Jawabin Jagora A Bukin Zagayowar Shekara ta 14 da Wafatin Imam Khumaini

  • Maudhu'i: Zagayowar Shekara ta 14 ga Wafatin Marigayi Imam.
  • Wuri: Haramin Imam Khumaini (r.a); Tehran.
  • Rana: 3/Rabi'al-Thani/1424 = 4/Yuni/ 2003.
  • Shimfida:A wannan rana ce Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Ayatullah al-Uzma Sayyid Ali Khamene'i (H), Ya gabatar da jawabi a Hubbaren Marigayi Imam Khumaini (r.a) saboda bukin zagayowar shekara ta 14 da rasuwar Imam din. Abin da ke biye shi ne fassaran wannan jawabi na Jagora.

    Jagora - Imam Khamene'i Tare Da Jikan Imam

    Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai

    Dukkan godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai, tsira da amincin Allah su tabbata ga Shugabanmu kana kuma Annabinmu Abul Kasim al-Mustafa Muhammad tare da tsarkakan Mutanen gidansa, shiryayyu masu shiryarwa, musamman ma dai Bakiyatullah (Imam Mahdi).

    Ranar Sha hudu ga watan Khordad (4 ga watan Yuni) na kowace shekara wata dama ce ga al'ummar Iran wajen sake nuna jinjinawa da mubaya'arsu ga koyarwa da kuma tafarkin Imam mai girma. Sai dai kuma duk da cewa duk cikin shekara al'umma a fili suna nuna ikhlasi da kuma kaunarsu ga wannan mutum mai girma wanda ba za a taba mancewa da shi cikin tarihinmu ba, to sai da kuma wannan rana ta Sha Hudu ga watan Khordad tana da nata abin da ta kebantu da shi; hakan kuwa saboda rashin wannan ni'ima mai girma da muka yi ne. To a saboda haka ne a wannan rana tsarkakakkun zukata, sama da kowane rana, suke jin cewa lallai ya zama wajibi su sake jaddada kauna da kuma sadaukarwarsu ga karfaffan jigon da wannan bawan Allah ya gina na Juyin Juya Halin Musulunci a wannan kasa.

    Ina ga yana da kyau in fara wannan jawabi nawa da wannan aya ta Alkur'ani mai girma, wannan Imam Mai girma ya kasance babban misdaki na wannan aya din. Cikin Suratul Sajdah, Allah Madaukakin Sarki, yayin da yake bayani kan yayanin al'ummomi da kuma muminai ma'abuta gwagwarmaya da kokari, Yana cewa:

    (وجعلنا منهم ائمه يهدون بامرنا لما صبروا وكانوا باياتنا يوقنون) "Muka kuma sanya shugabanni daga cikinsu masu shiryarwa da umarninMu don su yi hakuri, sun kuma kasance suna sakankancewa da ayoyinmu Nau'in mutane biyu da suka sami damar samar wa kawukansu wadannan abubuwa guda biyu to za su sami daukakuwa da wannan babbar ni'ima ta Ubangiji ta shiryar da al'ummomi.

    Wadannan abubuwa guda biyu kuwa su ne, guda dai shi ne hakuri gudan kuwa shi ne yakini; (لما صبروا وكانوا باياتنا يوقنون) yakini dai shi ne cikakken imani wanda waswasi ba ya iya raunani shi a zukata. Hakuri dai wata khususiyya ce wacce take ba wa dan'Adam mai girma damar tsayawa kyam akan tafarkin da ya zaba wa kansa cikin wa'ayi komai tsanani komai rintsi ba tare da ya juya da baya ba; ba ya taba juya baya ga manufofinsa ko kuma janyewa daga gare ta. Lalle dukkan Annabawa, dukkan masu shiryarwa haka nan suka kasance kuma dukkan mutanen da suka aikata wani abin yabo cikin tarihin dan'Adam sai da suka bi wannan tafarki, don haka ba ya kamata a yi sako-sako da wadannan abubuwa guda biyu. Hakika Marigayi Imam abin kaunarmu, wannan bawan Allah da ya jaddada rayuwar Musulunci a tsakanin al'ummarmu da kuma al'ummar musulmi, ya kasance ma'abucin wadannan abubuwa guda biyu.

