Ci Gaban Hudubar Imam Khamene'i Kan Iraki

Jirgin Sama 'Yan Mamaya (U.S da U.K) Kenan Yake Ruwan Bama-Bamai Akan Al'ummar Iraki.
Ruwan Bama-Bamai Akan Irakawa Marasa Galihu

Abu na biyu kuma shi ne irin danyen aiki da kisan gillan da aka yi wa al'ummar Irakin a yayin wannan yaki. Hakika wannan lamari ne da ba za a taba mancewa da shi ba. Ku duba ku gani, shekaru 27 kenan da yakin Vietnam, an kare wannan yaki ne dai a shekarar 1975, yanzu shekara 27 kenan da gama wannan yakin, amma ya zuwa yanzu dai an mance da wasu abubuwa da suka faru a wannan yaki, to sai dai kuma irin danyen aikin da Amurka ta aikata a kan al'ummar Vietnam din ba za a taba mancewa da shi ba. Ku duba dai ku ga yadda aka dinga shirya fina-finai da kuma labarurruka kan wannan yaki. Al'ummar duniya dai suna tune da irin wadannan abubuwa kamar yadda kuma za su ci gaba da tunawa da su.

Wannan dai shi ne hari a kan al'umma. Mafi girman hakkin al'umma dai shi ne samun daman su rayu, wadannan mutane ('yan mamaya) suna ikirarin cewa suna kare hakkokin 'yan Adam to amma suna hana mutanen wadannan garuruwa hakkin rayuwa ta hanyar yi musu ruwan bama-bamai. (Sojojin mamayan) sun jefa sama da makamai masu linzami samfurin "Cruise" guda 1000 akan al'ummar Irakin. Abin bakin cikin shi ne ba ni da cikakken yawan makaman da suka yi amfani da su a hannuna a halin yanzu, to amma dai sun jefa dubban bama-bamai na musamman, akwai kuma wasu dubban na harsasan sojin kasa da suka harba, sun ci gaba da jefa irin wadannan makamai a garuruwa daban-daban kuma ta hanayoyi daban-daban. Garuruwan Basra, Al-Nasiriyya, Diwaniyya, Al-Hillah da kuma Bagadad, da dai sauran garuruwa sun fuskanci irin wadannan hare-hare. Hakika mun riga da mun sam ma'anar yin ruwan bama-bamai akan wata kasa, don kuwa an yi mana hakan.

Makamai masu linzami sun fada mana a garuruwan Tehran, Dezful da dai sauran garuruwa, lalle mun san me hakan ya ke nufi.( A wannan lokacin) an jefa gomomi ko kuma ma darurrukan makamai masu linzami a gari guda cikin awa guda kawai. Shin hakan wasa ne? Suna cewa wai suna so ne su lalata sansanonin soji, shin sansanonin soji nawa ne a kasar Irakin da har ake bukatuwa da makamai masu linzami na Cruise guda dubu da kuma wasu bama-bamai sama da dubu wajen lalata su? Wadannan bama-bamai dai babu shakka sun kashe al'ummar Irakin da kuma raunana wasu. Sun haifar da yanayin tsoro da ta'addanci akan al'umma, yara sun tsorata, an kashe yara, an sanya mutane cikin halin yunwa da bukata.

Wadanda za su fahimci hakan su ne iyaye masu kananan yara wadanda suke bukatan shan nono, to amma ba su da wani nonon da za su ba su, iyaye mata ba su da wani abincin da za su ci, ba su da ruwan sha da za su ba wa 'ya'yayansu. Irin wadannan mutane su ne za su fahimci wannan zance. Ku duba ku ga irin yaran da suka karya zukatan iyayensu saboda kukan da suke yi. Ku duba ku ga matasa nawa ne aka kwantar a asibiti amma ba a iya kula da su da kuma ba su kulawan da ta kamata ba. Ku duba kuga yara nawa ne aka raba su da mahaifansu da abubuwan kaunarsu.

