MACE A RA'AYIN JAGORA, IMAM KHAMENE'I

Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Ayatullah al-Uzma Sayyid Ali Khamene'i (h) dai na daga cikin mutanen da suka fi ba da muhimmanci ga mata da kuma kare hakkokinsu, saboda irin matsayin da suke da shi wajen gida al'umma ta gari abin yabo a koda yaushe. Mace dai tana da wani matsayi na musamman a idon Jagoran, kamar yadda take da shi a idon dukkan wani mutum ma'abucin son gaskiya, musamman ma wanda ya yi riko da koyarwa irin ta Musulunci, don kuwa Musuluncin addini ne da ya zo don 'yanto mace din daga halin zalunci da ta kasance a ciki tsawon tarihi.

Bisa la'akari da hakan ne ma ya sa a lokuta da dama Jagoran ya sha maganganu kan kula da hakkokin matan da kuma kira ga 'yanto su daga cikin halin Sabuwar Jahiliyya da suka samu kansu a cikin a wannan duniya tamu.

Don haka ne na dan tsakuro mana wasu daga cikin maganganun da Jagoran ya yi a lokuta daban-daban kan mata da kuma irin gudummawar da za su iya bayarwa wajen haifar da al'umma saliha.

Abin da ke biye, kadan ne daga cikin irin wadannan kalamai nasa. Don haka ka na iya zaban maudhu'in da kake son a kasa don ganin abin da ya kunsa.

A sha karatu lafiya.

Mace A Mahangar Musulunci Gudummawar Mace Yayin Juyin Musulunci
Manufar Musulunci Na Kare MaceBa Da Himma Don Mata
Zaluntar Mace A Mahangar MusulunciAikin Mace
'Yancin Mace A TuraiMuhimman Abubuwan LuraMACE A MAHANGAR MUSULUNCI

Musulunci dai addini ne dake kira zuwa ga kamalar dan'Adam, babu wani banbanci a gurinsa tsakanin namiji da mace. Shi dai addini ne da ke daukaka matsayin mace a bangare guda a bangare guda kuma ya daukaka matsayin namiji gwagwardon yadda yanayi ya bayar a matsayinsu na rukunin duniyar 'yan Adam. Su dai wadannan halittu guda biyu ba su da wani banbanci kome kashinsa a bangaren siffofinsu na 'yan'Adam da kuma a mahanga ta Ubangiji....

Musulunci dai ba ya wulakanta jinsin dan'Adam namiji ne ko mace, abin da yake da muhimmanci a wajensa shi ne dabi'ar mutum, bunkasa baiwar da yake da shi da kuma sauke nauyin da ke wuyan kowani guda daga cikin wannan jinsi na dan'Adam (mace ce ko namiji).

Musulunci dai ya san yanayin kowani guda daga cikin maza ko mata cikakkiyar masaniya, don haka ne ma yake ba da muhimmancin gaske ga batun adalci da daidaito tsakanin dukkan 'yan'Adam daga cikinsu kuwa shi ne daidaito tsakanin mace da namiji.

Haka nan kuma Musulunci yana ba da muhimmanci ga daidaito wajen hakki tsakanin mace da namiji duk da cewa akan samu sabanin hukumci tsakaninsu gwargwadon yadda yanayi ya kasance.

MANUFAR MUSULUNCI NA KARE MACE

Manufar Musulunci dai na wajen kare mace ita ce don kada ta fada tarkon zalunci ne, don ka da namiji ya ji cewa yana da iko da daukaka akanta. Iyali dai suna da hakki da kuma iyaka, namiji na da nasa hakkin kamar yadda mace mace ma dai take da nata hakkin, wadannan hakkoki kuwa an tsara su ne bisa adalci da daidaito. Mu dai ba za mu amince da jingina duk wata shara ga Musulunci ba, ra'ayin Musulunci dai a wannan bangare dai a fili yake, shi ne kuwa tabbatar da daidaituwa ga dukkan namiji da mace cikin iyali.

