FATAWOYIN JAGORA KAN MAS'ALOLI DABAN-DABAN


Zabi Maudhu'in Da Kake So, Don Ganin Abin Dake Cikinsa




Izinin Amfani Da Wannan Risala Daga Jagora Gabatarwa
Babin Takalidi Marja'anci Da Wilaya
Wilayatul Fakih Da Kuma Hukumcin ShugabaBabin Tsarki
Babin SallaBabin Azumi
Babin KhumusiBabin Jihadi
Babin Umurni Da Mai Kyau Da Kuma Hani Da MummunaMas'aloli Daban-Daban

Mu'amaloli



IZININ AMFANI DA WANNAN RISALA DAGA WAJEN JAGORA:




GABATARWA
DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI

Godiya ta tabbata ga Allah wanda ya shar'anta halal da haram ya halatta abubuwa masu kyau kana ya haramta munana.Tsira da aminci su tabbata ga Manzon tsira Muhammad tare da tsarkakan Mutanen gidansa da zababbun sahabbansa.
Tun shekaru masu yawa tambayoyi daga kowani yanki na duniya suka dinga isowa zuwa ga ofishin Jagoran al'ummar Musulmai Ayatullah al-Uzma Sayyid Aliyu Khamene'i (Allah Ya kare shi Ya kuma kara masa tsawon rai). To haka dai wadannan wasiku suka ci gaba da isowa har suka wuce dubu goma, to cikin yaddar Allah Ayatullah Khamena'i ya sami damar amsa wadannan tambayoyi daidai da fatawarsa kana wasunsu kuma daidai da fatawar mujaddadin wannan karni Ayatullah al-Uzma al-Imam Ruhullah al- Musawi al- Khumaini (R.A).
To wadannan amsoshi sun kunshi dukkan babobin fikhu da kuma hukunce hukunce na sharia- musanman ma wadanda suka zamanto na rayuwan yau da kullun- bugu da kari kan sababbin mas'aloli na zamani wadanda al'umma suke tsananin bukatarsu.
A Saboda haka ne ya sa wadansu daga cikin manyan malamai suka nemi a buga su don muminai su amfana da su. Ko da yake daga farko Ayatullah Khamene'i ya nuna rashin amincewarsa ga hakan, to amma nacewar da Muminai daga ko ina a fadin duniya suka yi kan a buga wannan aiki dan su sami abin koyi, wanda hakan ya dada tsanani ne lokacin da wasu manyan malamai ma'abuta sani suka dora al'amarin marja'iyya a kansa da kuma dora masa wannan babban matsayi, ya sanya shi ya yarda da wannan bukata tasu, dan sauke wannan babban nauyi.
To bayan da aka gama tsattsarawa da kuma harhada wadannan tambayoyi da amsoshi an kaddamar da su gare shi domin ya kara dubawa, kuma ya ba da izinin buga shi da yada shi, inda kuma cikin yardar Allah aka samu hakan.
Daga karshe muna mika godiyarmu da kuma fatan alheri ga 'yan uwa muminai da suka yi dawainiyar wannan aiki daga bisani suka kaddamar da wannan ingantaccen aiki domin ya zan mai haskaka tafarki ga muminai, muna rokon Allah ya saka musu da alheri.

Bangaren Hukunce-Hukuncen Shari'a.
Ofishin Ayatullah al-Uzma Sayyid Aliyu Khamene'i
(Allah ya kara masa tsawon rai)


BABIN TAKALIDI:
A, fatawarka, shin aiki da"ihtiyat" shi ya fi ko kuma yin "taqlid"?
Kasantuwar aiki da"ihtiyat" ya ta'allaka ne da sanin wurarensa, kana da kuna sanin yanayin "ihtiyat" din, kuma ba kowa ya san su ba face mutane kadan, bugu da kari kan cewa aiki da "ihtiyat" yana bukatuwa ga sarrafar da lokaci mai yawa, don haka abin da ya fi shi ne yin taklid ga mujtahidin da ya cika sharuddan taklid.
Nan ba da jimawa ba 'ya ta za ta cika shekarun balaga, inda daga nan wajibi ne gare ta ta zabi marja'in da za ta masa taklid, tattare da cewa gano hakan babbar matsala ce, don haka mene ne ya wajaba a gare mu?
Idan har ita da kanta ba ta gano abin da ya wajaba a kanta dangane da wannan al'amari ba, to a nan abin da ya hau kanka dangane da ita shi ne tunatarwa da kuma shiryar da ita.
Wasu mutane wadanda ba sa da cikakkiyar masaniya yayin da muka tambaye su kan cewa ga wani marja'i suke yi wa "taklid", sukan amsa da cewa mu ba mu sani ba, ko kuma su ce muna wa wane (taklidi) ne. "sai dai kuma ba sa ganin cewa dole ne su koma ga risalarsa dan su yi aiki da ita, to anan mene ne hukuncin ayyukansu?
Idan har ayyukan nasu sun yi daidai da "ihtiyat" ko kuma da abin da ya dace ko kuma ga fatawar mujtahidin da daman wajibi ne su koma gare shi, to ayyukan sun inganta.
Wanda ya bar neman ilmin hukunce- hukuncen shari'a wadanda suka dame shi, shin ya aikata sabo ne ?
Idan har rashin neman ilmin hukunce hukuncen zai kai shi ga barin aikata wajibai ko kuma ya kai shi ga aikata haramun, to ya aikata sabo.

SHARUDDAN TAKALIDI

Shin ya halatta yin "taklid" ga mujtahidin da ba marja'i ba kana bai da risala?
Idan har ya tabbata ga baligi cewa shi mujtahidi ne da ya cika sharudda, to babu wata matsala ga hakan.
Shin yin taklidi ga malamai (mujtahidai) na wasu kasashe na waje ya halatta ko da kuwa saduwa da su ba zai yiwu ba?
Ba sharadi ba ne ga mujtahidin da ake masa taklidi ya kasance kasa daya ko gari daya da mai yi masa taklidi (mukallafi).
Bisa ga ra'ayin Imam Khumaini (r.a) na cewa dole ne marja'in da za'a yi masa takalidi ya kasance masani ne kan al'amurran siyasa, tattalin arziki, aikin soja, zamantakewa da shugabanci baki daya da kasancewarsa masani kan hukunce- hukuncen ibadu da mu;amaloli, to mu a halin yanzu bayan mun kasance muna taklidi da Imam Khumaini (r.a) sai muka ga ya zama wajibi- bisa la'akari da irin shiryarwar da muka samu daga wajen wasu manyan malaman kana kuma da abin da muka gani da kan mu- mu koma gare ka don yin taklid, ta yadda zai zamanto kenan mun hada shugabanci da kuma marji'iyya, to shin mene ne kake gani?
Sharuddan cancantar marja'in da za'a masa taklid suna nan an yi cikakken bayaninsu a cikin littafin Tahrirul wasila da sauran littattafa. To amma al'amarin gano wadannan sharudda da kuma zaben wanda ya dace dan yi masa takalidi daga cikin Fukaha'u to ya ta'allaka ne ga shi kansa mukallafin.
Shin Aalamiyya (fifikon marja'i bisa sauran' yan' uwansa) sharadi ne cikin taklid ko kuma a'a ? kana yaya ake gane Aalamiyya?
A bisa lhtiyat wajibi ne yin taklid ga A'alam cikin mas'alolin da fatawoyinsa suka saba da fatawoyin sauran maraji'ai. Kana Aalamiyya shi ne ya kasance ya fi sauran mujtahidai kudura kan sanin hukunce hukuncen Ubangiji da kuma kuduran ciro hukunce hukuncen daga inda ake ciro su. Kana kuma masaniya kan zamaminsa- gwargwadon abubuwan da suka shafi hukunce- hukuncen sharia da kuma sanin zamani ta yadda zai bayar da ra'ayin fikhu gwargwadon yadda ya dace da shari'a- shi ma yana daga cikin ababen da ke yin tasiri a ijtihadi.
Shin za'a iya hukunta, taklidin wanda ya yi takalidi ga wanda ba "A'alam" ba saboda zaton cewa shi "A'alam" din bai mallaki sharuddan taklid ba, shin za a hukunta irin wannan taklidi da cewa bai inganta ba ?
Ba ya halatta bisa ihtiyat yin taklidi ga wanda ba A'alam ba cikin mas'alolin da aka samu sabani a cikin su saboda kawai zaton rashin mallakan sharuddan A'alamiyya ga A'alam.
Yayin da aka bayyana wasu malamai da cewa su ne A'alam a cikin wasu mas'aloli (ta yadda ko wani daya daga cikinsu A'alam ne a cikin wasu takamammun mas'aloli). Shin ya halatta komawa gare su ko kuma a'a?
Rarraba taklid babu matsala a cikin sa, ballantana idan har A'alamiyyar kowane daya daga cikin su ta zamana akan mas'alar da yake masa takilidi ne to a wannan hali wajibi ne bisa ihtiyat ya rarraba taklid idan har fatawoyinsu sun bambanta.
Shin ya halatta taklidin wanda ba A'alam ba tare da cewa akwai a'alam?
Taklidin wanda ba A'alam ba cikin mas'alolin da fatawoyin da ba su saba wa fatawoyin A'alam ba babu matsala ga hakan.
Dangane da Taklid, wane ne ya wajaba mu yi masa takalidi?
Wajibi ne yin taklidi ga mujtahidi wanda ya cika sharuddan ba da fatawa da kuma marja'iyya, kana kuma ya kasance A'alam a bisa ihtiyat.
Shin ya halatta a yi taklidi ga mamaci a farkon farawa?
Ba a barin ihtiyat a farkon farawa, mutum ya yi taklid ga rayayyen mujtahidi wanda yake A'alam.
Shin taklidin mujtahidi mamaci, ya dogara ne kan taklidin rayayyen mujtahidi ko kuma a'a?
Halaccin taklidin mamaci a farkon farawa, ko kuma ci gaba da takalidin mamaci duka ya ta'allaka ne da izinin rayayyen mujtahidi A'alam.

HANYOYIN TABBATAR DA IJTIHADI DA A'ALAMIYYA DA KUMA GANO FATAWA


Shin ya wajaba a gare ni bayan na gano cancantar wani mujtahidi ta hanyar shaidar adilai guda biyu in sake tambayan wasu kan hakan?
Yana inganta a takaita ga shaidar adilai guda biyu daga cikin ma'abuta sani (Ahlul khibra) kan cancantar wani mujtahidi wanda ya cika sharudda, ba wajibi ba ne sai ya sake tambayar wasu jama'a .
Ya ya ake zaben marja'i da kuma karban fatawoyinsa?
Gano ijtihadi ko kuma A'alamiyyar marja'in Taklid dole ne ya zamanto ta hanyar gwaji, ko kuma ta hanyar ilimi kan hakan ko da kuwa ilimin ya samu ne ta hanyar yaduwar labarin cikin mutane ko kuma ta hanyar samun nitsuwa ko kuma ta hanyar ba da shaidar adilai biyu daga masana. Shi kuwa fatawar mujtahidi akan same ta ne ta hanyar ji daga gare shi, ko kuma daga fadin adilai biyu, kai ko da ma adali guda daya ne, ko kuma daga fadin wani amintacce wanda ake nitsuwa da maganarsa, ko kuma ta hanyar komawa ga risalarsa wacce ta kubuta daga kura-kurai .
Na tambayi wasu malamai kan wane ne A'alam sai suka amsa min da cewa yin taklid wa wane (suka ambaci sunansa)yana wadatarwa, to shin yana halatta in dogara ga maganarsu tattare da jahilcina kan A'alamiyyarsa ko kuma zatona ga a alamiyyarsa ko. kuma ya halatta in dogara kan nitsuwa da nake da ita a kan cewa ba shi ba ne A'alam domin kasantuwan wasu mutane da su ma aka ba da irin wannan shaidar dangane da su, da kuma ire- iren wannan halaye?
Idan har dalili na sharia (shaidar adilai biyu) ya tabbata kan A'alamiyyar mujtahidin da ya cika sharudda, matukar dai ba a sami mai inkarin wannan shaidar ba, to ita wannan shaidar ta zama hujja ta shari'a wanda za a dogara a kan ta, kana ba sharadi ba ne a ce sai an sami yakini ko nitsuwa a kan haka, sa'annan kuma babu bukatar a wannan hali a ce za a binciko wata shaidar da ta saba hakan.

AL-UDUL (CANZA TAKLIDI)


Shin ya halatta mutum ya bar taklidin A'alam cikin fararrun mas'alolin da suka shafi zamani saboda gazawarsa wajen ciro ingantattun hukuncinsu?
Idan har shi mukallafi bai so ya yi ihtiyati cikin mas'alar ba, ko kuma ya gagare shi to idan har ya sami wani mujtahidi A'alam wanda yake da fatawa akan mas'alar to wajibi ne a gare shi ya koma gare shi ya yi masa taklidi. a cikin mas' alar.
Dangane da juyawa daga daya daga cikin fatawoyin Imam Khumaini (r.a), shin wajibi ne a koma ga fatawar mujtahidin da ya ba da izinin ci gaba da taklidin mamaci ? ko kuma ya halatta a koma ga fatawar sauran wasu mujtahidai?
A nan wajibi ne a koma ga mujtahidin da ya ba da izinin ci gaba da takalidin mamaci.
Shin canza takalidi (al-udul) daga A'alam zuwa ga wanda ba A'alam ba ya halatta?
Uduli a nan ya saba wa ihtiyat, hakika ma dai ba ya halatta a bisa ihtiyat idan har fatawar A'alam din akan mas'alar ta saba wa fatawar wanda ba A'alam ba.
Na kasance na ci gaba da taklidin Imam (r.a) saboda la'akari da fatawar daya daga cikin manyan mujtahidai, to bayan da na yi nazarin amsoshinka cikin "al-lstifta'at" da kuma ra'ayinka kan ci gaba da takalidin Imam Khumaini (r.a), sai na bar wancan na ci gaba da ayyukana daidai da fatawoyin Imam (r.a) bugu da kari kan fatawoyinka, shin akwai wata matsala a cikin wannan "udulin" nawa?
Ba ya halatta a bisa ihtiyat na wajibi canza takalid daga rayayyen mujtahidi zuwa ga wani rayayyen, sai dai idan a ganin mukallafi na biyun ya fi na farkon ilimi kana kuma fatawarsa ta saba wa fatawar na farko, to a wannan halin wajibi ne bisa ihtiyat ya koma ga na biyun.
Wanda ya kasance yana takalidi wa lmam (r.a) kana kuma ya ci gaba da yi masa takalidi (bayan rasuwarsa), shin zai iya komawa ga waninsa na daga cikin maraji'ai cikin wata mas'ala kamar rashin daukar garin Teheran cikin manyan birane ko kuma a'a?
Hakan ya halatta a gare shi, ko da yake bai kamata a bar ihtiyat, ba wajen ci gaba da taklidin Imam (r.a), idan har yana ganin fifikonsa kan rayayyu.

CI GABA DA TAKLIDIN MAMACI


Wani mutum bayan rasuwar Imam al-Rahil (r.a) ya yi takalidi wa wani marja'i, to amma a yanzu yana so ya sake komawa ga taklidin Imam (r.a) a karo na biyu, shin hakan ya halatta a gare shi?
A bisa ihtiyat canza takalidi daga rayayyen mujtahidi wanda ya cika sharudda zuwa ga mamaci ba ya halatta, na'am idan har shi rayayye bai mallaki sharuddan takalidi ba to komawa gare shi tun farko bai inganta ba, dan haka, kenan har yanzu yana nan a kan taklidin waccan mamacin kuma yana da zabi imma dai ya ci gaba da takalidin mamacin ko kuma ya koma ga rayayyen mujtahidi wanda ya halatta a yi masa takalidi.
Mene ne hukuncin ci gaba da takalidin mamaci idan har mamacin shi ne A'alam?
Bisa dukan hali ci gaba da takalidin mamaci ya halatta ko da yake ba wajibi ba ne, to amma ya kamata kada abar lhtiyat wajen ci gaba da takalidin mamacin da yake shi ne A'alam.
Shin neman izinin A'alam wajen ci gaba da takalidin mamaci sharadi ne ko kuma za'a iya neman izinin kowane mujtahidi?
Ba wajibi ba ne takalidin A'alam cikin mas'alar ci gaba da takalidin mamaci, idan dukkan fukaha'u sun yarda da hakan.
Bayan rasuwar Imam (r.a) na zaci cewa ba ya halatta a ci gaba da taklidin mamaci kamar yadda fatawarsa ta nuna, don haka sai na zabi wani mujtahidi rayayye don in masa taklid to shin ya halatta in sake komawa ga Imam (r.a) a karo na biyu?
Ba ya halatta gare ka ka koma gare shi (Allah ya rahamshe shi) bayan ka canza takalidinka cikin dukkan mas'alolin fikihu daga gare shi zuwa ga wani rayayyen mujtahidi, sai dai idan fatawar shi wannan rayayyen mujtahidi ita ce wajibcin ci gaba da takalidin mamacin da yake A'alam kana kuma kai ka yarda da cewaImam (r.a) shi ne A' alam kan wannan rayayyen mujtahidi, to a wannan hali wajibi ne gare ka ka ci gaba da takalidin marigayi Imam (r.a).
Shin wajibi ne ga masu takalidin Imam (r.a) kana kuma suke son ci gaba da yi masa takalid su nemi izinin daya daga cikin rayayyun maraji'ai ko kuwa ittifakin da yawa daga cikin marajiai da manyan malamai kan halaccin ci gaba da takalidin mamaci ya wadatar?
Ittifakin manyan malaman wannan zamani kan halaccin ci gaba da takalidin mamaci ya wadatar wajen ci gaba da takalidin marigayi Imam (r.a) dan haka babu bukatan sai an koma ga wani takamammen mujtahidi.
Mene ne fatawarka kan ci gaba da takalidin mamaci cikin mas'alolin da mukallafi ya yi aiki da su yayin rayuwarsa da kuma wanda bai yi aiki da su ba ?
Ci gaba da takalidin mamaci cikin dukkan mas'aloli har ma wanda shi mukallafi bai yi aiki da su ba ya halatta kuma yana isarwa.
Mun kasance masu takalidin lmam khumaini (r.a) kana kuma muka ci gaba da yi masa takalidi bayan rasuwarsa, to yana iya yiyuwa wata mas'ala ta sharia ta bijiro mana musammam ma ga shi muna raye ne a zamanin manyan azzalumam duniya, dan haka sai muka ga yana da muhimmanci mu koma gare ka cikin dukkan masalolin sharia, a dalilin haka muke so mu komo gare ka mu yi maka Takalidi, shin za mu iya hakan?
Ya halatta muku ku ci gaba da takalidin marigayi Imam (r.a), babu wata bukatan ku canza takalidinku daga gare shi (r.a), to idan har wata bukatan neman hukuncin shari'a kan wasu sababbin mas'aloli ta taso, to kuna iya tuntubar ofishinmu, Allah ya shiryar da ku zuwa ga yardarsa.
Mene ne abin da ya wajaba kan mai yin takalidi ga wani marja'i yayin da A'alamiyyar wani marja'i ta bayyana masa?
Wajibi ne bisa ihtiyat ya koma zuwa ga marja'in da ya gano A'alamiyyarsa -cikin mas'alolin da fatawar wannar marja'i nasa suka saba da na shi wannan marja'i Aalam.
A wani hali ne ya halatta ga mukallafi ya canza marja'in da yake masa takalid?
Canza takalid yana wajaba ne bisa ihtiyat idan shi marja'i na biyun ya fi na farkon sani, kana fatawarsa cikin mas'ala ta saba wa ta farko, to amma idan dai-dai suke to a bisa lhtiyat ba ya halatta.
Shin ya halatta komawa zuwa ga wanda ba A'alam ba idan fatawoyin shi marja'i A'alam ba su dace da zamaninsu ba ko kuma aiki da su yana da wahalar gaske?
Bai halatta ba canza takalid daga A'alam zuwa ga wani mujtahidi saboda kawai zaton rashin dacewar fatawoyinsa da irin yanayin da ke kewaye da su, ko kuma dan kawai kasantuwar akwai wahala cikin aiki da wadannan fatawoyi.

MAS'ALOLI DABAN- DABAN KAN TAKLIDI


Mene ne ma'anar Jahilul Mukassir?
Jahilul Mukassir: Shi ne jahilin da ya san shi jahili ne, kuma ya san hanyoyin da zai iya bi wajen kawar da jahilcin amma ya ki ya bi su.
Wane ne kuma Jahilul Kaasir?
Al- Jahilul Kaasir: Shi ne wanda bai fadaka da jahilcinsa ba, ko kuma bai san hanyar da zai bi wajen kawar da jahilcin nasa ba?
Mene ne ma'anar ihtiyati na wajibi?
Ma'anarsa shi ne wajibi ne ayi aiki ko abar aikata wani aiki saboda ihtiyati (ko kuma a koma ga wani marja'i).
Shin wannan lafazi ta "fihi ishkal" (akwai matsala a cikinsa) wanda ake kawo shi a cikin fatawoyi yana nufin haramci ne?
Ma'anarta tana banbanta gwargwadon yadda ta zo, idan har matsalar a wajen halacci ne to tana nuna haramci ne a fagen aiki.
Shin wadannan ibarori: "Fihi lshkal", "mushkil" "la yakhlu min lshkal" (wato bai fita daga cikin matsala ba) "la ishkal fihi" (wato babu matsala a cikinsa) fatawoyi ne ko kuma ihtiyat ne?
Dukkansu ihtiyati ne in banda kore ishkal shi fatawa ce.
Mene ne banbanci tsakanin rashin halacci da haramun?
Babu wani banbanci tsakaninsu a wajen aiki.


