Imam Ali Khamene'i
Maudhu'i: Fassarar Sakon Jagoran Juyin Juya Hali IMAM KHAMENE'I (H) Ga Mahajjatan Bana (2004)
Kwanan Wata: 29 Janairu 2004

Shimfida:A kowace shekara yayin aikin hajji, Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Ayatullah al-Uzma Sayyid Aliyu Khamene'i (h), ya kan aike da sako ga mahajja a ranar Arfa. To a wannan shekarar ma Jagoran ya aike da irin wannan sako. Don haka abin da ke biye fassara sakon da Jagoran ya aike wa mahajjatan ne. A sha karatu lafiya:

Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai

A wannan karon ma al'ummar musulmi suna ci gaba da gudanar da ayyukansu na ibada na shekara-shekara suna masu amsa kiran Allah ta'ala: "Kuma kayi yekuwa ga mutane da wajibcin Hajji za su je maka suna masu tafiya da kafafunsu da kuma a kan rakuma suna masu zuwa daga ko wane lungu mai zurfi." Wannan farilla ta aikin Hajji kamar sauran farillai tana kunshe da wasu ni'imomi da rahama ta musamman da Allah ta'ala ya kunshe a cikin rumbun rahamarSa. Saboda haka wannan wata dama ce ta musamman da Allah yake baiwa bayin sa domin samun cikakken amfani da cin gajiyar ni'imomin da Allah ya taskacewa bayin naSa.

Babu shakka farilla ta Hajji wata dama ce da kowa zai iya cin moriyar abin da Allah ta'ala ya taskace gwargwadon karfin sa da imanin sa. Don haka nan wani fage ne na kowa yayi iyakar yunkurinsa don cin gajiyar ni'ima wadda bata da karshe. Haka nan kuma farilla ta aikin Hajji wata dama ce wadda ake hada dukkanin al'ummu daga ko wacce nahiya ta duniya wadanda suke da banbance-banbance ta fuskokin launin fata, tunani, al'adu da dai sauransu,wannan zai baiwa sauran musulmi na duniya damar haduwa da junansu da kuma fahimtar juna. Domin kuwa duk da banbancin harshe da kamannu amma kuma akida da imani ya hada su. Wannan dunkulewar waje guda da kuma hada karfi da karfe wajen tunkaran hadafi guda yana nuna wata dama ce da ake tsananin bukata a wannan lokaci.

Duniyar musulmi a yan kwanakin baya ta kasance ne cikin hali na gafala da rafkana da kuma gyangyadi mai dan nauyi wanda wannan ya sabbaba salladuwa da kuma mamaya ta yan mulkin mallaka akan su to amma fa a 'yan shekarun baya da suka wuce dukkanin alamu suna nuna cewa al'ummar musulmi suna farkawa kuma suna daukar matsaya guda wajen tunkarar makiyin su guda daya kuma babu shakka wannan babban hatsari ga makiya addinin musulunci da musulmi. Sakamakon wannan farkawa da kuma fahimtar ingantacciyar ma'ana ta musulunci mai dauke da cikakkiyar ma'ana ta siyasa da jagoranci ingantacce ya sa a yanzu ma'anoni irin su akida ta "Kwaminasanci" "Markisanci" Jari Hujja" da sauran kalmomi na siyasa mara sa wata takamammiyar ma'ana kamar sabon salon dimokradiyya ta yammacin turai watau "liberal democracy" "neman yancin 'yan Adam" "yancin kai" da dai sauran kalmomin da ake yadawa wadanda basu da wata tsayayyiyar ma'ana sun zama abin ihu da ban dariya.

Haka nan kuma a kullum samari da masu karfi a jika daga kasashe daban-daban na duniya sai kara samun wayewa suke yi kuma suna amfani da dukkanin damar da suka samu ta hanyoyi daban-daban na siyasa, tattalin arziki da halin zamantakewa wajen yakan masu girman kai na duniya. Alal misali inda zamu iya cewa wannan danniyar ta 'yan kama wuri zauna da azzaluman duniya tafi bayyana a sarari shi ne kasar Palasdinu inda al'ummarta ta kwashi shekaru masu yawa tana shan gwagwarmaya da danniya da mamaya na zalunci amma ga shi a kullum sai kara samun karfin gwiwa nayin fito na fito ake yi da wadannan azzalumai ta ko wacce fuska. Al'ummar wannan kasa ta Palasdinu kwansu da kwarkwatansu sun fito suna amfani da duk wata dama da suke da ita wajen nuna rashin yaddarsu da kuma nuna rashin amnicewar su da mamaya.

