Ci Gaban Hudubar Imam Khamene'i Kan Iraki

Nasarar soji (a Iraki), duk da dai akwai alamomin tambaya da dama kanta, bata kasance nasara ta gaba daya ba. Hakika Amurkawa sun yi hasarori da kuma rashin nasara a wannan yaki da Iraki, watakila ba za su fahimci haka ba, to amma shakka babu, nan gaba kadan za su ga tasirin wannan rashin nasara.

Sun fuskanci rashin nasara a bangarori uku manya. Rashin nasara ta farko ita ce kan taken demokradiyyar yammaci da kuma 'yanci da suke yi, ikirarin demokradiyya da suke ta yadawa a duk fadin duniya. Hakika duniya ta fahimci karyarsu a wannan bangare saboda wannan yaki. Sun nuna wa duniya cewa irin wannan demokradiyya ta su ba za ta iya kawo wa wata al'umma hakikanin 'yanci ba. Don kuwa matukar dai wani lamari ya gitta wa manufarsu da tattalin arziki, to a shirye suke su yi wasan kura da 'yancin al'umma, rayukansu da kuma hakkinsu na zaba wa kansu abin da ya dace da su.

Hakika da ace da gaske suke yi sun yi imani da demokradiyya; idan da sun yi amanna da hakkokin mutane, to da tuni sun janye sojojinsu daga kasar Iraki da kuma tsame hannayensu daga tsoma baki cikin harkokin mutanen Irakin. To amma lallai hakan ba zai taba faruwa ba. Lalle an ci nasara a kansu a bangaren akidar da suka ce sun yi imani da ita, duniya sun fahimci cewa taken da suke yi na fatar baki ne kawai, al'ummomin duniya sun ga hakan. Wannan lamari dai a fili yake cikin taken da suke yadawa a duk fadin duniya, ya tabbata duniya dai a halin yanzu ta fahimci rashin gaskiyarsu.

An kawo min wasu take misalin 10 zuwa 15 da mutane suke rerawa ko kuma suke rubutawa a jikin kwalaye da kuma totoci, dukkansu suna nuni da cewa al'ummomin duniya sun fahimci hakikanin gaskiya. Taken da al'ummomin suke rerawa sun hada da:

Wannan yaki ne na man fetur, ba yaki ne na 'yanci da kare hakkokin 'yan Adam ba. Wannan dai daya ne daga cikin irin taken, akwai kuma cewa:

Wannan yaki ne na ceto tattalin arzikin Amurka da ke kokarin faduwa.

Wannan yaki ne na zalunci da mamaya irin na Hitla.

Amurka, Birtaniyya da Isra'ila su ne Kusurwoyin Shaidan.

Wadannan dai suna daga cikin taken da al'ummomin duniya suke rerawa, ba wai kawai mutanen Tehran ba ne. Al'ummar Iran dai tun da jimawa suka fahimci da kuma rera irin wadannan take, madalla da irin hangen nesansu. A halin yanzu al'ummomin duniya sun fahimci hakan kuma suna rera su - da ma sauran irin wadannan take. Don haka, an ci nasara a kansu da kuma ikirarinsu na karya kan demokradiyya da kuma 'yancin dan'Adam.

Nasara ta biyu kuma da aka samu a kansu, ita ce nasara ta siyasa. A yau, Amurka ta zamanto saniyar ware a bangaren siyasa ta duniya. Wannan shiri na Amurka, wannan tsari na Amurka na dora shugaban mulkin soji - tsohon janar din sojin Amurka - akan al'ummar Iraki, abu ne da kusan dukkan duniya ta yi Allah wadai da shi, in banda wasu kasashe biyu ko uku da daman tare suke. Kasashen larabawa sun ki amince da hakan, haka nan sauran kasashen musulmi da ma na Turai.