MARJA'ANCI DA WILAYA:
A shar' ance mene ne ya wajaba kan musulmai kana kuma mene ne ya wajaba su aikata lokacin da aka sami saBani tsakanin fatawar shugaban musulmai (waliyu amril muslimin) da fatawar wani marja'i cikin mas'alolin zamantakewa, siyasa da al'adu? Shin akwai haddi da ke banbance hukunci da ya fito daga wani marja'i da kuma wanda ya fito daga "waliyul Fakih"? misali idan ra'ayin wani marja'i kan sauraren kida ya saba da ra'ayin "waliyil fakih", shin a cikinsu wanne ne ya zama wajibi a bi shi kana wanne ne bin sa ke wadatarwa?
A bin nufi a nan dai shin wadansu hukunce- hukunce ne ake kira "Ahkamul Hukumatiyya"(wadanda) hukuncin "waliyul fakih" a cikinsu yana da fifiko kan fatawar marja'i?
Fatawar waliyu amril muslimin ita ce za a bi (kuma ita ce abin bi)a lamurran da suka shafi hukuma da hukuncin kasa ta Musulunci hakana fatawarsa ita ce abin bi cikin ababen da suka game musulmai duka amma lamurran da suka shafi daidaikun mutane, to kowane baligi zai iya tuntubar marja'insa a kansu.
Misali idan na kasance ina takalidi wa wani marja'i, sai "waliyu amril muslimin" ya ba da umurnin fita yaki dan fuskantar kafirai azzalumai ko kuma ya wajabta jihadi, to amma marja'in da nake masa takalidi bai ba ni izinin shiga yakin ba, to shin zan bi ra'ayinsa ne ko kuma a'a?
Wajibi ne yin biyayya ga umarnin wali amril muslimin cikin al'amurran da suka game musulmai wanda kare addinin musulunci da musulmai yana daga cikin wadannan lamurra, domin kare su daga kafirai da azzalumai da suka kawo hari ma musulmai.


WILAYATUL FAKIH DA KUMA HUKUMCIN SHUGABA (JAGORA):

Shin za'a iya daukar mutumin da bai yarda da' wilayatul fakih na mutlaki ba cewa shi musulmi ne hakika?
Rashin yarda da wilayatul fakih na mutlaki a zamanin gaibar Imam Mahdi (A.F), bai sa mutum ya yi ridda kuma bai fitar da mutum daga Musulunci sawa'un ijtihadinsa ne ya kai shi ga haka, ko kuma taklidinsa.
Shin umarnin waliyul fakih suna wajaba kan dukkan musulmai ne ko kuma wajibcinsa kawai kan masu yi masa takalidi ne ? kana shin wajibi ne ga wanda yake takalid ga wanda bai yarda da wilayatul fakih na mutlaki ba ya yi biyayya ga waliyul fakih ko kuma a'a?
A bisa fikihun shia wajibi ne ga kowane musulmi ya yi biyayya ga umarnin da suka fito daga waliyu amril muslimin, da kuma mika wuya ga umarni da hane-hanensa hatta ga sauran manyan malamai (maraji'ai) to ina ga masu yi musu takalidi! Mu ba ma ganin biyayya ga wilayatul fakih wani abu ne da yake da bambanci da yin biyayya ga addinin Musulunci da kuma jagoranci na Imamai Maasumai (A.S).
Hakika ana amfani da kalmar wilayatul mudlaka (iko na gaba daya) a zamanin Manzon Allah(Sawa) da ma'anar cewa shi Annabi(sawa) idan da zai umarci wani mutum da aikata wani al'amari to wajibi ne ya aikata shi ko da kuwa alamarin yana daga lamurra mafi wahala, kamar da Annabi(sawa) zai umurci wani mutum da ya kashe kansa to wajibi ne ya aikata hakan, to tambaya anan ita ce: Shin "wilayatul mudlaka" har yanzu tana nan da wannan ma'ana ?tare da cewa shi annabi (sawa) ya kasance ma'asumi ne, amma a wannan zamani babu wani jagora Ma'asumi?
Abin nufi da "wilayatul mudlaka" ga fakih (mujtahidi) wanda ya cika sharudda shi ne cewa shi addinin Musulunci-wanda shi ne cikamakin saukakkun addinai wanda kuma zai ci gaba da wanzuwa har zuwa ranar alkiyama-addini ne na hukunci da kuma jagorantar al'amurran al'umma, dan haka dole ne al'ummar musulmai da dukkan bangarorinsu su kasance suna da jagora mai mulkinsu (malami) kuma shugaba wanda zai kare su da addininsu daga abokan gabansu, kana ya kare musu tsarinsu, sannan ya tsayar da adalci a tsakaninsu, ya kuma hana masu karfi su zalunci masu rauni, ya kuma samar da abubuwan ci gaba na al'adu, siyasa da zamantakewarsu.
Watakila wajen gudanar da wannan al'amari ya yi karo da manufofin wasu ko bukatunsu ko burace-buracensu ko amfaninsu ko kuma 'yancin wadansu mutane don haka wajibi ne ga jagoran musulmai yayin gudanar da al'amarin jagoranci bisa ga fikihun musulunci da ya dauki matakai da suka dace idan ya ga bukatan hakan.
Kana dole ne ya zamanto ikonsa da kuma abin da ya yi nufin zartarwa ya zama shi ke da rinjaye kan iko da kuma nufin sauran jama'a a duk lokacin da wadannan manufofi guda biyu suka yi karo- to wannan dan takaitaccen bayani ne dangane da ma'anar Wilayat al-Mutlaka.
Kamar yadda ci gaba da takalidin mamaci ya ta'allaka ne da izinin rayayyen mujtahidi bisa yadda fatawar malamai ya tafi akai, to shin umarni da hukunce -hukuncen jagoranci da suka fito daga wajen jagoran da ya rasu su ma suna bukatan izinin sabon (rayayyen) jagora kafin su ci gaba da wanzuwa ko kuma a'a?
Hukunce- hukuncen jagoranci da suka fito daga wajen "waliyi amril muslimin" da ya rasu in dai har ba na takaitaccen lokaci ba ne, to tana nan daram, sai dai idan sabon jagoran yana ganin akwai wata maslaha wajen shafe su, to yana da daman shafe su.
Shin wajibi ne ga fakihin da yake zaune a jamhuriyar musulunci ta lran idan har bai yarda da "wilayatul fakih"mudlaka ba-da ya yi biyayya ga umarnin waliyul fakih ? to idan ya saba wa umarnin waliyul fakih shin za'a iya daukansa fasiki?sannan idan wani fakihi ya kasance ya yarda da "wilayatul fakih" mudlaka, to amma yana ganin shi ya fi dacewa da wannan matsayi, to shin idan ya saba wa umarnin jagora da ke jagoranci ana iya daukansa a matasyin fasiki?
Wajibi ne ga kowane mukallafi, ko da kuwa mujtahidi ne, da ya yi biyayya ga hukunce-hukuncen jagoranci(hukuma) na waliy amril muslimin, ba ya halatta ga wani ya saba wa jagoran da yake jagoranci saboda da'awar cewa shi ya fi shi dacewa, hakan kuwa wajibi ne idan har shi jagoran da yake jagorancin ya hau wannan matsayin ne ta hanya da ta dace da dokokin da aka tsara domin haka, to amma in ba ta wannan yanayin ba, to al'amari ya bambanta.
Shin mujtahidin da ya cika sharudda- a zamanin buya (gaiba) yana da ikon zartar da haddi?
Wajibi ne a gudanar da haddi a lokacin gaiba, ikon hakan kuwa yana hannun waliyi amril muslimin ne kawai.


BABIN TSARKI:

HUKUNCE-HUKUNCEN RUWA


Idan sashin kasa na ruwa mara yawa (al'maul kalil) wanda yake gangarowa daga sama ba da karfi ba ya shafi najasa, to shin sashin samansa yana nan da tsarki ko kuwa?
Sashin sama na ruwan da yake gangarowa yana da tsarki idan dai har gangarowar nasa ta kasance ta yadda za'a iya kiranta gangarowa ce daga sama zuwa kasa.
Shin wajibi ne bayan wanke tufafi mai najasa da ruwa mai gudu ko kuma ruwan kur a matse shi a wajen ruwan kafin ya tsarkaka ko kuma yana ma iya tsarkakuwa idan aka matse shi a cikin ruwan?
Yayin tsarkake tufafi da makamantansa da ruwa mai gudu ko kuma ruwan kur matsewa ba sharadi ba ne, duk wata hanyar da aka bi wajen fitar da ruwan da ke jikinsa ya wadatar, ko da kuwa ta hanyar jijjiga mai tsanani ne a misali.
Mene ne hukuncin alwala da kuma wanka da ruwan da a dabi'ansa shi mai kauri ne? Misali kamar ruwan teku da saboda yawan gishirin da ke cikinsa ya mai da shi mai kauri.
Don kawai ruwa ya yi kauri saboda kasantuwan gishiri a cikinsa ba ya hana a kira shi "Ruwa Mudlak". A shar'ance abin da ke tabbatar da kasantuwan ruwa "mutlaki" shi ne idan har jama'a za su kira shi wannan ruwa da sunan mutlaki.
A wasu lokuta a kan sanya wa ruwa wani sinadarin da ke sanya shi ya zamanto da launin madara, to shin wannan ruwa ya zama "ma'ul Mudaf" ruwa wanda ya cudanya? Shin mene ne hunkuncin alwala ko tsarki da shi?
Hukuncinsa ba hukuncin "ma'ul Mudhaf" (ruwan da ya cudanya) ba ne.
Idan ruwa mai gishiri-gishiri ya tafasa, shin ana iya alwala da ruwan da ya taru na daga tururinsa?
Idan har abin da ya taru na daga wannan za'a iya kiransa "ma'ul Mudlak" (wato ruwa mutlaki) to ana iya amfani da shi.
Yayin wanke tufafi masu najasa da ruwa mai yawa shin wajibi ne a matse su ko kuma zuba (isasshen) ruwa kan inda najasar ta taba bayan gusar da najasar ya wadatar?
Zubo (isasshen) ruwa a kansu da kuma fitar sa daga gare su ya wadatar ko da kuwa ta hanyar jijjiga su cikin ruwa mai yawa, ne matsewa ba sharadi, ba ne.
A lokacin da muke son wanke darduma ko shimfida mai najasa da ruwan famfo, shin su kan tsarkaku ne da zarar saduwar ruwan famfon da wurin najasar ko kuma sai an fitar da ruwan wankin daga jikinsu.
Yayin tsarkake abu mai najasa da ruwan famfo fitar ruwan wankin ba sharadi ba ne, face dai yana tsarkakuwa ne daga zarar isar ruwan ga wurin da ya najastu bayan gushewar najasar da kuma gushewar ruwan wankin daga gurin.
Yayin tsarkake tafin kafa an shardanta taku goma sha biyar, to shin hakan bayan gushewar najasar ne ko kuma ko da ainihin najasar tana nan? Sannan tafin kafa yana tsarkakuwa ne da taku goma sha biyar bayan gushewar ainihin najasar idan mutum ya yi tafiya da kafar?
Abin lura ba shi ne taku goma sha biyar ba, face dai abin da ke wadatarwa shi ne takun da a dalilinsa ainihin najasar za ta iya gushewa. Kana kuma idan da najasar ta gushe kafin ya yi tafiya, to yanzu sai ya dan yi tafiya kadan shi kenan.
Shin za'a iya daukar hanyoyin da aka sanya musu kwalta da dai makamancinsa a matsayin kasa mai tsarkakewa ta yadda za su iya tsarkake tafin kafa yayin tafiya a kansu?
Kasar da aka sanya mata kwalta da makancinta ba ta tsarkake cikin tafin kafa ko kuma abin da aka sanya wa tafin kafar kamar takalmi.
Yaya za'a iya tsarkake tufafi masu najasa wadanda launinsu yake zuba a cikin ruwan yayin tarkake su?
Idan dai har zuban launin ba zai iya canza ruwan ya koma "mudaf" ba, to za'a iya tsarkake su ta hanyar zuba ruwa a kansu.
Mutum ne ya zuba ruwa a langa dan wankan janaba, to yajin da yake wankan sai wani sashi na ruwan da ke zuba daga jikinsa ya kasance yana komawa cikin langar, to shin a wannan halin ruwan yana nan da tsarkinsa? Shin akwai wani abin da zai hana gama wankan da shi wannan ruwan?
Idan har ruwan da ke zuba cikin langan yana zuba ne daga sashin jikinsa wanda ke da tsarki to ruwan yana da tsarki kuma babu wani abin da zai hana gama wankan da shi.

HUKUNCE- HUKUNCEN SHIGA BAYAN GIDA


Misali irin kabilun nan masu yawo daga guri zuwa guri kamar fulani idan ba su mallaki ruwan da za su yi tsarkin fitsari ba musamman a ranekun da suke kauran, shin tsarki da tsakuwa ko kuma itace yana wadatarwa?
Abin da ba ruwa ba ba ya tsarkaka gurin fitsari, to idan har bai samu daman tsarkake shi da ruwan ba, to sallarsa ta inganta.
Mene ne hukuncin tsarkake mafitar fitsari da bayan gida da ruwa kadan ma'ul kalil.
Wanke mafitar fitsari sau daya yana wadatarwa, amma mafitar bayan gida wajibi ne a wanke shi har sai ainin najasar da alamunsa ya gushe.
A bisa al'ada wajibi ne ga mai salla bayan gama fitsari ya yi istibra'i to amma ni ina da wani ciwo a al'aura ta, yayin da nake istibra'i jini ya kan fito min a dalilin mammatse shi da nake yi kana ya hadu da ruwan da nake amfani da shi wajen tsarkin sannan ya najasta min jiki da tufa, kana idan har ban yi istibra'i ba to ina sa tsammanin warkewan ciwon, kuma abu ne sananne cewa ciwon zai ci gaba da wanzuwa idan na ci gaba da istibra'i saboda mammatse al'auran da nake yi, dan haka nake so ka min bayani shin zan yi istibra'i ko kuma a'a?
Shi dai istibra'i ba wajibi ba ne, face ma dai idan har zai haifar da cutarwa to ba ya halatta a yi shi Na'am idan har ba'a yi istibra'i ba bayan gama fitsari sai wani danshi mai rikitarwa ya fito to ana daukansa a matsayin fitsari ne.
A wasu lokuta wani danshi (ruwa) mai kama da fitsari ya kan fito ma mutum ba tare da son sa ba bayan fitsari da kuma istibra'i, to shin wannan danshin najasa ne ko kuma yana da tsarki? Kana idan mutum ya fahimci hakan bayan wani lokaci, to mene ne hukuncin sallolin da ya riga ya yi sannan shin wajibi ne a nan gaba ya binciki fitar wannan danshi da ke fita ba tare da zabinsa ba?
Idan wani danshi ya fito bayan istibra'i kana aka yi shakkan kasantuwarsa fitsari to bai da hukuncin fitsari, yana da tsarki, ba wajibi ba ne a yi wani bincike.
Da za ka yi mana cikakken bayani kan nau'oin ruwa da suke fitowa daga jikin mutum.
Ruwan da a wasu lokuta yake fitowa bayan maniyyi ana kiransa da' wazi", kana ruwan da ke fitowa a wasu lokuta bayan fitsari ana kiransa da "wadi", sannan ruwan da ke fitowa a wasu lokuta bayan wasanni tsakanin ma'aurata biyu ana kiransa da "mazi" dukkan wadannan ruwa masu tsarki ne, ba sa warware tsarki.
Aiki a wasu kamfanoni da kuma mu'assasosi: ya ta'allaka da gudanar da wasu bincike kan lafiyar mutum wanda hakan yakan kai ga bude al'aura wani sa'i, to shin hakan ya halatta idan akwai bukatuwa ga aikin?
Ba ya halatta ga mutum ya bude al'aura gaba ga wani mutum ko da kuwa aikin da za a ba shi ya taallaka da hakan ne sai dai idan barin aikin zai sa shi cikin halin kaka nikai, kana kuma ya zama dole ne ya yi hakan.

HUKUNCE -HUKUNCEN ALWALA


Akwai wani mutum da ya sanya wa kansa gashin, kanti, idan har ya cire zai shiga cikin kunci, to shin ya halatta gare shi ya yi shafa akan wannan gashi (yayin alwala).
Ba ya halatta a yi shafa a kan gashin kanti, face ma dai wajibi ne a kawar da shi dan shafa kai sai dai idan a kawar da shi din akwai wahalan gaske da ya saba wa al'ada.
Wani mutum yana cewa: Yayin alwala a zuba ruwa a fuska sau biyu kawai amma sau, uku yana ?ata alwala, shin hakan gaskiya ne?
Zuba ruwa sau biyu ko fiye babu matsala a cikinsa, amma wanke fuska ko hannaye sama da sau biyu ba ya halatta.
Shin za'a iya kirga man da a bisa dabi' ar jikin mutum ya kan fito a kan gashin kan mutum ko fatansa har a kira shi a matsayin hajib(abin da ke hana isar ruwa ga fata).
Ba'a kirga shi a matsayin hajib sai idan ya kai yanayin da shi kansa mukallafi yake ganin sa a matsayin abin da zai hana isar ruwa zuwa ga fatar jiki ko kuma gashi.
Mene ne idon sawu (al-ka'ab) wanda shi ne karshen wajen shafa yayin shafan kafa?
A bisa mashhurin magana shi ne wurin da ya dan taso sama na kafar mutum wanda ake kira da tudun saman kafa, to amma kada a bar ihtiyat wajen isar da shafan har zuwa mahadan sawu.
Idan aka sami idaniyar ruwa tana bubbugowa daga wani guri (kasa) wanda yake gurin mallakar wani mutum ne to idan muna so mu jawo wannan ruwa ta hanyar amfani da bututun ruwa zuwa ga wani guri da ke da nisar kilomitoci hakan zai tilasta mana bi da wadannan bututu cikin filin wannan mutumin da kuma filayen wadansu mutane, to idan har wadannan mutane ba su yarda da hakan ba, shin ya halatta ayi amfani da wannan ruwa dan alwala da wanka da sauran ayyukan tsarki?
Babu matsala wajen amfani da ruwan idan har wannan idaniyar ruwa tana bubbugowa ne da kanta, kana kuma kafin gudanar ta akan kasa aka ja ruwan nata zuwa cikin wadannan bututu, kana kuma an yi amfani da shi gefen filin da idaniyar ruwan yake da kuma gefen sauran filayen ne ba dan komai ba sai domin kawai ya zama wuri ne na wucewa da bututun, to a wannan hali ba matsala, matsawar ba za'a iya ganin amfani da idon ruwan kamar amfani ne da filin da idon ruwan yake ciki ko kuma amfani ne da filayen sauran mutanen ba.
Yayin wanke fuska da hannaye lokacin alwala idan da mutum zai dinga budewa da kuma rufe famfon da yake alwala da shi, to mene ne hukuncin wannan taba famfo da yake yi da hannunsa mai danshi.
Babu matsala ga hakan, ba ya cutar da ingancin alwala, to amma bayan gama wanke hannun hagu kafin yin shafa da shi idan da mutum zai sanya shi a kan ruwan da ke kan famfon to akwai matsala wajen ingancin alwalarsa idan dai har aka dauka ruwan da ke hannunsa da ruwan da ke famfon sun cudanya.
Wasu mata suna daawar cewa sanya jan farce akan farce ba ya hana alwala, kana kuma yin shafa akan safa mara kauri (shara-shara)yana halatta, shin mene ne fatawarka kan hakan?
Idan har jan farcen yana hana isar ruwa zuwa ga faratu to alwala ta baci, sannan shafa akan safa ba ya inganta komi shara-sharansa.
Saboda ciwon shan inna da na samu a kafa ta sai ya zamanto ina amfani da wani takalmi na musamman da kuma sanduna biyu wajen tafiya, to saboda cire wadannan takalma yayin alwala ba zai yiwu ba, don Allah ina son ayi min bayani kan abin da ya wajaba a kaina dangane da shafan kafa?
Idan har cire takalmin dan shafan kafa zai zamanto kunci gare ka, to shafa a kansa ya wadatar kana ya inganta.
Yaya mutum mai yawan waswasin alwalarsa zai yi salla, ko karatun kuriani da ziyarar kabarin ma'asumai (a.s.)?
Ba'a damuwa da shakkan tsarki bayan alwala, ya halatta gare shi da ya yi salla da karatun kur'ani matukar dai bai sakankance da bacin alwalarsa ba.
Shin gudanar ruwa ga dukkan gabobin hannu sharadi ne na ingancin alwala ko kuma shafansu da sauran danshin da ke jikin hannu ya wadatar?
Ma'aunin tabbatuwar wankewa shi ne isar da ruwa ga dukkan gabobi ko da kuwa isar ruwan ga dukkan gabobin ta hanyar shafa hannu ne, to amma shafa da danshin da ke hannu kadai ba ya wadatarwa.
Shin yayin alwala ya halatta a shafi kai da danshin da ke hannun hagu kamar yadda ya halatta da na dama ? kana shin ya halatta shafan kai daga kasansa zuwa samansa?
Babu wata matsala wajen shafan kai da hannun hagu, ko da yake abin da yake ihtiyat shi ne shafa da hannun dama, sannan kuma a bisa ihtiyat shi ne shafan kai ya kasance daga sama ne zuwa kasa, wato daga tudun kai zuwa wajen goshi, ko da yake akasin haka ma yana wadatarwa.
Yayin shafan kai shin shafan gashi da danshin hannu yana wadatarwa ko kuma waijibi ne sai an sadar da danshin zuwa fatan kai? Kana kuma idan mutum yana amfani da gashin kanti to yaya zai yi shafar kai?
Shafar fatan kai ba wajibi ba ne, idan har gashin kanti ba za, a iya cire shi ba to shafa a kansa yana wadatarwa.
Mene ne hukuncin jinkirtawa tsakanin gabobin alwala ko wanka?
Rashin gaggautawa a cikin wanka ba matsala ba ce to amma a alwala idan har jinkirtawar zai kai ga bushewar gabobin da aka riga aka wanke to alwala ya baci.
Mutumin da tusa yake yawan fita masa me ya kamata ya aikata yayin alwala da salla?
Idan har ba shi da wani lokacin da zai iya kiyaye alwalarsa har zuwa karshen sallarsa, kana kuma sassake alwala yayin salla zai zamanto kunci a gare shi, to ya hatatta ya yi salla guda da alwala guda, wato ya takaita da alwala guda ga kowace salla ko da kuwa alwalar ta baci yayin sallar.
Mutum ne ya yi wankan janaba, to sai bayan awa 3 zuwa 4 ya so ya yi salla to amma bai san cewa shin wankansa ya baci ne ko kuma a'a, to shin akwai matsala idan ya yi alwala dan samun kwanciyar hankali (ihtiyat)?
A bisa wannan yanayi da ka ambata sake alwala ba wajibi ba ne, to amma yin "ihtiyat" ya halatta.
Mene ne hukuncin wata gaba daga cikin gabobin alwala da ta najastu bayan wanke ta amma kafin idar da alwalar?
Hakan ba ya cutar da ingancin alwala, na'am wajibi ne a tsarkake wannan gabar idan za'a yi salla.
Shin kasantuwar digo-digon ruwa akan kafa yana cutarwa yayin shafa?
Wajibi ne a busar da wurin shafa daga duk wani digo na ruwa kafin yin shafan?
Shin shafan kafar dama yana faduwa idan har hannun daman a yanke yake daga asalinsa?
A'a ba ya faduwa, face dai wajibi ne a yi shafan da hannun hagu.
Mene ne hukuncin mutumin da ya jahilci karyewar alwalarsa sai bayan ya gama ya fahimci hakan?
Wajibi ne ya sake alwalar, haka kuma ya sake duk wani aikin da ke bukatar alwala kamar salla da ya yi a baya da wannan alwalar.
Shin share ruwan alwala bayan idarwa makaruhi ne? Kana rashin sharewan mustahabi ne ?
Idan har an kebance wa wannan aiki wani kyalle na musamman, to babu wata matsala ga hakan.
Shin irin launi da mata suke shafawa akan gashin kai da giransu don rina su yana bata alwala ko wanka?
Idan har ba shi da maikon da zai hana isar ruwa ga gashin, shi dai kawai launi ne, to ba ya bata alwala ko wanka.
Shin ruwan biro yana daga cikin abubuwan da suke hana isar ruwa ga fata, ta yadda kasantuwarsa a hannu kan iya bata alwala?
Idan har yana hana isar ruwa ga fata to yana bata alwala, gane hakan kuwa yana hannun mukallafi ne.
Idan danshin shafa kai ya hadu da danshin fuska, shin alwala ya kan baci?
Babu matsala ga hakan, to amma kasantuwan ihtyat yayin shafan kafa shi ne ayi shafan da sauran danshin alwala da ya rage a hannu. to lalle ne ayi lhtiyat wajen kare isan hannu zuwa ga goshi yayin shafan kai, ta yadda ba zai hadu da danshin da ke fuska ba, don kada danshin hannu wanda za'a shafa kafa da shi ya hadu da danshi fuskar.
Mene ne hukuncin ruwan da ake kokwantonsa cewa fitsari ne ko maniyyi wanda ya fito bayan mutum ya yi fitsari da kuma istibra'i kana kuma ya yi alwala?
A wannan yanayi wajibi ne a hada alwala da wanka don a sami yakini kan tsarki.
Muna fatan za'a mana bayanin bambancin da ke tsakanin alwalan maza da na mata.
Babu wani bambanci tsakanin mace da namiji wajen ayyukan alwala da kuma yanayin alwalar, sai dai kawai mustahabi ne ga maza yayin wanke damtsensu da su fara da wajensa, su kuma mata mustahabi ne su fara da cikinsa.

