MAGANGANUN SAURAN MASANA KAN JAGORA


Malamai da dama sun yi maganganu kan matsayi da kuma daukakan Ayatullahi Khamene'i, ga kadan daga cikin abubuwan da suka fada:

AYATULLAHI SANI'I:

Girmamawa da kuma tabbatar da Ayatullahi Khamene'i ba wai kawai al'amari ne na mustahabi ba, a'a wajibi ne na addini (na Ubangiji), lamarin lamari ne kiyaye musulunci da kuma daukaka shi, ba wai lamari mai sauki ba.
Hakika kin girmama wannan lamari barin wajibi ne, kuma barin wajibi laifi ne mai girman gaske dake fitar da mutum daga kasancewa adali.
Ni ina ganin mas'alar (biyayya wa jagora) ce a matsayin mas'ala ta shari'a. Hakika saba wa umurnin Ayatullahi Khamene'i zunubi ne kana kuma sabo ne mai girma gaske, kuma mayar masa da martani kamar mayar wa Imam Sadik (a.s)ne, kuma mayar da martani wa Imam Sadik (a.s) tamkar mayar wa Manzon Allah (s) ne, kuma mayar da martani wa Manzon Allah (s) mayar wa Allah Madaukakin Sarki ne, wanda yake sanya mutum ya fita daga da'a wa Allah ya koma da da'a wa shaidan. Kuma kamar yadda ruwayar Umar bn Hanzala tazo cikin babin "Wilayatul Fakih cewa mayar da martani gare shi yana daidai da yin shirka wa Allah ne.

AYATULLAHI FADHIL LANKARANI:

Hakika Imam da kansa ya tabbatar da ijtihadi da kuma dacewar Sayyid Khamene'i ta bangarori daban-daban, a bangare guda kuma, duk kuwa da cewa bai samu daman bahasi irin na ilimi (a fili ba) saboda irin ayyukan da suka masa yawa, to amma ina iya tunawa tun shekaru 20 da suka gabata ya kasance yana karantar da Makasib da kuma Kifaya, kana kuma ya kasance mutum ne mai ra'ayi sannan kuma cikakken mujtahidi wanda ba'a kokwanto ijtihadinsa, sannan kuma a bangare na uku, da yawa daga cikin mujtahidai da suke cikin Majalisar Kwararru sun tabbatar da ijtihadin Sayyid Khamene'i.

AYATULLAHI JAWADI AMULI:

Hakika mayafin shugabancin da Ma'aikin Allah (s) ya sanya, a yau ya zamanto mayafinka (Sayyid Khamene'i).
A halin yanzu Shugaban fukaha'u da mujtahidai mai martaba Ayatullahil Uzma Araki, malamai da daliban hauza da dukkan al'umman da kuma dukkan raunanan duniya suna tare da kai (Sayyid Khamene'i).

AYATULLAHI MISHKINI:

An samu shaidu da yawa da suka nakalto Imam (r.a) yana bayyana cewa Ayatullahi Khamene'i yana da dukkan abubuwan da ake bukata ga shugabanci...don haka 'yan majalisar kwararru, saboda la'akari da doka da kuma sharuddan shugaba (da kuma shugabanci) da kuma girmama ra'ayin Imam, sun ayyana Ayatullahi Khamene'i a matsayin jagora.