Wannan irin yunkuri da dagewa ne ya sanya dukkanin irin makirce makircen 'yan mamaya ya shiga wani hali na dimuwa da rashin sanin inda za'a dafa kuma shine ummul abaisin rikicewarsu. A bangare guda kuma wannan irin dagewar ta al'ummar musulmi ta sanya cewa hakikanin koyarwa da kuma ingantattun dai'oi na addinin musulunci sai kara fitowa fili suke yi suna kara tabbata a ko ina ina cikin fadin duniya. Wannan sabanin abin da yan mulkin mallaka na da da kuma yan mamaya na yanzu ke nan suke son suga sun bice ta hanyar makirce-makircen su, wato suna tsananin jin tsoronsu ga al'ummar musulmi ta farka tana neman hakkinta. Sai dai ta Allah ba ta su ba domin kuwa a halin da ake ciki yanzu kyawawan ma'anoni da kaidoji na addinin musulunci sun riga sun fara bayyana kuma suna cika ko ina cikin sassan duniya. Dama dai in har rana ta fito to ai tafin hannu bai iya kare ta.

Wani abu da ya kamata musulmi su kasance cikin sani game da shi shi ne dole ne fa a kara shiri kuma a kasance cikinsa dangane da irin ci gaba da makircin masu girman kai da kawayensu domin ka da su bullo mana ta inda bama tsammani, idan muka ci gaba da zama cikin halin farkawa da fadaka babu yadda zasu yi damu amma in abin Allah ya kiyaye al'ummar musulmi ta ba da kafa ko yaya take to fa lalle dama su suna cikin jiran bango ya tsage ne don su sami wajen shiga.

Babu shakka cewa a duk lokacin da gaskiya ta tsaya a gaban bata to lallai ne gaskiya ce za ta yi galaba wannan wani alkawarin naAllah ta'ala, kuma Allah ba ya saba alkawarinSa. Amma fa ya kamata mu sani cewa wannan alkawari na Allah ta'ala yana da sharadi tare da shi sharadin kuwa shi ne dole ne musulmi su kasance suna masu misaltuwa da sakon musulunci kammalalle kuma suna masu dauke da imani mai karfi da ayyuka kyawawa. Idan har al'ummar musulmi ta siffantu da wannan sifa to tabbaci hakika zata samu nasara Allah ta'ala yana cewa:

"In kuka taimaki addinin Allah, Allah zai taimake ku, ya kuma tabbatar da duga-duganku."

"Lallai Allah zai taimaki wanda ya taimake shi [Addinin sa]"

"Lallai kasa ta Allah ce kuma yana gadar da ita ga bayin sa na gargaru."

A halin da ake ciki yanzu wata sankara da ta kakaba kanta a kasar Palasdinu watau Haramtacciyar kasar Israila tare da taimakon kawayenta suna amfani da dukkanin irin damar da suke da ita ta fuskar tattalin arziki, siyasa da dai sauransu don tursasawa kasashen musulmi da al'ummominsu wajen ganin sun tabbatar da manufofinsu na barna. Har ila yau kuma suna amfani da hanyoyi na ta'addanci da ko wane irin salo nashi akan alummar Palasdinu don ci gaba da danne su da mamaye su, sannan wannan bai ma tsaya kawai a kan al'ummar Palsadinu ba kawai yanzu za mu iya ganin yadda suke amfani da karfi wajen danne kasashen da suka hada da Iraqi da Afghanistan. Wadannan shedanu masu girman kai suna amfani da take na neman yanci da dimokradiyya don samar wa kansu halascin tafka mafi girman ta'addanci a bayan kasa.

Amurka tana da'awar cewa hakkinta take karewa wajen afkawa al'ummar kasar Iraqi da Afghanistan. Haka nan kuma haramtacciyar kasar Israila tana da'awar cewa wajen afkawa alummar Palasdinawa ita ma wai tana kare kanta ne alhali dukkanin mai son hakki da adalci ya san cewa wadannan suna da'awar abin da ba nasu ba ne. Babu shakka dukkanin wannan irin hauka da bacewar basira ta makiya tana fitowa ne daga irin tsananin tsoron da suke yi na ganin cewa su musulmi fa suna kara dunkulewa waje guda suna mantawa da irin kananan banbance-banbancen da suke da su domin fuskantar makiyi guda daya tilo.