TABA SUNAYEN ALLAH DA KUMA AYOYINSA

Mene ne hukuncin taba lamiran da suke komawa ga zatin Allah Ta'ala kamar lamirin da ke cikin "Bismihi Ta'ala" (wato "hi" da ya zo a wannan lafazi.)?
Lamiri ba shi da hukuncin lafazin sunan Allah.
Mene ne hukuncin taba sunayen mutane kamar Abdullahi ko Habibullah.... ba tare da alwala ba?
Ba ya halatta ga mara alwala da ya taba sunan Allah ko da kuwa ya kasance wani bangare ne na hadadden suna (kamar Abdullah).
Shin ya halatta ga mace mai haila ta sanya abin wuyan da aka rubuta sunan manzon Allah (sawa) a jiki?
Sanya shi a wuya ba matsala, sai dai wajibi ne kada sunan ya taba jikinta.
Shin haramcin taba rubutun Alkur'ani mai girma ba tare da tsarki ba ya kebanta ne kawai idan rubutun na cikin littafin Alkur'anin ne ko kuma ya hada da ko da yana jikin wani littafi ne daban, ko allo, ko katanga da dai sauransu ?
Ba kawai ya kebanta da littafin al-kur'ani ba ne, a'a ya hada da kalmomi da ayoyin al-kur'ani ko da kuwa a wani littafi na daban ne, ko cikin jarida, ko mujalla, ko allo ko kuma rubutu a jikin garu da dai sauransu .
A jikin wasu kwanuka da farantai da iyalanmu suke cin abinci an rubuta wasu ayoyin al-Kur'ani kamar ayatul kursiyyi, niyyarsu na yin hakan kuwa shi ne neman alheri da kuma albarka, to shin akwai wata matsala cikin hakan ?
Babu matsala ga hakan, sai dai wajibi ne a kiyaye kada a taba ayoyin Kur'ani ba tare da alwala ba.
Shin wajibi ne ga mutanen da suke rubuta sunayen Allah ko ayoyin Kur'ani ko sunayen ma'asumai (a.s) ta hanyar injunan rubutu su kasance cikin alwala yayin rubutun?
Ba sharadi ba ne a kasance cikin alwala sai dai taba rubutun ba tare da alwala ba ba ya halatta.
Mene ne hukuncin amfani da kan sarki da ake amfani da shi wajen aika wasiku (stamp) wadanda aka rubuta musu ayoyin Alkur'ani, kana mene ne hukuncin buga sunayen Allah da buga ayoyin Alkur'ani ko kuma buga take da kirarin wasu cibiyoyi wanda aka hada da Alkur ani a cikin jarida da mujalloli da suke yadawa kowace rana?
Ba matsala wajen bugawa da kuma yada ayoyin Alkur'ani da sunayen Allah da makamancinsu, sai dai wajibi ne ga wanda suka isa ga hannunsa ya kiyaye hukunce-hukuncen shari'a na rashin wulakanta su da kuma najasta su, da kuma taba su ba tare da alwala ba.
Shin ya halatta ga masu sai da kayayyaki da su kunshe abin sayarwarsu da jaridun da suke da sunan Allah ? kana shin ya halatta a taba su ba tare da alwala ba?
Amfani da wadannan jaridu wajen kunshe abin sayarwa babu matsala a cikinsa idan har ba a ganin hakan wulakanta sunayen Allah da ayoyin kur'ani da kuma sunayen imamai (as) da aka rubuta a jiki ne, to amma dai ba ya halatta ga mara alwala ya taba su alhali yana sane da shi.
Mene ne hukuncin rubuta sunayen annabawa da kuma ayoyin Alkur'ani a cikin jarida tare da yiyuwan kona su ko kuma fadawansu kasan kafa?
Shari'a dai ba ta hana rubuta ayoyin Alkur'ani da sunayen ma'asumai (a's) a cikin jaridu da mujalloli da sauransu ba, sai dai wajibi ne a nesanci wulakanta su da kuma najasta su, kana da kuma taba su ba tare da alwala ba.
Mene ne hukuncin jefa abubuwan da suke kunshe da sunayen Allah cikin kogi ko kuma rafi? Shin za'a kirga hakan a matsayin wulakantawa?
Ba matsala wajen jefa su cikin kogi ko rafi idan har jama'a ba sa ganin haka wulakanci ne.
Shin sharadi ne yayin jefar da takardun jarabawar da aka riga aka gyara su a cikin kwandon shara ko kuma kona su a tabbatar da rashin kasantuwar sunayen Allah da ma'asumai (a's) a jikinsu? Kana shin jefar da takardun da ba'a yi amfani da su ba almubazzaranci ne?
Yin bincike ba wajibi ba ne, idan dai har mutun bai san da cewa akwai sunan Allah a jikin takarda ba to jefar da ita tare da shara ba matsala, amma takardun da aka yi amfani da wani bangare nasu kana za'a iya amfani da daya bangaren wajen rubutu ko kuma amfani da shi wajen wani aiki, to konawa ko kuma jefar da ita akwai matsala a cikinsa, (wato za'a iya cewa almubazzaranci ne).
Wadanne ne sunaye masu albarkan da wajibi ne a girmama su kana haramun ne a taba su ba tare da alwala ba.
Ba ya halatta a taba sunayen zatin Allah madaukakin sarki, da kuma sunayen siffofin da suka kebantu da Allah Ta'ala ba tare da alwala ba kana kuma ihtiyat a nan ya wajabta cewa sunayen Annabawa (A.S) da kuma sunayen Imamai (A.S) su ma suna da wannan hukunci da muka ambata.
Muna da adadi mai yawa na jaridu da muka samu daga wasu mu'assasosi, wadanda da dama daga cikin shafukansu akwai sunayen Allah da dai makamantansu, dan haka muna so ayi mana bayani yadda za mu kiyaye su?
Kuna iya binne su a cikin kasa ko ku kai su jeji in har a cikin hakan babu wulakantarwa.
Wadansu hanyoyi ne sharia ta yadda da su wajen gogewa ko shafe sunaye masu albarka da ayoyin kur'ani yayin bukatar hakan? Kana mene ne hukuncin kona takardun da suke da sunayen Allah ko ayoyin kur'ani a jikinsu idan har bukatan rabuwa da su da taso?
Ba wata matsala wajen binne su cikin kasa, ko kuma mayar da su gari, to amma kona su akwai matsala, idan ana ganin konawa a matsayin walakantarwa ne to ba ya halatta, sai dai idan yin hakan ya zama lalura kana ba za'a iya yanke ayoyin Kur'anin ko sunaye masu albarka ba.
Mene ne hukuncin yayyanke sunaye masu albarka da ayoyin Alkur'ani yayyenkewa ta yadda babu wasu haruffa guda biyu da suka hade ballantana su karantu? Kana shin caccanza yanayin rubuta su ta hanyar kara wasu haruffa a kansu, ko kuma shafe wasu haruffa yana wadatarwa wajen goge su da kuma faduwar hukuncinsu?
Yayyenkewa ba ya wadatarwa matukar dai bai haifar da shafe rubutun sunan Allah ko ayoyin kur'anin ba, kamar yadda canza yanayin shakalin rubutun ba ya wadatarwa wajen gusar da, wannan hukunci akan haruffan da aka zana su da nufin rubuta sunan Allah, Na'am bai yi nisa ba ace hukuncin yana iya faduwa bayan canza shakalin haruffan, ta hanyar ba shi hukuncin shafewa ko da yake ihtiyat shi ne a nisanci yin hakan.

HUKUNCE-HUKUNCEN WANKAN JANABA

Shin ya halatta ga mai janaba ya yi salla da taimama kana da kuma najasar da ke jiki da tufafinsa idan lokaci ya yi kunci ko kuma ya jira har ya yi tsarki kana ya yi wanka sannan ya yi salla a matsayin ramako?
Idan har lokaci ba zai ba shi daman ya tsarkake jiki da tufafinsa ba, ko kuma ya canza tufafin ba, kana kuma ba zai iya salla tsirara ba saboda sanyi da makamancinsa, to sai ya yi salla a wannan hali cikin najasar amma tare da yin taimama wadda za ta zama a maimakon wankan janaba kuma ta wadatar kana ba wajibi ba ne ya rama ta.
Shin isar da maniyyi zuwa ga mahaifa ba ta hanyar jima'i ba yana haifar da janaba?
Janaba ba ta tabbatuwa da haka.
Shin wajibi ne ga mata bayan binciken da ake musu a cikin jikinsu ta hanyar amfani da kayan ayyukan likitanci da su yi wankan janaba?
Ba wajibi ba ne su yi wanka matukar dai maniyyi bai fito musu ba.
Idan har gwargwadon hashafan namiji ya buya a farjin mace, to amma maniyyi bai fita ba kana kuma macen ba ta kai kolin jin dadinta ba, to shin wanka ya wajaba a gare ta ne kawai ko kuma ga namijin ne kawai ko kuma wajibi ne a kansu su biyun ?
A bisa wannan yanayi da aka ambata wajibi ne gare su su biyun.
Dangane da mafarkin mata, shin a wani irin yanayi ne wankan janaba yake wajaba a gare su? Kana shin ruwan da yake fito musu yayin wasa da mazaje yana da hukuncin maniyyi ne? Kana kuma shin wajibi ne su yi wanka tattare da cewa basu kai ga jin dadinsu ba kana ba su ji mutuwar jiki ba? A takaice dai yaya janaba take tabbata ga mata ba tare da jima'i ba?
Idan mace ta ga alamar maniyyi a jikin tufafinta bayan farkawarta daga barci to wajibi ne ta yi wankan janaba to amma ruwan da yake fito musu yayin wasa da makamancinsa ba shi da hukuncin maniyyi, sai dai idan ya fito tare da mutuwar jiki da kuma isa ga jin dadi na koli.
Shin wanka yana wajaba ga budurwar da sha'awarta ta tashi ta hanyar karatun littafan batsa ko kuma ta wata hanya ta daban? To idan har wankan ya wajaba, to wane wankan ne ya wajaba a gare ta?
Karanta littattafan da suke motsa sha'awa bai halatta ba. Bisa dukkan hali dai wajibi ne gare ta ta yi wankan janaba idan har maniyyi ya fito mata.
Yayin da mace ta fahimci zuban wani ruwa cikin sha'awa lokacin wasa shin wajibi ne ta yi wankan janaba?
Idan har mace ta fahimci zuban maniyyi daga gare ta to wanka ya wajaba a gare ta, haka ma idan tana shakkan abin da ya fito din maniyyi ne ko kuma, a a matsawar dai ya fito ne tare da sha'awa ta musamman.
Idan mace ta yi wanka daga zarar saduwa da mijinta kana maniyyinsa ya ci gaba da zama cikin mahaifanta, shin wankanta yana nan da ingancinsa idan har maniyyin ya fito mata bayan wankan? Kana shin wannan maniyyi da ya fito bayan wanka yana da tsarki ko kuma a'a ?
Wannan maniyyi da ya fito mata najasa ne, sai dai idan har abin da ya fito mata din maniyyin mijin ne to ba ya wajabta wanka a karo na biyu.
Macen da ta samu janaba alhali tana cikin haila shin wajibi ne ta yi wankan janaba bayan ta sami tsarki ko kuma ba wajibi ba ne a gare ta tun da daman ba ta da tsarki?
Wajibi ne gare ta ta yi wankan janaba bugu da kari kan wankan hailar, ko da yake wankan janaba kawai yana wadatarwa, sai dai ihtiyat shi ne ta daura niyyar wankan biyu.
A wani irin hali ne za'a iya hukunta ruwan da ya fito wa mutum da cewa maniyyi ne?
Idan har ya biyo bayan sha'awa, da mutuwar jiki da kuma tunkuda yayin fitowa, to yana da hukuncin maniyyi.
A wasu lokuta bayan wanka za'a iya ganin sauran sabulu da ya makale a cikin faratun hannu ko na kafa, wanda ba'a iya ganinsa yayin wankan amma bayan fitowa daga bayan gida sai kaga farin sabulun ya bayyana, to mene ne abin yi? Bisa la'akari da cewa wadansu su kan yi wanka ko alwala tare da cewa sun jahilci hakan ko kuma ma hankalinsu bai kai ga hakan ba, kana tare da cewa ba'a da yakinin cewa ruwa ya ratsa wannan farin?
Dan kawai kasantuwan fari-farin sabulu wanda ya bayyana bayan gabobin jiki sun bushe bai cutar da ingancin alwala ko wanka, sai idan hakan zai hana tabbatuwan wanke fata.
Wani ya gaya min cewa: Wajibi ne kafin yin wanka a tsarkake jiki daga najasa, kana kuma ya ce wai tsarkake jiki dai dai lokacin da ake wanka, wato kamar a tsarkake shi daidai lokacin kana cikin wanka daga maniyyi yana bata wanka, to shin wajibi ne sai na sake Sallolin da na yi su a baya dan kuwa ni dama na jahilci wannan lamari.
Wajibi ne ya zama an raba tsakanin tsarkake jiki da kuma wankan janaba, to amma ba wajibi ba ne a tsarkake dukkan jikin kafin fara wankan, face dai wajibi ne kowace gaba ta zan tana da tsarki yayin wanke ta, dan haka da mutun zai san gabansa tana da tsarki kafin wanke ta, to wanka da sallarsa duk sun inganta, to amma fa idan da gaba za ta zama ba ta da tsarki kafin wanke ta, to wanka da sallar ba su inganta ba, wajibi ne ya sake su.
Idan mutum yayin wankan janaba sai ya yi wani abin da ke bata alwala, to shin wajibi ne ya faro wankan daga farko ko kuma ya karasa wanka kana daga baya ya yi alwala?
Ba wajibi ba ne ya koma ya faro wankan daga farko ba, face dai sai ya karasa wankan, to amma wajibi ne ya yi alwala yayin yin salla ko kuma wani aiki da yake bukatan alwala.
Idan wanka iri daban-daban wajibai ko mustahbbai ko dukkansu suka taru wa mutum, shin wanka guda ya kan wadatar?
Idan har a cikinsu akwai wankan janaba, kuma ya kudura niyyar wankan yana wadatarwa daga sauran hakana wanda ya yi wanka guda daya da niyyar dukkan wanka da ke kansa to ya isar masa kan sauran.
Shin wani wanka ba na janaba ba yana wadatarwa daga alwala?
A'a ba ya wadatarwa.
Idan mutum ya san cewa idan har ya sadu da matarsa ba zai sami ruwan wanka ba, ko kuma lokaci ba zai ishe shi ya yi wanka kana ya yi salla ba, to shin ya halatta ya kusanci matar tasa?
Idan har zai iya yin taimama a wannan hali, to babu wata matsala ga saduwa da matar tasa.
Ni dai saurayi ne dan shekara ashirin da biyu, to a kwanan nan sai gashina ya zama yana zuba wanda hakan ya jawo min matsala, to daga baya sai na kuduri aniyar na sa gashin kanti. To abin tambaya a nan shi ne: Mene ne hukuncin wankana idan har wannan gashi zai hana isar ruwa ga wasu bangarori na fatar kaina domin shi wannan gashin za a yi dashensa ne a kaina?
Idan har wannan gashi da aka dasa ba za, a iya cire shi ba, ko kuma kawar da shi din zai jawo maka cutarwa ko kunci, kana kuma ba za ka iya isar da ruwa zuwa ga fatar kan naka ba, to wankan tare da shi ya inganta.

ABIN DA YA WAJABA DANGANE DA WANKAN DA BAI INGANTA BA

Mutum ne ya samu janaba kana ya yi wanka, to amma wankan nasa bai yi shi dai-dai ba, to mene ne hukuncin sallar da ya yi bayan wankan, tare da cewa ya jahilci hakan?
Salla da wankan da ba'a yi dai-dai ba, ba ta inganta ba, wajibi ne a sake ta ko kuma a rama ta.

HUKUNCE- HUKUNCEN TAIMAMA

Idan abubuwan da ake yin taimama da su kamar turbaya, ko dutse da sauransu suka kasance a jikin gini ne, suke a damfare shin ya inganta a yi taimama da su ko kuma wajibi ne su kasance a kan kasa?
Kasantuwarsu a kan kasa ba sharadi ne na ingancin taimama da su ba.
Idan na wayi gari cikin janaba kana ba zan iya yin wanka ba, har na ci gaba da kasantuwa cikin janabar na wasu raneku, to shin wajibi ne kamar yadda ya kasance a baya in yi alwala ko kuma taimama ga duk wata sallar da zan yi bayan sallar da na yi mata taimama maimakon wanka, ko kuma ina iya takaita da sau guda kawai? Kana a irin wannan yanayi shin alwala ne ya wajaba ko kuma taimama ga kowace salla.
Da wani abin da ke bata alwala zai bijiro wa mai janaba bayan da ya yi sahihiyar taimama maimakon wankan janaba, to bisa ihtiyat sai ya yi taimama maimakon wanka kana ya yi alwala.
Shin taimamar da aka yi ta maimakon wanka tana da hukuncin wanka ne ? Wato shin zai iya aikata ayyukar da suka halatta ga wanda ya yi wanka ya aikata kamar shiga masallaci?
Duk wani aikin da ya halatta a aikata shi da wankan, yana ingantuwa a aikata shi da taimamar da aka yi ta maimakon wanka, sai dai ban da taimamar da aka yi ta maimakon wanka saboda kurewar lokaci.
A wasu lokuta wani ruwa ya kan fita wa mutum yayin barci, to bayan farkawarsa ba zai iya tuna komai ba sai dai kawai ya ga tufafinsa jike, kuma ba shi da lokacin da zai tsaya don yin tunani saboda sallar asuba za ta tsere masa, to shin me ya kamata ya aikata a irin wannan hali? Shin zai yi niyyar taimama ne maimakon alwala ko kuma wanka? A takaice dai mene ne ainihin abin da ya wajaba a kansa?
Idan har ya san janaba ya samu a dalilin wannan mafarki to wanka ya wajaba a kansa, to amma saboda kurewar lokaci sai ya yi taimama bayan tsarkaka jikinsa sannan daga baya ya yi wanka, to amma idan har yana shakkan mafarki da kuma janaba, to hukuncin janaba bai hau kan shi ba.
Mutum ne ya yi salla da taimama saboda karancin lokaci, to amma bayan idar da sallar sai ya bayyana masa cewa ashe yana da lokacin da zai iya alwala, to mene ne hukuncin sallarsa?
Wajibi ne gare shi ya sake wannan salla.
Muna raye ne a wani yanki da babu wurin da za'a yi wanka, to sai muka farka daga gabannin fitowar alfijir cikin janaba ga shi kuma cikin watan Ramalana ne, tattare da cewa mutane su ga saurayi yana wanka cikin dare da ruwan randa ko tanki babban aibi ne, kana kuma ga shi ruwan yana da tsananin sanyi, to mene ne abin yi dangane da azumin washe gari? Shin ya halatta mu yi taimama? Kana mene ne hukuncin karya azumin saboda rashin samun daman yin wankan?
A sabilin wahala ko kuma kasantuwan aikata wani aiki aibi ne a idon jama'a ba uzuri ba ne a fuskar shari'a face dai wajibi ne gare shi ya yi wanka ta duk yanayin da zai iya, matukar dai ba zai kasance da kunci ko cutarwa gare shi ba, to amma idan har akwai hakan to sai ya yi taimama, to zai yi taimama a wannan halin gabannin fitowar aifijir, kuma azuminsa ya inganta, in kuwa ya bari, fa azumin ya baci, to amma duk da haka wajibi ne ya rike bakinsa har zuwa faduwar rana.

