Bukatun Kasar Amurka Akan Jamhuriyar Musulunci ta Iran

Ya ku 'yan'uwa maza da mata! Ku 'yan majalisa ne kuma 'yan siyasa; me yiyuwa ne halin da ake ciki yanzu ya kasance a fili ga da dama daga cikinku, to amma dai abin da Amurka a yau - wacce take kan tafarkin kulla makirci ga Juyin Juya Halin Musulunci da kuma harkar Musulunci- take so daga al'ummar Iran, ba wai batun makaman kare dangi, ko kuma batun kare hakkokin 'yan'Adam ko kuma demokradiyya…..ba, face dai abin da suke so daga al'ummar Iran da kuma jami'an gwamnati, shi ne mika musu wuya kan dukkan abubuwan da suke so; bayan haka babu wani abin da suke so. Shin Amurka tana da wata alaka ce da demokradiyya? A yau wasu kasashe ne suke da irin wannan demokradiyya da Amurka take so? A halin da ake ciki duk wata gwamnatin da al'ummar kasar suka zaba a ko ina take a duniya, matukar dai ta dan kauce wa abin da sojojin Amurkan suke so komai kashinsa, to tuni wadannan sojojin kamar mahaukacin kare za su fada wa wannan kasa da kuma kokarin kawar da ita, shin ko ba haka lamarin ya ke ba? Ku duba kusa da ku ku gani, shin yaushe ne suka yi imani da demokradiyya? Su dai wadannan mutane a baki ne kawai suke bayyanar da batun demokradiyya, kuma su ma dai sun san cewa al'ummar duniya sun san hakan; sai dai kawai siyasar farfaganda ta duniya a halin yanzu ita ce nanata magana da kuma ci gaba da nanatawa, wannan dai yanayin farfagandar duniya kenan. Dole ne su fadi, su kuma nanata, su sake nanatawa, ko watakila daga karshe wasu mutane za su yarda da su. Alal akalla dai mutane sun riga da sun saba da jin hakan, to amma dai gaskiyar ita ce cewa wadannan mutane ba su imani da demokradiyya ba.

Babu shakka da dama daga cikin gwamnatocin da Amurkan take dasawa da su, ba su ma san ma'anar demokradiyya ba, kai hatta mutanen wadannan kasashe ba su ma san ma'anar zaben jami'an da za su jagorance su ba, amma duk da haka ba su taba nuna damuwarsu kan wadannan kasashe ba. Babu shakka a duk lokacin da suke tuhumar Jamhuriyar Musulunci (ta Iran) da mulkin kama karya, rashin demokradiyya da dai sauransu, -duk kuwa da irin zabubbukan da ake yi a Iran, duk da irin kasantuwan al'umma a fagen gudanar da mulki, duk da irin hukumomi da kungiyoyin tabbatar da 'yancin al'umma, wanda da wuya a samu kasar da take da irin hakan, duk da irin kyakkyawar alakar da take tsakanin al'umma da jami'an gwamnati, duk da irin yadda al'umma suke goyon baya da kuma kare jami'an-, to manufarsu a fili take. Manufarsu dai ba ita ce makaman kare dangi ko kuma demokradiyya ba, don kuwa su ne suka cika wannan yanki da irin wadannan muggan makamai.

Matsalar Amurka ita ce suna cewa ne: Ya ku al'ummar Iran! Ku saki hukuma da kuma abubuwa masu tsarkin da kuka yi imani da kuma girmama su, ku nisanci wadannan abubuwa. To babu makawa matukar muka saki wadannan abubuwa da kuma wannan hukuma wacce ta ginu akan dokokin kasa (na addini), wacce kuma cikin wadannan shekaru ashirin da wani abu ta aikata gagarumin abubuwa masu amfani ga al'umma, to ma'anar hakan shi ne cewa Amurkan za ta sami daman shigowa cikin Iran kamar yadda ta kasance lokacin mulkin Dagutu, wanda daman shi ne abin da suke so, duk wani abu kuma kasa da hakan ba za su amince da shi ba. Sai dai kuma idan abubuwa biyu suka hadu musu mai muni a mahangarsu da wanda yafi muni, to za su zabi mai munin ne; wani mutum a kan wani; wata kungiya akan wata; wata kalma akan wata; a yau dai komai ya fito fili ga al'ummomin duniya. A duk lokacin da wani abu ya saba wa ra'ayi da tunaninsu, daga ko ina kuma yake, to tuni za su fitar da maitarsu a fili.



Cin Zali da Babakeren Amurka a Kasar Iraki Bayan Faduwar Gwamnatin Saddam:

Hakika wadannan mutane sun cutar da al'umma. Sun shiga cikin gidajensu. Hakika irin wadannan abubuwa suna sosa rai. Sun shiga gidajen mutane, su kame mai gida su sa masa sarka a gaban iyalansa, su rufe masa kai kana su sa masa sarka.Daga nan kuma su ci mutumcin mutum da kuma yi masa barazana saboda kawai wani mutum ya zarge shi da wani abu, ko kuma sun gano wani abu na zargi tattare da shi. Ashe wadannan abubuwa ba abu ne da ya kamata a yi dubi cikinsu ba? Su sanya wa balarabe sarka ta baya su rufe musu kawuka, kana kuma su umarce su su kwanta a kasa su kuwa suna tsaye a kansu da bindigoginsu. Sojojin bakin haure sun shigo cikin wata kasa. Ashe hakan ba karamin bala'i ba ne? Shin akwai wani mutum da zai iya gyara akan wannan lamari? Hakika wannan lamari ne da yake da muhimmanci.

Sojojin Amurka suna cajin matan larabawa masu hijabi. Matan larabawa wadanda suke sanye da hijabi, manyan riguna da kuma mayafi, wadanda suka rufe jikinsu tun daga sama har kasa. To amma a samu wani matashin sojin Amurka wanda ba a ma san ko shi wane ne ba, yana cajin wadannan mata wai don gano ko suna dauke da bama-bamai. Shin wannan shi ne ma'anar hakkin dan'Adam? Shin wannan shi ne nuna kula da kuma girmama dan'Adam? Shin wannan shi ne ma'anar kiyaye hakkokin dan'Adam da wadannan makaryata suke ikirarin karewa? Hakika irin wannan cin mutumcin ba zai iya gushewa ta hanyar neman afuwa kawai ba. Sun kai musu hari, amma suna cewa ku yi hakuri mun yi kuskure ne. Hakan suka yi a kasar Afghanistan.

Babu makawa wannan aiki na Amurka a kasar Iraki ta tabbatar wa duniya cewa ita kasa ce mai bakar aniya, kamar yadda daya daga cikin shuwabannin Amurka ya lakaba wa wadansu kasashe na duniya. Kasa mai bakar aniya ce za ta aikata abin da Amurka ta aikata a kasar Iraki. Hakan shi ne abin da kasa mai bakar aniya za ta iya aikatawa ga 'yan Adam, ga zaman lafiya da kuma tabbatuwar wata kasa ta daban. Sun tabbatar wa duniya cewa su ne "Kusurwowin Shaidanci" (Axis of Evil) na hakika. Amurka ta tabbatar wa duniya cewa ta cancanci sunan nan da shugabanmu Imam Khumaini (R) ya sanya mata na "Uwar Shaidanu". Hakika Amurka ita ce uwar shaidanu.