Sakon Jagora Ayatullah Ali Khamene'i Ga Maniyyata Aikin Hajjin Bana (2003=1424):
Jagora-Ayatullah Khamene'i

Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai
Taron miliyoyin al’ummar musulmi a Hajj wani abu ne wanda bashi kama  a dukkanin tarurrukan da ake yi a duniya inda dukkanin musulmi suke taruwa a kusa da dakin Allah mai alfarma sannan kuma suna kusa da Annabin tsira mai daraja. Suna daukaka muryoyin su suna rera wasu kalmomi na take wadanda suke cike da wasu ma’anoni na Tauhidi. Haka nan suna ayyuka da suka hada da jifan Shaidan wanda ke nuna bara’a daga Dawagitai sannan da nuna kasakan da kai ga Allah mahallicin kowa da komai. Haka nan musulmi suna cike da ji a zuciyar su cewa musulmi da musulunci nada izza tare da samun sakon taimakawa juna da tausayin yanuwansu musulmi a duk inda suke a duniya da kuma nuna daukaka akan makiya kafirai kamar yadda addini ya nema daga gare su.

Hajji yana daya daga cikin abubuwan da suke koyawa musulmi yadda ya kamata su lamuntawa kansu rayuwa mai kyau da samun ci gaba. Ana iya takaita aikin Hajj a matsayin tamkar wata makaranta wadda zata samar da mutum wanda yake mai lamiri sannan kuma mai tafiya jihar Ubangiji Allah. Kuma tamkar wata makaranta ce wadda take kara kyautata zuciyar mutum da tsaftace ta saboda samun ci gaba ta samun yardan Allah. Kamar yadda Allah din yake fadi acikin littafin sa mai tsarki:

جعل اللة الكعبة البيت الحرام قياما للناس واللشهر اللحرام واللهدي واللقلائد

Ma'ana: Allah ya sanya ka’abah mai alfarma ta kasance wajen tsayuwa ga mutane da wata mai alfarma da hadaya da abin ratayawa.

Al’ummar musulmi har yanzu suna bukatar wani irin wannan na aikin Hajji wajen tafiyar da rayuwar su na hakika sawaun gwamnatoci ne ko kuma daidaikun mutane. Alummar musulmi cikin tsawon karni guda da ya wuce sun fuskanci wani irin danniya na salon mulkin mallaka daga yan mulkin mallaka daban daban wanda ya sabbaba cin moriyar dukiyarsu da irin baiwar da Allah ya kimsa masu a kasashen su daban daban.

Babban abin da wannan ya haifarwa alummar musulmi shine kasanceaw cikin wata irin danniya ta siyasa da tattalin arzikida koma bayanci ta fuskoki daban daban. Amma ta bangaren yan mulkin mallaka kuwa wannan ya basu damar cin moriyar abin da Allah yayiwa musulmi baiwa da shi ba tare da wata wahala ba, sannan kuma sai a lokaci guda suka ci gaba da samun salladuwa ta fuskar siyasa da dana tattalin arziki da gumin wasu. Amma cikin ikon Allah yasa bayan yan shekaru musulmi sun fara farfadowa daga barcin su kuma sai gashi Jamhuriyar Musulunci ta Iran da kudurar Allah ta’ala sun yunkura kuma daga karshe Allah ta’ala ya basu nasara a sake bude sabon tsari karkashin turbar Islam.

Abu wanda yake a sarari cewa manya manyan masu girman kan duniya ba cikin sauki ne suke mika wuya ga duk wata gaskiya da bayyana masu ba sai sun ja tukun na sai sadda suka ga karfinsu ya gaza, amma a lokaci guda su kuaw musulmi suna da akidar cewa ita gaskiya koda ace yanzu ta kasance ba’a yayin ta amma fa riko da ita shine zai kai mutum zuwa ga sa’ada ta har abada da kuma fita daga dukkanin danniya na rashin ci gaba da koma bayanci ta fuskar siyasa da tattalin arziki. Sai dai wannan hanya hanya ce ta gwagwarmaya ta fuskar ilmi, kokari na siyasa mai kyau da kuma kare gaskiya komai dacin ta. Tare da irin wannan sunna ta Allah wadda bata canzawa tana nuna cewa nasara zata tabbata ga masu taimakon Allah, kamar yadda yazo a littafin Allah mai tsarki.

اذن للذين يقاتلون بانهم ظلموا وان الله علي نصرهم لقدير

Allah yayi izni ga wadanda aka yaka da cewa an zalunce su kuma lallai ne Allah mai iko ne akan taimaka masu.