Hakika wadannan mutane sun cutar da al'umma. Sun shiga cikin gidajensu. Hakika irin wadannan abubuwa suna sosa rai. Sun shiga gidajen mutane, su kame mai gida su sa masa sarka a gaban iyalansa, su rufe masa kai kana su sa masa sarka.Daga nan kuma su ci mutumcin mutum da kuma yi masa barazana saboda kawai wani mutum ya zarge shi da wani abu, ko kuma sun gano wani abu na zargi tattare da shi. Ashe wadannan abubuwa ba abu ne da ya kamata a yi dubi cikinsu ba? Su sanya wa balarabe sarka ta baya su rufe musu kawuka, kana kuma su umarce su su kwanta a kasa su kuwa suna tsaye a kansu da bindigoginsu. Sojojin bakin haure sun shigo cikin wata kasa. Ashe hakan ba karamin bala'i ba ne? Shin akwai wani mutum da zai iya gyara akan wannan lamari? Hakika wannan lamari ne da yake da muhimmanci.

Matan Irakawa Cikin Halin Ka-Ka-Ni-Ka-Yi.
Allahu Akbar, Ku Yi Hakuri, Allah Zai Isar Muku

Sojojin Amurka suna cajin matan larabawa masu hijabi. Matan larabawa wadanda suke sanye da hijabi, manyan riguna da kuma mayafi, wadanda suka rufe jikinsu tun daga sama har kasa. To amma a samu wani matashin sojin Amurka wanda ba a ma san ko shi wane ne ba, yana cajin wadannan mata wai don gano ko suna dauke da bama-bamai. Shin wannan shi ne ma'anar hakkin dan'Adam? Shin wannan shi ne nuna kula da kuma girmama dan'Adam? Shin wannan shi ne ma'anar kiyaye hakkokin dan'Adam da wadannan makaryata suke ikirarin karewa? Hakika irin wannan cin mutumcin ba zai iya gushewa ta hanyar neman afuwa kawai ba. Sun kai musu hari, amma suna cewa ku yi hakuri mun yi kuskure ne. Hakan suka yi a kasar Afghanistan.

Irin wannan lamari shi ne ya dinga faruwar a kasar Afghanistan, irin wannan lamari ya sha faruwa a kasar Afghanistan tun farkon yakin da suka kaddamar a kasar Afghanistan din. Cikin 'yan kwanakin nan ma dai irin hakan ya faru. Sun tada al'umma gaba daya da bama-bamai, amma sai suka ce suna neman afuwa wai sun yi kuskure ne. Shin mutum yana iya share laifin da ya yi ta hanyar cewa a yi min afuwa, na yi kuskure ne?

Wannan dai shi ne abu na biyu, (matsayarmu kuwa) kan hakan ita ce muna taya al'ummar Iraki bakin cikin irin wannan mummunan hali da suke ciki, kamar yadda kuma muka yi Allah wadai da wadanda suka al'ummar Irakin cikin wannan yanayi. Idan har masu wuce gona da irin suka ce hakan shi ne kare hakkokin 'yan Adam, to sai mu ce musu ku makaryata ne.

To abu na uku kuma shi ne cewa mamayar soji da aka yi wa wata kasa (mai cin gashin kanta) da sunan cewa ta mallaki makaman kare dangi. To wannan dai shi ne abu mafi muni da cutarwa da za a iya yi. Babu shakka al'ummomin duniya dai sun yi Allah wadai da kuma tofin Allah tsine ga hakan da kuma bayyanar da hakan a matsayin haramtaccen abu da bai dace ba. Ina iya tunawa a lokacin yakin Vietnam, an gudanar da wasu zanga-zangogi a wasu bangarori na dunya don nuna rashin amincewa da hakan, to sai dai kuma ban ga irin zanga-zangogin da muke gani a halin yanzu ba (na nuna rashin amincewa da wannan yaki) a wancan lokaci na yakin Vietnam din, a takaice dai irin zanga-zangogin da ake gudanarwa a halin yanzu nesa ba kusa ba ya fi na wancan lokacin yawa. A wancan lokacin dai an ce tsohuwar Tarayyar Sobiyet ce ta shirya wadancan zanga-zangogi da nuna rashin amincewa, to a halin kuma wane ne ya shirya wadannan zanga-zangogi da ake yi?