    A yau, bayan shekaru arba'in da faruwar waki'ar Sha biyar ga watan Khordad (mafarin Juyin Juya Halin Musulunci), ku duba ku gani yadda wannan yunkuri na Imam ya mamaye dukkan duniyar musulmi.

    Wata rana a dai wannan gari na Tehran da kuma birnin Kum, kamar yau da gobe, an kashe wasu mutane ba tare da sun aikata komai ba, hakan kuwa don sun ambaci sunan Musulunci da kuma bin tafarkin Imam mai girma; don sun nuna rashin amincewarsu da mulkin bakin haure da kuma tatse arzikin wannan kasa. A wancan lokacin duk wanda ya ga abin da ya faru, zai yi tsammanin an kawo karshen irin wadannan jawabai da kuma irin wadannan take. A lokacin cikin dukkan ma'anar kalmar rashin imani da tausayi suka kama Imam da kuma tsare shi, sannan kuma suka fada wa jama'a da nufin kawo karshensu; to amma duk da haka wannan tafarki, bisa ka'idan nan ta Ubangiji - tagwaitakan hakuri da yakini - ya ci gaba ba tare da tsayawa ba.


    Ya ku masoyana! Ya ku al'ummar Iran madaukaka! (Ku duba ku gani) duk inda muka yi aiki da wannan wasiyya ta Imam, shin a bangare tsare-tsarenmu ne ko kuma a bangaren nadi da kuma cire wani jami'i ne, to lalle za ku ga mun sami nasara. Musulunci dai addini ne dake ba da muhimmanci ga nasara da kuma sa'adar dan'Adam.

    Imam, shekaru goma sha biyar ya yi yana gwagwarmaya, kuma saboda wannan imani nasa dake cike da wayewa ya samu damar fuskantar mulkin mallaka na cikin gida da kuma girman kai na kasa da kasa; lallai babu shakka a duk lokacin da al'umma suka yi tsayin daka (wajen fuskantar 'yan mulkin mallaka), to kuwa nasara tana tare da su.

    Wannan dai shi ne bambancin Imam mai girma da sauran masu gyara a addinin Musulunci cikin karni daya zuwa biyu na baya-bayan nan. Imam dai ta haka ya shigo filin daga, ya kasance tare da al'umma da kuma tattaunawa da su yana mai masu bayani kan koyarwa da kuma tafarkinsa ta haka kuma ya janyo su zuwa ga cikakken imani mai zurfi da kuma wannan tafarki nasa da kuma kokari wajen tabbatar da gaskiya da adalci ta hanyar koyarwa ta addinin Musulunci da kuma cikakken imani. Wasu dai sun gaza kuma sun gagara wajen bin wannan tafarki mai wahala, to amma Imam ya iya yin hakan. Kamar yadda kuma al'ummar Iran ma suka sami damar gano wannan tafarki, suka yi imani da shi kuma suka ba da himma wajen cimma wannan manufa. Sakamakon hakan dai shi ne samar da tsarin Musulunci na farko duk kuwa da irin gaba da makirce-makircen da ya fuskanta, kuma tun daga wannan lokaci har zuwa yau din nan a kullum jigon (tsarin) sai dada yaduwa yake yi; abu na biyu kuma shi ne fikirar sabunta da kuma rayar da Musulunci bugu da kari kan 'yantar da al'ummar musulmi daga zalunci da kuma girman kan manyan kasashe ma'abuta girman kai na duniya, kuma hakan bai ta'allaka da kan iyakokin wannan kasa ba.

    A halin da ake ciki, ko ina a duniyan nan kuka je - shin a yankin Gabas ta Tsakiya ne, ko kuma kasashen larabawa ko kuma arewacin nahiyar Afirka ko kuma kasashen gabashin nahiyar Asiya, a yankunan da al'ummar musulmi suka fi yawa - za ku ga cewa kaunar Musulunci, son tabbatar da mulkin Musulunci da kuma gaba da mulkin mallaka da fir'aunanci a tsakankanin al'umma, musamman ma dai matasa da kuma masana. A da dai babu irin wannan yanayi a kasashen musulmi, to abin tambaya a nan shi ne wani abu ne Imam ya yi riko da shi da ya sami damar haifar da irin wannan yanayi mai girma?

