MAHANGAR JAGORA
(Saddam Da Magoya Bayansa)Masu iya magana dai suna cewa wai karshen alewa kasa, daga karshe dai bayan kimanin watanni takwas na guje-guje, sojojin Amurka sun ba da sanarwar cewa sun sami nasarar kame tsohon shugaban kasar Iraki Saddam Husaini a ranar 13 ga Disamban 2003. Lalle kan wannan labari dai ya dadawa wa mutane da dama rai musamman ma dai wadanda suka fuskanci zaluncin tsohon dan kama karyan a fili wato al'ummar Iraki. Shakka babu, Saddam Husaini dai yana daga cikin manyan 'yan mulkin kama karyan wannan zamani namu ko ma a ce yana sahun gaba, ba wai kawai akan al'ummarsa ba face ma dai akan wasu kasashe guda biyu da suke makwabtaka da shi wato Iran da Kuwaiti.

Yayin da yake magana kan batun kame Saddam da kuma kiyayyar da al'ummar Iraki suke nuna masa, Ayatullah Ali Khamene'i, Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci, cewa yake:

"Saddam dai mutum ne dan mulkin kama karya, mugu, azzalumi, mai taka dukkan yarjejeniyar da aka cimma kana masharranci. Shi dai ya mulki wata al'umma ce da karfi da kama karya. Ya kasance mugun mutum ne ga al'ummar Iraki kana gare mu a matsayinmu na makwabta".

A wani bangare kuma Jagoran ya bayyana kame Saddam da irin halin da yake ciki a matsayin babban darasi ga dukkan 'yan'Adam, inda yake cewa:

"A yau halin da Saddam Husaini, azzalumi, mashayi jini kana ma'abucin girman kai ya sanya shi rayuwa cikin rami kuma a shirye yake ya yi wannan muguwar rayuwa don tseratar da ransa. A halin yanzu dai da yake an kame shi, duniyar musulmi za su fahimta matsayin wannan dabban daji".

A ra'ayin Jagora dai babban dalilin faduwa da halin da Saddam Husaini yake ciki shi ne rashin samun goyon baya da kariyar al'umma, Jagoran yana cewa:


"Na ji shugaban Amurka yana ce wa Saddam, wai duniya ba tare da shi (Saddam) ba za ta yi kyau, to ni ma son in gaya wa shugaban Amurka cewa duniya ba tare da Bush da Sharon ba lalle za ta yi kyaun gaske".

"Da a ce zukatan al'ummar Iraki suna tare da Saddam Husain, to da kuwa sojojin Amurka ba su samu daman kawar da shi ba. Hakika zukatan al'ummar Iraki ba sa tare da Saddam".

Tun dai bayan kame Saddam da aka yi, muhimmiyar tambayar da take yawo a fagen siyasa ita ce wai shin ya ya aka yi ne Saddam Husaini ya zamanto dan mulkin kama karya, kana kuma da wani karfi ko gwamnati ce ya dogara wajen aika wannan aika-aika da ya aikata?

Shakka babu kowa dai ya san irin gudummawar da kasashen yammaci suka bai wa Saddam a lokacin yakin da ya kallafa wa Iran da kuma goyon bayan da suka ba shi a shirinsa na makaman kare dangi wanda da ba don irin wannan goyon baya ba da bai samu mallakan irin wadannan makamai ba. kamar yadda kuma irin goyon bayan Amurka a wannan bangare a fili yake.

To har ila yau wata tambayar kuma ita ce mene ne dalilin samun wannan alaka ta kurkusa tsakanin Saddam da jami'an fadar White House da harin da ya kai wa Iran a 1980. Jagora, Imam Khamene'i dai yana ganin dalilin dai shi ne irin tsoron da ke cikin zukatan Amurkawan dangane da Juyin Juya Halin Musulunci da kuma irin kokarin da al'ummar Iran suke yi na neman 'yancin kansu. Ga dai abin da Jagoran yake cewa:

"Bayan fara wannan yaki, Amurka ta ba da dukkan goyon bayanta ga Saddam Husaini. Saddam ya bata mana shekaru 8 muhimmai na wannan juyi namu don Amurka ta cimma manufofinta".

Har ila yau Ayatullah Khamene'i, a ci gaba da bayani kan alakar Amurka da Saddam don kawo karshen Juyin Juya Halin Musulunci, cewa yake:

"Wadannan Amurkawa dai da a halin yanzu suke takurawa Saddam, suke farin ciki da kame shi da suka yi, su ne dai a shekarun baya suke mika masa hannuwan abokantaka, suke kulla alaka da kuma taimaka masa. (Ku duba ku gani) sakataren tsaron Amurka na yanzu Donald Rumsfeld a wancan lokacin, shi ne ya tafi Bagadada da ganawa da Saddam da kuma yi masa alkawarin taimako. A hakikanin gaskiya dai sun taimaka wa Saddam don su matsa wa Jamhuriyar Musulunci ta Iran lamba".

