Imam Ali Khamene'i
Maudhu'i: Fassarar Sakon Jagoran Juyin Juya Hali IMAM KHAMENE'I (H) Ga Mahajjatan Bana (2005).
Kwanan Wata: 12 Janairu 2005

Shimfida:A kowace shekara yayin aikin hajji, Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Ayatullah al-Uzma Sayyid Aliyu Khamene'i (h), ya kan aike da sako ga mahajja a ranar Arfa. To a wannan shekarar ma Jagoran ya aike da irin wannan sako. Don haka abin da ke biye fassara sakon da Jagoran ya aike wa mahajjatan ne. A sha karatu lafiya:

Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai

 يَا قَوْمَنَا أَجِيبُوا دَاعِيَ اللَّهِ وَآمِنُوا بِهِ يَغْفِرْ لَكُم مِّن ذُنُوبِكُمْ وَيُجِرْكُم مِّنْ عَذَابٍ أَلِيمٍ

"Ya ku mutane na ku amsa kiran Allah kuma kuyi imani da shi zai gafarta maku zunuban ku kuma ya tsare ku daga zaba mai radadi".

A wannan karon ma masu amsa kiran Allah ta'ala sun amsa yayin da suka rika fadin "Labbaik" watau amsawar ka sannan kuma suka rika yin sassarfa zuwa ga dakin Allah mai alfarma.

An riga an soma aikin hajji a lokacin da dukkanin zukata suke shauki zuwa ga cikakkaiyar ma'ana dake kunshe cikin yin sa'ayi da samun falalar dake cikin ta, sararin Arafa da Mash'arul haram dake Muzdalifa sun matso kusa da al'umma sannan kuma Safa da Marwa sun shirya kansu don daukar mutane zuwa ga rahamar Allah ta'ala. Don haka wannan wata dama ce da kowa yake jira saboda haka ya kamata ko wane mai aikin hajji ya kasance yayi tunani kan hakikanin hadafin aikin hajji don ya kasance ya samiiya cin cikakken amfani dake cikin sa.

Aikin Hajj wanda kamar yadda aka sani daya daga cikin farillai ne in aka yishi da cikakken sani da kuma farkawa zai haifar da wani tasiri mai girma cikin al'ummar musulmi sannan kuma zai kara samar da hadin kai da dunkulewar musulmi wanda zai lamunta masu izza da daukaka.

Abu na farko da ko wane mai aikin Hajji ya kamata ya kula dashi shine gyaran zuciyar sa. Watau aikin dawafi ,harami, da salloli da zai rika yi, da kuma wurare masu tsarki kamar su sararin arfa, Mina, wurin jifa yin layya da yin aski bayan an kare aikin hajji dukkanin su abubuwa ne da zasu kara kusantar da mutum zuwa ga mahallicin Allah ta'ala. Don haka nan bai kamata ba koda wasa mai aikin hajji ya kasance yayi wasa da wadanan abubuwa da kuma karfafa su wajen kara samun kamala.

Ya kamata dukkanin masu aikin hajji su kasance suna kallon zatin Allah ne cikin dukkanin ayyukan su na wannan lokacin tun daga lokacin da suka taso daga gidan su har zuwa lokacin da suka iso wannan birni mai tsarki. Suyi kokari su ga cewa sun kawar da shaidan da soyace-soyacen zukata iyakar iyawan su, cututtuka irin su kwadayi, hassada, tsoro, duk su nisantar dasu.

A hakika shi aikin hajji wani irin nau'in aiki ne wanda yake na taro, kamar yadda Allah ta'ala yayi kira zuwa gare shi alkur'ani mai tsarki. Alokacin da al'umma suka taru wuri guda zasu iya gane hakikanin yadda suke, haka nan kuma a dunkule ne zasu yi bara'a daga dukkanin mushurikai na duniya, da yin bara'a daga shaidanun mutane dana aljanu, ina ganin kuma babu lokacin da aka fi bukatan yin haka nan kamar wannan lokacin da muke ciki.


A wannan halin da muke an rutsa da duniyar musulmi ta ko wane bangare ta harkar ilmi, tattalin arziki, yada labarai da kuma ta fuskar soji. Haka nan kuma mamayar da aka yiwa Qudus da Palasdin a bangare guda ga kuma Afganistan da Irak a daya bangaren. Sannan kuma ga irin yadda ake munanan kulle-kulle akan kasashen nahiyar Afrika da baki dayan gabas ta tsakiya da dai sauran dukkanin kasashen musulmi na duniya.

Haka nan kuma Amurka da sauran kasashen turai sun riga sun tabbatar da cewa lallai in har ya kasance al'umma ta farka daga wannan dogon barci da take ciki to kuwa lallai zasu rasa cimma munanan manufofin su na mallakan dukkanin arzikin kasa musamman ma man fetur da gas wanda suke da tsananin bukata wajen ci gaban masana'antun su da kuma harkokin su na yau da kullum.