ZALUNTAR MACE A MAHANGAR MUSULUNCI

Irin yanayin da namiji da mace suke ciki a rayuwa ta iyali, ya kan sa a samu alaka ta soyayya da kauna tsakaninsu, duk da cewa a wasu lokuta akan samu faruwar zalunci idan wannan alaka ta ci gaba.

A wasu lokuta namiji (mai gida) ya kan gudanar da mu'amala a gidansa tamkar sarki, ko kuma ya kalli mace da kallo na kaskanci da wulakanci, wannan dai zalunci ne. Abin bakin cikin dai shi ne da dama daga cikin mazaje suna aikata wannan zaluncin.

Haka yanayin ma dai yake a wajen rayuwa ta iyali. Matukar dai aka hana mace samun dama ta neman ilmi, aiki, neman halal da hutu, to wannan ma dai zalunci ne da dole ne a hana faruwarsa.

Haka nan zalunci ne hana mace samun ilmi da ingantacciyar tarbiyya, kamar yadda hana mace iko kan abubuwan da ta mallaka cikin 'yanci da walwala zalunci ne.

Haka nan kuma zalunci ne a hana mace hakkin zabin miji da tilasta mata mijin da ba shi take so ba.

Kamar yadda kuma hana mace damar amfana da kuma aiwatar da baiwar da take da shi na ilmi, kirkire-kirkire da harkokin siyasa zalunci ne.

Wajibi ne kawar da dukkan nau'oi na zalunci, to sai dai kuma a daidai wannan lokaci, wajibi ne a yi dubi da idon basira ga nauyin da mace da namiji suke da shi wajen gina iyali, don kuwa hakan tafarki ne na sa'adar namiji da mace.

'YANCIN MACE A TURAI

Taken da ke yawo a yammanci dai shi ne 'yancin mace...to amma abin bakin ciki shi ne cewa mafi girman abin da za a iya fahimta dangane da ma'anar wannan 'yanci a kasashen yammaci shi ne ma'anarsa mai cutarwa wanda aka cakuda shi, wato 'yanci daga dokoki na iyali, ficewa daga katanga irin ta aure da kuma yin karen tsaye wa dokoki da sharuddan iyali da tarbiyya yara...lalle wannan ba shi ne ingantaccen ma'ana na 'yancin mata ba.

GUDUMMAWAR MACE YAYIN JUYIN MUSULUNCI

Hakika mace dai bayan nasarar Juyin Juya Halin Musulunci ta samu gagarumar girmamawa, babban wanda ya ba ta wannan girmamawa kuwa shi ne Imam (Khumaini) wanda ya kasance yana girmama matan Iraniyawa musulmi, dukkan girmamawa. Irin wannan mahanga tasa kuwa ita ce ta sanya mata ba da gudummawa ga wannan juyi na Musulunci, ta yadda ana iya cewa ba don irin wannan gudummawa ta mata ba, da akwai yiyuwar cewa da ba a samu nasara da irin wannan yanayi ba, ko kuma ma dai da ba a samu nasarar ba, ko kuma ma dai da ba a samu nasarar ba, ko kuma da an samu wasu matsaloli. Bisa hakan ne kasantuwan mata ta bude hanyar nasarar wannan juyi. Haka dai matan suka kasance duk tsawon lokacin kallafaffen yaki da dai sauran abubuwan da suka shafi wannan juyi tun farko-farkonsa har zuwa yau din nan.

BA DA HIMMA DON MATA

Hakika mun kasance masu kokari da ba da himma don mace ta samu isa zuwa ga kamala, wato a mataki na farko dai mace ta samu hakkokinta na 'yan'Adamtaka cikin al'umma, sannan a mataki na biyu kuma don ta samu damar bunkasa baiwar da take da shi don daga karshe dai ta isa zuwa ga cika ta dan'Adamtaka da kuma samun matsayanta na 'yan Adam a tsakankanin al'umma, kana kuma ta samu damar ba da gudummawar da za ta iya wajen ci gabantar da al'umma daga da kuma duniya baki daya.

