Ci Gaban Jawabin Jagora A Ziyarar Da Ya Kai Garin Waramin

Lalle abin da a yau yake da muhimmanci a matakin farko a fahimta, shi ne cewa wannan kokari na abokan gaba dai ya ginu ne akan rauni, don kuwa sun san cewa ba za su iya fuskantar wannan al'umma ta Iran da wannan imani da hadin kan da take da shi ba. Don haka ne tun da farko suke son ganin sun kawar da wannan hadin kai sannan kuma su samar da gibi cikin imanin al'umma, don su sami damar cimma burorinsu akan al'ummar Iran; to amma ina, al'ummar Iran dai za ta ci gaba da kiyaye wadannan abubuwa masu girma nata.

Akwai wasu mutanen kuma da suke kokarin sanya al'umma din su yanke kauna, wannan kokarin kuwa sukan yi shi ne a wasu lokuta da fatar baki a wasu lokutan kuma a aikace. Ayyukan wadansu dai ya kan sa al'umma din su yanke kauna, wadansu sukan yi hakan ne ba da gangan ba, wadansu ma ba su san me suka aikata ba, wadansu kuma sukan gafala ne, ta wadannan ayyuka na su sai su sanya al'umma yanke kauna; wannan ma dai wani babban laifi ne kuma hidima ce ga abokan gaban wannan al'umma.

A gaskiya dai yanke kauna ba shi da muhalli, al'ummar Iran dai ba su da wani abin da zai sa su yanke kauna. Don me ya sa al'ummar Iran za ta yanke kauna, a matsayinta na al'umma madaukakiya, wannan kasa mai dimbin arziki, kasar da take da yanayi mai kyau na aiki, hidima da kokari, kasar da take da irin wannan karfi na matasa? Jami'an gwamnati dai suna nan suna ta kokarin tsara tsare-tsare wajen ci gaban kasa, kuma suna aikata abubuwan da suka cancanci yabo. Lalle mutanen da suke son haifar da yanayin yanke kauna tsakanin al'umma, suna kara yawan matsalolin da ake da su ne, suna sa a mance da irin gagaruman ayyukan da aka yi wa kasa ne. A halin yanzu dai an gudanar da ayyuka masu yawa da muhimmancin gaske a duk fadin kasa, sai dai kuma abin da aka yin din kadan ne idan aka kwatanta da abin da ya kamata a aikata, kamata ya yi a ce an aikata sama da haka.

Babu shakka ban amince da yadda wasu sassa na gwamnati da kuma wasu jami'ai suke gudanar da ayyukansu ba, to sai dai kuma ina ganin ba dole ba ne in nuna wannan rashin amince da yarda a gaban al'umma gaba daya, saboda babu wani amfani ga hakan. To amma duk da haka, na kan tunasar da wadannan jami'ai da kuma nuna musu abin da ya kamata su yi wajen gyara ayyukansu da kuma gudanar da su kamar yadda ya kamata. To sai dai kuma akwai lokacin da wani zai ga wani jami'i ba zai iya yin aikin da aka dora masa ba, to wannan dai wani bahasi ne na daban; jami'ai dai suna nan suna gudanar da ayyukansu kuma ayyukan da suke gudanarwa din ma ayyuka ne masu kyau abin yabo. Akwai wadansu mutane kuma da suke kokarin take hakkokin jami'an, dole ne a kawo karshe wannan lamarin, misalin hakan kuwa shi ne batun tsadar kayayyakin da ake fuskanta cikin 'yan kwanakin nan.


