"Idan Kuna Tunani Cewa Kuna Iya Samun, A Duk Duniya, Mutum Guda Daga Dukkan Shuwagabannin Kasashe, Sarakuna Da Sauransu Wajen Sadaukar Da Kai Ga Musulunci Kamar Sayyid Khamene'i Kuma Wanda Zuciyarsa Take Cike Da Shaukin Hidima Wa Al'umma, Lallai Ba Zaku Iya Samu Ba"----- IMAM KHUMAINI (R.A).

AYATULLAHIL UZMA SAYYID ALIYU KHAMENE'I
HAIHUWA DA DANGANTAKARSA KARATUNSA
KOYARWARSAGWAGWARMAYARSA
MUKAMAN DA YA RIKEJAGORANCINSA

HAIHUWA DA DANGANTAKARSA
An haifi mai girma Ayatullahil Uzma Sayyid Aliyu Khamene'i ne a shekarar 1939 a garin Mashhad mai tsarki na kasar Iran. Mahaifinsa shi ne Ayatullah Haj Sayyif Jawad, yana daga cikin fitattun malaman garin na Mashhad kana kuma shahararren mai wa'azi. Mahaifiyarsa kuwa ta kasance 'ya ce Sayyid Hashim Najafabadi, shi ma sanannen malami ne a nan birnin Mashhad din. Ta kasance mace ce mai tsoron Allah da lamewa, kana kuma ma'abuciya ilimin addini.
Ayatullah Khamene'i ya girma ne a karkashin kulawan mahaifinsa, wanda yake muhimmmancin gaske wajen tarbiyantar da 'ya'yayensa, don haka bai bata lokaci ba wajen tarbiyantar da shi wannan madaukakin da nasa (Ayatullahi Khamene'i). Koda yake dai rayuwa dai bata kasance cikin da sauki ba a lokacin gare su saboda irin tsanannin talaucin da suke fama da shi a lokacin. Dangane da wannan lamari, an ruwaito Sayyid Khamene'i yana cewa: " Ina iya tunawa a wasu lokutan ma bamu ko abin da zamu ci, a wasu lokutan mahaifiya ta takan karbi kudin da kaka na ya bani kyauta da ni da 'yan uwana, don ta saya mana abinci mu ci"
KARATUNSA
Lokacin da Ayatullah Khamene'i ya kai shekaru 5 a duniya, sai mahaifinsu ya tura shi tare da wansa Sayyid Muhammad zuwa makarantar karatun Alkur'ani mai girma, inda aka sanya su a wata makarantar piramare ta addini mai suna "Darut Ta'alimi Diyanati". To bayan da ya gama wannan makaranta sai ya fara halartar karatu a wata makaranta ta hukuma, amma ba tare da sanin mahaifinsa ba, inda ya samu satifiket. Daga nan sai ya shiga makarantar sakandare na shekaru biyu inda nan ma ya samu satifiket.
To a bangaren karatun addini kuwa, ya fara ne da karantan nahawun larabci, inda ya karanci littafin nan na "Jami'al Muqaddimat" a wajen mahaifinsa. Yayin da ya kai shekaru 14, sai ya shiga wata makaranta da ake ce ma Sulaiman Khan inda yaci gaba da karatun addinin musulunci. Inda yaci gaba da karatu, daga baya kuma sai ya koma wata makarantan kuma don kare wannan marhala na karatun nasa (sutuh) lokacin kuwa yana dan shekara 16 da haihuwa. Hakan ya bashi daman shiga marhala ta gaba wato Bahthul Kharij karkashin kulawan Ayatullahil Uzma Sayyid Milani.
Ayatullah Khamene'i, baya ga karatun fikhu da kuma usulu, ya kuma karanci falsafan musulunci, Ilmul Rijal, Ilmul Diraya, Ilimin Taurari, Tafsirin Alkur'ani da dai sauransu. Yayi karatu a wajen sanannun malamai kamarsu Ayatullah Mirza Jawad Agha Tehrani, Ayatullahi Hakim, Imam Khumaini, Ayatullahil Uzma Burujurdi da kuma Allamah Tabataba'i.