HUKUNCE- HUKUNCEN MATA
Mene ne hukuncin dan ruwa-ruwan da mace ta ke gani bayan tana da yakinin ta samu tsarki, tattare da cewa ba shi da wani siffa na jini ko kuma jinin da ya hadu da ruwa?
Idan har ba jini ba ne to ba shi da hukuncin haila, banbance wannan al'amari kuwa yana hannun macen ne.
Mene ne hukuncin hana yin haila ta hanyar shan magunguna don saboda samun daman yin azumi?
Ba wata matsala ga hakan.
Idan mace ta sami matsalar zuban jini yayin da ta ke da ciki, ko da yake cikin bai zube ba, to shin wanka ya wajaba gare ta ko a a? A takaice dai mene ne ya wajaba gare ta ta aikata?
Jinin da mace ta gan shi yayin da take da ciki idan yana da siffofi ko kuma sharuddan haila, to haila ne, in kuwa ba haka ba to istihala ne, idan har istihala mai yawa (kasira) ne ko kuma matsakaici (mutawassida) ne to wajibi ne ta yi wanka.
Macen da ta ke da takamammen al'ada misali kwana bakwai, to sai daga baya ta fara ganin jini har na tsawon kwanaki goma sha biyu saboda amfani da bututun hana ciki, to shin wannan jini da ya karu akan kwanaki bakwai haila ne ko istihala?
Idan har jini ya wuce kwanaki goma, to dai-dai kwanakin hailanta shi ne haila sauran kuma istihala ne.
Shin macen da ta yi bari ko kuma aka mata aikin zubar da ciki, ta zama mace mai jinin haihuwa ne ko kuma?
Idan har bayan faduwar jaririn-ko da kuwa gudan jini ne- ta ga jini to ana daukan ta a matsayin mai jinin haihuwa ne.

HUKUNCE- HUKUNCEN MAMACI

Shin taba kashin da yake da nama a jikinsa da aka cire ko ya fita daga jikin mutum rayayye, yana wajabta wankan taba jikin mamaci?
Na'am a wannan yanayi da aka ambata yana wajabta wanka.
Yayin cire hakori ya kan fita tare da wani bangare na dasashin mutum, to shin taba wannan dasashin yana wajabta wankan taba mamaci?
A'a ba ya wajabta wankan.
Ni dalibi ne na jami'a a bangaren likitanci, to a wasu lokuta ya kan zama dole mu taba jikin mamata yayin darasi, tare da cewa ba mu san wadannan mamata musulmai ne ko kuma a'a ba? To amma shuwagabannin gurin su kan ce mana an riga an yi wanka wa wadannan mamata, dan haka muke so a mana bayani kan abin da ya wajaba a kan mu dangane da salla da dai sauransu bayan taba wadannan gawawwaki kana bisa ga abin da aka ambata shin wajibi ne sai mun yi wanka?
Idan har asalin yin wanka ga wadannan mamata bai bayyana maka ba kana kuma kana da shakkan faruwar hakan, to wajibi ne ka yi wankan shafan mamaci idan har ka taba su ko wani bangare na jikinsu kana salla ba ta inganta in har ba ka yi wanka ba. To amma idan har ya bayyana maka cewa an yi musu wanka to babu wata matsala idan ka shafi jikin nasu ko kuma wani bangare na jikin ko da kuwa kana shakkan ingancin wankan.
Idan wani mutun ya fara rurrushe makabartan musulmai ba tare da la'akari da abin da shari'a ta shinfida ba, to mene ne abin da ya wajaba kan sauran musulmai dangane da wannan mutum?
Abin da ya wajaba kansu shi ne hana faruwar mummunan aiki amma tare da la'akari da sharudodi da kuma martabobinsa.

NAJASOSI, DA KUMA HUKUNCE-HUKUNCENSU
Shin jini yana da tsarki?
Jinin dabban da jininta yake gudanya yayin yanka shin dan' Adam ko kuma waninsa najasa ne.
Alamar jini da yake saura a jikin tufafin mutum bayan wanke shi, shin najasa ne?
Idan dai har abin da ya saura din ba ainihin jinin ba ne, kana kuma ya ki fita bayan an wanke shi, to ba najasa ba ne.
Mene ne hukuncin gudan jinin da ke cikin kwai?
Ba najasa ba ne amma cin sa ya haramta.
Mene ne hukuncin gumin mai janaba ta hanyar haram da kuma gumin dabban da take cin najasa?
Gumin rakumin da yake cin najasa najasa ne, to amma gumin sauran dabbobin da suke cin najasa in ban da rakumi, haka ma kuma gumin mai janaba ta hanyar haram ba najasa ba ne a bisa magana mai karfi, to amma lhtiyat na wajibi shi ne kada a yi salla tare da gumin janaba ta hanyar haram.
Malamai a cikin littafan fikhu sun nuna cewan kashin dabbobi da kuma tsuntsayen da cin namansu bai halatta ba najasa ne, to shin kashin dabbobin da ake cin namansu, kamar shanu, tumaki da kaji najasa ne ko kuma a'a?
Kashin dabbobin da cin namansu ya halatta ba najasa ba ne.
Idan bako ya najasta daya daga cikin kayayyakin gidan mai masaukinsa, shin wajibi ne ya sanar da mai gidan?
Ba wajibi ba ne ya sanar da shi sai dai in abinci ne ko abin sha ko kuma kwanukan cin abinci.
Shin abin da ya shafi wani abin da ya najastu yana najastuwa? To idan yana najastuwa, shin hakan ya shafi dukkan abubuwan da suka shafe shi ne daya bayan daya ko kuma kawai ya takaita ga na kurkusa ne ?
Abin da ya shafi najasa yana najastuwa haka ma abin da ya shafe shi, kana abin da ya shafi na biyun ma bisa lhtiyat shi ma yana najastuwa, to amma abin da ya shafi na ukun ba ya najastuwa.
Idan mutum ya yi amfani da takalmin da aka yi shi da fatar dabbar da ba'a yanka ta (kamar yadda musulunci ya tsara), ba to shin wajibi ne gare shi da ya wanke kafarsa duk lokacin da zai yi alwala kasantuwar a wasu lokuta kafar tasa ta kan yi gumi?
Idan har ya tabbatar da cewa kafar tasa ta yi gumi a cikin irin wannan takalmi, to wajibi ne ya tsarkake ta.
Mene ne hukuncin tufafin da ake ba da su ga masu wanki dan wankewa kasantuwa sauran wasu mutanen da ba musulmai ba su ma suna kawo wankin kayayyakinsu tattare da cewa su masu wankin suna amfani da wasu magunguna wajen wankin?
Tufafin da ake ba wa masu wanki idan har ba daman can suna da najasa ba ne to masu tsarki ne, haduwar tufafi da tufafin mabiya sauran addinai na daga cikin Ahlul- kitab ba ya najastar da su.
Shin ruwan da ke zuba akan titi ta hanyar motocin diban shara idan ya fantsamu a jikin mutum, shin wannan ruwa ana hukunta shi da abu ne mai tsarki ko kuma mai najasa?
Abu ne mai tsarki sai dai idan mutum ya samu yakini kan cewa ruwan ya najastu ta hanyar haduwa da najasa.
Shin ruwan da ke taruwa a cikin' yan ramukan da suke kan tituna mai tsarki ne ko kuma najasa ne?
Wannan ruwa mai tsarki ne.
Mutum ne ya ke sai da abinci kana kuma yana amfani da hannunsa da ke da jika wajen hakan tattare da cewa ba'a san shi mabiyin wani addini ba ne, to shin wajibi ne a tambaye shi addininsa ko kuma ana iya gudanar masa da hukuncin tsarki (wato ko wani abu mai tsarki ne har sai in najastuwansa ya bayyana)? Tare da cewa shi ba daga garin musulmai ya ke ba.
Tambaya kan addininsa ba wajibi ba ne, ana iya gudanar da hukuncin tsarki gare shi da kuma abin da ya taba da jikinsa da ke da jika .

ABU MAI SA MAYE DA MAKAMANCINSA

A wannan zamani namu ana amfani da alkwan "alcohol" wajen yin da yawa daga magunguna (musamman magungunan da ake sha) da kuma turare, shin ya halatta ga mutumin da ya san hakan ko kuma wanda ma bai sani ba da ya sayar ko ya saya ko kuma ya yi amfani da wadannan abubuwa?
"Alcohol" din da ba'a tabbatar da kasantuwarsa ruwa ba ne tun asali to shi yana da tsarki ko da kuwa yana sa maye, babu wata matsala wajen amfani da shi wajen magani da sauransu, kamar yadda babu laifi wajen salla da tufafin da wannan alkwan "alcohol" ya taba.
Mene ne ake lura da shi wajen najastuwan "alcohol"? Kana wasu hanyoyi ne ake bi wajen tabbatar da abin sha yana sa maye?
Abin da ake lura da shi ya kasance yana sa maye kana kuma ya kasance asalinsa ruwa ne. Sannan hanyar da ake bi ita ce ta hanyar ba da labarin wadanda suka san kan al'amarin idan har shi mukallafi bai da yakini a kan haka.
Mene ne hukuncin shan lemunan kwalban da ake sayarwa a kasuwa (kamar su Coca- Cola, pepsi.....) tattare da akan ce ainihin abubuwa da ake yin su da su daga waje ake shigowa da su, kana kuma akwai yiyuwan cewa sun kunshi "alcohol"?
Masu tsarki ne kuma sun halatta a sha, sai dai idan shi mukallafi yana da yakinin cewa sun kunshi "alcohol" mai sa maye wanda asalinsa ruwa ne.
Yayin sayen kayayyakin abinci (musamman na gwangwani) shin wajibi ne a nemi sanin cewa sun kunshi "alcohol" ko kuma sun taba hannun wanda ya yi su ko kuma ba wajibi ba ne?
Tambaya ko bincike kan hakan ba wajibi ba ne.

WASWASI DA KUMA MAGANINSA

Ni na kasance tsawon shekaru an jarrabe ni da bala'in waswasi, hakika wannan al'amari sai gaba-gaba ya ke yi har ya zamanto ina samun shakku cikin kowani abu ta yadda rayuwata ta kasance cikin shakku, kuma mafi yawan shakkun nawa kan abinci ne da kuma abubuwan da suke da jika a jikinsu, dan haka na kasance ba na iya gudanar da rayuwa kamar sauran mutane. Domin a duk lokacin da zan shiga wani guri sai na cire safa ta don ina tunanin cewa watakila safan tawa ta jike da gumin cikin takalmi ta yadda za su iya najastuwa idan suka taba najasa. Kana kuma ba na iya zama a kan darduma, kai idan har ma na zauna to na dinga juye-juye kenan wai don kada in dauki gashin darduman a jikin rigata ta yadda zai zama dole in wanke ta da ruwa, ko da yake da ba haka nake ba, to amma wannan abu ya dame ni sosai, ta yadda a ko da yaushe na kan so da wata mu'ujiza za ta zo ta tsamo ni daga wannan matsala in koma kamar yadda nake da, dan haka na ke bukatan ka shiryar da ni kan abin da ya dace?
Hukunce- hukuncen tsarki da najasa su ne dai wadannan da aka riga aka yi bayaninsu cikin littattafan fikhu, a sharia kowani abu mai tsarki ne sai dai abin da sharia ta nuna cewa shi najasa ne, kuma najastuwansa ya tabbata ga mutum ta hanyar yakini. Dan haka fita daga waswasi ko shakku ba ya bukatuwa ga wata mu'ujiza, face dai kawai wajibi ne mutum ya ajiye tunace- tunacen radin kansa a gefe ya yi riko ya kuma yi imani da karantarwar shari'ar Musulunci, ya yi aiki da shi kada ya dauki wani abin da bai da yakini kan najastuwansa a matsayin najasa, daga ina kika sami yakinin cewa kofa, garu ko darduma da sauran abubuwan da kike amfani da su najasa ne? Yaya aka yi kika sami yakinin cewa gashin dardumar da kike tafiya akai ko kuma kike zama akai najasa ne ? Har ma kike ganin cewa najasar su zata komo ga safa, ko tufafi ko kuma jikinki ? To ko ma dai yaya ne, ba ya halatta gare ki, ki kula da wannan waswasi naki, dan haka rashin kulawa da wannan waswasi da kuma gwada rashin kulawan lalle zai taimake ki (InshaAllah)wajen kubutar da kanki daga bala'in waswasi.

NAJASAR KAFIRI, TSARKIN AHLUL-KITAB DA HUKUMCIN SAURAN KAFIRAI

Wasu malaman suna ganin cewa su Ahlul kitab ba najasa ba ne, to mene ne fatawarka kan su Ahlul kitab?
Najasar zatin Ahlul - kitab bai bayyana ba, face dai mu muna ganin su masu tsarki ne a zatinsu.
Ni da wasu daga cikin abokaina mun dauki hayar gida, to amma sai na gano cewa daya daga cikinsu ba ya salla, ko da muka bukaci karin bayani daga wajensa, sai ya amsa mana da cewa shi dai ya yi imani da Allah amma dai salla ce kawai ba ya yi, to bisa la'akari da cewa muna cin abinci da kuma sauran mu'amaloli tare, to shin shi najasa ne ko kuma a'a?
Dan barin salla ko azumi da kuma sauran wajiban shari'a ba ya tabbatar da riddan musulmi, ko najasarsa matukar dai ba a tabbatar da cewa ya yi ridda ba to hukuncinsa kamar sauran musulmai ne.
Mene ne ake nufi da Ahlul-Kitab? kana mene ne abin lura wajen iyakance yin mu'amala da su?
Abin da ake nufi da Ahlul- Kitab shi ne duk wani wanda ya riki addini na Allah kana kuma yake ganin kansa daga cikin al'ummar wani Annabi daga cikin Annabawan Allah-tsira da amincin Allah ya tabbata ga Annabinmu da mutanen gidansa da kuma gare su-kana kuma ya kasance suna da wani littafi daga cikin littattafan sama wanda aka saukar wa Annabawa (a.s), kamar Yahudawa, nasara, zorostawa da kuma sabi'awa domin kuwa duk wadannan-kamar yadda muka yi tahkiki- suna daga cikin Ahlul-kitabi don haka hukuncin wadannan hukuncin Ahlul kitab ne, mu'amala da su tare da kulawa da tsari- da kuma dabi'u na musulunci babu matsala a cikinsa.
Akwai wata kungiya da take ganin Amirul muminin Aliyu bn Abi Talib (a.s) Ubangiji ne kana sun yi imani da karanta addu'oi maimakon yin salla, da azumi to shin wadannan najasa ne?
Idan har sun yi imani da cewa Amirul muminin(a.s) (ubangiji ne), Allah ya tsare mu da haka, to hukuncinsu kamar hukuncin sauran wadanda ba musulmai ba ne amma banda Ahlul-kitab.
Shin ya halatta ga' yan shia isna Ashariyya su bayar da abubuwan da aka yi bakance ga lmam Hussain (a.s) ko kuma ga sauran Ahlul, Baiti(a.s) su bayar da su zuwa ga wasu cibiyoyin mutanen da suke ganin lmam Aliyu (a.s) a matsayin ubangiji wanda hakan zai iya zama taimako ne wajen raya wadannan cibiyoyi ?
Imani da Allantakan shugaban masu tauhidi Aliyu bn Abi Talib (A.s) batacciyar akida ce, da take fitar da duk wani ma'abucinta daga musulunci, hakika taimakawa wajen yada wannan batacciyar akida haramun ne, kana kuma sarrafa dukiyar bakance ba ya halatta ga abin da ba dan shi a ka yi bakance ba.
Mafi yawan mutanen garinmu kafirai ne, lokacin da wani kamar dalibin jami'a ya kama hayan gida a gurin, to yaya zai yi da najasar da ke gidan ? shin dole ne ya wanke ya kuma tsarkake gidan ko kuma a'a? Yana da kyau a sani cewa yawancin gidajen da katako aka yi su inda wanke su ba zai yiwu ba, kana mene ne hukuncin kujeru da sauran kayayyakin gidan ko kuma guraren saukan baki a garin?
Matukar dai ba'a tabbatar da shafuwan jikaken hannu ko jikin kafiri wanda ba Ahlul-kitabi ba, ba za'a hukunta shi da najastuwa ba, to ko da ma an tabbatar da najasar ba wajibi ba ne a tsarkake kofofi da kuma garun gidan, haka ma kujeru da sauran kayayyakin gidan, da wurin saukan baki face dai abin da yake wajibi shi ne tsarkake abubuwan da suka najastu na daga abubuwan da ake amfani da su wajen ci da sha da kuma salla.
Mene ne hukuncin aiki a gurin yahudawa da sauran kungiyoyin kafirai, da kuma karban albashi a wajensu?
Shi kansa aikin babu matsala tare da shi matukar dai aikin ba yana cikin al'amurran da suka haramta ba ne ko kuma suka saba wa maslahohin musulunci da musulmai na gaba daya ba.
Mene ne hukuncin kujerun motoci da jiragen kasa wanda musulmai da kafirai suke amfani da shi dukkansu tattare da cewa a wasu wuraren kafiran sun fi musulman yawa, shin za'a yi musu hukunci da tsarki ne, tattare da cewa zafin da ke gurin ya kan sa yin gumi da kuma zubansa?
Idan dai har ba'a tabbatar da najasar ba, to ana musu hukunci da tsarki ne.
Mutumin da ya yi inkarin wasu bayyanannun lamurra na addini kamar salla, azumi da dai sauransu, shin hukuncin kafiri ya hau kansa ne ko kuma a'a?"
Idan har inkarin nasa ya jawo inkarin sakon Manzon Allah (Sawa) ko kuma karyata shi Manzon Muhammad ko kuma ya jawo rashin daraja ga shari'a, to ya kafirta ya kuma bar musulunci.

BABIN SALLA:
MUHIMMANCI DA KUMA SHARUDDAN SALLA

Mene ne hukuncin mai barin salla da gangan ko kuma wasa da ita?
Sallolin nan na wajibi guda biyar suna daga cikin muhimman wajibai a shariar musulunci kai su ne ma ginshikin addini, don haka barinsu ko kuma wasa da su haramun ne wanda ke sa mutum ya cancanci azaba.
Shin salla tana wajaba ga wanda ya rasa abubuwan tsarkin nan guda biyu (ruwa da kasa)?
A bisa lhtiyat zai yi salla cikin lokaci, to amma daga baya ya rama ta tare da alwala ko kuma taimama.
A bisa fatawarka, a wasu halaye ne ya halatta a yi "udul" a cikin salla da ta zan wajiba (wato canza niyyar salla daga sallar da kake cikinta zuwa ga wata sallar)?
Yin "udul" yana wajaba a wasu halaye Daga cikinsu akwai: Yin sa daga sallar la'asar zuwa Azahar idan har mutum ya tuna cewa bai yi sallar azahar ba. Kana kuma: Daga sallar isha zuwa magariba idan har ya tuna yayinta kana kuma kafin ya wuce wajen yin "udul" din sai ya tuna cewa bai yi sallar magariba ba. Kana da kuma : Idan yana da ramakon salloli guda biyu wadanda suke a jere sai ya manta har ya fara da ta biyun kafin ta farkon.
Sannan mustahabi ne yin "udul" a wasu wurare Daga cikinsu akwai : Yin uduli daga sallar da ake yin ta cikin lokacinta zuwa ga ramako na wajibi, hakan kuwa mustahabbi ne idan har lokacin falalar ita wannan salla da ake lokacinta ba zai tsere ba.
Kana kuma yin uduli daga salla wajiba zuwa ga ta mustahabi domin samun daman yin ta (wato wajibar) tare da liman.
Sannan kuma akwai: Yin uduli daga sallar farilla zuwa ga nafila yayin sallar azahar din ranar juma'a ga wanda ya mance karanta suratul juma'ati, ya karanta wata sura ta daban har ya kai tsakiyarta ko ma ya wuce hakan, to mustahabi ne ya canza wannan farilla zuwa ga nafila dan ya sake sallar farillar da suratul juma'ati.
Idan har jini ya ci gaba da zubowa daga hanci ko bakin mutum tun daga farkon lokacin salla har kusa da karshen lokacinta, to mene ne hukuncin salla anan?
Idan har ba zai iya tsarkake jikinsa ba kana kuma yana tsoron fitar lokacin sallar to sai ya yi salla a cikin wannan halin.
Yayin zikirorin mustahabi na cikin sallolin farilla, shin daidaita jiki da kuma rashin motsa shi wajibi ne?
Al'amarin daidaita jiki da kuma nitsuwa yayin salla ba shi da wani bambanci shin cikin zikirori na wajibi ne ko kuma na mustahabi.
A wasu lokuta akan sa wa maras lafiya wata roba don fitan fitsari saboda rashin lafiyar da yake damunsa, a irin wannan hali fitsari zai dinga fito masa ko ba da sonsa ba, ko yana barci ko idonsa biyu, ko da kuwa yana salla ne, to a irin wannan hali shin wajibi ne ya sake salla ko kuma wannan sallar da ya yi ta wadatar?
Idan har yayi salla a cikin irin wannan hali dai-dai da yadda sharia ta wajabta masa, to sallarsa ta yi, ba wajibi ba ne ya sake ko kuma ya rama ta ba.