    Ana iya takaita madafa da madogaran wannan aiki na Imam dinmu mai girma akan abubuwa guda biyu, su ne: Musulunci da kuma al'umma. Wannan dogaro da al'umma da Imam mai girma ya yi imani da shi ya samo shi ne daga addinin Musulunci. Don kuwa Musulunci shi ne addinin da ya jaddada da kuma ba da muhimmanci kan hakkin al'umma da kuma muhimmancin da ra'ayinsu yake da shi cikin gudanar da lamurra. Don haka ne Imam mai girma ya riki Musulunci da kuma al'umma a matsayin madogarar aikinsa; daukakar Musulunci dai shi ne daukakan al'umma, kula da Musulunci, shi ne kula da al'umma, haka nan kuma rashin nasarar Musulunci, rashin nasarar al'umma ne.

    Mafi muhimmancin aikin da Imaminmu mai girma ya yi a duniyar Musulunci shi ne rayar da bangarori daban-daban na siyasa da zamantakewa na Musulunci. Daga lokacin da mulkin mallaka ya shigo kasashen musulmi, babban kokari da kuma aikin da suka fi ba shi muhimmanci shi ne shafe bangarorin siyasa da zamantakewa na Musulunci da kuma kira zuwa ga adalci da kuma 'yancin da Musulunci ya ke jaddadawa. 'Yan mulkin mallaka dai suna ganin cewa matukar dai suna son mallake al'umma da kuma dimbin arzikin kasashen musulmi; to fa dole ne ta ko wace hanya su raba Musulunci da bangarorinsa na siyasa, su mai she shi matsayin mika kai ga 'yan mamaya, mika kai ga abokin gaba ma'abucin karfi.

    Hakika Imam ya raya sanannun al'amurra na Musulunci; shi ne ya daga taken adalcin Musulunci sama, sannan kuma ya bayyanar da adawar da Musulunci yake yi ga nuna wariya da kuma bambanci tsakanin dabaka-dabaka ta al'umma. Tun daga ranar farko dai har zuwa ranakun karshe na rayuwarsa, Imam mai girma ya kasance ne tare da dabakar raunanan mutane da marasa galihu. A lokuta daban-daban, tun lokacin kafa tsarin Musulunci da kuma shekaru goma da yayi a matsayin Jagoran tsarin Musulunci, Imam ya sha jaddada wa jami'an gwamnati, gare mu gaba daya, kan kula da raunanan mutane, ya kasance yana tunasar da su cewa akwai bashin talakawa akansu.

    Ya ku masoyana! Ya ku al'ummar Iran madaukaka! (Ku duba ku gani) duk inda muka yi aiki da wannan wasiyya ta Imam, shin a bangare tsare-tsarenmu ne ko kuma a bangaren nadi da kuma cire wani jami'i ne, to lalle za ku ga mun sami nasara. Musulunci dai addini ne dake ba da muhimmanci ga nasara da kuma sa'adar dan'Adam.

    Addinin Musulunci dai addini ne da ke fada da fasadi, zalunci da wariya. Musulunci ya zo ne don jin dadin al'umma tare da kula da abubuwan da suke gina ruhi, wannan lamari kuwa shi ne abin da Imam mai girma ya sha jaddadawa a lokuta daban-daban tun farkon gwagwarmaya har lokacin da aka kafa tsarin Musulunci har kuma zuwa karshen rayuwarsa. Imam abin kaunarmu ya nuna wa duniyar musulmi yadda fikihun Musulunci (wato dokoki masu tsara rayuwar mutane) tare da falsafar Musulunci (wato ingantaccen tunani mai zurfi da kuma hujja) da kuma irfani na Musulunci (wato guje wa duniya da kuma komawa gaba daya ga Allah Madaukakin Sarki da nesantar burace-buracen rai) za su iya haifar da babbar mu'ujiza. A aikace Imam ya tabbatar da cewa Musuluncin siyasa shi ne dai Musulunci na ruhi da ma'anawiyya. Duk tsawon lokacin mulkin mallaka, makiya Musulunci da kuma farkawar da musulmi suke yi, suke ta yada farfagandar cewa akwai bambanci tsakanin Musulunci na ma'anawiyya da aiki da kuma Musulunci na siyasa, har yau din nan ma dai irin farfagandar da suke yadawa kenan. A yau ma dai 'yan barandan makiya da kungiyoyin da ke gaba da tsarin Musulunci, ta hanyoyi daban-daban na karya kokari suke su nuna Musulunci na siyasa, neman adalci da zamantakewa a matsayin tashin hankali da amfani da karfi, a bangare guda kuma suna kwadaitar da mutane riko da Musuluncin da ke mika wuya, musuluncin da ba shi nuna wata damuwa ga azzalumai masu wuce gona da iri. Imam dai irin wannan Musulunci na karya ya ruguza da kuma kawo Musulunci na asali.

