Imam Ali Khamene'i
Maudhu'i: Fassarar Sakon Jagoran Juyin Juya Hali IMAM KHAMENE'I (H) Ga Al'ummar Musulmi Kan Ta'addancin Amurkawa A Fallujah.
Kwanan Wata: 18 Nuwamba 2004

Shimfida:Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Ayatullah al-Uzma Sayyid Ali Khamene'i, a wani muhimmin sako da ya aike wa al'ummar musulmi a ranar 18 ga watan Nuwamba 2004, ya kiraye su, gwamnatocinsu da masanansu da su yi aiki da nauyin da ya hau kansu wajen fuskantar ayyukan ta'addanci da zubar da jinin da sojojin mamayan Amurka suke yi wa al'ummar garin Fallujah na kasar Iraki. Abin da ke biye fassarar wannan sako ne:

Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai

Ya Ku Al'ummar Musulmi,

Hakika irin kisan gilla da sauran munanan ayyuka da kasar Iraki take fama da shi a halin yanzu ya kai wani matsayin da ke ta da hankalin duk wani musulmi da kuma duk wani dan'Adam da ke da lamirin dan'Adamtaka a tattare da shi. Babu shakka irin kisan gilla da raunana dubban mata, kananan yara da sauran fararen hula, harbewa da kashe wadanda suka sami rauni, kame mutanen da ba su ci ba su sha ba, rusa gidaje da masallatai da kuma keta hurumin iyalai da ke faruwa a halin yanzu a garin Fallujah ya dauke barci daga idanuwa da kuma hana zukata samun kwanciyar hankali. To ba ma wai kawai abin ya tsaya a nan ba ne, akwai rahotanni da suke cewa akwai yiyuwar sake aikata wannan danyen aiki da aka ambata a sama a garuruwan Musil, Samarra, Bakuba da sauran wasu garuruwa na kasar Irakin.

Wadannan 'yan mamaya dai suna fakewa da cewa wai akwai 'yan ta'adda cikin al'umma (a wadannan wajaje) wajen halalta irin wannan danyen aiki na su na ta'addanci. To ko da ma dai da gaske ne cewa akwai 'yan ta'adda cikin al'umma - duk da cewa akwai ma shakku cikin hakan - to shin akwai wani halalci wajen kashe mutanen da ba su ci ba su sha ba, ko kuma barin wadanda suka sami rauni ba tare da magani ba da kuma barin yara ba tare da abinci ba?

Abin mamaki ne yadda mutanen da suke cewa suna alfahari da dauke hukumcin kisa akan masu laifi amma a halin yanzu ga su nan suna kashe al'umman musulmin Iraki wadanda ba su ci ba su sha ba ba kyakkyaftawa? Kuma me ya sa kasashen musulmi da na larabawa suka yi shiru da rikon sakainar kashi wa wannan lamari?

Al'ummar Iraki dai (a halin yanzu) suna kira da neman taimako daga wajen 'yan'uwansu musulmi. Shin al'ummar Iraki da gwamnatocinsu ba sa jin cewa akwai nauyi ne a kansu, alal akalla, wajen daya hannayensu da nuna rashin amincewarsu da irin zalunci da ta'addancin da ma'abuta girman kai suka sanya al'ummar musulmi wadanda ba su ci ba su sha ba?

Don haka ina kiran al'ummar musulmi a duk inda suke a fadin duniya, musamman ma dai kasashen musulmi da larabawa da kuma masanansu, da su sauke nauyin da ya hau kansu dangane da wadannan matsala da al'ummar musulmi ke ciki a halin yanzu.

Wa La Haula Wa La Kuwata Illa Billah.


Sayyid Ali Khamenei
29/01/2004.