LOKUTAN SALLA
Bisa la'akari da cewa karshen lokacin sallar la'asar shi ne gurub, kana kuma karshen lokacin sallar azahar shi ne kafin magriba da gwargwadon lokacin da sallar la'asar ta ke bukata, to tambaya a nan ita ce: Mene ne ake nufi da gurub ko magariba, shin shi ne faduwar rana ko kuma yayin da ake kiran sallar magriba (gwargwadon yanayin gurin da mutum yake)?
Karshen lokacin sallar la'a sar shi ne faduwar rana.
Mene ne gwargwadon abin da idan mutum ya aikata za'a iya cewa ya riski salla a cikin lokacinta? Kana niyyarsa ta yin ta a cikin lokacinta ta inganta Kana kuma mene ne hukunci yayin da mutum ya ke shakkan shin wannan gwargwadon zai iya yin sa a cikin lokaci ko kuma?
Gwargwadon ra'aka guda cikin karshen lokaci yana wadatarwa a ce an yi salla a cikin lokaci, to amma idan kana kokwanto cewa lokacin da ya saura zai ishe ka yin raka'a guda a cikin lokaci ko a a, to a nan sai kawai ka yi niyyar saukar da abin da ke kanka ba tare da ka yi niyyar yin ta a cikin lokaci ko kuma ramako ba.
Shin mene ne fatawarka kan lamarin alfijir din gaskiya da kuma na karya? Kana kuma mene ne ya wajaba kan mai salla dangane da wannan al'amari?
Abin lura dangane da lokacin salla ko kuma azumi shi ne alfijir din gaskiya, gano hakan kuma yana wuyan mutum ne.
Shin wajibi ne raba sallar azahar da La'asar wato a yi sallar azahar bayan shigan lokacinta kana kuma sallar la asar bayan shigan lokacinta sannan kuma magriba da isha ma haka?
Bayan shigan lokaci mutum yana da zabi ko ya hada su ko kuma ya rarraba su.
Ahlus- Sunna su kan yi sallar magriba gabannin ainihin faduwar rana wanda shari'a ta tanadar, to shin yana halatta a gare mu lokacin aikin hajji da kuma sauran lokuta mu bi su salla ba tare da mun sake ta ba?
Ba tabbataccen al'amari ba ne cewa suna yin salla gabannin lokaci, kana bin su salla ba wata matsala a cikinsa kuma ya wadatar, to amma dai shigan lokaci al'amari ne da ba makawa sai da shi, sai dai in shi ma lokaci wuri ne na yin takiyya.
Shin abin lura dangane da karshen lokacin sallar asuba shi ne fitowar rana ko kuma fitan haskenta zuwa ga duniya?
Abin lura shi ne fitowar rana da kuma ganin ta a gurin da mutum yake.
A wasu lokuta kafafen watsa labarai sukan sanar da lokutan salla na kowace rana tun daga ranar da ta gabace ta, to shin ya halatta a dogara ga hakan da kuma irin kiran sallar da ake sa wa a gidajen Rediyo da talebijin wajen shigan lokaci?
Abin lura kawai anan shi ne mutum ya sami nitsuwar kan cewa lokaci ya shiga.
Shin mutum yana iya fara salla daga lokacin da aka fara kiran salla, ko kuma wajibi ne sai ya jira an kare? Kana kuma shin yana halatta ga mai azumi da ya bude bakinsa daga lokacin da aka fara kiran salla ko kuma wajibi ne har sai an gama?
Idan har yana da nitsuwa kan cewa an fara kiran salla ne yayin da lokaci ya shiga, to ba wajibi ba ne ya jira har sai an gama.
Shin sallar wanda ya gabatar da salla ta biyu a kan ta farko, kamar gabatar da sallar isha a kan magriba, tana inganta?
Idan har ya gabatar da ita din ne a bisa kuskure ko kuma gafala har ya kai karshenta, to ta inganta, to amma idan da gangan ne to ta baci.

HUKUNCE- HUKUNCEN AL- KIBLA

Me ya wajaba mu aikata yayin da muka gagara gano Alkibla kana kuma ba mu da wani na'uran da za mu iya gano ta? Tattare da cewa muna zaton kasantuwar kibla a duk bangarorin nan guda hudu?
Idan har zato ya zama guda tsakanin bangarorin nan guda hudu, to wajibi ne a yi salla a duk bangarorin guda hudu domin a samu yakinin an yi salla a bangaren alkibla.

HUKUNCE- HUKUNCEN WURIN MAI SALLA

Shin zama ko yin salla ko kuma wucewa ya halatta a wuraren da hukuma azzaluma ta kwace daga wajen masu shi ba tare da yardansu ba?
Idan har mutum yana da masaniya kan kwacen to hukuncinsa yana daidai da hukuncin kwace ba ya halatta a yi amfani da shi wajen salla da sauransu.
Ni na kasance ina limancin salla a wasu makarantu, alhali kuma wasu bangare na wadannan makarantu an kwace su ne daga masu shi ba tare da yardansu ba, to shin mene ne hukuncin sallata kuma Sallar sauran daliban a irin wadannan makarantu.
Idan har kwace wadannan filaye daga wajen masu shi bai tabbata ba, to babu wata matsala ga sallar taku.
Mutum ne yake zaune a gidan gwamnati, to sai aka umurce shi da ya bar gurin bayan cikan kwanakin da aka yarda masa ya zauna, to mene ne hukuncin salla da kuma azuminsa a wannan gidan bayan wannan lokaci ?
Idan har ba an yarda masa ya ci gaba da zama a gidan ba ne bayan cikan kwanakin, to amfanin da zai yi da gidan yana matsayin kwace ne.
Idan da mutum zai yi salla a gurin kwace to amma akan darduma ko tabarma da makamancinsu to shin sallarsa ta inganta ko kuma?
Salla a wajen kwace ba ta inganta ko da kuwa a kan darduma ce ko tabarma da aka shimfida a wajen.
Shin salla a gurin da aka sanya haramtacciyar kida ta inganta ko kuma?
Yin salla a wannan wuri idan ya jawo sauraron kida na haram to bai halatta a zauna a gurin ba, sai dai kuma sallarsa ta inganta, idan kuma kidan zai hana mutum samun fadaka da mai da hankali, to yin salla a gurin makaruhi ne.

HUKUNCE- HUKUNCEN MASALLACI

Shin salla a masallacin da kafirai ne maginansa yana halatta?
Ba wata matsala ga sallar da aka yi a cikin irin wannan masallaci.
Shin ana iya karban taimakon da kafiri ya bayar wajen gina, masallaci?
Ba wata matsala ga hakan.
Idan mutum ya yi mafarki a cikin masallaci cikin dare, to idan ba zai iya fita daga masallacin ba yayin da ya farka, to mene ne zai yi?
Idan har ba zai iya fita daga masallacin zuwa wani guri ba, to wajibi ne ya gaggauta yin taimama don ya halatta masa zama a cikin masallacin.

TUFAFIN MAI SALLA

Idan har ina shakkan najastuwan tufafina, shin sallata tana inganta idan na yi salla da su?
Duk tufafin da ake da shakka kan najastuwarsu to ana daukarsu masu tsarki ne kana kuma salla da su tana inganta.
Idan har mai salla yana da tabbacin rashin najasa a jikinsa ko tufafinsa, sai ya yi salla, to bayan hakan sai ta bayyana masa cewa jikinsa ko tufafinsa suna da najasa, shin sallarsa ta baci ko kuma? Kana kuma da ace zai gano hakan a tsakiyar sallar tasa, yaya zai yi?
Idan har bai san da kasantuwar najasar ba sai bayan da ya idar da sallar, to sallarsa ta inganta ba wajibi ba ne ya sake sallar ko kuma ya rama to amma idan ya gano hakan yayin da yake cikin salla, idan har zai iya kawar da najasar ba tare da ya aikata abin da zai kore masa salla ba, to wajibi ne ya yi hakan kana ya cika sallarsa, idan kuwa ba zai iya kawar da najasar tare da kiyaye yanayin sallar ba, kuma ya zan akwai yalwataccen lokaci to a nan wajibi ne ya yanke sallar, kana ya sake ta bayan ya gusar da najasar.
Mace ce ta ga gashinta ya fito fili yayin da take salla, sai ta yi maza- maza ta rufe shi, shin wajibi ne ta sake sallar?
A wannan yanayi ba wajibi ba ne ta sake sallar.
Da ace mutum zai rike hankici mai najasa ko kuma ya sanya shi a cikin aljihunsa yayin da yake salla, shin sallarsa tana inganta?
Idan har hankicin karami ne ta yadda ba za, a iya rufe al'aura da shi ba, to babu wata matsala.
Shin salla da tufafin da aka sanya masa turaren da akwai alkohol a cikinsa tana inganta?
Ba laifi a yi salla da shi idan har najasar wannan turare bai tabbata masa ba.
Shin ina ne ya zama wajibi ga mace ta rufe shi yayin salla, shin akwai matsala a sanya guntayen tufafi da kuma rashin sanya safa?
Abin da ake lura da shi shi ne kasantuwan tufafin ya rufe dukkan jiki banda fuska (wanda ake wankewa yayin alwala), kana ban da tafukan hannu kuma ban da kafafe zuwa idon kafa.
Shin kasantuwan gashi ko kuma yawun kyanwa a jikin tufan masallaci yana bata salla?
Na'am yana bata salla.
KARATU DA HUKUNCE- HUKUNCENSA

Shin mutum yana iya karatun salla a cikin zuciyarsa ba tare da fitar da lafuza ba?
Hakan ba ya wadatarwa dole ne a fitar da lafuzan.
Kamar yadda wasu malamai suka bayyana cewa wasu daga cikin surorin Alkur'ani kamar suratul Fil da kuraish, da kuma suratul lnshirah da suratu Duha sura guda, wato idan mutum ya karanta misali suratul Fil to wajibi ne ya zo da suratu Kuraish, ko kuma idan ya karanta suratu Duha to wajibi ne ya zo da Alam Nashraha, to da ace mutum zai karanta suratul Fil ita kadai, ko kuma Alam Nashraha ita kadai, tare da rashin sanin hukuncin, to mene ne hukuncinsa?
Idan har ya jahilci hukuncin ne to sallarsa ta inganta.
Idan mutun ya mance yayin da yake salla misali a raka'a ta uku ta sallar azahar ya karanta fatiha da sura, kana bai gano hakan ba sai bayan ya idar da sallarsa, to shin wajibi ne ya sake ta? kana kuma idan ma bai gano hakan ba, gaba daya shin sallarsa ta inganta?
A irin wannan yanayi sallarsa ta inganta.
Shin wajibi ne a salla a karanta sura cikakkiya bayan Fatiha, ko kuma wani sashi na surar ya wadatar? A yanayi na farko shin yana halatta bayan karanta sura cikakkiya mutum ya sake karanta wasu ayoyi na Alkur'ani?
A sallolin farilla karanta wasu ayoyin na Alkur'ani maimakon sura cikakkiya ba ya wadatarwa, to amma karanta wasu ayoyin na Alkur'ani da nufin Alkur'ani bayan sura cikakkiya babu wata matsala ga hakan.

HUKUNCE- HUKUNCEN SUJADA
Mene ne hukuncin sujada ko taimama a kan siminti?
Babu wata matsala ga hakan.
Yayin zaman da ake bayan sujada ta biyu wace kafa ce ake dora ta kan yar uwarta?
: Mustahabi ne a sanya zahirin kafar dama a kan tafin kafar hagu.
Mene ne ya wajaba mutum ya aikata yayin da ya ji an karanto ayoyin da ake musu sujada a cikin rediyo ko kuma ta hanyar rakoda?
Sauraren ayoyin sujada ta hanyar kaset ba ya wajabta sujada, to amma yayin da mutum ya saurare su ta hanyar rediyo ko kuma ta hanyar "lasafika" daga mai karatun kai tsaye, to wajibi ne, bisa ihtiyat, ya yi sujada.

AMSA SALLAMA

Shin amsa sallamar kananan yara wajibi ne?
Wajibi ne amsa sallamar kananan yara masu iya rarrabewa kamar yadda ya wajaba a amsa sallamar manyan mutane.
Mene ne fatawarka kan amsa gaisuwar da ba da sigar sallama aka yi ta ba?
Idan a salla ne ba ya halatta a amsa ta, to amma idan ba, a salla ba ne, to lhtiyati shi ne a amsa ta idan har furta ta a ka yi kuma mutane suna kirga ta a matsayin gaisuwa.
Da wani mutum zai yi sallama sama da daya a lokaci guda, ko kuma mutane da yawa suka yi sallama, to shin amsa sallama guda yana wadatarwa ga gaba dayansu?
Dangane da tambaya ta farko, amsa guda daya ya wadatar, a ta biyu kuma amsa guda da sigar da za ta game dukkansu, da nufin amsa sallamarsu, ya wadatar.

ABUBUWAN DA SUKE BATA SALLA

Idan mutum ya ga wani karamin yaro zai aikata wani abin da zai cutar da shi yaron alhali kuwa yana cikin salla, to shin ya halatta ya daga muryarsa yayin karatu ko zikiri dan tunasar da yaron, ko kuma dan jawo hankalin wani da yake cikin gidan dan kawar da wannan abu? Kana kuma mene ne hukuncin yin ishara da hannu ko kuma gira don jawo hankalin wani mutum daban kan wani al'amari, ko kuma dan amsa wata tambayar da aka masa?
Idan har wannan daga sauti yayin karatu ko zikiri dan jawo hankalin wani ba zai iya canza tsarin sallar ba, to babu wata matsala, amma da sharadin cewa ya yi hakan ne da niyyar yin karatun ko kuma zikirin, Na' am magana yayin salla, ko kuma motsin da zai haifar da rashin nitsuwa, ko kuma ya kawar da yanayin salla to hakan yana bata salla.
Idan mutum ya yi dariya yayin salla dan tunawa da wani abin dariya, ko kuma don faruwar wani abin dariya, shin haka yana bata salla ko kuma?
Idan har dariyar tana da sauti- wato kyalkyalawa- to salla ta baci.
Shin rufe ido yayin salla yana halatta domin a wasu lokuta barin idon a bude kan iya kawar da hankalin mutum daga sallar?
Babu matsala ga hakan, kuma ba ya bata salla.

SHAKKA YAYIN SALLA DA KUMA HUKUNCINSA

Ana cewa mai yawan shakka kada ya damu da shakkan nasa, to amma me zai yi yayin da shakkar ta zo masa yayin salla?
Abin da zai yi shi ne ya dauka cewa ya riga ya aikata aikin da yake shakkun a kansa, sai dai idan hakan ya zan a wurin da zai haifar da bacin salla, to a wannan hali sai ya dauka cewa bai aikata shi ba, wannan shi ne zai aikata shin cikin aiyukan salla ne ko maganganu, ko kuma raka oi.
Idan mutum ya gane cewa lbadunsa na shekaru ba daidai ya yi su ba, ko kuma ya yi shakkan hakan, to mene ne zai yi?
Ba'a lura da duk wata shakkar da aka yi ta bayan aiki, idan kuma har yana da yakinin bacin ayyukan nasa, to wajibi ne ya rama abin da za a iya riskarsa.
Da mutum zai mance wata raka;a kana sai a raka'ar karshe ya tuna misali, kamar idan ya zaci cewa raka'ar farko ta sallarsa a matsayin raka'a ta biyu sai ya zo da ta uku da ta hudu, to amma a raka' a ta karshe (wato ta hudun) sai ya fahinci ita ce ta uku, to me zai yi?
Wajibi ne gabannin sallama ya zo da raka'a guda da ya mance kana sai ya yi sallama bayan haka, to a irin wannan yanayin da zai zo da kari a bisa rabkanuwa, ko kuma ya bar wasu wajibai wadanda ba rukuni ba ne, to wajibi ne ya zo da sujadar rabkanuwa, da kuma zai bar tahiyar wajibi to wajibi ne a bisa lhtiyati ya rama ta.

SALLAR RAMAKO

Da mutum zai yi wankan janaba sau uku a cikin watan Ramalana misali a ranar ashirin da ranar ashirin da biyar da kuma ranar ashirin da bakwai to bayan hakan sai ta bayyana masa cewa daya daga cikin wadannan wanka ba daidai ya yi shi ba, to mene ne ya wajaba a kansa dangane da salla da azumi?
Azuminsa dai ya inganta, amma wajibi ne ya sake salla ta yadda zai sami yakini kan cewa ya sauke abin da ya rataya a wuyansa.
Mene ne hukuncin ayyukan ibadu misali salla da azumi na mutumin da cikin jahilci ya kasance ba ya kula da jerantawa a cikin wankan janaba?
Idan har wannan rashin jerantawa ya kasance ne ta yadda har zai bata wankan, kamar a ce ya gabatar da wanke bangaren dama a kan wanke kai da wuya, ko kuma ya gabatar da wanke bangaren hagu a kan na dama, to dole ne ya rama sallolin da ya sallace su da janaba, to amma azuminsa ya inganta matukar dai a waccan Lokacin yana ganin wankan nasa ingantacciya ce.
Mutum da yake so ya rama salloli na shekara guda, ta yaya ne ya wajaba ya rama su?
Zai iya farawa da daya daga cikin sallolin kuma ya yi ta kamar yadda yake yin salloli na farilla guda biyar.

RAMAKON SALLAR BABBAN DA GA MAHAIFINSA DA MAHAIFIYARSA

Idan mutum ya rasu rama azumin kaffaran da ya bari yana kan wane ne?
Shin wajibi ne a kan 'ya'yansa maza da mata su yi masa, ko kuwa yana yiwuwa wani mutum daban ya yi masa?
Kaffaran azumi da ke kan mahaifi idan har 'yar zabi ce wato ko ya yi azumi ko ya ciyar, kuma yana da halin yin biyun duka to idan zai yiwu a cire ta daga cikin abin da ya bari na gadonsa sai a cire, in kuwa ba zai yiwu ba, to a bisa lhtiyati yin azumin yana kan babban da ne.
Idan babban dan mutum mace ce, na biyun ne namiji, to shin ramakon salla da azumin mahaifiya da mahaifinsa suna kansa ne a wannan hali ma?
Abin lura a cikin wannan al'amari shi ne babban da namiji daga cikin 'ya'yaye mazaje idan har mahaifinsa yana da'ya'ya maza, to dangane da wannan tambaya, ramakon salla da azumin mahaifi haka ma mahaifiya yana kan wannan da na biyu ne.
Idan babban da ya rasu kafin rasuwar mahaifinsa, to shin ramakon sallar mahaifi ya fadi daga kan sauran 'ya'yan kenan?
Wajibcin ramakon salla da azumin mahaifa yana wajaba ne kan babban dan da ya kasance a raye yayin rasuwar mahaifan ko da kuwa ba shi ne dan farko ga mamacin ba.
Mahaifin da ya bar dukkan ayyukansa na ibada da gangan, to shin wajibi ne ga babban dansa da ya rama masa dukkan wadannan ayyukan wadanda sun kai ayyukan shekaru hamsin (50)?
Ba abu ne mai nisa ba ace ba wajibi ba ne ga babban da rama ayyukan da mahaifinsa ya bari don shishshigi, ko da yake yana da kyau dai ya rama masa bisa ihtiyat.

SALLAR JAM'I

Yayin sallar jam'i lokacin da liman yake cikin raka'a ta uku ko ta hudu a sallar isha, shi kuwa mamu yana raka'a ta biyu ce, to shin wajibi ne ya yi karatun (Fatiha da sura) a bayyane?
A'a wajibi ne ya karanta su a boye.
Mutumin da ya bi limamin da yake cikin raka'a ta uku alhali shi kuma yana tsammanin raka'ar farko ce, dan haka sai bai yi karatu ba, to shin wajibi ne ya sake sallar?
Idan har ya fahinci hakan kafin ya tafi zuwa ga ruku'u to wajibi ne ya zo da wannan karatu, in kuwa bayan ruku'u ne, to sallarsa ta inganta kuma babu abin da zai yi, ko da yake ihtiyati na mustahabi shi ne ya yi sujadar rabkanuwa saboda barin karatu.

BIN AHLUS SUNNA SALLA

Shin bin Ahlus sunna salla ya halatta?
Na'am, salla a bayansu ta halatta.
Yayin da muke cikin Ahlus sunna mu kan yi salla tare da su kamar yadda suke yi misali yin kama kirji(kabalu)da kuma yin sujada a kan darduman salla da dai sauransu to shin sallar ta inganta ko kuma sai mun sake?
Idan har hakan yana jawo kare hadin kan musulmai to salla tare da su ta inganta kana ta wadatar ko da kuwa da yin sujada akan darduma da dai makamantansu, to amma yin kabalu a salla tare da su bai halatta ba sai dai idan a bisa lalura ne.
Yayin da muke salla da Ahlus sunna to shin mene ne hukuncin harhada gefen kafafu da suke yi yayin da suke tsaye?
To hakan dai ba wajibi ba ne, to amma idan mutum ya yi haka sallarsa ba ta baci ba.

SALLAR JUMA'A

Mene ne fatawarka kan sallar juma'a? Ga shi kuma muna zamanin "gaibar" lmam Mahdi ne, kana kuma idan mutum bai yarda da adalcin limamin juma'a ba, to shin wajibcin halartan sallar tana faduwa akansa ko kuma a'a?
Ko da yake Sallar juma'a a wannan lokaci namu wajiba ce'yar zabi, (wato tsakaninta da sallar azahar) halartarta ba wajibi ba ne, to amma saboda la'akari da falalolin da ke cikinta, to bai kamata ga muminai su haramta wa kansu albarkar da ke cikinta ba dan kawai saboda shakkar adalcin liman, ko kuma saboda irin wadannan dalilai da ba su da wani muhimmanci.
Mene ne ma'anar wajibi yar zabi a mas'alar sallar juma'a?
Ma'anarsa shi ne mutum yana da zabi imma dai ya yi sallar juma'a ko kuma sallar azahar.
Mene ne fatawarka kan mutumin da ke barin sallar juma'a saboda rashin daukanta da muhimmanci?
Barin sallar juma'a saboda rashin daukanta da muhimmanci abin zargi ne a shari'a.
Idan mutum yana ganin limamin juma'a ba adali ba ne, ko kuma yana shakkan adalcinsa, to shin ya halatta ya bi shi don kiyaye hadin kan musulmai? Kana shin yana halatta ga wanda ba ya halartar sallar juma'a da ya yi kokarin hana sauran mutane halarta?
Ba ya inganta gare shi da ya bi mutumin da ba ya ganinsa adali, ko kuma yake shakkar adalcinsa, kuma sallar da ya yi a bayansa ba ta inganta, to amma babu laifi ya yi hakan dan kiyaye hadin kan musulmai, to amma a kowace hali dai bai da damar da zai kwadaitar da wasu a kan barin halartan sallar ko kuma ya karfafa su kan hakan.
To yayin da mutum yake shakkar ko kuma ma yake da yakinin rashin adalcin limamin juma'a, kana ya riga ya yi sallolin juma'a a bayansa, to shin dole sai ya sake su?
Idan har shakkar kan adalcinsa ko kuma yakinin rashin adalcin bayan idar da sallolin ne, to sallolin nasa sun inganta, kuma ba wajibi ba ne ya sake su.
Mutumin da bai samu daman halartar sallar juma'a ba, shin zai iya yin sallar azahar da la'asar dinsa tun farkon shigan lokaci? ko kuma wajibi ne ya jira sai an idar da sallar juma'a kafin ya yi su?
Ba wajibi ne ya jira sai an idar da sallar juma'a ba ya halatta ya yi sallolinsa na azahar da la'asar tun farkon lokaci.