Ayatullahil Uzma Khamene'i ya gabatar da kusan dukkan ranakun dalibtansa ne a garin Masshad, koda yake a shekarar 1947 ya tafi birnin ilimin nan na Najaf, inda yayi karatu na shekaru biyu. Daga baya a shekarar 1958 ya koma garin Kum don ci gaba da karatunsa, inda ya zauna har na tsawon shekaru shida
KOYARWANSA
Ayatullahil Uzma Khamene'i ya fara koyarwa ne tun lokacin yana dalibi. Ya kasance ya kan karantar da abubuwan da ya karanto kuma cikin kwarewa, don kuwa an shaide shi da kwazo, hazaka da kuma fahimta cikin gaggawa. Dangane da hakan an ruwaito shi yana cewa:
"Na fara koyarwa ne tun daga lokacin da na gama makarantar piramare, yayin da nake karatu a makarantar addini. Har zuwa shekarar 1958, lokacin da nake Mashhad, na kasance ina karantar da nahwun larabci, balagah, usulul fikihu da kuma fikhu. A yayin da nake garin Kum, na hada karatu da karantarwa. Bayan dawowa ta Mashhad daga Kum a shekarar 1964, karantarwa ta kasance babban aikin da nake yi. Tun daga wannan lokacin har zuwa shekarar 1977, na kasance ina karantar da dalibai littafa irinsu Makasib, Kifaya da Aka'id".
A shekarar 1974 ne, Ayatullah Khamene'i ya sami darajar kai wa ga ijtihadi daga wajen malaminsa Ayatullahil Uzma Ha'iri, bayan da yayi shekaru 15 yana halartar Bahthul Kharij. Saboda irin tsananin kauna karatu da bincike na ilimi, an shaida cewa Ayatullahi Khamene'i bai bar karatu ba duk kuwa da irin ayyukan da suka masa yawa bayan samun nasarar Juyin Juya Halin Musulunci.
GWAGWARMAYARSA
Ku san ana iya cewa Ayatullah Khamene'i ya gabatar da rayuwarsa ne wajen gwagwarmaya da kokarin tabbatar da gaskiya, imma dai ta hanyar rubuce-rubuce da kalamominsa, ko kuma ta hanyar daukan makami, musamman ma bayan da Marigayi Imam Khumaini (r.a) ya kaddamar da gwagwarmayan musulunci a shekarar 1963. Hakika ana iya cewa bayani kan gwagwarmayansa yana bukatan manya-manya littattafai, to amma dai bari mu kawo shi a takaice.
A saboda amsa wannan kira na Imam, makarantun addini da suke birnin Kum sun taka gagarumar rawa, inda malamai da daliban wadannnan makarantu suka sha alwashin yada wannan kira zuwa kowane lungu na kasar Iran. Inda suka ci gaba buga irin wadannan kiraye-kiraye kana da yada su ko ina. To ta haka wannan kira ya yadu zuwa sauran makarantun addini na kasar, musamman ma a makarantun addini na garin Mashhad.
To daga cikin wadanda suka yada wannan kira, ana iya cewa Ayatullah Khamene'i ya taka babbar rawa wajen wannan aiki. Baya ga irin kokarin da yake yi a garin na Kum, yaci gaba da yada wannan kira da kuma hada gwuiwa da maluman Mashhad, a sabili da irin wannan goyon baya da ya samu a wajen malaman na Mashhad, hakan ya taimaka masa wajen isa da wannan sako zuwa ga sauran dalibai na wannan gari mai alfarma.
Wannan gagarumin aiki da yake yi na wayar wa mutane kai da kuma tona asirin gwamnatin Shah ta wancan lokacin, ya sanya gwamnatin ta kama shi da kuma tsare shi cikin mummunan yanayi da kuma gallazawa. Bayan da aka sako, sai yayi shawarar ci gaba da zama a garin na Mashhad maimakon komawa garin Kum ko kuma Tehran. Inda yaci gaba da karantar da Alkur'ani da kuma dada wayar wa al'umma kai musamman ma matasan cikinsu da kuma yada ra'ayuyyukan wannan kira, hakan kuwa ya janyo masa kauna da shahara a idon al'umman garin Mashhad. A sabili da irin wannan jarunta tasa da kuma irin dimbin hikimar da Allah Ya yi masa bugu da kari kuma kan kyawawan dabi'un da yake da su, ya sanya makarantu da kungiyoyi daga garuruwa irinsu Isfahanm Kerman, Yazd da Tehran suka dinga gayyatarsa don bada laccoci da kuma bayanai kan wannan kira. Inda bai yi wata-wata ba yaci gaba da yada wannan kira da kuma dada tona asirin azzaluman hukumar wannan lokacin.