Girman kan duniya sun fito da karfin su don tabbatar da wannan guri nasu, a wasu wuraren suna amfani ne da tursasawa na siyasa in sun ga cewa wannan ne zata fidda su, a wani wajen kuma sai suyi amfani da makamin tattalin arziki su rika yin barazana da maida kasa saniyar ware a duniya, sannan kuma a wasu wuraren suna amfani ne da makamin yada labarai na karya ta kafafen yada labarai da zasu bakanta inda suke so, sai kuma a wasu wuraren kamar Iraki da Afganistan inda suka shiga da karfin soja don tabbatar da wannan manufa tasu.

Babban abin da ya kamata al'umma su gane game da wadanan makiya shine irin yadda suke amfani da hanyar munafunci wajen cimma wadanan gurace-gurace nasu. Basa taba fitowa fili su bayyana mummunar hadafin su, ko yaushe suna fakewa ne da fada da ta'addanci misali don su tafka mafi girman ta'addanci akan al'umma inda suke kashe mata da maza da tsofaffi da kuma kananan yara.

Wadannan makiya suna kera makamai munana na kare dangi kuma suna raba su don ayi amfani dasu, sannan kuma su kansu ma sun kasance sun yi amfani da irin wadanan makaman kamar a Hiroshima na Japan ,Halabja na kasar Irakida kuma wasu wurare na kan iyakar kasar Iran lokacin yakin kariya da aka yi na tsawon shekaru takwas, amma a lokaci guda su wadannan makiya suna rera taken kare duniya daga makaman kare dangi.

Wadannan makiya a boye suna tallan muggan kwayoyi a duniya kuma suna kara yada su a wuraren da suke so amma kuma alokaci guda suna fitowa fili suna rera taken dole sai an kawar da muggan kwayoyi a duniya.

Wadannan makiya suna takama da ilmi da ci gaban da ilmi ya haifar a duniya amma a lokaci guda kuma suna hana dukkanin kasashen musulmi mallakan hanyar yada ilmi da ci gaban sa a kasashe su.

Suna da'awar kare hakkin mara sa rinjaye a kasashe daban-daban na duniya amma a lokaci guda sun hana mata musulmi samun ilmi a kasashen da suke sune mara sa rinjaye da hujjar suna sa lullubi na musulunci.

Wadannan makiya suna maganar yancin fadin albarkacin baki amma kuma alokaci guda sun hana duku wani wanda zai bayyana wani abu game da lamarin yahudawan sahayoniya a duniya. Haka kuma sun hana a buga da kuma yada abubuwan da aka samu bayan mamayar ofishin jakadancin Amurka da aka yi a Iran a baki dayan fadin Amurka.

Wadannan makiya suna da'awar kare hakkin dan adam amma a lokaci guda suna tafka mafi munin keta hakkin dan adam a wurare kamar su kurkukun Abu guraib na kasar Iraki da kuma sansanin Gwantanamo na Cuba.

Wadannan makiya suna da'awar kiyaye wurare masu tsarki na addinai amma a lokaci guda suna bada kariya ga murtaddi kamar Salman Rushdie wanda ya bayyana kalamai na kafirci ga musulunci sannan kuma hatta a kafar watsa labarai na turai ana bashi dama yayi wadannan maganganun.

A wannan lokaci da muke ciki saboda irin yadda Amurka da Birtaniya suka kasance dumu dumu cikin wadannan laifuffuka yasa al'umma gaba daya ta juya daga barin su kuma lallai inda za'a bada dama aji ra'ayin al'ummar duniya kan wadannan kasashe ba tare da shiga tsakanin su ba to kuwa tabbas da sun kasance sun bada mummunar shaida akan su.

A wannan lokaci da zaben kasar Iraki yake kusantowa al'ummar kasar suna so ne su zabarwa kansu makomar kasar su da kansu kuma suna fatan ne suga karshen mamaya da danniya su sami yancin kansu a matsayin su na al'umma guda. Haka nan kuma suna son ne suga sun canza mummunan akidar nan ta yahudawa da suka dade suna fatan gani na yekuwar da suke yi "Daga Nil zuwa Furat" wanda ke neman rarraba kansu zuwa ga hadin kai da zamada juna. Sai dai babu shakka su yan mamaya wani abu daban ne suke nufi da gudanar da zabe a kasar Iraki. Su wadannan yan mamaya suna so ne ya zama da sunan gudanar da zabe sai su kawo wasu mutane yan koren su su damka masu ragamar mulkin kasar, ta haka nan sai ya kasance dukkanin irin abubuwan da suka kashe a lokacin mamaya zasu sami damar fitarwa cikin albarkatun kasar a hankali. Watau suna sone su boye maitar salon mulkin mallaka ta hanayr nunawa duniya cewa al'umma sun zabi mutumin da suke so, alhali kuwa an tabka magudi ne da almundahana don kawo wanda su yan mamaya din suke so. A takaice a zahiri mutane suna ganin dimokradiyya amma a boye kuwa danniyar yan mamaya ne take aiki.