Daya daga cikin dalilan da Amurka ta ce na kai wa Iraki hari shi ne batun kasantuwan makaman kare dangi a kasar, to sai dai har ya zuwa yanzu Amurkawan sun gagara samo wadannan makamai. Amma fasa koyin da wasu kafafen watsa labarai suka yi a baya-bayan nan sun tabbatar da cewa Irakin ta samo wadannan makamai ne da taimakon Amurka don ta yaki Iran. Don haka yayin da yake ishara da irin wannan harshen damo da karo da juna cikin maganganu da ayyukan Amurka, Imam Khamene'i cewa yake:

"(Amurkawa) suna cewa mu mun zo ne (Iraki) don makaman kare dangi. To amma tambayar da al'ummar musulmi suke musu ita ce cewa wai shin wane ne ya ba wa Saddam irin wadannan makamai na kare dangi da sauran abubuwan da ya aikata irin wadannan aika-aika nasa? Shin ba su da kansu ne suka ba shi ba? Gaskiyar lamarin dai shi ne cewa su ne suka ba wa Saddam wadannan makamai don cutar da Musulunci da Juyin Juya Halin Musulunci".

Amurka dai ita ce ta gina Saddam, sai dai kuma bayan harin da ya kai wa kasar Kuwaiti da kuma mamaye kasar ya tabbatar wa Amurka kuma sun fahimci cewa shi (Saddam) dai hatsabibin mutum ne wanda ba abin a yarda da shi ba ne. Tun dai daga wannan lokaci (bayan ya gama musu aiki da suke so ko kuma mu ce ya gaza wajen haka), Amurka ta dauki Saddam din a matsayin abokin gaba na farko-farko. Dangane da hakan, ga abin da Jagoran yake cewa:

"A shekarar 1990 ne Saddam ya kai hari wa kasar Kuwaiti, bayan wannan lokaci dai Amurkawa sun fahimci cewa wannan mutum ya yi fuka-fukin da hatta manufofinsu ma a yankin na cikin hatsari. Duk da cewa dai Amurkawa sun kori Saddam daga Kuwaiti a shekarar 1991, to amma dai ba su kawar da shi kwata-kwata ba, hakan kuwa don su ci gaba da amfani da shi a matsayin mutum mai hatsarin gaske don cimma manufofinsu da sanya kasashen yankin su ci gaba da sayen makamai a wajensu. To da yake a halin yanzu an sami canji a gwamnatin Amurka (saboda zuwan sabbin shugabanni) wadanda suka mai da batun yaki a matsayin daya daga cikin siyasarsu ta waje, don haka suka dau nauyin canza Saddam da kawo karshen mulkinsa".

Wannan kamu da Amurkawa suka yi wa Saddam dai ya sanya su cikin gururi da jiji da kai da jin cewa babu wani mutum da ya isa ya ja da su. To amma Imam Khamene'i yana ganin cewa wannan kamu sam ba yana nuni ne da karfin Amurka ba. Dangane da batun nasarar da Amurka ta samu akan Saddam, Jagoran na cewa:

"Nasarar soji akan al'ummomi ta hannun mahara kamarsu Jankhez Khan da irinsu suka yi, sun aikata abin da suka aikata kuma sun kare an kuma gama da su, don haka al'ummomi suka samu damar mikewa tsaye ta hakan. To sai dai yana da kyau a fahimci cewa a duk inda al'umma suke son tsayawa da kafafunsu, babu wani makiyi da zai iya fuskantarsu da kuma ci gaba da aika-aikan da yake musu".

Wannan magana ta Jagora dai tana nuni ne da cewa dalilin faduwar gwamnatin Saddam cikin dan karamin lokaci shi ne rashin goyon bayan al'umma, kai al'ummar ma farin ciki suke yi da kawar da ita da kuma kamun karen kuku da aka masa.

To sai dai kuma Imam Khamene'i ya yi amanna da cewa su ma dai 'yan mamayan Amurka, kamar Saddam, za a fatattake su daga kasar saboda hawan kawarar da suke wa bukatun al'umma. Don haka ne Jagoran yake gaya wa jami'an Amurkan cewa:

"Dukkan kokarinku dai shi ne ku kawar da Saddam daga karagar mulki….to da kyau, a halin yanzu kun yi hakan, to me kuma kuke jira a Irakin?….ku sani fa al'ummar Iraki ba su kori Saddam don su sake kasancewa karkashin mulkin mallaka da kama karyan Amurka ba".

A bisa haka, Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci yana ganin Amurka ne a matsayin wata gwamnati ta kama karyan kasa da kasa da suka sami ikon kawar da dan karamin dan mulkin kama karya irin Saddam.

Daga karshe da yake daya daga cikin manufar Amurka ita ce haifar da fitina a fadin duniya da mallake su, kuma da alama suna ganin cewa duniyan nan ba za ta taba zama cikin kwanciyar hankali ba har sai an kawo karshen wannan 'yar kama karya.

Bari mu rufe bayanin namu da abin da Jagoran yake fadi a wannan bangare:

"Na ji shugaban Amurka yana ce wa Saddam, wai duniya ba tare da shi (Saddam) ba za ta yi kyau, to ni ma son in gaya wa shugaban Amurka cewa duniya ba tare da Bush da Sharon ba lalle za ta yi kyaun gaske".