Sharon da sahyoniyawa ba ne, face dai gwamnatocin Amurka ma za su kasance a sahun farko na wadanda za a tuhuma. Don haka Amurka dai ba ma abin da za a yi magana a kanta ba ne, wadanda ake maganarsu dai su ne sauran kasashen duniya, Majalisar Dinkin Duniya, kasashen Turai, wadanda suke maganan kare hakkokin bil'adama. A hakikanin gaskiya dai wadannan mutane ba su ma san ma'anar hakkin dan'Adam ba kuma ba sa ma girmama shi.

Babban abin bakin cikin dai shi ne shirin da kasashen musulmi suka yi, wannan shi ne abin mamakin.

To abin tambaya a nan shi ne mene ne abin yi, mene ne ya hau kan sauran al'ummomi. To a nan dai tasirin ranar Kudus zai iya shigowa. Wato su fito kan tituna suna rera take, su nuna wa wannan al'umma (ta Palastinu) ma'abuciyar gwagwarmaya da tsayin daka cewa mu magoya bayanku ne, duk da cewa dai gwamnatocinmu suna hana mu mu kasance tare da ku ko kuma mu taimaka muku, to amma ku san cewa zukatanmu suna tare da ku, babu makawa hakan zai karfafa zukatansu. (Kabbarorin masallata)

(Daga nan sai Jagora Imam Khamene'i yaci gaba da hudubar tasa da harshen larabci don amfanuwar sauran al'ummar larabawa, inda ya tabo mas'alolin Palastinu da Iraki)

Bayan gama hudubar Jagora ya karanta Suratul Ikhlas daga nan ya cika hudubar tasa da cewa: Wassalamu Alaikum Wa Rahmatullahi Ta'ala Wa Barakatuhu.