Akwai wasu hadurra guda biyu manya da suke fuskantar Iraki a daidai wannan lokaci na farkon su shine kamar yadda na bayyana magudi a lokacin gudanar da zabubbuka. To in kuwa har samari da masana sun fito sun yi amfani da damar da suke da ita na hana wannan aukuwa to kuma akwai wani hadarin na biyu wannan kuwa shine yiwuwan yan mamaya suyi juyin mulki na soji su kawo wani dan kama karya wanda zai tabbatar masu da abubuwan da suke so.

Dukkanin wadannan hadurra ana iya kawar dasu yayin da aka yi amfani da cikakkaiyar dama da ake da ita a hannu. Hadin kai da kuma kau da kai daga banbance banbance kanana sune keda muhimmanci a wannan lokacin. Larabawa, kurdawa, Turkman duk ya kamata su hade waje guda su manta da banbanci na harshe don tabbatar da babban maniufa.

Haka nan kuma banbancin shi'a ko sunni shima ya kamata a ajiye shi gefe guda saboda makiya ne kawai suke son amfani da wannan a matsayin makami na cimma manufar su.

Ya kamata a sami cewa babu yadda zai zama wanda yake daukan makami wajen zubar da jinin yan uwan sa malamai da masana da kuma fararen hula wadanda basu ji ba basu gani zai kasance shine wanda zai yi yunkuri na ganin bayan yan mamaya.

Ya yan uwa na masu aikin hajji maza da mata da kuma hukumomi na kasashen musulmi!

A yau fa duniyar musulmi na tsananin bukatar hadin kai da kuma riko da Al-kur'ani littafin Allah mai tsarki, haka nan kuma ya kara bayyana a fili cewa makiya addinin Allah basu da wata manufa mai kyau ga al'ummar musulmi, sannan kuma tabbas su makiya basa son duk wani abu da zai iya haifar da farkawa da kuma Karin hadin kai na al'ummar musulmi.

Saboda haka yau rana ce ta nuna hadin kai da kuma kusantar juna tsakanin al'ummar musulmi. Rana ce wadda zamu tuna da wadannan ayoyin na Alkur'ani mai tsarki.

 إِنَّمَا الْمُؤْمِنُونَ إِخْوَةٌ فَأَصْلِحُوا بَيْنَ أَخَوَيْكُمْ وَاتَّقُوا اللَّهَ لَعَلَّكُمْ تُرْحَمُونَ

"Lallai su muminai yan uwan juna ne to kuyi sulhu tsakanin yan uwan ku"

 وَلاَ تَقُولُواْ لِمَنْ أَلْقَى إِلَيْكُمُ السَّلاَمَ لَسْتَ مُؤْمِنًا تَبْتَغُونَ عَرَضَ الْحَيَاةِ الدُّنْيَا فَعِندَ اللّهِ مَغَانِمُ كَثِيرَةٌ

"Kada kucewa wanda ya jefa maku sallama ba mumini ne ba don kuna neman wani tarkace na duniya akwai ganimomi masu yawa a wajen Allah"

 أَشِدَّاء عَلَى الْكُفَّارِ رُحَمَاء بَيْنَهُمْ

"Masu tsanani ga kafirai sannan kuma masu rahama a tsakaninsu"

Haka nan kuma wajibi ne ya zama muna tunawa da wadannan ayoyi a lokacin mamayar Iraki ne ko kuwa a lokacin kai hare-hare a biranen Najaf , Fallujah da Musil ne ko kuma lokacin igiyar ruwa na tsunami ne. Mu musulmi an kira mu zuwa ga hadin kai ne ba akan mabiya sauran addinai kamar kirista ko wanin su ba a'a amma akan makiyan mu ne masu wuce iyaka da ta'addanci akan dukkanin bil adama. Wadanda basa son ganin ci gaban ilmi da adalci a doron kasa.

Idan za'a iya tunawa a lokacin da birnin Qudus ya kasance karkashin ikon daular Usmaniyya ta musulunci gaba dayan kiristoci da yahudawa sun kasance cikin aminci ne amma bayan mamayar yahudawan sahayoniya yaya al'amarin ya kasance akan musulmi?

Ina mai fatan dukkanin maniyyata zasu kare aikin su cikin lumana da kuma karbuwan aiki sannan muna fata wannan aiki ya zama wata taska ta alheri gare mu gaba daya.

Wassalamu Alaikum Wa Rahmatullah

Ali Al-Hussaini Al-Khamene'i.

Zul Hajji 1425.