Wadannan mutane cewa suke wai dakarun Amurka dakaru ne da ba za a iya ja da su ba, sun tabbatar wa zukatansu cewa Afghanistan ta gagara ja da su, haka ma kasar Iraki. To sai dai abin da ba sa fadi shi ne irin ha'inci da wasu suka yi (da ya kawo faduwan wadannan gwamnatoci); ba sa fadin wasu irin gwamnatoci ne a wadannan kasashe; ba sa fadin yadda al'ummomin wadannan kasashe suka kosa da wadannan gwamnatoci nasu na kama-karya; kamar yadda kuma ba sa fadin irin sadaukarwa da tsayin dakan da al'ummar Iran suke nunawa wajen kare mutumcin Musulunci da kuma gwamnatin Musuluncinsu. Wadannan mutane dai duk ba sa fadin wadannan abubuwa, abin da kawai ya dame su shi ne razanar da mutane.

Wannan lamari na tsadar kayayyaki dai ba shi daga cikin siyasar gudanarwa na gwamnati da na jami'ai, ni na san cewa wannan lamari ya kasance abin da ke ta da hankulansu. Don haka dole ne abi sawun wannan lamari da kuma ba da himma gaske wajen magance shi, muma dai na ba da umarni kan hakan. Shugaban kasa, shugaban ma'aikatar shari'a da sauran jami'ai duk sun nuna damuwarsu kan wannan batu kuma sun ba da himma wajen magance shi, mu ma dai mun bukace su da su yi dubi cikin wannan matsala don magance su.

A bisa tsari dai cibiyoyi daban-daban ne ake ba su izinin mu'amala da farashin kayayyaki da kuma yin hidima, to amma (abin bakin cikin shi ne) kansu kawai suke dubi, ba su dubin amfanin dukkan al'umma, wannan dai shi ne yake kawo wannan matsala. Don haka dole ne a sanya idanuwa da kuma kula da wannan lamari. Ba ma inkarin cewa akwai matsaloli daban-daban, to amma ba ya kamata wadannan matsaloli su zamanto kafar ungulu wajen gudanar da manyan ayyuka masu amfanar al'umma. A halin yanzu akwai ayyuka da daman gaske da aka aikata, kuma da yardar Allah, a nan gaba ma akwai wasu da yawan da za a aikata.

Haka nan kuma a dabi'ance dole ne al'umma su bukaci jami'ai su gudanar musu da wasu ayyuka, ni dai na yi imani da kuma yarda da wannan ra'ayi na al'umma su bukaci wani abu daga wajen jami'ai ta hanyar wakilansu a majalisar shawarar Musulunci ko malamai ko kuma masu magana da yawunsu; babu matsala wajen neman wani abu, don kuwa bukata wani abu ne na daban sannan tabbatar da ma'anar hakan cikin kwakwalan al'umma ta hanyar ba ta dace ba, kamar yadda wasu suke yi, shi ma wani abu ne na daban. A yau din nan dai, abin bakin ciki, shi ne akwai wasu mutane da suke bayyanar da siyasa ta gaba daya ta gwamnati kamar yadda Amurkawa suke bayyanarwa, suna bayyanar da maganganu kamar yadda jami'an Amurka suke bayyanarwa, suna kallon al'ummar Iran kamar yadda Amurkawa suke ganinsu, su dai wadannan mutane ko dai suna yin hakan ne bisa gafala ko kuma bisa ha'inci, daya ne dai cikin biyu. Don haka ya zamo wajibi akan mutanen da suke da kafafen magana da isar da sako su yi hankali, sannan kuma su kula da manufofin wannan al'umma ma'abuciyar daukaka daga burorin wadannan abokan gaba da ba su san komai ba face kansu da manufofinsu.

A halin da ake ciki abin da Amurka take son haifarwa shi ne wani irin nau'i na mulkin kama karya a duniya; sai dai kuma sun mance da cewa al'ummomin duniya ma'abuta 'yanci ba za su taba amincewa da hakan ba kuma ma za su fuskanci wannan kama-karya da aka samar da shi da karfin bindiga da kuma ganin bayansa. Al'ummar da take da 'yanci da daukaka, ba za ta taba amincewa da mulkin kama-karya ba, kamar yadda al'ummar Iran ba su amince da gwamnatin dagutanci ta Shah ba, to ina ga mulkin bakin haure kuma!