Rashin nasara na uku kuwa shi ne yadda aka kunyata karfin sojinsu. Da farko dai sun yi ikirarin gamawa da kasar Iraki cikin kwanaki uku ko hudu, to amma fa sai suka fahimci cewa ana bukatan sama da kwanaki uku, hudu kai sama da haka ma. Hakika da sojojin Iraki sun ci gaba da fada da wannan labari ya ci gaba, kuma ba ma za a iya tabbatarwa cewa daga karshe ma ko za su ci nasara ko ba za su ci ba, saboda irin gagarumar hasarar da aka jawo musu.

Hakika sojojin Iraki ba su yi fada ba a lokacin da ya kamata a ce sun yi hakan, wannan lamari dai ya bar alamun tambayoyi da daman gaske. Kamar yadda na fadi tun da farko, ba wai muna yanke hukumci ba ne a nan, to amma dai wannan dai na daga cikin tambayoyin da amsarsu nan gaba za su fito.

Rashin nasararsu na hudu kuwa shi ne nasarar da aka samu kan mutumci da ingancin kafafen watsa labaransu. Hakika kafafen watsa labaransu sun yi babban hasara ta gaba daya. Dukkan duniya dai ta fahimci cewa suna hana yaduwar labarai (sanya takunkumin watsa labarai) kana kuma suna kashe masu aiko da rahoto. Sun kashe wani dan jarida amma suka ce wai kuskure ne suka yi, to sai dai babu wani wanda ya yarda da cewa kuskuren ne suka yi.

Sun kasance sukan watsa rahotannin karya kan irin hasarorin da suka yi da kuma irin sojojin da aka kashe musu. A wancan lokacin sun ce an kashe musu sojoji ko 80, 90 ne ko kuma 100, kowa dai ya san wannan karya ce kawai. Ba mu san yawan sojojin da aka kashe musu ba, to sai dai kuma ana iya tabbatar da hakan ta hanyar tambayar 'yan kasar Kuwaiti da suke aiki a wajajen ajiye gawawwaki, ya kamata su sani, don haka mutane Amurka suna iya bincikawa su gani. Bayan yakin Vietnam, sun bayyana cewa sun rasa sojoji 50,000, a lokacin da ake yakin haka suka dinga ambato irin wadannan lambobi na 10, 20, 100 da kuma 200. To koma dai mene ne wannan dai na daga cikin rashin nasararsu.

Karen Farautar yahudawa (Bush) Yana Babatu A Gaban ubangijinsa, Kamar Yadda Aka Umarce Shi Ya Yi
Mai Gida (Dan'Adam Sharon) Da Karensa (Bush Sauna)

Bari in fadi wata jumla guda, a karshen wannan bayani nawa. Da farko dai, yadda nake kallon lamarin shi ne cewa, a wannan lamari da ya faru - batun yakin Iraki - yahudawan sahyoniya suna da gagarumar gudummawar da suka bayar; ta hanyar kwadaita wa Amurka ta aikata abin da ta aikata da kuma share fagen yin hakan. Hakika yahudawan sahyoniya sun ba da gagarumar gudummawa.

Dangane da yahudawan sahyoniyan dai, wannan taswira (Road-Map) ta yankin Gabas ta Tsakiya da Bush yake magana a kai -tare da 'yan amshin shatansa -tana nufin taswira ce ta yaduwar yahudawan sahyoniya a yankin Gabas ta Tsakiya, a kasashen Larabawa da wadanda ba na Larabawa ba da suke kewaye da mu. Yaduwa ta siyasa da kuma ta tattalin arziki, kana kuma idan ma suka sami dama har da fadadar kasa da kuma mamaya.

Wannan dai shi ne abin da wannan sabon taswira ta Gabas ta Tsakiya take nufi. Su (yahudawan sahyoniya) ne wadanda za su fi amfanuwa da wannan sabon shiri, kuma su ne suka ma share fagen hakan.

To amma a halin da ake ciki dai, shaidanun yahudawa da Sharon shaidan sun amfanu da hakan sosai. A yau din nan dai, dukkan idanuwan duniya sun koma ga kasar Iraki ne, don haka suke ta kashe Palastinawa a kowace rana ta Ubangiji. Manyan al'amurra masu sosa zuciya suna faruwa a wannan gurin (kasar Palastinu).