AIKIN MACE

Musulunci dai bai hana mace yin aiki ba sai dai a wasu yanayi na musamman, to sai dai babban abin da ke da muhimmanci ba shi ne mace ta samu aiki ko kada ta samu ba, face dai abin da ke da muhimmanci wanda kuma a yau kasashen Turai sun rasa shi, shi ne tabbatuwar tsaro da kwanciyar hankali ga mace da kuma ba ta damar bunkasa baiwar da Allah ya yi mata. Bugu da kari kuma kada ta kasance abin cutarwar zaluncin al'umma da dai sauransu. Wannan dai shi ne abin da ya kamata masu kula da al'amurran mata su ba shi muhimmanci.

MUHIMMAN ABUBUWAN LURA

Anan dai zan so in yi nuni da wadansu muhimman abubuwa da suke bukatuwa da a lura da su:

 1. Bunkasa tunanin mace a bangaren kyawawan dabi'u da ruhi, su kansu mata ana bukatarsu wajen yada ingantaccen tunani tsakaninsu da kuma ba da muhimmanci ga masaniyya da bincike kan manyan lamurra na rayuwa...
 2. Yin gyara ga dokoki, don kuwa wasu dokokin da suka shafi maza da mata suna bukatuwa da kwaskwarima. Wannan kuwa lamari ne da ya hau kan masana wadannan dokoki da suke bukatuwa da gyara.
 3. Akwai wasu abubuwa da suke tasowa da suke sanya ba wa wannan lamari muhimmanci, hakan kuwa shi ne wajibcin kariya ta kyawawan dabi'u da dokokin da suka shafi mace musamman cikin iyali, kuma ana samun kariya ta doka ne ta hanyar gyara dokoki
 4. Kame kai dai a gurin mace na daga cikin abubuwa masu muhimmanci a shaksiyyarta wanda ya zama wajibi ta kiyaye kuma kada ta yi wasa da shi. Musulunci dai yana ba da muhimmanci mai girman gaske ga batun kame kan mata, kamar yadda kame kai ga namiji ma dai abun so ne. Ba da muhimmanci ga batun kare kai da riko da hijabi suna daga cikin abubuwan da Musulunci ya sha jaddadawa akansa.
 5. Akwai kuma batun tarbiyya da neman ilmin mata, wanda na daga cikin abubuwan da a fili Musulunci ya yi magana da ba da muhimmanci gare su.
 6. Maudhu'i na karshe shi ne wajibcin kafa dokoki da ukuba akan duk wani wanda yake kokarin keta hurumin mata, kuma wadannan dokoki dole ne su hada da azaba mai tsananin gaske da irin wadannan mutane.
 7. Ku duba wannan aya mai girma da kuma abubuwan da suke cikinta dangane da mace da namiji a cikin zamantakewa ta iyali kan batun hakkoki. Wannan aya dai tana cewa: (و من ءاياته آن خلق لكم من آنفسكم آزواجا)  "Kuma akwai daga ayoyinSa, Ya halitta muku matan aure daga kanku.."., wato ma'anar Ya halitta muku mata Ya ku mazaje haka kuma ma mata Ya halitta muku maza "daga kanku" wato ba wai daga wani jinsi na daban ba, ba daga wasu abubuwa guda biyu ba face dai daga abu guda da kuma zati guda, duk da cewa dai akwai wadansu 'yan banbance-bambance na halitta, wannan kuwa saboda sabanin yanayi da halin da ake ciki ne.

  Daga nan sai Allah Madaukakin Sarki ya ce: ( لتسكنوا اليها ) "Domin ku natsu zuwa gare ta", wato ya sanya aure a matsayin dabi'a ta dan'Adam saboda wata manufa mai girma, hakan kuwa shi ne samun kwanciyar hankali da nitsuwar dukkan bangarorin biyu namiji ko mace.


  Matsa Wannan Alama Don Komawa Sama