A yau din nan ku dubi kasar Palastinu ku ga abin da gwamnatin 'yan fashi ta yahudawan sahyoniya take aikatawa, wannan dai wata alama ce ta tursasawa da kuma amfani da karfi. Haramtacciyar kasar Isra'ilan dai ta'addanci take aikatawa akan al'ummar Palastinu wadanda su ne asalin ma'abuta wannan kasa, a waje guda kuma ga Amurka nan a fili tana goyon bayansu. Wadannan mutane dai su ne a yau din nan suka isa kasar Iraki, suka kallafa musu mulkinsu kana kuma suke aikata duk wani nau'i na amfani da karfi da tursasawa a kansu, suna masu tunanin cewa za su iya cimma manufofinsu. To amma ko shakka babu ba za su kai ga ko ina ba, kuma al'ummar Iraki ba za su taba amincewa da hakan ba. Kamar yadda kuma shakka babu wannan buri na kama-karya a duk fadin duniya da Amurkan take son aiwatarwa ba zai yi nasara ba.

Don haka ina kira ga al'ummar Iran madaukaka ma'abuta imani da kuma jami'an gwamnati da su yi hankali da kuma lura da ayyukansu. Kamar yadda a farkon shekara na bukaci jami'ai, sannan kuma a lokuta daban-daban na sha gaya musu, wajibi ne su ba da himma wajen ayyukan kyautata jin dadin al'umma. Haka nan kuma ina kira ga hukumomin kasa masu gudanarwa wajen gudanar da ayyukan yin hidima da kuma amfanin al'umma bugu da kari kan kauce wa muggun amfani da iko wajen cimma manufofi na daidaiku, sannan kuma ina kira ga majalisar shawarar Musulunci wajen biyan bukatun al'umma ta hanyar samar da wasu dokoki masu amfani ga al'umma, da kuma rage tattaunawa kan wasu abubuwa na sabanin siyasa da ba da himma wajen magance muhimman abubuwan da suke damun al'umma. Dole ne a soke izinin da wasu hukumomi suke da su da suke sanya kayayyaki su yi tsada. Haka nan kuma ina kira ga ma'aikatar shari'a a ta yi taka tsantsan wajen gudanar da hukumci akan wadanda suke saba wa dokokin kasa, kamar yadda kuma dole ne hukumomin 'yan sanda da sauran jami'an tsaro su ma su yi taka tsantsan wajen gudanar da ayyukansu.

Wannan al'umma dai ta mika dogaro da kuma yardarta ne ga hukumomin da suka yarda suka su dau nauyin yin hidima wa al'umma karkashin tsarin Musulunci; don haka ya hau kan wadannan hukumomi su kiyaye wannan amana ta al'umma, kuma da yardar Allah hakan ne zai kasance. Da ikon Allah, farkawa da kuma karfafawar tabbataccen imani wannan al'umma, jami'an gwamnatin wannan kasa ba za su taba barin Amurka ta cimma buri da manufofinta a wannan kasa ba.

Har ila yau ina sake mika godiya da jinjinawa ta gare ku Ya ku al'ummar garin Waramin madaukaka da sauran al'ummomin yankuna daban-daban na wannan yanki tun daga Karjak, Bakir Abad da Jawad Abad da kuma madaukakan al'umman Pakdosht, saboda irin wannan kauna da imani naku, kuma ina cikin farin cikin cewa Allah Madaukakin Sarki Ya bani wannan dama ta ziyartarku a yau, duk da cewa dai kun kasance cikin wannan zafin rana, amma dai duk da haka kun yi hakuri. Ina rokon Allah Ya sanya ku cikin kula da kiyayewa na Bakiyatullah (Imam al-Mahdi), rayukanmu su kasance fansa gare shi.

Wassalamu Alaikum Wa Rahmatullahi Wa Barakatuhu.