SALLAR IDI

A fatawarka sallar idi da kuma juma'a daga cikin wani nau'i na wajibi suke?
A wannan zamani da muke ciki sallar idi ba wajibi ba ne, mustahabi ne, to amma sallar juma'a wajiba ce 'yar zabi (tsakaninta da sallar azahar).
Shin kari ko kuma ragi cikin kunutin sallar idi suna bata sallar?
A'a hakan ba ya bata sallar.
Shin ana wa sallar idi ikama?
A'a ba ta da ikama.

SALLAR MATAFIYI

Mene ne sharuddan wajibcin yin kasaru ga matafiyi a salloli masu raka'oi hudu?
Sharudda guda takwas ne:
(1). Dole ne tafiyar ta zamanto ta kai" farsaki" takwas (kimanin kilomita 45 ko mil 24) tafiya, ko kuma dawowa, ko kuma tafiya da dawowa da sharadin kada tafiyan ya gaza farsaki hudu.
(2). Niyyar isa ga wannan haddi tun yayin fita zuwa tafiyar, idan mutum bai yi wannan niyya ba, ko kuma ya yi niyyar kasa da haka to bayan isarsa inda ya yi niyya, sai ya sake yin niyyar isa ga wani guri na daban ta yadda daga wajen zuwa inda zai je na biyu din bai kai gwargwadon da shari a ta yarda da shi ba wajen kasaru, sai dai kuma da zai hada dukkan tafiyar guda biyu za su kai hakan, to a wannan hali ba zai yi kasaru ba saboda rashin niyyar isa haddin kasaru tun daga farko.
(3). Dawwamar wannan niyya har ya kai wannan haddin, da zai sake niyya kafin isa ga haddin farsakhi hudu, ko kuma ya fara kokwanto, to daga nan hukuncin kasaru ya fadi a kansa ko da yake kasaru da ya yi kafin nan ba laifi.
(4) Kada ya yi niyyar yanke wannan tafiya tasa ta hanyar wucewa ta garinsu ko kuma niyyar zama a guri na kwanaki goma, ko kuma fiye da haka.
(5) Tafiyar ta kasance ta halas ce, idan tafiyar ta kasance don sakon Allah ce ko kuma ta haram ce, shin ita tafiyar ce ta haramun kamar gudu daga filin yaki, ko kuma manufarta ce ta haramun kamar yin tafiya don yin sata, to a irin wannan hali mutum ba zai yi kasaru ba.
(6) Kada matafiyin ya kasance daga cikin irin mutanen da suke tafiya tare da gidajensu ne kamar fulanin da ba su da takamammen muhalli, suna yawo ne duk inda suka sami ruwa da ciyawa sai su zauna a gurin.
(7) Kada tafiya ta kasance aikin mutum kamar direbobi da matuka jirgin ruwa da dai sauransu, haka kuma ya hada har da wanda aikinsa ya ta'allaka ne da yin tafiya wato aikinsa a tattare ne cikin tafiye-tafiye.
(8) Isa ga "haddin Tarakkhus" wato wurin da ba zai ji kiran sallar garinsu ba ko kuma ba zai ga ganuwar garinsu ba.

WANDA TAFIYA TA KASANCE AIKINSA KO KUMA TA KASANCE MATAKIN FARKO NA AIKINSA

Mutumin da tafiya ta kasance matakin farko na aikinsa, shin shi ma zai cika sallarsa ne, ko kuma hakan ya kebantu ne ga mutumin da tafiya ta zama aikinsa ne kawai? Kana mene ne maraja'ai kamar lmam khumaini (r.a) suke nufi yayin da suke cewa! "Mutumin da tafiya ta kasance aikinsa", shin akwai mutumin da tafiya take kasancewa aikinsa? Domin kuwa hatta makiyayi, ko kuma direbobi da dai sauransn aikinsu shi ne kiwo, ko kuma tuki, ba wai tafiya ba dan haka babu wani mutumin da tafiya ita ce aikinsa?
Duk mutumin da tafiya ta kasance matakin farko na aikinsa idan har a duk kwana goma zai yi tafiya sau guda zuwa wajen aikin nasa dan yin aikin to zai cika salla kuma azuminsa ya inganta. Kana kuma ma'anar mutumin da tafiya ta kasance aikinsa-cikin maganganun malaman fikhu-shi ne duk mutumin da aikinsa bai yiwuwa sai da tafiya-tafiye kamar irin aiyuka da aka ambata a cikin wannan tambaya.
Ni na kasance ma'aikaci ne a wani gari kana kuma daga gidan da nake zaune zuwa wajen aiki kimanin kilomita 35 ne, haka kullum na ke wannan tafiya kafin in isa ga wajen aikin nawa, to yaya sallata za ta kasance lokacin da nake da wani abu na musamman (wanda ba ya daga cikin aikin nawa) a wannan gari kana kuma zan zauna a wannan gari na wasu raneku. To shin zan cika salla ne ko kuma kasaru zan yi?
Idan har tafiyar ba saboda wannan aiki naka ba ne wanda kullum kake tafiya saboda shi, to hukuncin matafiyin da tafiya ita ce aikinsa ba ta hau kanka ba, to amma idan har tafiyar saboda wannan aiki naka ne, to amma yayin da kake wannan gari za ka yi wani abu na daban kamar ziyarar dangi, ta yadda har ma wani lokaci za ka kwana ko ma kwanaki, to wannan hukunci dai na matafiyin da tafiya ita ce aikinsa yana nan a kanka, wato za ka cika salla kana za ka yi azumi.

"HADDUT TARAKKHUS"

"Haddut tarakkhus: Shi ne daga inda mutum ya daina jin kiran sallar garin da ya fito kana kuma buyan ganuwar garin, to shin wajibi ne sai wadannan abubuwa biyu sun kasance ko kuma guda ma daga cikinsu yana wadatarwa?
Ihtiyati shi ne lura da dukkansu, ko da yake rashin jin kiran salla ma yana wadatarwa.
Shin abin lura wajen gane "haddut tarakkhus" shin jin kiran sallar gidajen farko da suke farkon gari ne ko kuma masallatan tsakiyan gari?
Ma' aunin dai shi ne kiran sallar gidajen karshe na garin daga ta wajen da matafiyi zai bar garin ko kuma zai shigo.
An sami sab?ani tsakanin wasu jama' a: Wasu suna cewa abin lura dangane da "haddut tarakkhus" shi ne gidajen karshe na garin, wasu kuma suna cewa a'a abin lura shi ne kamfamoni da masana'antu da suke bayan garin, to tambaya a nan ita ce, yaya ake gane karshen gari?
Hakan yana hannun mutane ne.

HUKUNCE- HUKUNCEN GARI

Ni na kasance an haife ni ne a wani gari misali garin Bauchi kana kuma mahaifana mutanen Kaduna ne misali, dan haka a kowace shekara su kan je Kaduna sau da yawa to ni ma na kasance ina tafiyar tare da su, to mene ne hukuncin sallata?
Tattare da cewa ni ba ni da niyyar komawa wannan gari na iyayena don zama a garin, ni dai zan ci gaba da zama ne a wannan gari na Bauchi.
Bisa ga wannan yanayi da ka ambata, hukuncin sallar ka da azuminka a wannan gari na mahaifanka shi ne hukuncin salla da azumin matafiyi (wato kasaru za ka yi).
Ni na kasance a cikin shekara na kan zauna a wani gari na wata shida, kana kuma wata shida a wani gari na daban wanda shi ne inda nake zaune da kuma iyalaina, to amma zamana a wannan garin na farko ba a jere ba ne a wasu lokuta na kan zauna a gurin ne na tsawon sati biyu ko kuma kwana goma ko kuma kasa da haka, sannan sai in koma wannan gari wanda ni da iyalaina muke da zama a ciki, to tambaya a nan ita ce yayin da na yi niyyar zama a wannan gari na farko na kwanaki kasa da goma, to shin hukuncina hukuncin matafiyi ne ko kuma a'a?
Idan har wannan gari ba garinku ba ne kuma ba ka da niyyar mayar da shi ya Zama garinka, to hukuncinka a duk lokacin da ba za ka zauna Na kwanaki goma ko fiye a gurin ba hukuncin matafiyi ne.
Shin hukuncin garin da mutum yake aiki a ciki dai-dai yake da hukuncin garinsu?
Yin aiki a guri ba ya mayar da gurin ya zama garin mutum, to amma da a duk kwanaki goma zai tafi wurin wannan aiki nasa sau guda alal akalla idan har ratan wurin aikin nasa daga garin da yake da zama ya kai nisan da shari'a ta yarda da shi wajen yin kasaru, to zai cika sallarsa ne kana kuma azuminsa ya inganta a wannan gurin aiki nasa.
Muna so ka yi mana bayani Kan mas'alar garin asali da kuma gari na biyu?
Garin asali: Shi ne wurin da aka haifi mutum, kana ya girma a gurin Gari Na biyu kuwa: Shi ne wurin da mutum ya zaba don ya rayu a gurin na dindindin ko da kuwa Na tsawon wasu watanni ne a kowace shekara.
Shin ana daukan garin da aka haifi mutum a ciki a matsayin garinsa ko da kuwa bai zauna a garin ba?
Idan har ya zauna a garin na wani lokaci kana kuma a garin ya girma, to matukar dai bai canza gari ba to garin yana da hukuncin garinsa ne, idan kuwa ba haka ba to bai kasance garinsa ba.

SALLAR AYOYI

Me ake nufi da "salatul Ayat" (sallar aya) kana kuma wasu abubuwa ne suke wajabta ta a shar'ance?
Ita salla ce mai raka'a biyu wacce kowace raka'a tana da ruku'u biyar da sujada guda biyu, abubuwan da suke wajabta ta kuwa a shar'ance su ne rashin lafiyar rana ko wata (wato husufin rana ko wata) ko da kuwa wani sashe ne nasu, da girgizar kasa da kuma duk wani abin da ya tsorata mafi yawan mutane, kamar baka ko jan guguwa wanda ta saba wa yadda aka saba ganin guguwa, da kuma tsananin duhu, da tsawa mai tsananin gaske, da wuta wanda kan baiyana a sama dukkan wadannan abubuwa in banda husufin wata da rana da kuma girgizan kasa to sallar ba ta wajaba har sai idan sun kasance abin tsoratarwa ga mafi yawan jama'a.
Yaya ake yin'salatul Ayat.
Tana da yanayi dadan - daban:
Yanayi na Farko: Shi ne bayan niyya da kabbarar harama sai ya karanta fatiha da sura sai ya yi ruku'u kana sai ya dago ya sake karanta fatiha da sura ya yi ruku'u ya daga, ya sake karanta fatiha da sura ya yi ruku'u ya daga, haka dai zai ta yi har ya cika ruku'u na biyar daga nan sai ya tafi zuwa sujada ya yi sujada guda biyu kana ya taso ya kawo raka'a ta biyu kamar yadda ya yi ta farko, daga nan sai ya yi tahiya ya yi sallama.
Yanayi na Biyu: Bayan niyya da kabbarar harama sai ya karanta fatiha da wata aya ta cikin wata sura (misali suratul Tauhid) sai ya yi ruku'u, sannan ya dago ya karanta wata aya kuma ta wannan surar ya yi ruku' a, sannan ya dago ya karanta wata aya ta wannan sura ya yi ruku'u, haka dai zai ci gaba da yi har ya kai ga ruku'u na biyar da ayar karshe na wannan sura, daga nan sai ya yi sujada guda biyu kana ya taso ya kawo raka'a ta biyu kamar yadda ya yi ta farko, kana sai ya yi tahiya ya yi sallama to amma a irin wannan yanayi fatiha guda kawai zai karanta a kowace raka'a.
Yanayi na Uku: Shi ne ya yi raka'a ta farko a daya daga cikin wadannan yanayi da aka ambata a sama kana a raka'a ta biyu kuwa ya yi daya yanayin.
Yanayi na hudu: Shi ne ya cika surar da ya riga ya karanta farkonta tun a tsayuwarsa ta farko to sai ya cika ta a tsayuwansa na biyu ko na uku ko na hudu, to a nan wajibi ne gare shi bayan dagowa daga ruku'u ya sake karanta fatiha a tsayuwar da za ta biyo baya kana kuma ya karanta sura ko kuma wata aya na wata sura, to amma idan kafin tsayuwa ta biyar aya ce ya karanta daga wata sura a tsayuwa ta hudu to wajibi ne ya cika waccan surar kafin ya yi ruku'u na biyar.
Shin wajibcin salatul ayat ta ta'allaka ne ga mutumin da ke garin da wannan al' amari ya faru ne? Ko kuma ya hada da dukkan wani baligin da yake da masaniya wajen faruwarsa ko da kuwa ba' a garin yake ba?
Wajibcin nata ya ta'allaka ne ga mutumin da ke garin da abin ya faru, hakan kuwa ya hada har da mutanen da suke hade da garin da wannan abu ya faru idan dai har ana ganinsu kamar gari guda ne.

SALLOLIN NAFILA

Shin sallar nafila a boye ake yin ta ko kuma a bayyane?
Mustahabi ne a yi sallar nafilolin rana a boye kana nafilolin dare kuwa a bayyane.
Muna so ka yi mana cikakken bayanin yadda a ke sallar dare.
Sallar dare dukkanta raka'oi goma sha daya ne, rakaoi takwas wadanda ake yin su raka' a bibbiyu ana kiran su sallar dare, sannan guda biyu da suke biye musu su ne shafai ana yin su ne kamar sallar asuba, raka'a ta karshe kuwa ita ce ake kira da witri, mustahabi ne a cikin kunutinsu a nemi gafara, a kuma yi addua wa muminai, da kuma neman biyan bukata kamar dai yadda aka bayyana a littattafan adduo'i.


BABIN AZUMI:
SHARUDDAN WAJIBCI DA KUMA INGANCIN AZUMI

Mene ne hukuncin' yan matan da suka isa shekarun balaga to amma yin azumi na yi musu wahala zuwa wani haddi? Kuma shin shekarun balaga ga mata shi ne shekara tara?
A bisa mashahurin magana shekarun balaga a wajen 'yan mata shi ne shekara tara, na kamariyya to a wannan hali wajibi ne su yi azumi, kuma ba ya halatta su bar azumi dan kawai wasu uzuri, to amma da azumin zai cutar da su ko ya zama kunci a gare su, to ya halatta su sha ruwa.
Da mutum zai tsammani sama da kashi hamsin bisa dari kana kuma bisa ga wani uzuri mai karfi cewa azumi bai wajaba a gare shi ba dan haka sai ya ki yin azumi, to amma sai daga baya ta bayyana masa cewa azumin nan fa wajibi ne a gare shi, to mene ne hukuncinsa dangane da ramuwa da kaffara?
Idan dai har ya sha ruwan ne saboda kawai tsammanin cewa azumi bai wajabta a gare shi ba, to a nan wajibi ne ya yi ramuwa kuma ya yi kaffara a kamar yadda yake a tambayar to amma idan har ya sha ruwan ne saboda tsoron cutarwa kuma tsoron nasa abin karbuwa ne a gurin masu hankali, to babu kaffara a gare shi sai dai kawai zai rama azumin ne.
Mutumin da yake da azumin wajibi a kansa sai ya kuduri aniyar rama azumin, to amma sai wani abu ya bijiro masa da zai hana yin azumin, kamar tafiya ta same shi bayan ketowar alfijir inda ya yi tafiyar to amma bai dawo ba sai bayan azahar kana bai aikata komai daga cikin abubuwan da suke karya azumi ba, sai dai kawai lokacin yin niyyar azumin wajibi ya wuce masa, kuma wannan ranar tana daga cikin ranakun da yin azumi mustahabi ne a cikinsu, to shin ya inganta ya yi niyyar azumin mustahabi?
Idan dai har yana da azumin wajibi a kansa to azumin mustahabi ba ya inganta a gare shi ko da kuwa bayan wucewar lokacin yin niyyar azumin wajibi ne.

MACE MAI CIKI KO SHAYASWA

Shin mace mai cikin da ba ta san ko azumin zai cutar da jaririn nata ko kuma a'a ba, wajibi ne ta yi azumi?
Idan har tana tsoron cewa azumin zai cutar da jaririn nata kuma tsoron nata yana da tushe na masu hankali, to wajibi ne ta sha ruwa idan kuwa ba haka ba, to wajibi ne ta yi azumi.
Macen da take shayarwa kana kuma ga ciki sannan kuma a dai-dai lokacin tana azumi na watan Ramalana, to yayin da ta haihu sai dan bai zo da, rai ba to idan dama tun farko tana tsammanin cutarwar to amma duk da haka ta yi azumin shin:
(1) Azumin nata ya inganta?
(2) Kuma dole ne ta biya diyya?
(3) Kana kuma idan daman ba ta yi tsammanin cutarwar ba, to amma sai daga baya ta gano hakan, to mene ne hukuncinta?
Idan har ta yi azumin tattare da wannan tsoro na cutarwa wanda yake da tushe na masu hankali, ko kuma daga baya ya bayyana mata cewa azumin ya cutar da ita ko kuma ga jinjirinta to azuminta bai inganta ba dole ne ta rama shi, to amma tabbatar da biyan diyyar cikin ya ta'allaka ne kan tabbatuwar cewa mutuwan jaririn ya samo asali ne daga wannan azumi nata.
Ni na kasance mai shayarwa ne bayan da Allah ya arzurta mu da yaro, kuma ga shi watan azumi ya gabato, amma a halin yanzu ina iya azumi, to amma a duk lokacin da na yi azumin ruwan nono na ya kan kafe don kuwa ni mai raunin jiki ne kuma wannan da nawa ya kan bukaci nono a duk bayan mintoci goma, to yaya zan yi?
Idan har wannan kafewa da ruwan nonon naki yake yi a sanadiyyar azumi, kin ji tsoron zai cutar da jaririn to ya halatta ki sha ruwa, to amma za ki dinga bayar da mudu guda na abinci ga fakirai a kowace rana bugu da kari kan rama azumin da za ki yi daga baya.

RASHIN LAFIYA DA KUMA HANIN LIKITA

Wasu likitoci 'yan ko a kula sukan hana marasa lafiya yin azumi wai saboda cutarwa, to shin maganar irin wadannan likitoci hujja ce?
Idan har likita ba amintacce ba ne, kuma maganarsa ba ta haifar da nitsuwa ba, kana ba ta sa an ji tsoron aukuwar cuta ba, to ba'a lura da maganarsa.
Wani likitan ido ya hana ni yin azumi inda yake ce mini ba ya halatta ka yi azumi saboda ciwon idon da yake tare da kai, to amma duk da haka sai na fara, to amma na dinga samun matsaloli kala-kala, ta yadda a wasu ranakun zan yi azumin ba tare da jin wani ciwo ba, a wasu lokutan kuma na kan ji ciwo da yamma, to amma tattare da taraddadin da nake da shi kan ko in bar azumin ko kuma in hakura da zafin ciwo na kasance na kan wuce da azumi har faduwan rana, to tambaya a nan ita ce, shin tun farko ma wajibi ne in yi azumi?A ranakun da nake yin azumi a halin ina kokwanton zan iya kaiwa har faduwar rana ko ba zan iya ba to zan ci gaba da azumi ko aa? Kana kuma yaya niyyata za ta kasance?
Idan har ka sami nitsuwa da kuma yakini kan maganar wani likita mai rikon addini, amintacce na cewa azumi zai cutar da kai, ko kuma ka zan kana tsoron cutarwa ga idon naka saboda azumi, to bai wajaba a gare ka ba, kai bai ma halatta ka yi azumin ba, kana ba ya inganta ka yi niyyar azumin idan kana tsoron zai cutar da kai, to amma idan ba ka tsoron wata cutarwa to babu matsala ga hakan, to amma kuma ingancin azumin naka ya ta'allaka ne da rashin cutarwar a hakika.
A shekarar da ta wuce wani kwararren likita ya yi min tiyata a koda ta biyu inda daga baya ya hana ni yin azumi har zuwa karshen rayuwa ta, to amma a halin yanzu ba ni jin wata matsala, ina ci ina sha kamar da, ba na jin wani ciwo, to mene ne ya wajaba a gare ni?
Idan har kai kanka ba ka jin wani tsoron cewa azumin zai cutar da kai, kana ba ka da wata hujja ta shari'a a kan hakan to wajibi ne ka yi azumi.
Idan likita ya hana mutum yin azumi, to shin wajibi ne ya lizimtu da wannan magana tasa? Tattare da cewa wasu likitocin ba sa da masaniya kan hukunce-hukuncen shari'a.
Idan har mutum ya samu nitsuwa da wannan magana tasa cewa azumi zai cutar da shi, ko kuma a sanadiyyar maganar likita sai ya ji tsoro kan cewa azumin zai cutar da shi, ko kuma hakan ya samu (wato tsoron cutarwa) daga wani sababi wanda masu hankali suka yarda da shi, to a wannan hali azumi ba wajibi ba ne a kansa.

KAN ABUBUWAN DA SUKE BATA AZUMI

Idan mutum yana azumi sai jini ya fito masa a bakinsa, to hakan ya bata masa azumi ?
Hakan ba ya bata azumi, to amma wajibi ne ya kare wucewar jinin zuwa makogwaronsa.
Wata rana na kasance cikin azumin watan Ramalana to amma bayan suhur sai ban wanke bakina da man goge baki ba to sauran abincin da ya saura a baki na ya wuce zuwa cikina, ba da so na ba to shin wajibi ne a rama azumin wannan rana?
To idan har ba ka san da kasantuwar sauran abincin a jikin hakwaran naka, ba ko kuma ba ka san zai wuce zuwa cikin naka ba, kana kuma ba da gangan ka hadiya ba, ba kuma tare da mai da hankali ba to ba komai a gare ka dangane da wannan azumi naka.
Muna bukatar ka yi mana bayani kan hukuncin yin allura yayin da mutum yake, cikin azumin watan Ramalana?
Babu wata matsala ga yin allura sai dai in allurar ta kasance ta sanya wa maras lafiyan abinci ne, to bisa lhtiyati wajibi ne a nesance ta yayin da ake azumi.