A halin yanzu dubban mutane kai ko kuma ma darurrukan dubbai ne suka gudanar da zanga-zangogi a kasashen Indiya, Pakistan, Indonisiya, Malaysiya, kasashen Afurka, kasashen Turai kai har ma da ita kanta Amurkan. Dukkansu dai take guda suke rerawa. To abin tambaya anan shi ne wane ne ya shirya wadannan zanga-zangogi? Shin akwai wata helkwata ce da take shirya wadannan zanga-zangogi? Gaskiyar maganar dai ita ce cewa babu hakan, face dai sanin ya kamatar mutane ne yake sa su yin hakan, wanda ya ke Allah wadai da duk irin wannan mummunan aiki. Lallai kan wannan lamari ya cancanci yin Allah wadai, don kuwa lamari ne abin kyama. Saboda wannan lamari yana nuni ne da komawa baya zuwa zamanin yakin zalunci da kuma fadada kasa da ake yi a shekarun baya.

Su dai kawai suna neman wata hujja ce akan wata kasa ta daban, don haka koda sau dubu nawa ne sufetocin Majalisar Dinkin Duniya masu binciken makamai suka bayyana musu cewa abin da suke fadi fa ba gaskiya ba ne, ba za su yarda ba, za su ce musu ne ba su san abin da suke fadi ba. Za su ce musu sun sun yi imani kan cewa abin da suke fadi gaskiya ce. Don haka sai suka kai hari. Babu shakka hakan kuskure ne babba. A bangarenmu dai mun yi Allah wadai da hakan, kuma za mu ci gaba da yin tofin Allah tsine a hakan.

Babu shakka, mu mun yi imanin cewa Majalisar Dinkin Duniya ta gaza wajen aiwatar da abin da ya hau kanta dangane da wannan batu na yaki a kan kasar Iraki. Me ya sa kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniyan bai yi Allah wadai da wannan hari da Amurka da Birtaniyya suka kaddamar a kan kasar Iraki ba? Me ya sa ba su fitar da wani kuduri akan su ba? Hakika zai fi kyau su fitar da wannan kuduri, koda kuwa Amurka da Birtaniyyan za su hau kujerar naki kansa, alal akalla dai fitar da wani kuduri kan wannan lamari zai nuna cewa kwamitin ya yi aikinsa. Me ya sa ba su yi hakan ba? Me ya sa ba su kira taron babban zauren Majalisar Dinkin Duniyan ba, don babban zauren ya yi Allah wadai da wannan lamari? Hakika akwai abubuwa da dama da ya kamata babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya ya yi kan wannan lamari. Hakika akwai abubuwa da daman gaske da mutane suke tsammani daga Majalisar Dinkin Duniyar. Duk da cewa dai tun shekarun da suka wuce muka fidda tsammani ganin wani abin kirki daga Majalisar ta Dinkin Duniya, don kuwa mun riga da mun ga yadda take gudanar da ayyukanta, mun ga wadanda suke da bakin magana a cikinta, to amma duk da hakan dai al'umma sun yi tsammanin majalisar za ta dan tagaza, to sai dai kuma (abin bakin ciki) majalisar ta gagara aiwatar da abin da ya hau kanta.