Allahu Akbar! Maniyyata Aikin Hajjin Bana
Kenan A Mina
Allahu Akbar! Labbaikallahumma Labbaik

Ko shakka babu cewa masu girman kan duniya wadanda kamfanonin kera makamai da rijiyoyin mai yake hannayen su da kuma wadanda suke tare da su duk suna kwana suna tashi ne da fargaban cewa kada musulmi su farka su gane hakkokin su, don haka nan suna iya saka dukkanin jarin dake tare da in dai har zasu iya samun tabbacin cewa musulmi zasu ci gaba da barci su kuwa suna can suna ta nasu makirce makircen. Don haka nan sun sanya musulmi cikin tsoron cewa akoda yaushe ana iya afka masu, muna iya ganin wannan a fili cikin abin da yake faruwa yanzu ta bangaren gwamantin kasar Amurka wanda shugaban kasar ke ta yayatawa haka kuma yake ga yar uwar ta HARAMTACCIYAR KASAR ISRA'ILA. Muna iya ganin yadda al’ummar Palsadinu suke ta jurewa kai hare haren sojojin HARAMTACCIYAR KASAR ISRA'ILA shekara da shekaru ba don komai ba sai don sun kasance suna cewa su sai sun nemi hakkin su kuma zasu ci gaba da riko da gaskiya har sai sun ci nasara.

To su ma alummar kasar Iraqi ba wani abu yasa suke fuskantar wannan irin barazan ta kai hari ba face sai kawai don gwamantin kasar Amurka tana son ta kasance tana da iko da arzikin ta da rijiyoyin man fetur din da Allah ya ajiye mata, don haka nan laifin alummar kasar Iraqi kawai shine don sun kasance a wajen da ke da arziki. Haka nan kuma ita Amurka tana son ta kasance baya ga cewa ta sami salladuwa akn man Iraqi sanna kuma ta kasance tana da karfi akan iyakar Palasdin,Iran,Syriada Saudi Arabia wanda wannan zai bata damar samun iko akan dukkanin kasashen dake gabas ta tsakiya.

Wannan abu iri daya yake akan alummar kasar Afganistan in muka duba da kyau domin kuwa suma sun kasance fiye da shekara gida suna cikin hare hare na sojojin Amurka wanda  ake kaiwa da makamai na kare dangi wanda cikin munafunci yanzu Amurka ke nuna ta kokarin kawarwa. Ba kuwa Amurka ita daya ba a’a harma da kawayen ta musamman kasar Britaniya. Irin wannan kwadayi na kasashe masu girman kai bai san kan iyaka ko bangare ba, son mamaya ne kawai tsantsa tare da jiji da kai da kuma wauta hade da zari.

Lallai babu shakka cewa Amurka da kawayen ta nan gaba kadan zasu ga abin da basa so na cewa karshen ya zo kuma wannan girman kan zai kau gefe guda. Sai dai kawai abin Allah ya kiayaye idan har gwamnatocin musulmi da alummomin su basu aikata abin da ya dace ba kuma suka yi sakaci da abin da ya doru akan su to lallai fa su sani suna iya samun hasarori mai yawa wanda hannayen zai jawo masu.

Kamar dai yadda kowa ya sani ne dai ita Amurka tun bayan lokacin da abin da ya faru na ranar 11 ga watan sept ya faru ta fara wani sabon salo na wata farfaganda ta karya, watau ta dauki kirarin kalmomi guda biyu fada da ta’addanci da Dimocradiyya domin yin fada da kuma mamaye kasashen musulmi da cin moriyar arzikin da suke da shi. Suna fakewa da neman makaman kare dangi da makami masu guba wajen samun wani halacci wanda zai basu damar aiwatar da abin da suke so. Abin tambaya anan shine su waye suka baiya gwamantin Ba’th damar samun abbubuwa daga kamfanoni wanda ya basu damar yin wadan nan makaman?  Wadanan boma bomai guda dubu sha tara na guba wanda kuke tuhumar gwamnatin ba’ath dashi acikin store da kuma dubu goma sha uku da suka sanyawa Iraniyawa a lokacin kallafeffen yaki, dukkanin wannan wa ya baiwa gwamnatin ta Iraqi? A ina suka samo wadannan makamai? Akwai wani ne banda ku wanda ya baiwa gwamnatin ta Iraqi wadannan makamai? Sannan kuna so ne ku nuna cewa ku bakuyi tarayya ba a cikin laifin da Iraqin ta tafka?