Baya ga irin laccocin da ya dinga yi, haka kuma littafan da ya rubuta ko kuma ya fassara sun taimaka nesa ba kusa ba wajen ci gabantar wannan kira na Imam (r.a), misali littattafa irinsu "Yarjejeniyar (sulhun) Imam Hasan (a.s)", "Gudummawar Musulman Kasar Indiya Wajen Farkar da Mutanen Kasar", sun taimaka sosai wajen wayar wa matasa kai.
Bayan rasuwar Ayatullahi Burujurdi a shekarar 1970, Sayyid Khamene'i ya gudanar da aiki tukuru wajen fitar da girman Imam da kuma matsayinsa na Marja'i. Don haka sai ya ci gaba da ilmantar da matasa kan koyarwa irin ta addini da kuma wannan sabon yunkuri a duk wata dama da ya samu, misali ta hanyar yin wa'azi a masallatai, makarantu, tattaunawa da mutane, rubuce-rubuce da dai sauransu.
To saboda la'akari da irin karfin da wannan yunkuri yayi da kuma irin karbuwar da yayi a idon jama'a, don haka sai bukatar kafa wata karfafaffiyar kungiya da zata ci gaba da isar da sakon wannan yunkuri karkashin jagorancin malamai masana ta taso. Don haka sai aka kafa irin wannan kungiya ta farko karkashin jagorancin Imam Khumaini da kuma kulawan malaman garin Mashhad. Daga nan sai aka kafa kungiyar Malamai Ma'abuta Jihadi, wacce daga baya bayan samun nasarar Juyin Juya Hali ta zama Jam'iyyar Musulunci. Ita wannan kungiya aikinta shi ne tattaro mutane yayin zanga-zangogin da aka dinga yi tun daga shekarar 1977 zuwa 1978. To irin rawar da Ayatullahi Khamene'i ya taka a wannan kungiya abu ne da yake a fili.
MUKAMAN DA YA RIKE
Ayatullah Khamene'i ya rike mukamai da yawan gaske yayin gwagwarmaya da kuma bayan samun nasara da kuma kafa gwamnatin musulunci. Daga cikin irin mukaman da ya rike akwai:
1. Wakili a hukumar kula da juyin juya hali.
2. Wakili a kwamitin tarban Imam Khumaini (r.a).
3. Wakilin Imam Khumaini (r.a) a kwamitin gwagwarmaya ta Ma'aikatan Tsaro.
4. Kwamandan Dakarun Juyin Juya Hali.
5. Limamin Juma'ar birnin Tehran.
6. Wakili a Kwamitin Shawarar Musulunci.
7. Wakilin Imam Khumaini (r.a) a Majalisar Koli na Tsaron Kasa.
8. Shugaban Jamhuriyar Musulunci ta Iran.
JAGORANCINSA
Bayan rasuwar Imam Khumaini (r.a) a ran 3 ga watan Yunin 1989, Majalisar Kwararru sun zabe Ayatullahi Khamene'i a matsayin magajin Imam Khumaini kana kuma Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci (shugaban musulmi) a ranar 4 ga watan Yunin 1989. Tun daga wancan lokacin har ya zuwa yanzu yana nan yana gudanar da wannan nauyi da aka dora masa cikin kwarewa da kuma nuna sanin yakamata, bugu da kari kan tafiya akan tafarkin musulunci da kuma Imam. Muna fatan Allah Madaukakin Sarki Ya ci gaba da kare shi har zuwa bayyanan Imamul Mahdi (a.s).

Matsa Wannan Alama Don Komawa Sama