Ayyukan Mai Girma Imam Khamene'i (H) Na Yau Da Kullum
(Watan Satumban 2003)


-24 ga Satumban 2003

Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci A Bukin Ranar Aiko Manzon Tsira Muhammad (s)

Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Ayatullah al-Uzma Sayyid Ali Khamene'i (h) ya bayyana cewa: "Madaukaka al'ummar Iran, ta hanyar dogaro da darussan da ke cikin aiko Manzon Allah (s) za su ci gaba da tafarkinsu na daukaka da sa'ada da dukkan karfinsu.

Jagoran ya bayyana hakan ne a yau Laraba (24 ga Satumba 2003) yayin da yake isar da sakon taya murnarsa ga al'ummar Iran da sauran al'ummar musulmi na duniya a ganawar da ya yi da shugabannin bangarorin gwamnati guda uku, shugaban majalisar fayyace maslahar tsarin Musulunci ta Iran, sauran jami'an gwamnati da na soji, al'ummomi daban-daban na Iran, jakadoji da kuma wakilan kasashen daban-daban na Musulunci, inda yayin da yake bayyana cewa al'ummomin duniya, a halin yanzu sama da kullum suna bukatuwa da sakonnin da ke cikin aiko Ma'aiki (s) ya kara da cewa: "Aiko Manzon Allah lamari ne da ke kiran dan'Adam zuwa ga tauhidi da hadin kai a matsayin wata hakika ta rayuwa bugu da kari kan gutsure hannuwan azzaluman da suke zaluntar dan'Adam, don samun sa'ada ta duniya da ta lahira, duk da cewa cimma wannan manufa tana bukatuwa da kokari da tsayin daka".

Haka nan kuma Jagoran ya bayyana tsarkake zuciya, tarbiyyar ruhi, girmama matsayin ilmi, tsayuwa domin Allah da kuma hadin kai da 'yan'uwantaka a matsayin kadan daga cikin sakonnin aiko da Manzon Allah (s).

Yayin da kuma ya koma kan Jami'an gwamnati da kuma bayyana nauyin da ke kansu a matsayin nauyi mai girman gaske, Imam Khamene'i ya ce: "Kamar Manzon Allah (s) ya fadi, gyaran kowace al'umma yana da alaka da gyaruwar zababbun wannan al'umma ne, don haka ya hau kan malamai da masana su sauke nauyin da ya hau kansu wajen tabbatar da tsayuwar al'umman musulmi a gaban abokan gaba".

Haka nan kuma Jagoran ya bayyana gazawar da H.K. Isra'ila ta yi wajen fuskantar tsayin dakan al'ummar Palastinu a matsayin babbar alama ta tasirin tsayuwar wata al'umma a gaban abokan gaba, inda ya ce: "A ko ina aka samu al'umman musulmi sun mike tsaye wajen fuskantar abokan gaba, to babu shakka za a ga irin wannan tasiri a fili".

Har ila yau kuma Jagoran ya ja kunnen al'ummar musulmi dangane da irin makirce-makircen makiya musamman kasar Amurka dangane da kokarin da take yi rarraba kan al'ummar musulmi da nufin mamaye su, inda ya ce: "A yau manyan kasashen duniya ma'abuta girman kai a kokarin da suke yi na fada da al'ummar musulmi, sun zaro dukkan fararunsu na zalunci akan Iran, ba don komai ba sai dai saboda irin tsayin dakan al'umman Iran da kuma farkawarsu sun kasance babban kafar ungulu ga cimma manufofinsu".

Kafin jawabin Jagoran sai dai Shugaban kasa Sayyid Muhammad Khatami ya gabatar da jawabi inda yayin da yake isar da sakon taya murnarsa na wannan rana ta aiko Manzon Allah ga Jagoran da kuma al'ummar musulmi ya bayyana hadin kai da 'yantuwa daga zalunci, jahilci son kai da kuma nuna banbanci a matsayin abubuwan da aiko Manzo din ya zo da su.



-20 ga Satumban 2003

Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci A Bukin Yaye Daliban Jami'ar Soji A Garin Nushahr

Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci kuma kwamandan dukkan dakarun tsaro na Iran Ayatullah al-Uzma Sayyid Ali Khamene'i ya bayyana cewa: "Gaba da Musulunci da kuma Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba abin da zai haifar wa abokan gaba in ban da kunya da rashin nasara".