Yaya kuke tsammanin cewa zaku rudi alummar duniya da cewa ku kuan yaki da ta’addanci alhali kuwa kun kyale HARAMTACCIYAR KASAR ISRA'ILA tana irin wannan ta’addanci da babu kamar sa a duniya sannan kuan tsammanin cewa alummar duniya ba zata gane karyar ku da daukan mtsayin ku a sarari ba? Ita dai Amurka da irin girman kai rawanin tsiya da take da shi bata iya samun cimma manufofin ta a Afganistan da Palsadin ba sannan kuma tana jin takaicin irin hasarar dukiya da na rai da samu kuma da yaddan Allah irin wannan kaye da sha a wadannan kasashe shine kuamzata sake sha a duk inda ta fada.

A Iraqi ma sunawa duniya cewa babban hadafin su shi ne ture Saddam da gwamnatin Ba’ath amma lallai karya kawai suke yi, domin kuwa babban hadafin su shine tauye OPEC da mamayar kasuwar man fetur ta duniya ta kasance a hannun su da kuma kasancewa a kusa wajen kara goyon bayan HARAMTACCIYAR KASAR ISRA'ILA da ci gaba da takurawa Jamhuriyar Musulunci ta Iran da kasashen Syria da Saudi Arabia. Ya kamat asani cewa idan har Amurka ta sami nasarar kai wannan hari to fa shi ke nan gaba dayan mutunci da alfarman kasar ya kawo karshe ke nan. Wani abu kuma da ya kamata mu sani shine cewa su kasashen girman kan duniya sun riga sun san cewa su musulmi sna tare ne da koyarwans u na addini da rayuwa kunshe a cikin addinin su don haka nan suna ganin in su ka raba musulmi da addinin su to wannan hanya suna iya kasancewa sun sami iko akan su don haka nema zamu iya gani awannan lkoacin yadda suka dauki salo na kokarin kawar da tunani na addini a cikinzukatan musulmi. Tun bayan abin da ya faru a ranar 11 ga watan sept suka rika nuna alamu akan dukkanin musulmi ako ina suke da zimmar kokarin tsoarata musulmi da snay su su kasance sun fita daga wannan riga ta musulunci don haka nan a koda yaushe shi musulmin dfan ta’adda ne a’a shi musulunci dauke yake da sako na ta’addanci da dai sauransu. T a wannan ya kasance suka dauki wani adadi na musulmi suka kai su can suka sanya su cikin anu’oi na azabtarwa, tun kafin ma a tabbatar da irin laifin da wadanna  muatane suka kai wani lkoaci ma ba tare da an tuhume su da wani laifi. Da yawa daga cikin musulmin da kama aka tsare basu san ma dalilan daya sa aka kama su ahr yanzu.

To dama fa shi musulunci addini ne na yancin yin bayani, addini ne da bai san nuna karfi ko kama karya ba domin kuwa kamar yadda yake a kaida babu tilastawa acikin sa addini ne da ake yin cikin fahimta da bincike. Saidai koda yaushe ana kaiwa addinin hari ta hanyar nana shi amtsayin addini na ta’addanci da kama karya. To babu shakka alummar musulmi tana cikin hadari kuma da irin darussan dake cikin ayyukan Hajji tana mai tsananin bukata, Allah ta’ala yana cewa a cikin littafin sa mai tsarki.

اللذين امنوا يقاتلون في سبيل الله واللذين كفروا يقاتلون في سبيل اللطاغوت فقاتلوا اولياء اللشيطان ان كيد اللشيطان كان ضعيفا

Wadanda suka yi imani suna yin yaki ne akan tafarkin Allah amma wadanda suka kafirce suna yaki ne akan tafarkin dagutu to ku yaki kaidin shaidan lallai kaidin shaidan ya kasance mai rauni ne.

وقال موسي لقومه استعينو بالله واصبروا ان الارض لله يورثها من يشاء من عباده واللعاقبه للمتقين

Annabi Musa [AS] yana cewa mutanen sa ku nemitaimakon Allah kuma ku daure lallai kasa ta Allah ce yana gadar da ita ga wanda yake so cikin bayinsa kyakyawan karshe yana ga masu tsoron Allah.

Wassalamu Alaikum Wa Rahmatullahi Ta'ala Wa Barakatuhu.

Sayyid Aliyu Khamene'i.
8 Ga Watan Zil Hajji 1423 (20 Bahman 1381)