Amurka Ce Kusurwar Shaidanci

Babu makawa wannan aiki na Amurka a kasar Iraki ta tabbatar wa duniya cewa ita kasa ce mai bakar aniya, kamar yadda daya daga cikin shuwabannin Amurka ya lakaba wa wadansu kasashe na duniya. Kasa mai bakar aniya ce za ta aikata abin da Amurka ta aikata a kasar Iraki. Hakan shi ne abin da kasa mai bakar aniya za ta iya aikatawa ga 'yan Adam, ga zaman lafiya da kuma tabbatuwar wata kasa ta daban. Sun tabbatar wa duniya cewa su ne "Kusurwowin Shaidanci" (Axis of Evil) na hakika. Amurka ta tabbatar wa duniya cewa ta cancanci sunan nan da shugabanmu Imam Khumaini (R) ya sanya mata na "Uwar Shaidanu". Hakika Amurka ita ce uwar shaidanu.

Babu shakka kasar Birtaniyya ma ta yi babban kuskure. Sun biye wa Amurka don su dan samu garar da za a samu bayan yakin, to sai dai kuma sun yi babban kuskure. Hakan kuwa saboda cewa a wannan yankin dai, musamman ma a kasashen Iran, Iraki da Indiya, Birtaniyya ba ta da kyakkyawan fuska a idon al'umma, a takaice dai al'umman sun ki jininta saboda mummunan zalunci da ta aikata akan al'ummar yankin. To amma bayan shekaru 30 ko 40, an fara mance wannan mummunan fuska ta Birtaniyya, saboda bayyanar wata gwamnati da ta fi ta zalunci da shedanci a duniya. To amma babu shakka Mr. Blair ya sake dawo da wannan yanayi da kuma kiyayyar da ake yi da Birtaniyyan a zukatan mutane. Hakika hakan babban kuskure ne.

To (matsayarmu dai) dangane da wannan lamari na uku, wanda yake hari ne na soji, shi ne cewa muna tare da al'ummomin duniya kan matsayar da suka dauka kuma za mu ci gaba da hakan. Mun yi imanin cewa hakan babban karen tsaye ne ga alakar kasa da kasa kana kuma wuce gona da iri ne akan wata kasa ta musulmi, al'ummar musulmin da kuma kasashen musulmi.

Abu ba hudu kuwa, ya sha banban da sauran, shi ne kuwa ci gaba da mamaye kasar Iraki da Amurka za ta yi. Baya ga cewa Amurkan ta kai hari da kuma aikata abin da ta aikata na zalunci da take hakkokin mutane, to a halin yanzu kuma tana son kafa wata gwamnatin soji ne (karkashin tsohon janar din sojin Amurka) wanda ko dai Bayahuden Sahyoniya ne ko kuma dai yana da kakkarfar alaka da yahudawan sahyoniya na duniya, a kasar Irakin. Suna son su dora shi a matsayin shugaba akan wata kasa ta musulmi kana kuma wata jarumar kasa ta larabawa. Wannan dai shi ne lamari na hudu mai matukar muhimmanci.

Hakika, (Amurka da Birtaniyya) sun raba kasar tsakaninsu kamar yadda suke tsammani, duk da cewa akwai bayyanannen banbanci tsakaninsu. To sai dai kuma, akwai alamar cewa sun rarraba kasar tsakaninsu. (Misali) Yankin Basra, inda ake jin kamshin man fetur kana kuma tana kusanci da yankunan da suke da man fetur, an bar wa Birtaniyya, saboda Birtaniyya tana son kamshin man fetur. Bagadada kuwa, helkwatar mulki, aka bar wa Amurka, hakan kuwa don Amurka tana son nuna karfin iko da kuma nuna karfi, don haka Bagadada ta kasance ta su ce. Ta haka ne suka aiwatar da wannan rabo.

Sai dai kuma babu shakka, suna da sabani tsakaninsu masu yawa kuma za a ci gaba da samun hakan kuma zai bayyana wa duniya nan gaba, to sai dai kuma a halin yanzu dai suna nuna cewa akwai fahimtar juna tsakaninsu kuma sun yarda da yarjejeniyar da suka cimma tsakaninsu.