GANGANTA ZAMA CIKIN JANABA

Idan mutum ya zauna cikin janaba (saboda wasu wahalhalu) har aka kira sallar asuba, to shin ya halatta ya yi azumi a wannan ranar?
Babu wata matsala ga azuminsa idan dai azumin ba na Ramalana ko ramakonsa ba ne, to amma a azumin Ramalana ko ramakonsa, idan har ba zai iya wanka ba to dole ne ya yi taimama, idan har ya bar taimama, to azuminsa ba ya inganta.
Idan ya yi azumi na wasu raneku alhalin yana cikin janaba, ba tare da ya san cewa tsarki daga janaba yana daga cikin sharadin azumi ba, to shin wajibi ne ya yi kaffaran wadannan raneku da ya yi azumi a cikinsu da janaba, ko kuma ramakonsu kawai ya wadatar?
Idan mutum ya wayi gari da janaba-alhali yana sane da cewa yana da janaba-to amma ya jahilci wajibcin yin wanka ko taimama (kafin fitowar alfijir), to wajibi ne a gare shi bisa ihtiyati ya yi kaffara bayan ramako, sai dai idan jahilcin nasa ba'a sakacinsa ba ne to a nan ba wajibi ba ne ya yi kaffara, ko da yake ihtiyat ne yin kaffarar.
Mutum ne ya tafi bakunta cikin watan Ramalana, to cikin tsakiyan dare sai ya yi mafarki, to dan saboba shi bako ne ba shi da wasu tufafi, dan haka sai ya kuduri aniyar yin tafiya washe gari dan gudu daga azumin, to bayan kiran sallar asuba sai ya fito dan yin wannan tafiya ba tare da aikata wani abin da ke bata azumi ba, to tambaya a nan ita ce: Shin kudura anniyar tafiya a wajen wannan mutum yakan sauke masa yin kaffara ko kuwa?
Kudura anniyar tafiya cikin dare kawai ba ya wadatarwa haka kuma yin tafiya da rana bai wadatarwa wajen kaffara daga gare shi idan har ya wayi gari cikin janaba-tattare da cewa ya san yana da janabar- ba tare da ya gaggauta yin wanka ko taimama kafin fitowar alfijir ba.
Shin ya halatta ga wanda ba shi da ruwa ko kuma dai wasu uzurorin na daban da suke hana wankan janaba (banda kurewar lokaci) da ya yi janaba da gangan cikin watan Ramalana?
Hakan yana halatta a gare shi idan har abin da ya hau kansa shi ne taimama, kana kuma yana da cikakken lokaci na yin taimamar bayan da ya yi janabar.
Mutum ne cikin watan Ramalana ya farka gabannin kiran sallar asuba, to amma bai san cewa ya yi mafarki ba, sai ya koma da barcinsa, to sai yayin da ake kiran sallar asuba ya gane cewa ya yi mafarki kuma ya tabbatar da cewa mafarkin nasa ya yi shi ne kafin kiran sallar, to mene ne hukuncin azuminsa?
Idan har bai gano hakan (wato janabar) ba kafin kiran sallar asuba din, to azuminsa ya inganta.
Idan mutum ya farka daga barci bayan kiran sallar asuba na watan Ramalana to sai ya ga ya riga ya yi mafarki, to amma sai ya ci gaba da barcinsa har zuwa bayan fitowar rana (ba tare da ya yi sallar asuba ba) ya jinkirta yin wankan har zuwa lokacin sallar azahar sannan ya yi wanka ya yi salla to shin mene ne hukuncin azuminsa?
Azuminsa ya inganta, jinkirta yin wankan har zuwa kiran sallar azahar ba ya cutarwa.
Idan mutum ya yi shakka kafin kiran sallar asuba na watan Ramalana kan cewa shin ya yi mafarki ko kuma, a a sai dai bai kula da wannan shakka tasa ba, ya ci gaba da barcinsa, to sai dai da ya farka bayan kiran salla sai ya ga ashe ya yi mafarkin kuma kafin kiran sallar, to mene ne hukuncin azuminsa?
Idan har a farkawar tasa ta farko bai ga wata alama na mafarki ba, kawai tsammani ne yake yi, ba tare da ya tabbatar ba to, azuminsa ya inganta, ko da kuwa daga baya ya bayyana masa cewa mafarkin ya yi shi ne kafin kiran sallar.
Idan mutum ya yi wanka da ruwa mai najasa a cikin watan Ramalana, to sai bayan sati guda sai ya tuna cewa ruwan da ya yi wankan da shi mai najasa ne, to mene ne hukuncin azumi da sallarsa cikin wannan lokaci?
Sallarsa batacciya ce wajibi ne ya sake ta, to amma azuminsa ya inganta.

HUKUNCE- HUKUNCEN SHAN RUWA

Shin bin Ahlus sunna wajen shan ruwa yayin da mutum yake tare da su yana halatta? Kana mene ne ya wajaba kan mutum idan har ya ga cewa yin hakan ya fita daga cikin takiyya, kuma bai kasance dole ba?
Ba ya halatta ga mukallafi ya bi wani wajen shigan lokacin shan ruwa, kuma ba ya halatta gare shi idan har yana da zabi ya sha ruwa, sai har ya tabbatar da faduwar rana shi da kansa ko kuma ta hanya ta shari' a.
Idan mutum ya jahilci hukuncin rashin halaccin shan ruwa kafin karkatan rana zuwa yamma (zawali) idan har bai isa ga "Haddil tarakhus", ba to shi bai san wannan lamari ba, sai ya sha ruwa kafin isa ga haddin tarakhus dan ganin cewa shi matafiyi ne, to mene ne hukuncin wannan mutum, shin ramuwa ne ya hau kansa, ko kuma akwai wani hukuncin?
Hukuncinsa kamar hukuncin shan ruwa da gangan ne.
Yayin da nake fama da mura majina ta kan taru min a baki, to maimakon in zubar da ita sai na hadiye, to shin azumina ya inganta ko kuma?
Kana kuma a wasu kwanaki na watan Ramalana na kasance a gidan wani dangimmu ne, to a dalilin mura da kuma kunya sai na gaza yin wankan wajibi sai dai taimama, ba na yin wanka har sai kusan sallar azahar, kuma na ci, gaba da yin hakan har na tsawon lokaci to shin azumina sun inganta a wadannan ranaku ko kuma?
Babu abin da ya taba maka azuminka daga wannan hadiye majina da ka yi, ko da yake lhtiyati shi ne ka rama azumin idan har hakan ya kasance bayan majinan ta isa a cikin sararin bakinka, to amma barin wankan janabar da ka yi kafin alfijir ya fito, da kuma yin taimama a maimakonsa, idan har uzurin naka uzuri ne da shari' a ta yarda da shi, ko kuma taimamar taka ta kasance ne. a karshen lokaci saboda ?arancin lokaci, to azuminka ya inganta, in kuwa ba haka ba ne to azuminka a wadannan ranaku sun baci.

KAFFARAR AZUMI DA KUMA GWARGWADONTA

Shin bayar da kudi gwargwadon mudu na abinci ga fakiri dan ya sayi abincin da kansa (yayin kaffara) yana wadatarwa?
Idan har yana da nitsuwa kan cewa wannan fakirin zai wakilce shi ya sayi abincin da wannan kudi daga bisani ya mallaki abincin a matsayin kaffara, to babu wata matsala ga hakan.
Macen da aka dauke mata azumi saboda rashin lafiya, kuma ba ta samu daman rama azumin ba har watan azumi na gaba ya iso, to a irin wannan hali shin kaffarar yana kanta ne ko kuma yana kan mijinta?
A irin wannan hali wajibi ne gare ta ta ba da mudu na abinci a madadin kowace rana, kuma hakan bai hau kan mijinta ba.
Mutum ne yake da ramakon azumi na kwanaki goma, to sai a rana ta ashirin na watan sha'aban ya fara azumi, to shin a irin wannan hali zai iya karya azumin da gangan kafin "zawali" ko kuma bayanta? Kuma idan ya karya, to shin mene ne gwargwadon kaffararsa idan da ya karya azumin kafin zawali ne ko kuma bayansa?
A irin wannan hali ba ya halatta ya karya azumin da gangan, to amma idan ya karya da gangan, idan kafin "zawali" ne to babu kaffara a gare shi, idan kuwa bayan "zawali" ne, to kaffara ta hau kansa, wato ciyar da miskinai goma, idan kuwa hakan ya gagara, to sai ya yi azumin kwanaki uku.

MAS'ALOLI DABAN-DABAN KAN AZUMI

Mene ne hukuncin macen da jinin haila ya zo mata yayin da take azumin bakance mai takamammen lokacin yinsa wato ayyananne?
Daga fitowar jinin azumin nata yakan baci, to amma wajibi ne ta rama shi bayan ta sami tsarki.
Mutum ne yake zaune a wani gari to sai ya yi azumi tun daga farko har zuwa rana ta ashirin da bakwai na wannan wata mai alfarma, to ran ashirin da takwas na wannan wata sai ya yi tafiya zuwa wata kasa inda ya isa ran ashirin da tara, sai ya samu sun sanar da ganin wata, to daga nan sai ya koma kasarsu, to shin wajibi ne ya rama abin da ya tsere masa na daga azumin?
Idan ya rama rana guda, to watan Ramalana zai kasance kwana ashirin da takwas kenan a gare shi, idan kuma ya ce zai rama kwanaki biyu ne, to ai a ranan 29 na wannan wata yana garin da suka riga suka sanar da ganin wata ne, to a nan mene ne hukuncin wannan mutum?
Idan har wannan sanarwa na ganin wata ran 29 a wancan kasa da ya je dai- dai ne a mahangan shari a, to ramakon azumin wannan rana a gare shi ba wajibi ba ne, sai dai hakan yana tabbatar da kubucewar daya azumin gare shi a farkon watan, dan haka wajibi ne ya rama abin da ya tsere masa bisa yakini na daga azumin.
Da mutum zai sha ruwa bayan faduwar rana a wani gari, to sai ya tafi wani garin da su a gurinsu rana ba ta fadi ba, to mene ne hukuncin azuminsa na wannan rana? Kana shin zai iya ci gaba da cin abincinsa a wannan garin kafin faduwar ranarsu?
Azuminsa ya inganta kuma zai iya ci gaba da cin abincinsa kafin faduwar rana a wannan garin.
Mu kan ji daga bakin wasu maluma cewa idan aka gayyaci mutum ga walimar cin abinci alhali kuwa yana azumi na mustahabi, zai iya cin wannan abinci kuma hakan bai bata masa azuminsa ba, to a nan muna so mu ji fatawarka kan hakan.
Amsa gayyatar mumini zuwa ga cin abinci yayin azumin mustahabi, al'amari ne da a ka so shi a sharia, cin abincin muminin da ya gayyaci dan ' uwansa mumini ko da yake yana bata azumi, to amma ba ya hana samun ladansa.

GANIN WATA

Kamar yadda dai ka sani ne cewa yanayin jinjirin wata a karshensa (ko kuma a farkonsa) ba ya fita daga daya daga cikin wadannan halaye:
(1) Buyan wata ya kasance kafin faduwar rana.
(2) Buyan wata ya kasance dai-dai da faduwar rana.
(3) Buyan wata ya kasance bayan faduwar rana.
To muna so ayi mana bayanin wadannan al'amura:
Na farko: A cikin wadannan halaye guda uku, a mahangan fikhu wanne ne a ke daukansa farkon wata.
Na biyu Idan muka yi la'akari da cewa dukkan wadannan halaye guda uku a kan iya gano su ta hanyar naurori da suke yin wannan aiki to shin ana iya amfani da wannan na'ura wajen gano farkon wata, ko kuma dai wajibi ne sai an gan shi da ido?
Abin la'akari dangane da farkon wata shi ne watan da yake buya bayan faduwar rana, wanda za'a iya ganin sa kafin faduwar rana ta yadda aka saba.
Idan aka samu sabani tsakanin maluman wani gari dangane da ganin wata da kuma rashin ganin sa, kuma adalcin wadannan malamai dukkansu ya tabbata ga mutum, kuma yana da yakini kan bincike da bin diddigin kowane daya daga cikinsu, to mene ne ya wajaba ya aikata?
Idan har wannan sabani nasu kan korewa ne da kuma tabbatar (da ganin watan) kamar wasunsu su yi da'awar tabbatar watan kana wasu kuma su yi daawar tabbabar da rashin tsayuwarsa, to hakan karo ne tsakanin hujjojin guda biyu, to a wannan hali sai mutum ya jefar da dukkan wadannan maganganu biyu, ya koma ya yi riko da abin da shari 'a ta tabbatar na yin aiki da asali daga usul, wato kamar babu wadannan maganganu, to amma da sabanin nasu ya ta'allaka ne da tabbatarwa da kuma rashin masaniya kan tabbatuwan, kamar wasunsu su yi da'awar ganinsa wasu kuwa su ce su ba su gan shi ba, to maganar wadanda suka ce sun gani idan dai adilai ne shi ne abin riko a shar'ance ga mutum kuma, wajibi ne ya bi hakan, haka kuma da marja'i ko kuma waliyul fakih zai bayar da sanarwar ganin watan, to hukuncinsa hujja ce ga dukkan mutane, kuma wajibi ne su bi shi.
Wasu hanyoyi ne ake bi wajen gano watan Ramalana da kuma daren idi? Shin ya inganta a dogara ga kalanda?
Hakan yana tabbata ne da ganin shi kansa mukallafi ga watan, ko kuma shaidar mutane biyu adalai, ko kuma yaduwan labarin ganin watan tsakanin al'umma, ta yadda mutum ya sami ilimi ta haka ko kuma da cikan watan kwana talatin, ko kuma da hukuncin marja'i ko waliyul fakih.
Da ace ya halatta a bi abin da wata hukuma ta sanar dangane da ganin wata, kuma wannan sanarwa ya kasance wani mizani na tabbatuwan ganin wata a wasu garuruwan, to shin wajibi ne wannan hukuma ta zama ta musulunci, ko kuma za'a iya amfani da hakan ko da kuwa hukuncin ya fito ne daga hukuma azzaluma fajira?
Abin la'akari kawai shi ne samuwar nitsuwa kan ganin watan a wannan guri.


BABIN KHUMSI:
KAN ABUBUWAN DA KHUMSI YA WAJABA AKANSU

KYAUTA, SADAKI DA KUMA GADO

Shin akwai " Khumsi"a cikin abin da aka ba wa mutum kyautarsa ko taimakonsa ko kuma a'a?
Babu "Khumsi" a cikin kyauta ko taimako, ko da yake a bisa ihtiyat ne a cire khumsin abin da ya saura daga cikinsu bayan bukatunsa na cikin shekara.
Shin ana lissafa abin ciyarwar da mahaifi, ko dan uwa ko daya daga cikin dangi ke bayarwa ga mutum a matsayin kyauta ne ko kuma? To idan shi mai bayarwan ba ya cire khumsin dukiyarsa, shin wajibi ne ga wanda aka ba shi din da ya cire khumsinsa?
Tabbatuwar kyauta ko taimako ya ta'allaka ne da niyyar mai bayarwar, kana matukar dai bai ga yakinin ta'allakan khumsi da abin da aka ba shi, ba to ba wajibi ba ne ya cire khumsinsa.
A cikin littafin "Tahrirul wasila" an ambaci cewa khumsi ba ya ta'allaka da kudin sadaki . to amma ba 'a ambaci cewa sadakin da aka bayar ne gare ta ko kuma wanda take bin bashinsa to dan haka muke son karin bayani.
Babu wani bambanci shin sadakin an riga an karba ne ko kuma ana bin bashinsa, hakana ba bambanci shin kudi ne ko kuma kadara.
Shin khumsi ya ta'allaka da irin kudin nan da ma'aikatan ilmi take ba wa dalibai (sukolashif) don saukaka musu alamurran karatunsu?
Babu khumsi a cikin taimakon da ake bayarwa dan saukaka al'amurran karatu.

DUKIYAR DA AKA TONO DA KUMA HALAL DIN DA YA HADU DA HARAM

Mene ne fatawarka dangane da dukiyar tsintuwa da mutane suka tono a cikin kasar da mallakarsu ce?
Idan har ba ya tsammanin cewa dukiyar ta tsohon mai gurin ne, to ta wanda ya samo ta ne kuma a wannan hali khumsi ya hau kansa idan ta kai dinare ashirin na zinare ko kuma dirhami dari biyu na azurfa, a abin da kuma ba zinare ko azurfa ba ne shi ma wajibi ne a fitar da khumusinsa idan ya kai kimar yawan zinare ko azurfa da muka ambata, idan har hukuma ko wani ba su hana shi mallakarta ba, amma idan suka hana shi ko kuma suka kwace abin da ya samo din, to idan har akwai wani abin da ya saura a hannunsa kana kuma ya kai nisabi, to wajibi ne ya cire masa khumsi, to idan kuwa ba haka ba ne to babu khumsi a gare shi.
Da dukiyar haramun zai shiga dukiyar mutum, to mene ne hukuncin wannan dukiyar, kana yaya zai halatta ? kana kuma mene ne ya wajaba a gare shi ya aikata idan yana da ilimi kan haramcinsa ko kuma bai da shi?
Idan har yana da yakinin samuwar dukiyar haramun a cikin dukiyarsa, to amma bai san daidai yawanta ba kana kuma bai san mai ita ba, to hanyar tsarkake ta ita ce fitar da khumsinta, to amma idan har shakkan haduwan nata da ta haramun din yake yi to babu komai a gare shi.

BASHI, ALBASHI, INSHORA DA KUMA FANSHO

Idan mutum ya karbi bashin kudi, to sai bai samu biyan bashin ba gabanni shekaran khumsinsa, shin khumsin dukiyar tana kan wanda ya karbi bashin ne ko kuma wanda ya bayar?
Babu khumsi ga kudin bashin akan wanda ya karbi bashin, to amma wanda ya bayar, idan har abin da ya bayar din daga cikin riban kasuwancinsa ne kuma bai riga ya cire masa khumsi ba, to idan har zai iya karban dukiyar tasa daga hannun wanda ya ba da bashin gare shi kafin cikan shekaran khumsinsa, to a wannan hali wajibi ne ya fitar da khumsinsa, idan kuwa ba zai iya karba ba har cikan shekaransa to a wannan hali khumusinsa bai wajaba a kansa ba a yanzu haka sai dai kawai ya jira lokacin da za a dawo masa da dukiyar, idan aka dawo da shi to a yayin nan wajibi ne a yi khumusinsa.
Mutanen da suke karban kudin fansho shin wajibi ne fitar da khumsin albashin da suke karba a shekara?
Albashin da ma'aikata suke karba bayan barin aikinsu idan daga cikin abin da ake yankewa daga cikin albashin su yayin da suke aiki, ne kana a basu bayan sun yi ritaya, to idan har ya wuce abin da suke bukatuwa da shi na shekara da ya karba to wajibi ne su fitar masa da khumsi.
Albashin ma'aikatan da hukuma ta jinkirta ba su tun shekaru, to shin yayin da ya karbe su za'a kidanya su ne a matsayin riban wannan shekarar (wato shekarar da ya karba) ta yadda khumsinsa zai kasance a daidai lokacin da shekaransa ta cika, ko kuma shin tun asali ma khumsi bai ta'allaka da wannan dukiya ba?
Zai lissafa ta ne daga cikin riban shekarar da ya karbe ta kana kuma khumsi ta hau kansa idan har ta wuce bukatunsa na shekara.
Shin khumsi yana wajaba akan kudin da kamfanonin inshora suke bayarwa ga masu alaka da su kan asarorin da suka shafe su?
Babu khumsi ga kudin da kamfanonin inshora take bayarwa ga mutanen da suke da alaka da su.

ABUBUWAN BUKATA (NA YAU DA KULLUM)

Shin khumsi yana hawa kan irin zinaren da miji yake saya wa matarsa ko kuma?
Idan har yawansa bai wuce na abin da aka saba wanda ya dace da halinsa ba to babu khumsi a cikinsa.
Idan mutum yana da wani fili na biyu da ya yi dai-dai da irin yanayinsa, kana kuma yana da bukatarsa dan shi ma'abucin iyalai ne, kana kuma bai samu daman gina filin ba a cikin shekaran khumsinsa, ko kuma bai iya gama gina shi a cikin shekara guda ba, to shin khumsi ya hau kansa?
Babu bambanci wajen rashin wajabcin khumsi tsakanin fili guda daya da kuma filaye da yawa, kana kuma tsakanin matsuguni guda ko kuma da yawa abin lura dai shi ne bukatuwansa gare shi gwargwadon yanayinsa da kuma yanayin tattalin arzikinsa wajen ginin a hankali- a hankali.
Idan mutum bai yi amfani da kayayyakin girki da cin abinci na gida ba ko kuma bai yi aiki da darduman salla ba har na tsawon shekara guda, ko da yake yana bukatuwa da su wajen hidima ga baki (idan suka zo), to shin khumsi ya hau kansu?
Babu khumsi a kansu.
Bisa la'akari da fatawar lmam khumaini (r.a) kan mas'alar kayayyakin gida da amarya take tafiya da shi zuwa gidan mijinta, to idan a wata al'umman ya kasance shi mijin ne ko kuma iyayensa ne za su tanadar da wadannan kayayyaki, to dan haka sai suka fara sayen kayayyakin a hankali a hankali har shekara ta zagayo, to shin mene ne hukuncin wadannan kayayyaki?
Idan har wannan tari da suke yi na wadannan kayayyaki dan saboda gaba ana iya kirga shi a matsayin abubuwan da suke bukata kuma basu da wata hanyar da za su same shi sai ta wannan hanya ta tari, to babu khumsi a cikinsu.
Yaya ake lisafin khumsin kayayyakin gida?
Kayayyakin da za'a iya amfani da su a dai-dai lokacin da kuma asalinsu yana nan kamar darduma da dai sauransu babu khumsi a cikinsu, amma kayayyaki masu karewa kamar su shinkafa man gyada da wasunsu to duk abin da ya wuce har ya kai dai-dai shekara, to za'a fitar da khumsinsa.
A wasu lokuta a kan sayar mana da wasu kayayyakin gida kamar firinji da araha kasa da yadda ake sayarwa a kasuwa, to kuma wadannan kayayyaki dole ne mu neme su a nan gaba yayin da muka yi aure, kuma tattare da cewa in ba mu saya yanzu ba to nan gaba lokacin auren dole mu saye su da kudi ninkin ba ninkiya, to shin khumsi ya hau kan wadannan kayayyakin da muka ajiye su dan mu yi amfani da su?
Idan har kun saye su da riban kasuwancinku na shekara don ku amfana da su nan gaba, kuma ba su kasance abin bukatuwanku a wannan shakaran da kuka saya din ba, to akwai khumsi a cikinsu dai-dai da farashinsu matsakaici lokacin da shekarar ta yi, sai dai idan sun kasance a bisa al'ada suna daga cikin kayayyakin da ake sayansu kadan - kadan ne da kuma ajiye su har lokacin bukata saboda rashin iya sayensu lokaci guda yayin da ake bukatuwa da su, kuma sun yi dai-dai da irin yanayinku, to anan ana kirga su a cikin abubuwan bukatuwa, don haka babu khumsi a cikinsu.
Shin khumsi ya wajaba kan kudin da nake tarawa daga cikin albashi na dan sayen kayayyakin aure?
Idan har ainin kudin (kudin da kansa) ne ka tara to wajibi ne ka fitar masa da khumsi idan shekara ta zagayo, ko da kuwa don sayen kayayyakin auren ne.