Jagoran ya bayyana hakan ne a yau din nan asabar (10/9/2003) a wajen bukin yaye daliban jami’ar dakarun sojin sama, kasa da na ruwa a garin Nushahr da ke arewacin Iran, inda yayin da yake magana kan asalin dalilin da ya sa makiya suke gaba da tsarin Musulunci na Iran, ya bayyana cewa: “Dakarun tsaron Iran, babu shakka ba za su kasa a gwuiwa ba wajen sauke nauyin da ya hau kansu na kare Musulunci da Jamhuriyar Musulunci".

Haka nan kuma yayin da yake magana kan kokarin abokan gaba wajen sanya jin kaskanci cikin zukatan al’ummar Iran, Jagoran Juyin Juya Halin Musuluncin ya ce: "Mallakan ilmi mai zurfi a bangaren kere-kere da matasa masanan Iran suka yi yana nuni da cewa al’ummar Iran suna da dama mai girman gaske na ilmi da kuma kere-kere na ci gaba wanda hakan na daga cikin abubuwan da suke damun makiya Jamhuriyar Musulunci ta Iran.

Har ila yau Jagoran a ganawar da yayi da kwamandojin bangarori uku na dakarun Iran din, wato dakarun sama, kasa da na ruwa, ya nuna jin dadi da amincewarsa da irin ci gaban da dakarun suka samu musamman dakarun ruwa a bangarorin kere-keren makaman kariya da dai sauran kayayyakin da suka shafi ayyukansu, inda ya ce: “Bisa la’akari da wannan ci gaba da aka samu, ya zama dole dakarun su ci gaba da ba da kokari a wannan bangare har a kai ga manufa".

Haka nan kuma Jagoran ya bayyana dogaro da Allah da kuma jaruntaka a matsayin abubuwan alfaharin al’umma a gaban makiya inda ya ce: “Dakarun tsaron kasa da suka hada da sojoji, dakarun kare Juyin Juya Halin Musulunci, dakarun sa kai, ta hanyar imani da jaruntaka za su ci gaba da ba da gagarumar gudummawa wajen tabbatar da ‘yanci kasar Iran.

Shi ma a nasa jawabin babban hafsan hafsoshin sojojin Iran din General Sulaimi ya ce dakarun Iran din karkashin jagoranci mai cike da hikima na Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci a shirye-shirye hannu daya wajen kare Musulunci da kuma tsarin Musulunci.

A yayin wannan buki dai Jagoran baya ga halartar wani fareti na soji ya kuma halarci makabartar shahidan da ke wannan jami’a inda ya karanta musu fatiha.



-10 ga Satumban 2003

Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Yayin Ganawa da 'Yan Majalisar Kwararru Masu Kula da Kuma Zaban Jagora

Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Ayatullah al-Uzma Sayyid Ali Khamene'i (H) ya bayyana cewa koyi da kuma biyayya ga Amirul Muminina Ali (a.s) ya kasance abin alfaharin al'umma da kuma jami'an gwamnatin Musulunci ta Iran

Jagoran ya bayyana hakan ne a yau din nan Laraba (10/9/2003) a lokacin da yake maraba da 'yan majalisar kwararru masu zabe da kuma kula da ayyukan Jagora a nan Iran yayin da suka kai masa a yau ranar haihuwar Imam Ali (13 ga watan Rajab).

Yayin da yake kiran al'umma da jami'an gwamnati da su ba da himma wajen kyautata ayyukansu da kuma koyi da Imam Ali (a.s) da sauran Imamai (a.s), Imam Khamene'i (h) cewa yayi: "Akwai banbanci mai girman gaske tsakanin ayyuka da dabi'unmu da kuma darussa da koyarwar da Amirul Muminina (a.s) ya koya mana, don haka ya zama dole, ta hanyar neman taimakon Allah da kuma kokari, mu zama masu kusanci da Imamai da kuma riko da tafarkinsu".

Yayin da kuma yake magana kan hanyoyin da za a bi wajen magance matsalolin da ake ciki, Jagoran Juyin Juya Halin Musuluncin ya bayyana kokari a bangarorin kiyaye 'yanci da daukakan al'umma, yada al'adun Musulunci da koyarwarsa na asali, gyara kasa da kyautata yanayin zamantakewar al'umma, yada adalci da kawar da nuna bambanci a matsayin hanyar da kawai za a bi wajen fita daga cikin matsalolin da ake fama da su.