Hakan dai komawa ne ga lokacin farko na mulkin mallaka, tsantsan mulkin mallaka, don kuwa haka lamarin ya kasance a lokacin mulkin mallaka. Gwamnatocin 'yan mulkin mallaka na Turai haka suke zuwa su kwace kasa da karfin cin tuwo a nahiyoyin Asiya da Afirka, daga nan kuma sai su kafa wani shugaban mulkin soji a gurin da zai gudanar musu da al'amurran da suke so. Haka suka yi a kasar Indiya, haka suka yi a Australiya, a Kanada, a da dama daga cikin kasashen Afirka. Bayan wani lokaci kuma sai suka fahimci cewa sun yi kuskure. Kafa wata gwamnati ta soji a wata kasa kuskure ne, don haka sai suka canza wannan yanayi. Inda suke zaban wasu mutane ko kuma wani mutum daga cikin wannan kasa su dora shi akan karagar mulki, don su kasance masu yi musu da'a da kuma gudanar musu da abin da suke so a wurin. Sukan taimaka musu da kuma samar musu da abubuwan da suke so, su kuwa sai su bar su su ci karensu babu babbaka a kasar.

To hakan ma dai bayan wani lokaci sai suka fahimci cewa shi ma kuskure ne, hakan ba daidai ba ne, don kuwa al'ummar kasar sukan tashi su fuskanci wadannan shuwagabanni, duk kuwa da cewa wadannan shuwagabanni su ma 'yan kasa ne, saboda alakar da suke da ita da wadannan azzaluman kasashe.

Don haka daga nan sai suka canza wannan tafarki, inda suka fito da abin da suka kira demokradiyya ta hanyar mamayan al'adu da kuma mulkin mallaka. Su kan zabi shugaba wanda yake ba su goyon baya ta hanyar zaben jeka-na yi-ka, kamar yadda ya faru a lokacin mulkin dagutanci na tsohon sarki Shah.

Da farko dai, gwamnatin Birtaniyya ta kawo Ridha Pahlawi kan mulki daga nan kuma Muhammad Ridha, tsohon Shah da mahaifinsa kafin samun nasarar Juyin Juya Halin Musulunci. Anan ma dai sai suka fahimci cewa akwai matsaloli dai. Don haka sai suka tilasta wa Shah da ya nada Ali Amini a matsayin Prime Ministan don ya kawo canje-canjen da suke so. Bayan haka dai Shah ya fahimci cewa akwai yiyuwar fa zai rasa ikon da ya ke da shi, don haka sai ya ce a bar shi zai gudanar da wadannan canje-canje da ake so, inda ya gabatar da wadansu tsare-tsare guda shida na abin kunya da aka gabatar a lokacin mulkin dagutancinsa. Hakika wannan siyasa dai ita ce wacce 'yan mulkin mallakan suka gabatar a wurare da dama kana kuma a lokuta daban-daban.


Babu shakka idan da a ce al'ummar Iraki sun tsaya a bayan Saddam a wannan yaki, to da 'yan mamayan ba su sami irin wannan nasara ba, su ma kansu sun san hakan. Wannan dai shi ne yadda yanayin yake a lokacin da al'umma ba ta yarda da tsarin da ke gudana ba, da kuma jami'an wannan gwamnati. Al'ummar Iraki dai ta fuskanci zalunci, cutarwa da kuma cin mutumci daga jami'an gwamnatin Irakin, shi ya sa suka ki taimaka musu. Wannan lamari shi ne ya ba wa abokan gaban, abokan gaban kasar Irakin, 'yan mamaya, suka sami damar samun wannan nasara da suka samu
To a halin yanzu dai, sun koma zuwa ga tafarkin farko, wanda shi ne mamaye wata kasa da karfin cin tuwo (soji) kana kuma su nada shugaban da suke so da kansu. Hakika wannan bakon abu ne kana kuma mummuna wanda ya samo asali daga girman kai, wanda babu kokwanto zai koma kansu. Wannan dai shi ne abin da zai faru nan gaba. Kusan dukkan al'ummomin duniya sun yi Allah wadai da wannan mummunan aiki, suna masu cewa hakan ba abin amincewa ba ne.

