Matanin Sakon Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Imam Khamene'i
Dangane da Shahadar
Ayatullah Muhammad Bakir Hakim

Shugaban Majalisar Koli ta Gwagwarmayar Musulunci ta Kasar Iraki
(29/8/2003)



Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai

INNA LILLAHI WA INNA ILAIHI AL-RAJI'UN.

Muggan hannayen 'yan koren ma'abuta girman kan duniya sun sake aiwatar da wani babban aika-aika da kuma dauke wa al'ummar Iraki wani mutum mai girma da ya kasance babbar katanga wa 'yan mamaya da kuma kawar da wannan katanga.

A yau din nan Ayatullah Sayyid Muhammad Bakir Hakim tare da wasu jam'i na mumimai maza da mata da suka zo sallar juma'a a haramin Shugaban muminai Ali (a.s) sun cimma nasarar shahada inda suka tafi zuwa ga rahamar Ubangiji na musamman.

Wannan shahidi abin kauna (Ayatullah Hakim), ya kasance malami ne ma'abucin jihadi da yayi shekara da shekaru yana gwagwarmaya da gwamnatin kama-karyar Saddam don tabbatar da hakkokin al'ummar Iraki, wanda kuma hatta bayan faduwar gunkin sharri da fasadi a hannun 'yan mamayan Amurka da Birtaniyya, ya ci gaba da tsayin daka da fuskantar 'yan mamayan, kana kuma ya ci gaba da shirin yin shahada a wannan tafarki na jihadi mai girma da kuma shiga jirgin shahidan da Iyalan Hakim madaukaka da sauran shahidan kasar Iraki suka shiga.

Babu shakka wannan aikin ta'addanci na garin Najaf mai tsarki da shahadar wannan jika na Annabi mai girma kana kuma malami ma'abucin jihadi zai kasance babbar hidima ce ga manufofin Amurka da yahudawan sahyoniya azzalumai.

Shahid Ayatullah Bakir Hakim dai ya kasance misali ne na kare hakkokin al'umma, wanda ya ke ganin addini, 'yanci da makomar kasarsa na fuskantar barazana da hatsarin 'yan mamaya, don haka ne ya ci gaba da gwagwarmaya wajen kare addini da kuma kasarsa daga wannan barazana ta masu wuce gona da irin. Shahadar wannan jika na Manzon Allah (s.a.w.a) mai girma wani babbar musiba ce ga al'ummar Iraki kana kuma wani dalili na daban na ci gaba da zaluncin 'yan mamaya wadanda suka haifar da rashin tsaro da fitina a sanadiyyar wannan mamaya tasu maras halalci.

To sai dai duk da hakan ya kamata makiya al'ummar Iraki da sauran al'umman musulmi su sani cewa wannan shahada ko da wasa ba zata raunana ruhin gwagwarmayar al'ummar Iraki da kuma fuskantar manufofin manyan kasashen duniya ma'abuta girman kai da kuma yahudawan sahyoniya ba, kamar yadda kuma ba zata raunana ruhinsu na yin hidima wa tafarkin addinin Musulunci da kuma riko da shi ba, face ma dai hakan zai kara musu karfin gwuiwa ne, InshaAllah.

To sai dai duk da hakan ya kamata makiya al'ummar Iraki da sauran al'umman musulmi su sani cewa wannan shahada ko da wasa ba zata raunana ruhin gwagwarmayar al'ummar Iraki da kuma fuskantar manufofin manyan kasashen duniya ma'abuta girman kai da kuma yahudawan sahyoniya ba, kamar yadda kuma ba zata raunana ruhinsu na yin hidima wa tafarkin addinin Musulunci da kuma riko da shi ba, face ma dai hakan zai kara musu karfin gwuiwa ne, InshaAllah.

Ina mika sakon ta'azziyyata ga Mai Girma Bakiyatullah (Imam Mahdi), raina ya kasance fansa gare shi, dukkan al'ummar Iraki da Iran, makarantun Hawza, manyan maraja'ai da malaman Najaf da Kum, majalisar koli ta Juyin Juya Halin Musulunci ta Iraki musamman ma ga iyalan Hakim ma'abuta daukaka, musamman ma dai dan'uwansa mai girma mai girma Sayyid Abdul'aziz Hakim da dukkan 'ya'yaye da iyalan wannan shahidin masallaci, sannan kuma ina taya su murnar samun wannan matsayi na shahada. Kamar yadda kuma nake kiransu zuwa ga hakuri da juriya saboda wannan babbar musiba.

Ina rokon Allah Madaukakin Sarki da ya daukaka darajar dukkan shahidai da kuma ninnika musu ladansu sannan wadanda suka sami raunuka Allah Ya gaggauta ba su sauki. Saboda girmama matsayin wannan shahidi mai girma da sauran shahidan wannan bala'i mai girma, ina sanar da ware kwanaki uku a matsayin ranakun zaman makoki na gaba daya.

( æóÓóíóÚúáóãõ ÇáøóÐíäó ÙóáóãõæÇ Ãóíøó ãõäúÞóáóÈò íóäúÞóáöÈõæäó)


(Kuma da Sannu wadanda suka yi zalunci, za su sani a wace majuya suke juyawa)

Sayyid Aliyu Khamene'i
1 ga Watan Rajab 1424(H.K)
7 ga Watan Shahrivar 1382 (H.S)
29 ga Watan Augusta 2003 (M)