Imam Ali Khamene'i

Kana iya sauraron sakon ta nan

Maudhu'i: Fassarar Sakon Jagoran Juyin Juya Hali IMAM KHAMENE'I (H) Ga Mahajjatan Bana (2006).
Kwanan Wata: 09 Janairu 2006

Shimfida:A kowace shekara yayin aikin hajji, Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Ayatullah al-Uzma Sayyid Aliyu Khamene'i (h), ya kan aike da sako ga mahajja a ranar Arfa. To a wannan shekarar ma Jagoran ya aike da irin wannan sako. Don haka abin da ke biye fassara sakon da Jagoran ya aike wa mahajjatan ne. A sha karatu lafiya:

Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai

"Idan kun kare aikin hajji ku tuna Allah kamar yadda kuke tuna iyayenku ko fiye da haka"
(Suratul Bakara 2:200)

Ranakun aikin hajji ranaku ne na karfafa guri da kyakyawan fata hade da tsarkin zuciya. Ta bangaren yadda al'umma suka taru a waje guda, Cibiyar Tauhidin Allah Ta'ala suna masu shu'uri da cewa daya suke, abu ne wanda yake karfafa zuciya, haka nan kuma ta bangaren irin ibadar da aka yi na ambaton Allah a lokacin ayyukan hajjin shi kuma abu ne dake tsarkake zukata.

Bayan alhazai sun kamala ayyukan su na hajji wanda yake cike da ambaton Allah cikin wasu siffofi sai kuma Allah Ta'ala ya sake kiran su zuwa ga wani ambaton nashi. Dalilin wannan karfafa kira ga ambaton Allah da aka yi wa muminai shi ne saboda wannan ne asasi na tsarkin zuciya da kuma haskenta. Kuma duk lokacin da zuciyar mutum ta kasance mai tsarki zai zama ya shiryawa fuskantar rayuwa komai hadarin ta domin ya isa zuwa ga kamala.

Tarbiyyar da ke cikin aikin hajji, wadda take fitowa da wannan ambaton Allah ya kamata ne ta kasance tare da mutum har abada tsawon rayuwarsa.

Mutane suna fadawa tarko a tsawon rayuwarsu saboda dalilin gafala daga ambaton Allah da suke shiga. Wannan kuma wani lokacin ya kan jawo al'umma ta shiga hali na kaskanci saboda gafalar da daidaikun 'ya'yan al'ummar suka yi. Aikin hajji yana cikin irin hanyoyin da Allah Ta'ala Ya tsara domin kawar da wannan mushkilar. Ibadar aikin hajji tana ba mu dama koda kuwa na wani dan lokaci ne na nutsewa cikin tuna Allah.

Wannan haduwa a lokacin aikin hajji tana bamu damar gane irin girman wannan al'umma ta musulmi tare da bambance-bambancen harshe da kabilu. Dukkanin yawan jama'ar da suka taru a lokacin aikin na hajji tare da cewa sun fito daga bangarori daban-daban ne na duniya; amma dai suna takama da kuma alfahari da abu guda, wannan kuwa shi ne dukkanin su musulmi ne; al'umma guda.

Alal hakika, al'ummar musulmi sun shiga wani lokaci da ya kasance sun shiga gafala, kuma sakamakon wannan gafala shi ne muke gani a yanzu na koma baya ta fuskar ilmi, da ci gaban sana'oi da tattalin arziki. Sai dai idan har wannan al'umma ta fito daga wannan hali na gafala to kuwa lalle za ta dawo da matsayinta da aka santa da shi, kuma babu shakka akwai alamu da suke nuna hakan a yanzun.


Wajibi ne mu kwana da sanin cewa girman kan duniya suna ganin cewa hadin kan al'ummar musulmi a fagen ilmi da siyasa wata babbar barazana ce gare su, saboda haka nan ne ma suke bi ta ko wacce hanya wajen ganin sun rarraba kan al'umma, kuma sun hana ta dukkanin ci gaba na ilmi.

Ya kamata mu yi amfani da darasin da ke cikin lokacin danniya na mulkin mallaka na farko saboda mu yi amfani da shi wajen kawar da wannan nau'in mulkin mallakan na yanzu.

'Yan mulkin mallaka na farko sun yi amfani da dukkanin irin damar da suke da ita a wancan lokacin na siyasa, tattalin arziki, ilmi da karfin soja wajen mayar da mu saniyar ware da kuma sace dukiyar da Allah Ta'ala Ya ba mu, ta yadda muka kasance matalauta, jahilai, sannan kuma muka sami tabarbarewar yanayi yini bayan yini. A wannan lokacin da muke ciki ganin irin yadda wasu daga cikin masana cikin wannan al'ummar suka farka a kasashen musulmi daban-daban ya sa kafiran duniya sun sake zabura suna amfani da hanyoyi daban-daban na makirci domin ganin sun dankwafe mu.