Babu shakka hakan kara kuskuke a kan kuskure. Ba ya kamata shugaban kasar (Iraki) ya zamanto bako daga waje ko kuma bayahuden sahyoniya. Mutanen Iraki dai suna son shugaba ne wadanda suka zaba da hannuwansu ba tare da goyon baya ko tsoma bakin kasashe ma'abuta girman kai ba.

Amurkawa dai suna tsammanin sun gama tsara komai. Suna tsammanin za su dora wannan shugaban mulkin soja (Jay Garner) da kuma gudanar da al'amurran mulki a kasar Iraki. A bangare guda su dan taimaka wa al'ummar Iraki (da abin da bai taka kara ya karya ba), kana a daidai lokacin kuma su canza al'adu da kuma koyarwa irin ta al'umma ta hanyar kame tsarin koyarwa.

Suna tunanin yin hakan a kasar Afghanistan. Don kuwa Amurkawan sun buga ton-ton na littattafan makarantun primare cikin harshen Farisanci da kuma Pushtun a wata kasa ta nahiyar Asiya da nufin raba su a makarantun kasar Afghanistan din. Ta hakan kuwa kokari suke su canza al'adun yaran kasar Afghanistan da kuma irin kaunarsu da mahangarsu ga addini da kuma tarihi, don su kaunaci Amurka da kuma ganinta da gashi a idanuwansu. To wannan shi ne abin da suke tsammanin za su aikata a kasar Iraki.

To a kasar Iraki dai da wuya hakan ya faru, don kuwa kiyayyar da take cikin zukatan malamai da al'ummar Iraki ga zaluncin Amurka da Birtaniyya ta riga da ta samu gindin zama, kuma babu shakka hakan zai ci gaba da kasantuwa cikin zukatan al'ummar Iraki masu zuwa.

To wannan dai shi ne shirin Amurka da Birtaniyya. Wannan dai shi ne abu na hudu, wanda ya sha banban da sauran abubuwan da suka gabata. To koda ma dai ba su yi hakan ba, to wuce gona da irinsu dai, wanda babban kuskure kana kuma laifi ne, zai ci gaba da wanzuwa. To koma dai sun yi hakan ko kuma ba su yi ba, babu shakka kowani guda daga cikin dukkan wadannan abubuwa da na ambata, laifi ne kuma kuskure ne, kuma cin mutumci ne ga al'ummar Iraki. Hakika mutum zai yi mamakin wasu irin mutane ne su da ba sa jin kunya. A shirye suke su fito cikin gidajen talabijin su ce wai al'ummar Iraki ba za su iya zaban shugaban da zai jagorance su ba. Kai ya ya mutum zai kasance maras kunya haka kuma ya shirya yin irin wannan magana da kuma zargin wata al'umma, wacce take da tsohon tarihi, masana da 'yan siyasa,da cewa ba za ta iya ba? Hakika mun dauki hakan a matsayin cin mutumci ga al'ummar Irakin. Babu shakka mun yi Allah wadai da wannan lamari kuma ba za mu taba amincewa da shi ba. Mutanen Iraki dai ba za su taba yarda da wani sabon mulkin kama-karya ba. Al'ummar Iraki ba su fito daga ramin Saddam don su fada cikin wani sabon ramin na shugaban mulkin sojin Amurka ba.

Kai matukar ma dai suka kawo wani mutumin Iraki a irin wannan hali, babu makawa al'ummar Irakin ba za su amince da shi ba. To ala kulli hal dai, mun yi imani da cewa abin da suke fadi a halin yanzu dai wuce gona da iri ne akan hurumin Musulunci da kuma musulmi.