To bari yanzu kuma in dan fadi 'yan kalmomi ga 'yan siyasar kasar Iraki. Kasar Iraki dai tana da 'yan siyasa da yawan gaske. A yau 'yan siyasar kasar Irakin suna fuskantar babbar jarabawa ta rayuwarsu, jarabawa ta tarihi, don haka dole ne su yi hankali kada su yi kuskure. Ya zama dole kada su bari guguwar nasarar da Amurka ta samu akan Saddam ta debe su, haka nan kuma kada su razana; dukkan wadannan abubuwa biyu idan suka faru gare su suna iya cutar da su.

Dole ne 'yan siyasar Iraki su sanya idanuwa kan abubuwa guda biyu: na farko dai shi ne batun tashin hankali, batun daukan fansa maras tsari da kuma gaba na gaira babu dalili. Wannan dai guda kenan daga ciki, dole ne su maida hankalinsu. Hakika tashin hankali ba zai kasance mai amfanuwa ga mutanen Iraki da kuma makomarsu ba. Ba abin da zai haifar in ban da ba wa 'yan mamaya damar ci gaba da zama a kasar.

Dole ne su hana abkuwar gaba maras amfani da kuma kokarin daukan fansa maras tushe. Dole ne su zauna su yi tunani da kuma tsara abin da ya dace, kuma hakan mai yiyuwa ne. Wannan dai shi ne abu na farko.

Abu na biyu kuwa, shi ne batun ba da hadin kai da kuma taimakon bakin haure masu son mulkan kasar, su yi hankali kada su yi wannan kuskuren, don kuwa idan suka yi hakan to fa sunansu zai shiga cikin tarihin kasar Iraki (a matsayin maciya amana). A halin da ake ciki, idan wani mutum ya taimaki bakin haure masu son mulki suka cimma manufarsu, lalle za a sanya hakan cikin tarihin Irakin, kuma hakan zai kasance babban bakin fenti ga mutumcin duk wani mutum ko kuma wata kungiya da ta yi hakan.

Mutanen Iraki suna son 'yancin kai ne, suna son 'yanci, suna son gwamnati ce wacce ta ginu akan addininsu da kuma akidar 'yan kasancinsu, wannan dai shi ne abin da mutanen Irakin suke so. Dole mutanen da suke magana da sunan al'ummar Irakin cikin shekarun da suka gabata su kasance masu da'a ga bukatun al'ummar Irakin. Dole ne su kasance masu biyayya ga wannan akida ta mutanen Irakin. Dole ne su nuna hakan a aikace. Hada kai da da bakin haure ma'abuta mamaya zai sa mutane su juya musu baya ne kawai. Abin da ya zama wajibi su sanya a cikin zukatansu shi ne Allah da kuma bukatun mutanensu. Ya kamata su san cewa samun nasarar soji akan gwamnatin Saddam ba yana nufin samun nasarar siyasa da al'adu akan al'ummar Iraki ba ne.

Babu makawa, sun sami nasarar soji akan gwamnatin Saddam, to amma hakan ba yana nufin sun kawar da al'ummar Irakin daga fagen siyasa da al'adu ba ne.

Muna neman tsarin Allah da kuma rokonSa da ya karbi jinin da al'ummar da ake zalunta suka zubar, Ya kuma taimakawa al'ummar Iraki, dukkan al'ummomin da ake zalunta da kuma al'ummar Palastinu wajen yin fito na fito da azzalumai da 'yan koransu. Muna rokonSa da Ya ba su daman yin nasara saboda tsayin dakan da suka yi da kuma son da suke yi wa addini. Muna kuma rokon Allah da Ya saukar da albarka da kuma falalolinsa ga madaukakan al'ummarmu.


(Karshen Huduba ta Farko Kenan)