    Wannan Musulunci da Imam ya gabatar shi ne dai wannan Musulunci da ke adawa da da zaman jagwam, camfe-camfe da kuma riko da tafarkin mika kai ga bakin haure. Tun wancan lokaci, da ma tsawon shekarun gwagwarmaya don kafa tsarin Musulunci, kai har ma zuwa yau din nan, wannan batu na raba addini da siyasa na daga cikin abubuwan da abokan gaba suke ci gaba da jaddadawa. Wato duk mutumin da yake so ya zama musulmi to dole ya mika kansa, ya koma gefen fili ya zauna, babu ruwansa da abin da abokan gaba da 'yan mamaya suke aikatawa. A halin yanzu ma dai irin wannan farfaganda suke yadawa, to sai dai kuma Imam sabanin wannan akida ya gabatar wa al'ummar musulmin duniya, kuma a yau din nan dukkan al'ummomi suka rungumi wannan akida ta Imam. A yau din nan ko ina kuka duba a duk fadin kasashen musulmi, za ku ga rayayyen Musulunci ne ya ke yawo tsakanin matasa, 'yan boko, masana da ma'abuta 'yanci, wannan Musuluncin da ya iya kare al'umma daga makircin manyan kurayen duniya ma'abuta girman kai da wuce gona da iri, wanda kuma ya hana makiya damar tsoma baki da kuma mallake al'umma. Wannan dai shi ne Musuluncin da ake so, wannan kuma shi ne asalin Musuluncin Muhammadiyya.

    To a bangaren al'umma kuwa, babban aikin da Imam ya aikata shi ne banbance tsakanin ma'anar demokradiyya ta hakika da kuma abin da masu ikirarin demokradiyya da 'yan korensu suke fadi. Abin da dai su wadannan makiya suke kokarin nunawa shi ne cewa demokradiyya ta al'umma da kuma hukuma ta addini abubuwa ne guda biyu da ba za su taba haduwa guri guda ba. To sai dai Imam ya ruguza wannan ikirari na su na karya, yayin da ya kaddamar wa duniya asalin demokradiyya wato wannan Jamhuriyar Musulunci (da kuke gani), Imam dai ba wai kawai ya takaita ne da zance baki ba kafa hujjoji ba, face dai ya tabbatar da hakan ne a aikace.

    A yau din nan tsarin Jamhuriyar Musulunci - wanda ya kasance wani tsari ne na addini wanda dukkan kafafunsa sun dogara ne akan akidu na addini - ya zamanto tsari ne na demokradiyyar al'umma ta hakika, kuma a duk fadin duniyan nan ba za ka taba samun wata kasa da take da tsarin mulkin na al'umma mai fadi kamar wadda ya ke a nan Jamhuriyar Musulunci ba. Babu shakka wannan lamari kuwa wani abu ne mai bakanta rai ga abokan gaba wadanda a koda yaushe ba sa so su ga tutar addini da demokradiyya tana kadawa. Abokan gaba dai kokari suke su sanya Katanga tsakanin addini da demokradiyya, don haka ne Jamhuriyar Musulunci take sanya bakin ciki da damuwa cikin zukatansu. Don wofantar da hankulan duniya ne suke amfani da kafafen watsa labarai da farfagandojinsu wajen kiran Iran zuwa ga tsarin demokradiyya, babu shakka hakan na daga cikin abubuwan ban dariya na duniya da kuma tarihi.