Yekuwar da suke yi na dimokradiyya da kare hakkin dan'Adam yana daya daga cikin wadannan hanyoyi. Irin demokradiyyar da Amurka ke tallatawa kuma take son ta kafa a duniya shi ne zaben al'umma a zahiri amma Amurka a badinin lamarin, mutane na zabe a bayyane amma Amurka ta bi ta hanyar rashawa ta sayi sakamakon zaben; saboda ta tabbatar da manufofinta a kasar. Daga cikin abin da suke nema a yi masu akwai tsayar da ci gaban addinin Musulunci da kyawawan dabi'u.

Dukkanin kafofin yada labarai na Amurka a halin da ake ciki sun shirya suna son ganin cewa sun takura addinin Musulunci da musulmi, don haka ya hau kan dukkanin daidaikun wannan al'umma da su farka kuma su kasance cikin fadaka; kamar yadda ya hau kan malamai da maraja'ai na addini da marubuta da dukkain wanda Allah Ta'ala Ya yi wa wata baiwa ta musamman da su mike su tabbatar da cewa sun hana Amurka cimma wannan mummunar manufa nata.

Hakika rera taken dimokradiyya daga bangaren makwadaita wadanda suka karfafi mulkin kama-karya shekara da shekaru, a yankin Asiya, Afirka, da Amurka abu ne da ba zai sami karbuwa a gare mu ba. Kamar yadda da'awar kare hakkin dan'Adam daga bangaren wadanda ke karfafa ta'addancin yahudawan sahyoniya, tare da tafka dukkanin barna a Iraki da Afghanistan shi ma ba zai taba samun wurin zama ba a wajenmu. Wadannan mutane da suka tafka munanan ayyuka a gidajen yarin Abu-Ghuraib, Guantanamo da wuraren tsare mutane na asiri a kasashen Turai kuma suka kirkiro kungiyoyin da suke halalta jinin al'umma ba su cancanta su kasance masu kiran kare hakkin dan'Adam ba. Gwamnatocin Amurka da turawan Ingila wadanda suka halasta azabtar da wadanda ake tuhuma har ma da zubar da jininsu a kan tituna, tare da satar jin zancen su ta hanyar wayar tarho ba tare da sun sani ba, duk ba su cancanci su yi kira kan kare hakkin dan'Adam ba.

Ya 'yan'uwa na musulmi maza da mata! A yau fa duniya ta shiga wani irin hali ne, ta bangare guda makircin Amurka yana ta kara bayyana ga al'ummar duniya, sannan kuma a wani bangaren kasashen musulmi kamar Iran suna kara samun karfafa. Iraki, Palastinu da Labanon sun kasance a yau wurare da raunin Amurka da gwamnatin yahudawan sahayoniya ya bayyana a sarari. Taimakon al'umma Palastinu wadanda ake zalunta, karfafa al'ummar Iraki, wadanda ke da fadaka da kuma tabbatar da cikakken 'yancin Labanon da Siriya yana cikin wajiban kowani musulmi a yau. Sannan kuma masana da manazarta na siyasa suna da wani Karin nauyi a kan na sauran al'umma.

Hadin kan al'umma da haduwar zukata da kuma ture dukkanin bangaranci dole ne ya zamanto jerin irin take da masana ke rerawa a yanzun kamar yadda dole ne ya zamanto sun motsa ta hanyar yada ilmi da wayewa ingantacciya. Musulmi basa bukatar su dauko wani ilmi ko ci gaba daga Turai wanda ko a can ma sun gano kuskuren ilmin, domin su ci gaba; da tafiyar da rayuwar al'ummarsu.

Na'am za mu dauko ilmi da hikima daga ko ina suke, amma dai ya kamata mu sani cewa dole ne mu tashi daga hali na dalibta.

Masana dole ne su tashi su wayar da kan sauran al'umma kan yadda yankin Turai ya sunkuyo kasa ta fuskar kyawawan dabi'u da kuma yadda kamala da kyawawan dabi'u suke a Musulunci, saboda haka musulmi bai kamata su zama masu koyi da wadannan ba.

Ya 'yan'uwana musulmi maza da mata! Ku sani cewa dogaro ga Allah da kuma riko da alkawarin Alkur'ani da tsaida farillan ayyukan hajji da dukkanin abin dake tattare da shi zai iya zama hanya ta tabbatar da wannan manufa tamu da muka sanya a gaba, sannan kuma zai iya zama hanya da za mu bayyana bara'armu ta baki da kuma ta hanyar aikinmu ga dukkanin kafiran duniya.

Daga karshe ina rokon Allah Madaukakin Sarki dacewa ga dukkanin maniyyata da kuma sauran al'ummar musulmi da su shiga cikin addu'ar Imam Mahdi (a.s). Wassalamu Alaikum Wa Rahmatullah

Sayyid Ali Al-Hussaini Al-Khamene'i.

Zul Hajji 1426.