Matanin Sakon Jagoran Juyin Juya Hali Imam Khamene'i
A Taron Na Sha Uku Na
Kwamitin Tsayar da Sallah

A Garin Shahr-e-Kord, Babban Birnin Lardin Char-Mahal Bakhtiari
(06/9/2003)


Shimfida:A wannan rana ta Asabar (6/9/2003) ne Jagora Imam Khamene'i (h) ya aike da sako ga taron kara wa juna sani da kwamitin tsayar da salla na Iran ya ke shiryawa kowace shekara. Abin da ke biye fassara sakon jagoran ne da aka karanta a wannan taro kafin a fara shi:

Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai

A yau bayan shekaru sha biyu da fara wannan shiri mai albarka na tsai da salla, lalle ya zama dole a sake bude wani sabon shafi na wannan kokari da kuma jihadi mai albarka. Lalle dole ne wannan sabon shafi ya ba da muhimmanci ga tsare-tsare na kurkusa da na nesa wajen cimma manufofin da aka tsara cimma su a aikace cikin wannan lokaci da kuma wasiyoyin da suka gabata.

Hakika manufar da ake son cimmawa a wannan shiri na nesa na shirin tsayar da salla ita ce gyaran al'umma da kuma sa'adanta, sai dai kuma tabbatuwan wannan manufa za ta kasance ne bayan fitilar salla mai haskakawa ta samu gindin zama cikin gidaje da zukatan al'umma bugu da kari kan haskaka su. Shi kuwa shiri na kurkusa na tsayar da sallan shi ne amfani da dukkan karfi na ilmi, aiki da kafafen watsa labaran kasa da kuma ba da dukkan karfi wajen cimma wannan manufa madaukakiya

Kamar yadda sanin alkibla da kuma fuskantarta yayin salla ya zama wajibi, haka nan ma samu da kuma isa gare ta wajibi ne saboda kawata duniyar mutum da kuma haskaka zukata da hasken salla, don kuwa alkibla ita ce madaukakiyar manufa kana ta karshe ta salla kuma tafarkin isa gare ta don haskaka duniya da zukata wanda hakan na daga cikin tsare-tsare na kurkusa da na nesa.

A halin da ake ciki, da ikon Allah da kuma kokarin mai girma shugaban kasa, an gama isar da sakon kira ga dukkan hukumomi da cibiyoyi da su ba da himma wajen ayyukan tsayar da salla, kamar yadda kuma aka bukaci kafafen watsa labarai musamman hukumar radio da talabijin ta kasa da kuma ma'aikatar al'adu da sauran jami'ai da su ba da himma a wannan bangare kamar yadda muka bukace su a shekarun da suka gabata.

Abin da yake wajibi a halin yanzu shi ne samar da kwamitocin da su tsara ayyukan da wadannan cibiyoyi za su gudanar bisa la'akari da ilmi da kuma yadda yanayi yake, sannan kuma a kafa wani kwamitin na daban da zai sa ido kan ayyukan wadannan kwamitoci.

Bisa wadannan abubuwa da muka fadi, dole ne wannan taro naku kada ya kasance taro ne kawai na jawabi da tattaunawa, face dai dole ne ya kasance taro ne na gabatar wa wadannan kwamitoci da aka ambata rahotannin da bayanai kan irin ci gaban da aka samu cikin takamammen lokaci da kuma jinjinawa kwamitocin da suka aikata abin a zo a gani da kuma nuna wa kwamitin da ya gaza - muna neman tsarin Allah - wajen aikata abin da ya hau kansa da kuma gabatar da tsare-tsaren da suka dace; hakan kuwa don cimma nasara ne. Shakka babu gwamnati da kuma mai girma shugaban kasa za su iya ba da gagarumar gudummawa a wannan bangaren.

Ina rokon Allah da ya kasance tare da dukkanku musamman Hujjatul Islam Qara'ati (shugaban kwamitin tsayar da salla) wajen tabbatar da wannan madaukakiyar manufa. Ina rokon Allah Madaukakin Sarki da Ya sanya ku cikin addu'oin Imam al-Asr (a.s).

Wassalamu Alaikum Wa Rahmatullah Wa Barakatuhu

Sayyid Aliyu Khamene'i
9 ga Watan Rajab 1424(H.K)
15 ga Watan Shahrivar 1382 (H.S)
6 ga Watan Satumba 2003 (M)