Ayatullah Khamene'i, yayin da kuma ya koma kan fada da makirce-makircen manyan kasashen duniya ma'abuta girman kai akan J.M. ta Iran cikin shekaru 25 din da suka gabata, ya bayyana cewa: "Kafa gwamnatin Musulunci a Iran ya kasance babbar barazana ga haramtattun manufofin ma'abuta girman kai na duniya kamar yadda kuma ya kasance ummul aba'isin din farkawar duniyar musulmi, wadannan abubuwa dai su ne suka sa tun farkon kafa wannan tsari zuwa yau din nan take fuskantar matsaloli da makirce-makircen abokan gaba".

Har ila yau Jagoran ya bayyana kokari a bangarori daban-daban da kuma fuskantar matsaloli da dukkan karfi a matsayin hanya guda kawai ta ci gaba da tafarkin nasarar al'ummar Iran, inda ya kara da cewa: "Kokari a tafarkin kiyaye 'yanci da daukakar kasa da kuma fuskantar bakar siyasar 'yan mulkin mallaka da kuma mamayan Amurka, suna daga cikin ayyukan da suka hau kan al'umma da suke bukatuwa da taka tsantsan".

Haka nan kuma Jagora Imam Khamene'i, yayin da yake ishara da kokarin makiya wajen haifar da rikicin mazhabobi tsakanin al'ummar musulmi, cewa ya yi: "Kokarin haifar da sabani da rikici tsakanin 'yan shi'a da 'yan sunna, wanda a halin yanzu ake ci gaba da yi a kasar Iraki, na daga cikin makirce-makircen 'yan mulkin mallaka kuma hakan na daga cikin tsohuwar siyasar turawan Ingila na rarraba kan al'umma, to sai dai kuma addinin musulunci ya jaddada wajibcin hadin kai da fahimtar juna tsakanin al'ummar musulmi...".

Har ila yau Jagoran ya jaddada wajibcin ba da kokari da himma wajen kyautata yanayin rayuwar al'umma da kuma saukaka musu samun abubuwan da suke bukatuwa da su don rayuwa.

Kafin jawabin Jagoran dai sai da shugaban majalisar kwararrun Ayatullah Mishkini ya gabatar da jawabi da kuma isar da sakon taya murnarsu ga Jagoran da kuma al'ummar musulmi dangane da zagayowar ranar haihuwar Imam Ali (a.s).

A yayin jawabin nasa Ayatullahi Mishkini ya bayyana biyayya ga adilan shuwagabanni a matsayin babbar ni'imar Ubangiji, inda yayin da yake wajibcin fahimtar ni'imar da ke cikin tsarin Musulunci ya bayyana cewa: "Dole ne dukkan al'umma musamman malamai su fahimci wannan lamari da kuma sauke nauyin da ya hau kansu".

Har ila yau kuma yau din dai a yayin wannan ganawa, Ayatullah Ibrahim Amini, na'ibin shugaban majalisar kwararrun din ya gabatar da rahoto kan zaman majalisar ta kwanaki biyun da suka gabata na majalisar.



-03 ga Satumban 2003

Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Yayin Ganawa da Sarkin Jordan Abdullahi na Biyu Da Tawagarsa

Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Ayatullah al-Uzma Sayyid Ali Khamene'i (H) ya bayyana cewa ana iya magance matsalolin kasashen musulmi ta hanyar dogaro da Ubangiji, kishi, hadin kai da kuma dogaro da al'umma.

Jagoran ya bayyana hakan ne a yau din nan Laraba (3/9/2003) yayin da yake ganawa da Sarki Abdullahi na biyu na kasar Jordan a lokacin da ya kai masa ziyarar ban girma a gidansa da ke birnin Tehran, inda yayin da yake ishara da makwabtakan da Iran da Jordan suke da shi da kasar Iraki ya kara da cewa tattaunawa tsakanin jami'an kasashen biyu kan kasar Iraki abu ne mai muhimmanci wanda kuma ya zama wajibi.

Imam Khamene'i ya kara da cewa: "Babu shakka yanayin da kasar Iraki take ciki lamari ne mai daga hankali saboda ci gaba da mamayan da sojojin Amurka suke wa kasar wanda hakan ya sanya kasar ta rasa wata takamammiyar makoma".

Har ila yau Jagoran, yayin da yake ishara da wajibcin hadin kai da 'yancin dukkan kasar Iraki, ya bayyana cewa: "Dole 'yan mamaya su gaggauta barin kasar Iraki, su ba wa al'ummar Iraki damar gudanar da mulkin kasarsu da hannunsu".