Lallai abin da yake a fili ne cewa irin gadon da musulmi suke da shi na tunani ingantacce da irin ci gaba da kwarewa da kuma a bangare guda irin dukiyar da Allah ta'ala ya bisne a kasashensu ya isa ya zama wani babban makami na kore dukkanin wata barazana da ka iya tasowa.

Babu shakka dukkanin masana na duniyar musulmi a wannan lokaci suna da wani babban aiki da ya doru a kansu na bayyanwa dukkanin musulmi hakikanin abin da musulunci ya kunsa da kuma fito da kyawawan ababen koyi na musulunci ta yadda za su kasance abin alfahari ga kowa da kowa. Wasu ma'anoni da ake yawo da su a wannan zamani kamar su yancin dan adam, hakkin mata, hakkin fadin albarkacin baki, ta'addanci, dimokradiyya da dai sauransu ya kamata ne su sami mahanga mai tasarki ba yadda makiya a yanzu suke son yin amfani dasu ta gurguwan hanya ba. Yammacin duniya suna amfani da hanyar kafafen watsa labaran su don sauya tunanin juatne game da ingantaccen fahimtar kalmomi kamar su ta'addanci, makaman kare dangi da dai sauransu don haka nan ya zama wajibi a kan masana da su amfani da hikimar da Allah ya basu wajen yaye wannan farfagandar. Ya kamata a sanya yammacin duniya a gaba har sai sun fito sun ba da amsar abin da ya sa suke tafka munanan ta'addanci a kan yara kanana da keta hakkin mata da cin mutuncinsu. Ashe hana mata sanya tufafin musulunci ba hana su 'yancin aiwatar da addininsu ba ne? Ashe kuma wannan bai nuna cewa da'awar kare hakkin dan adam da yammacin turai suke yi karya ce kawai ba.

Gwamnatocin kasashen musulmi suna da wani babban aiki a kan su na yin amfani da dukiyoyin su da karfin su na siyasa wajen ganin cewa sun hada karfi da karfe don tsamakar da kasashe da al'ummu daga danniya da kuma mamayar masu neman mulki na wannan zamanin,dole ne ya kasance taken imani da riko da addini shine abin da zai zama kasashen musulmi na yadawa. Kungiyar hadin kan kasashen musulmi watau [OIC] tana da babban aiki na hada kasashen musulmi da kuma cin moriyar abin dake gare su wajen yada addinin Allah.

Jamhuriyar Musulunci Ta Iran wadda a wannan lokacin take cikin bukukuwan tunawa da shekaru 25 da tabbatan gwamnatin musulunci ta riga ta zama kasa wadda ta jarraba wannan abu a aikace, kuma lallai bata samu wannan damar ba face tare da imani da dogaro Allah ta'ala. Don haka nan Jamhuriyar Musulunci Ta Iran tana amfani da wannan damar wajen yada ma'anoni da ingantaccen 'yanci wanda yake karkashin yadda da kariya ta al'ummarta. Wannan kasa tamu Jamhuriyar Musulunci Ta Iran a yan shekarun da suka wuce ta fuskanci barazanoni masu dinbin yawa daga makiya kuma tabbas wannan alumma ta Iran ta yi amfani da imanin ta da kuma dogaronta da Allah wajen dagewa dukkanin wannan barazanar, wannan ya mayar da wannan alumma tamkar wani wajen gwaji na fadin Allah ta'ala cewa:

"Lallai makircin shaidan ya kasance rarrauna".

Da kuma fadin Allah ta'ala:

" Lallai Allah yana tare da wadanda suke da takawa kuma masu kyautata ayyukansu."

Sannan da kuma fadin Allah:

" Lallai Allah akan taimakon su [muminai] mai iko ne"

Sannan da kuma fadin Allah:

Babu shakka muna ganin kyakyawan natija game da musulunci da al'ummar musulmi a nan gaba saboda alkawarin Allah ta'ala kuma da yaddan Allah zamu ci gaba akan wannan tafarkin na marigayi Imam Khumaini [RA] kuma kyakyawan karshe tana tare da masu tsoron Allah.

Wassalamu Ala Ibadullah al-Salihin.

Sayyid Ali Khamenei
29/01/2004.