    (Abin dariyan dai shi ne) wadannan mutane da suka amince da gwamnatin kama-karya da babakere ta Shah Pahlawi, da kuma sauran gwamnatoci da ma ba su san ma'anar kalmar demokradiyya ba ko kuma ma ba su yarda da ita ba, amma suna kiran gwamnatin Musulunci na Iran, wacce cikin shekaru ashirin da hudu da kafuwarta ta gudanar da zabubbuka sama da ashirin, kuma jami'anta tun daga jagora, shugaban kasa da 'yan majalisu duk al'umma ne suke zabensu kai tsaye ko kuma ba kai tsaye ba, haka nan kuma al'umma sun san su kuma sun amince da su, zuwa ga demokradiyya. Lalle wannan abin dariya ne. Alhali kuwa irin demokradiyya da kuma shaukin da al'umma suke da shi wajen kada kuri'a wajen zaben jami'an gwamnatin da ake da shi a Iran ko a Amurka - wacce ta kasance abokiyar gabanmu ce wacce kuma take daga muryar farfaganda a kanmu - ba za a samu irinsa ba. Kai shugaban Amurka ma na yanzu ta hanyar da ta saba wa demokradiyya ya dare karagar mulkin kasar, wannan lamari ne dai da kowa ya san shi. Wadannan mutane dai suna da alaka da gwamnatocin kama-karya kuma sun amince da su, hakan kuwa saboda suna mika musu kai ne, to amma tsarin Musulunci, wanda ya yi amanna da 'yancin kai da kuma dogaro da akidun da ya yi imani da su, kuma ba a shirye yake da ya mika kai ga mulkin danniyarsu ba, ba su amince da shi ba, kai ya ma kasance abin zargi da tuhuma da take hakkokin 'yan'Adam daga bangarensu.

    A halin da ake ciki, dukkan kokarin abokan gaban Musulunci ya dankaru ne akan kokarin kawar da wayewar Musuluncin da al'umma suka samu musamman ma a Iran, hakan kuwa don al'ummar Iran sun kasance abin koyi ne ga al'ummomin duniya, don babu shakka sun fitar wa al'ummomin da wani sabon salo, haka nan kuma ta hanyar sadaukarwa da jaruntar da al'ummar Iran din mazansu da matansu, yaransu da manyansu suka nuna cikin wadannan shekaru ashirin da hudu na nasarar Juyin Juya Halin Musulunci, sun samu nasarar farkar da al'ummar musulmi da kuma jawo hankulansu zuwa ga hasken Musulunci, don haka ne wannan gaba da kiyayya akan Iran din ta fi na ko ina. Don haka ne ta hanyoyi daban-daban suke ta yada karairayi da kuma tuhumce-tuhumce akan Iran din, sai dai manufar hakan ita ce razanar da al'umma da kuma jami'an gwamnati, don kowa ya ji tsoro. So suke su yi amfani da tajruban da suke da shi maras nasara da yake sa su girman kai wajen sanya wannan al'umma ma'abuciya irin wannan daukaka da kuma wannan juyin juya hali da ke da irin wannan yanayi na tsayin daka a gaban abokan gaba su razana da kuma mika kai.


    Duk da cewa dai a lokuta da dama na sha gaya wa jami'an gwamnati, kuma a yau ma zan sake nanatawa: Hidima wa wannan al'umma shi ne babban fada da Amurka, duk wani wanda yake son ya yi fada da Amurka fada na asasi, to dole ne ya yi hidima ga wannan al'umma. Duk wani wanda yake son fada da abokan gaban wannan al'umma a aikace, to dole ne ya yi fada da fasadi.
    Haka nan kuma suna amfani da kafafen watsa labaransu wajen tuhumar Jamhuriyar Musulunci ta Iran da goyon bayan ta'addanci ko kuma cewa suna ba wa 'yan ta'adda mafaka, hakika wannan wata karya ce da take tare da wauta da rashin jin kunya. Idan har abin da suke nufi da 'yan ta'adda shi ne mutanen da saboda son zuciyarsu suke cutar da mutanen da ba su ci ba su sha ba, to muna iya cewa a halin da ake ciki manyan 'yan ta'addan duniya suna karkashin kulawan Amurka ne inda suke ci gaba da ayyukansu. A yau din nan babban alamar ta'addanci a duniya haramtacciyar kasar Isra'ila ce, ku duba ku gani shin akwai wata rana da 'yan ta'addan yahudawan sahyoniya ba za su kai hari wa Palastinawa da suke cikin gidansu, suke rayuwa a kasarsu ba? Ba mu mance ba, a shekarun baya da suka wuce a makwabtanmu, mun ga yadda Amurkawan suka samar da wasu 'yan ta'adda masu tsananin ra'ayin rikau da nufin kawo cikas wa Jamhuriyar Musulunci ta Iran; sai dai sun gagara cimma wannan manufa ta su. A yau din shika ta koma kan mashekiya, don wadannan 'yan ta'adda da Amurkawan suka kawo su don cutar da Jamhuriyar Musulunci, a yau sun zamanto musu karfen kafa kuma suna cutar da su.