Yayin da kuma ya koma kan kasar Palastinu da kuma jaddada wajibcin da ke kan al'ummar musulmi da kasashensu wajen goyon bayan al'ummar Palastinun, Imam Khamene'i ya ce: "Goyon bayan al'ummar Palastinu ba wai kawai goyon bayan wata kasa ko kuma al'umma guda ba ne, face dai wani kokari ne na magance matsalar dukkan kasashen musulmi da na larabawa".

Yayin da kuma yake jaddada wajibcin taka tsantsan wajen fuskantar abokan gaba, Jagoran Juyin Juya Halin Musuluncin ya ce: "Kasar Amurka cikin shekaru hamsin din da suke wuce ta kasance tana goyon bayan haramtacciyar kasar Isra'ila ne, don haka idan dai ana magana kan lamarin Palastinu ne, Amurka za a lissafa ta ne a matsayin mai fuskantar al'umman musulmi, don haka babu yadda za ta kasance mai shiga tsakani".

Har ila yau yayin da yake ishara da karen tsayen da haramtacciyar kasar Isra'ilan take wa dukkan yarjejeniyoyin da aka sanya wa hannu na sulhu, Imam Khamene'i ya ce: "A irin wannan yanayi na rashin girmama yarjejeniyoyin da aka cimma da abokan gaban suke yi, hanya kawai ta magance wannan matsala ita ce hadin kai tsakanin larabawa da sauran al'umman musulmi da kuma ba da himmarsu wajen goyon bayan al'ummar Palastinu marasa kariya".

Shi ma a nasa bangaren, Sarkin Jordan din Abdullahi na biyu, yayin da yake bayyana jin dadinsa da wannan ziyara da ya kawo Tehran din ya ce: "Akwai bangarori da dama da za a bi wajen fadada alakar da ke tsakanin kasashen biyu, don haka ina fatan za a yi amfani da su wajen karfafa alakar Tehran da Oman".

Har ila Sarki Abdullahin ya bayyana matsalar kasashen Palastinu da Iraki a matsayin manyan matsalolin da suke fuskantar duniyar musulmi, inda ya kara da cewa: "Shawara da hadin gwuiwa tsakanin Iran da Jordan wajen kiraye manufofin dukkan bangarorin biyu zai taimaka wajen tabbatar da zaman lafiya a yankin".

Har ila yau Prime ministan Jordan din Abu Ragib ya gabatar wa Jagora da wani rahoto kan yadda lamurra suke gudana a yankin Gabas ta Tsakiya.

Haka nan kuma ministan tsaron cikin gida na kasar Jordan din shi ma ya gabatar wa Jagora Imam Khamene'i da rahoto kan mahangar kasarsa kan kasar Iraki, inda ya bayyana wajibcin hadin kai tsakankanin al'umma Iraki saboda yanayin halin damuwa da kasar take ciki.





-02 ga Satumban 2003

Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Ya Jinjina Wa Masana Ilmin Kimiyya Na Iran

Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Ayatullah al-Uzma Sayyid Ali Khamene'i (H) ya bayyana cewa irin nasarorin da masana Iraniyawa suke yi wajen kirkiro abubuwa da ya sanya sauran al'ummomi samun karfin gwuiwa wajen dogaro da kai na daga cikin abubuwan da suka sa makiya suke adawa da al'umman Iran din.

Jagoran ya bayyana hakan ne a yau Talata (2/9/2003) a yayin da yake maraba da wasu masana ilmin kimiyya na Iran wadanda suka sami nasarar kirkiro da kuma yawaita wasu matsi-matsin halitta, a lokacin da suka kai masa ziyara a gidansa dake Tehran yana mai cewa Juyin Juya Halin Musulunci na Iran ya kasance babban ummul aba'isin din 'yantar da duniyar musulmi daga danniya da mulkin mallakan ma'abuta son danniya na duniya.

Har ila yau Jagoran ya bayyana cewa wannan kokari da masanan suka yi wajen kirkiro wadannan kwayun halittu nesa ba kusa ba ya ruguza dukkan wani shingen da makiya suka sanya wa al'umman Iran din cikin shekarun baya-bayan nan don hana su amfanuwa da karfin da suke da shi.

Haka nan kuma yayin da yake ishara da irin nasarori da kirkire-kirkiren da matasa muminai Iraniyawa suka samu bayan nasarar Juyin Juya Halin Musulunci, Imam Khamene'i ya ce: "Dole ne a tuge jijiyan jin shu'urin gajiyawa a tsakankanin al'ummar Iran, don kuwa tun tsawon tarihi al'umman Iran sun tabbatar wa duniya a fili karfin da suke da shi a bangaren ilmi da nasarorinsa".

             

Koma Sama