    Su dai wadannan mutane suna tuhumar Iran da ayyukan ta'addanci! To Iran dai ba ta goyon baya da taimaka wa ta'addanci, kuma ba ta ba wa kowani dan ta'adda mafaka kuma ma ba ta taba bayarwa ba. Amma dai Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi imani da cewa akwai miliyoyin matasa da ma'abuta 'yanci a duk fadin duniyar musulmi da suke gaba da mamaya da zaluncin Amurka, lalle ba za ku iya kiran wadannan 'yan ta'adda ba, lalle ba ku da ikon lakaba wa miliyoyin al'ummomin da suke Iraki, Masar, Saudiyya, Arewacin Afirka, Pakistan da Afghanistan sunan 'yan ta'adda. A halin da ake ciki akwai miliyoyin mutanen da suke gani (da kuma dandana) zaluncin sojojin Amurka - a Afghanistan a jiya ko kuma a kasar Iraki da ake zalunta a yau - shin wadannan 'yan ta'adda ne? Haka nan shin Palastinawa da suke fada don kare kasarsu su ma 'yan ta'adda ne? Al'ummar Palastinu da a kullum suke fuskantar makaman tankunan yakin yahudawan sahyoniya wajen kare kasarsu su ma 'yan ta'adda ne? Shin matasan kasar Labanon ma'abuta imani da suke tsayin daka wajen fuskantar wuce gona da irin yahudawan sahyoniya, kuma suka ba da rayukansu wajen korar yahudawan daga kasarsu, sannan kuma a halin yanzu kasantuwansu ya zamanto kafar ungulu ga yahudawa ta yadda ba sa iya jaruntar kai wa kasar Labanon hari, su ma 'yan ta'adda ne? Hakika da a ce wadannan muminan matasa 'yan gwagwarmayan kasar Labanon ba sa nan, to lalle da haramtacciyar kasar Isra'ila ta samu damar shigowa har cikin garin Beirut, kamar yadda kudancin Labanon ya kasance karkashin mamayansu na wasu shekaru, sun iso har birnin Beirut inda suka aikata aika-aikan da suka aikata wanda ba zai taba fakuwa daga zukatan al'ummomi ba. Haka wadannan muminan matasa na kasar Labanon suka zage damtse, suka amshi kira da farkawar da Imaminmu mai girma ya ba wa duniyar musulmi sannan kuma suka yi tsayin daka. Irin wannan tsayin daka na wadannan matasa ne dai ya sa haramtacciyar kasar Isra'ila ba za ta iya bugan kirji ta kai wa Labanon hari ba, shin wadannan ma 'yan ta'adda ne? 'Yan ta'adda dai su ne wadanda suke kai wa mutane hare-hare a cikin gidaje, garuruwa da kasashensu.

    A yau din nan zukatan duniyar musulmi cike suke da gaba da mamayan da (Amurka) ta yi wa Iraki. Shin me ya sa kuka mamaye kasar Iraki? Shin me ya sa ba za ku bar al'ummar Iraki su zaba wa kawukansu abin da ya dace da su ba? Mene ne banbancinku da Saddam? Saddam ma dai dan kama-karya ne ku ma dai 'yan kama-karya ne. Saddam dai ta wata hanya ya ke irin nasa kama-karyar, ku ma ta wata hanya kuke taku kama-karyar, (mene ne banbancinku?), sai dai babu wani abin da za ku iya yi.