ABUBUWAN DA KHUMSI BAI HAU KANSU BA

Shin khumsi ya wajaba kan mutumin da wani abu ya saura a cikin kudinsa na shekara, tattare da cewa shekarar ta yi ne alhali yana da bashi akansa? Ko da yake yana da lokaci mai yawa na biyan wannan bashi nasa?
Bashi, shin na yanzu ko kuma wanda biyansa sai daga baya (wato za'a iya jinkirta shi) ba'a cire shi daga cikin riban shekara, sai dai bashin da aka karbe shi dan biyan bukatun shekarar da aka ci ribar, to shi kan ana cire shi daga cikinsa (riban shekara), don haka babu khumsi a cikinsa.
Ina da wani gwargwado, na riban kasuwancina na shekara wadanda khumsi ya hau kansu, to a dai-dai lokacin kuma ana bi na bashin wasu gwargwado na kudi, to tambaya a nan ita ce, shin zan iya ware kudin bashin da ake bi na daga cikin dukkan riban kasuwancin shekarar ko kuma? Tattare da cewa bashin da na karba din dan sayan mota ce ga kaina?
Ba'a Kebance bashin da aka karba don sayen mota daga cikin riban kasuwancin shekara.
Shin khumsi ya wajaba kan ma'aikatan da abin da suke da shi na kudi ya kan wuce abin da suke bukata na shekararsu? Tattare da cewa suna da basussuka a kansu.
Idan har bashin ya samo asali ne daga bashin kudin da aka karba a cikin wannan shekarar, dan biyan bukatu na yau da kullum na masarufi ko kuma wajen sayen wasu abubuwan bukatuwa na shekara (wato bashin kaya) to ana cire shi daga riban da ta saura, in kuwa ba haka ba to sauran abin da ya saura dole ne a cire masa khumsi.
Ni na kasance ana bi na bashin wasu kudade, to idan shekara ta yi kuma mai kudin bai bukaci in biya shi ba, kana kuma ina da wani gwargwado na riban shekara, wato ina da daman biyan bashin, sai dai mai kudin bai bukaci hakan ba, to shin za'a iya ware wannan bashi daga riban shekara ko kuma?
Bashin da ya samo asali daga aron kudi ko kuma sayen wasu kayayyaki bashi, idan har an karbe shi saboda biyan bukatun kayan masarufi na yau da kullum na shekara, to ana cire shi daga cikin riban shekara, dan haka babu khumsi a cikinsa, to amma idan bai kasance bashi ne na bukatun kayan masarufi na shekara ba, ko kuma bashi ne na shekarun da suka gabata, to shi, ko da yake ya halatta a sarrafa riban shekara wajen biyansa (wato bashin), to amma idan har aka kai karshen shekara, ba a bayar ba to ba'a cire shi daga cikin riban shekara.

AYYANA FARKON SHEKARA

Mutumin da ya tabbatar cewa babu wani abin da zai saura a gare shi na daga riban kasuwancinsa na shekara har zuwa karshen shekara, face dai duk riban kasuwancin nasa zai tafi wajen abubuwan bukatuwa na masarufi a shekara, to shin duk da haka wajibi ne gare shi ya ayyana farkon shekarar Khumusinsa?
Shin ayyana farkon shekara wajibi ne? Kana mene ne hukuncin mutumin da bai ayyana wa kansa farkon shekara ba saboda yakinin cewa ba abin da zai saura a gare shi?
Ayyana farkon shekarar khumsi ba yana hannun mukallafi ba, ne face dai tabbataccen al'amari ne da yake farawa daga lokacin da mutum ya fara kasuwanci ga wanda yake sana'ar kasuwanci, kana da zuwan lokacin girbi ga manomi, Kana daga lokacin karban albashi ga ma' aikata, dan haka lissafin farkon shekara da kuma shigowar shekara ba wani wajibi ne mai cin gashin kansa ba, face dai hanya ce kawai ta sanin abin da ya wajaba na daga khumsi, saboda haka yake wajaba to idan har ba abin da ya saura na daga riban kasuwancinsa, duk abin da ya samu ya sarrafa shi wajen abubuwan bukatunsa na shekara, to babu abin da ya wajaba a kansa.
Shin miji da matan da suke hada albashinsu waje guda dan gudanar da ayyukan gida zai yiwu su yi amfani da shekaran khumsi guda?
Kowannensu zai kasance da lokacinsa na khumsi na daban ne (mai cin gashin kansa) dan haka wajibi ne ga kowannensu ya fitar da khumsin abin da ya saura na daga albashi da kuma kudin shigarsa na shekara a karshen shekarar khumsinsa.

UWAR KUDI

Shin Khumsi ya wajaba kan kudin da mutum yake kasuwanci da su ko kuma?
Idan har asalin uwar kudin ya kasance daga cikin riban kasuwanci ne to dole ne ya fitar da khumsinsa, to amma kudin da yake sarrafa shi daga uwar kudin wajen neman riba na daga ayyukan kula da kayan, kudin daukan kayan da kuma auna shi da sauransu to ana cire shi daga cikin riban kasuwanci, don haka babu khumsi a cikinsa.
Shin khumsi yana wajaba kan naurori ko kuma kayayyakin da ake yin amfani da su wajen kasuwancin?
Hukuncin na'urori da kuma kayayyakin kasuwanci dai- dai yake da hukuncin uwar kudi wajen wajibcin fitar da khumsinsa.
Mene ne hukuncin kayayyakin da mutum kan saye su cikin shekararsa ta khumsi kana ya sayar da su bayan shigan shekararsa ta khumsi?
Idan har ya saye su ne dan ya sayar, to idan sayar da su din zai yiwu . zuwa cikan shekaran khumsi, to wajibi ne ya fitar da khumsin ribarsu, in kuma ba haka ba to matsawar bai sayar ba, khumsi ba ya hawa kansa, idan kuwa ya sayar da su to ribar da ya samu ana kirga ta daga cikin ribar wannar shekarar da ya sayar a ciki ne.

HANYAR KIRGEN KHUMSI

Ni na kasance ma'abucin shago ne, to kowani shekara na kan kirga abin da nake da shi na daga kudi da kuma sauran kayayyakin, to kasantuwan wasu daga cikin kayayyakin ba sa sayuwa har zuwa karshen shekarar khumsi, shin wajibi ne cire khumsin su karshen shekarar kafin a sayar da su ko kuma khumsi yana wajaba a kansu ne bayan sayar da su? Kana kuma idan na ba da khumsin kaya kana daga baya na sayar da shi to yaya zan yi lissafain khumsin shekara mai zuwa? Sannan kuma idan ban sayar da su ba har sai da farashinsu ya sake, to mene ne hukuncin hakan?
Duk kayan da ba ka sayar ba kana kuma ba ka samu mai sayan sa ba har zuwa farkon shekara, a wannan halin ba wajibi ba ne ka fitar da khumsin abin da ya karu na kudinsa, face dai za ka yi lissafin ribar da ka samu ne bayan sayar da su nan gaba kuma khumusinsu za a fitar ne a cikin shekara da aka sayar da su, to amma kayan da kudinsa ya tashi kana kuma ka sami wanda zai saya a cikin shekarar amma sai ba a sayar ba har zuwa karshen shekara dan neman kari, to wajibi ne ka ba da khumsin abin da ya karu na daga kudinsa lokacin da shekara ta cika.
Shekaru uku da suka wuce na bude shago da kudin da aka fitar masa da khumsi, kuma farkon shekarar khumsina shi ne karshen shekarar hijira ta shamsiyya, to lokacin da shekara ta cika sai ya kasance dukkan uwar kudin nawa suna hannun mutane a matsayin, bashi a daidai lokacin kuma ana bi na basussuka to ina so a min bayanin abin da ya hau kaina?
Idan har lokacin shigan shekarar babu komai a hannunka na daga uwar kudin ko kuma na daga ribar, ko kuma dukkan jimillar abin da ya saura na daga kudi da kayayyaki a cikin shagon dai- dai yake da uwar kudin da aka riga aka fitar masa da khumsi, to khumsi ba wajibi ba ne a gare ka, kana basussukanka da ke hannun mutane za su kasance riba ne ta shekarar da ka karbe su a cikinta.
A karshen shekara lissafin kudin kayayyakin da ke cikin shagonmu ya kan zama mana da tsananin wahala, to ta wace hanya za mu yi lissafinsu?
Wajibi ne a kayyade kudin kayyakin da ke cikin shagon ta duk wata hanyar da ta sauwaka ko da kuwa ta hanyar kintatawa ne dan lissafin ribar da aka samu a shekara domin a fitar musu da khumsi da ya wajaba.
Muna so ayi mana bayanin hanya mafi sauki ga ma'abucin shago wajen fitar da khumsi?
Farko ya yi lissafi da kuma kimanta abubuwan da ke hannunsa na daga kudi da kuma kayayyaki a dai-dai shigar shekaran, khumusinsa to sai ya kwatanta dukkan abin da 'ya lissafta da ainihin asalin uwar kudin, idan har akwai kari akan uwar kudin, to za'a lissafa ta a matsayin riba, dan haka khumsi ya hau kanta.

HADUWAR KUDIN DA KHUMSI YA HAU KANSA DA WANDA BAI HAU KANSA BA
Da kudin da khumsi bai hau kansa ba kamar kyauta da dai sauransu za su hadu da uwar kudi, to shin ya halatta a karshen shekarar khumsi a ware su daga uwar kudin, kana daga baya mu cire khumsin sauran kudin?
Babu matsala ga hakan.

HUKUNCIN AMFANI DA KUDIN DA BA'A FITAR MUSU DA KHUMSI BA
Shin khumsi ya hau kan gidan da aka gina shi da kudin da ba'a cire masa khumsi ba ? A bisa kasantuwan wajibci, to shin za'a fitar da khumsin ne gwargwadon kudinsa na wannan lokacin ko kuma dai-dai da kudin lokacin da aka gina?
Idan har gidan na zamansa ne ya gina da ainihin kudin da ba'a cire masa khumsi ba wajen sayen kayayyakin ginin da kuma kudin masu aikin to zai fitar da khumsin ne gwargwadon kudin gidan a halin da ake ciki, to amma da ya gina gidan ne da kudin bashi kana sai ya biya bashin da kudin da ba' a cire masa khumsi ba, to babu komai a gare shi sai dai khumsin wannan kudi da ya biya bashi da su.
Ni na kasance saurayi ne da nake rayuwa da iyayena, to mahaifina ya kasance ba ya fitar da khumsi da zakkan da suka hau kansa, har ma ya gina gida da kudi na riba a hakikanin gaskiya haramcin abincin da nake ci a fili yake, to bisa la' akari da cewa ba zan iya rabuwa da shi ba, dan haka nake so ayi min bayani kan abin da ya hau kaina daga hukunci?
Idan har kana da yakinin cewa kudin mahaifin naka sun hadu da kudin riba (kudin ruwa), ko kuma kana da masaniyar cewa ba ya fitar da khumsi ko zakka da suka hau kansa to haka ba zai iya tabbatar maka da haramcin abin da kake amfani da shi na dukiyarsa ba, to matukar ba ka da tabbacin haramcin abin, ba haramun ba ne ka yi amfani da shi, naam da za' ka samu yakinin haramcin abin da kake amfani da shi na dukiyar, to ba ya halatta a gare ka ka yi amfani da shi, sai dai idan rabuwa da mahaifin naka zai sanya ka cikin wani hali na kunci, to a wannan hali ya halatta ka yi amfani da dukiyar tasa, to amma wajibi ne ka dauki nauyin fitar da abin da ya hau wannan dukiya da kake amfani da ita na daga khumsi, zakka ko dukiyar wasu.
Idan har na kasance ban yi lissafin khumsi ba har na tsawon shekaru ta yadda har uwar kudin nawa suka karu, to sai daga baya na fara fitar da khumsin sauran kudin da ba uwar kudin na da ba, shin akwai wata matsala ga hakan?
Idan har a farkon shekarar khumsi dukiyar taka wani abu na khumsi ya hau kanta, ko da kuwa kadan ne, matukar dai ba ka yi lissafin su ba kuma ba ka fitar da abin da ya hau kansu na daga khumsi ba, to ba ka da hakkin amfani da wannan dukiya, da za ka yi amfani da ita ta hanyar saye da sayarwa kafin ka fitar da khumsinta, to wannan amfani naka ya zamanto amfani da kayan wani wanda yake bukatar izinin ma'abucin khumsin tukun, a daidai gwar gwadon kudin khumusin da ke ciki to bayan ba da izinin ma wajibi ne da farko ka fitar da khumsin dukkan kudin, kana ka fitar da khumsin ribar da ya karu a kan abubuwan masarufi da kake bukatuwa da shi na shekara.
Mu mun kasance muna mu'amala da mutanen da ba sa fitar da khumsi, muna saye da sayarwa tsakaninmu kana kuma sauran mu'amaloli kamar ziyarar juna da cin abinci duk tare, to mene ne hukuncin wannan mas'ala.
Idan har kana da yakinin kasantuwar khumsi a cikin dukiyar da kake mu'amala da su na saye da sayarwa ko kuma kake amfanuwa da ita yayin da kuke tare, to ba ya halatta a gare ku ku yi amfani da ita, dan kuwa wannan mu'amala taku ta kasance amfani da abin wani ne wanda yake bukatar izinin ma'abucin khumsin ko kuma wakilinsa a daidai gwargwadon khumusin da ke ciki tilas, sai dai idan barin mu'amala da su zai haifar maka da kunci, to a irin wannan halin ya halarta ku yi amfani da ita, sai dai biyan khumsin dukiyarsu da ka yi amfani da shi yana kanka.
Mene ne hukuncin jinkirta bayar da khumsin shekara (da ake ciki) har zuwa shekara ta gaba?
Bayar da khumsi na wajibi ko da yake yin haka kan iya zuwa bayan an riga an jinkirta shi har zuwa shekara ta gaba, sai dai ba ya halatta ya yi amfani da kudinsa da khumsi ya hau kansa matukar dai shekarar khumsinsa ta shiga, har sai idan ya fitar da khumusin da kuwa zai yi amfani da shi kafin fitar da khumsi kamar wajen sayen wasu kayayyaki ko fili da sauransu to bayan samun izinin yin mu' amala da dukiyar daga wajen ma'abucin khumsin, wajibi ne ya lissafa wannan kaya ko kuma fili da kudinsa na wannan lokacin kana ya fitar da khumsinsa.

SULHU DA KUMA MUDAWARA
Akwai wasu mutane da khumsi ya wajaba a kansu amma ba sa fitar da shi, inda a halin yanzu ba za su iya fitar da shi ba ko kuma fitar da shi zai yi musu wahala, to mene ne hukuncinsu?
Khumsi wajibi ba ya faduwa a kansu dan kawai fitar da shi zai yi musu wahala, face dai wajibi ne su fitar da shi ta duk wata hanyar da ta saukaka, ko da kuwa da yin mudawara ne tsakaninsu da majibincin khumsin ko kuma wakilinsa kan ya dinga bayarwa kadan kadan gwargwadon yadda zai iya.

MAJIBINCIN KHUMSI, WAKILANSA DA KUMA YADDA ZA' A SARRAFA SHI
Idan mutum ya kasance yana taklidi wa wani marja'i ne ba jagora (waliyyi amr- il- Muslimin) ba, to ga wani daya daga cikinsu ya wajaba ya ba da khumsinsa?
Wajibi ne a bayar da khumsi ga jagora, dan kuwa shi ne yake gudanar da al'amurran musulmai, sai dai idan fatawar mujtahidin da yake masa taklid ya saba wa hakan.
Masu taklidi ga marigayi Imam Khomaini (r.a) ga wa za su ba da khumsin dukiyarsu?
Za ku iya aiko da ita ga ofishinmu da ke Tehran, ko kuma ku ba da ita ga wakilanmu da suke sauran garuruwa wanda muka ba su izini.


BABIN JIHADI:
Mene ne hukuncin fara jihadi (jihadul -Ibtida'i) a lokacin buyar lmamuz zaman (a.s)? Kana kuma shin hakan yana halatta ga "waliyi amril muslimin" ya hukunta hakan?
Bai yi nisa ba ace hakan ya halatta ga mujtahidin da ya cika sharudda wanda ke gudanar da al'amurran musulmai idan har ya ga akwai maslaha ga hakan, kai wannan maganar ma ita ce karfaffa.
Mene ne hukuncin kare musulunci yayin da yake fuskantar hatsari ba tare da yardar iyaye ba?
Kariyar da ta wajaba ga musulunci da kuma musulmai bai dogara kan izinin iyaye ba, to amma duk da haka yana da kyau a kokarta neman yardar tasu ta duk hanyar da ta saukaka.
Da zamu dauka cewa kare addinin Musuluci na asali ya ta'allaka ne da zubar da jinin wani mutum, shin ya halatta gare mu mu aikata hakan?
Hakika zubar da jinin dan' Adam ba tare da hakki ba haramun ne kuma ya saba wa hukuncin addinin musulunci na asali, dan haka wannan kalami na cewa kare addinin musulunci na asali ya ta' allaka ga zubar da jinin wata rai mara laifi ba shi da ma' ana, to amma idan har abin da ake nufi da hakan shi ne yin jihadi fi sabilillah da kuma kariya ga musuluncin asali ta hanyar da la alla za' a iya kashe shi, to hakan yana da halaye kala- kala, idan har mutum da kansa ya gano cewa tushen addini yana fuskantar hatsari to wajibi ne gare shi ya kare musulunci, ko da kuwa akwai tsoron cewa za' a iya kashe shi.


BABIN UMURNI DA AIKI MAI KYAU DA KUMA HANI DA MUMMUNAN:

Idan har umurni da aiki mai kyau da kuma hani da mummuna zai kai ga dukan mai aikata mummunar aiki ko kuma takura rayuwarsa, ko kuma amfani da dukiyarsa, ko halakar da ita shin hakan yana halatta ba tare da izinin waliyul Amri ba ko kuma izinin Marja'i?
Wannan al'amari yana da matakai dadan-daban, to a sura ta gaba daya dai, idan dai har umurni da mai kyau da kuma hani kan mummunan aiki bai ta'allaka da jiki ko kuma sanya hannu akan dukiyar mai aikaita munkarin ba, to bai bukatar izinin wani mutum, face ma dai wannan alamari ne da ya wajaba kan dukkan mukallafai, amma a matakin da yake bukatar fiye da amfani da harshe to idan har hakan a guri ne da ake kula da tsari irin na addinin musulunci, wanda ake lura da wajibin nan na amr bil ma'aruf to al'amarin yana bukatan izinin jagora Waliyul amr, ko kuma hakan aiki ne da ya hau kan hukuma.
Idan har gudanar da umurni da kyakkyawan aiki da kuma hani da mummuna da ya shafi aiki mai muhimmancin gaske kamar kare rai ya zan bai yiwuwa sai da amfani da hannu wanda zai kai ga jin ciwo ko kuma ga kisan kai a wasu lokuta, to shin hakan ma yana bukatar izinin jagora ko Marja'i?
Idan har kiyaye rai da kuma kare afkuwar kisan kai ya ta'allaka ne ga daukan mataki na gaggawa, kuma kai tsaye to ya halatta, kana hakan ma wajibi ne saboda la'akari da kariya ga rai, hakan bai ta'allaka da izinin jagora ba ko umarninsa sai dai idan har kare rai zai rataya ga zubar da jinin wanda ya kawo harin, to hakan yana da halaye daban-daban yana yiwuwa hukuncin nasa ya bambanta.
Shin wajibi ne yayin da mutum yake so ya yi umurni da alheri da kuma hani da mummunan aiki ya kasance yana da karfin yin hakan? Sannan yaushe ne yake wajaba mutum ya yi umurni da kyakkyawa da kuma hani da mummuna?
Dole ne mai umurni da kyakkyawa da kuma hani ga munanan aiki ya kasance ya san kyakkawa da mummunan aikin, kana kuma ya tabbatar cewa mai aikata wannan (mummunan aikin) shi ma yana da masaniya kan hakan, amma duk da haka yake aikatawa da gangan ba tare da wani uzuri na shari'a ba.
Sannan umurni da kyakkawa da kuma hani da mummunan yana wajaba a gare shi ne idan har yana tsammanin umarnin ko hanin da zai yi yana da tasiri ga mutumin da ke aikata mummunan ko wanda ya bar kyakkyawan kana kuma shi kansa zai tsira daga cutarwa, wato sai ya auna ya gani cewa cutarwar da zai samu nawa take kana wane irin muhimmanci ne abin da zai hana din yake da shi ko kuma abin da zai yi umurni a aikata din, to bayan ya auna ya gani cewa sun dace sai ya aikata amma idan ba haka ba to ba wajibi ba ne.
Shin ya halatta mutum ya ki kula da umurni da kyakkyawan aiki da kuma hani da mummuna saboda tsoron kora daga wajen aiki?
(Kamar misalin shugaban ma'aikatar da, yake aiki a ciki yana aikata wasu munanan ayyuka ko kuma ya ba da daman aikatawa).
A shakali na gaba daya, idan har mutum yana tsoron afkuwar cutarwa gare shi yayin gudanar da umurni da kyawawan aiki da kuma hani da munana, to hakan ba wajibi ba ne a gare shi.
Wasu direbobi su kan sanya kasetocin da haramun ne jin su, duk kuwa da nasihohin da aka masa to amma ya ki ya cire dan haka muke so ka yi mana bayanin abin da ya kamata mu aikata a irin wannan hali?
Ba ya wajaba a gare ku da ku yi fiye da abin da ya wuce hani da baki hakan ma sai dai idan har duk sharuddan hani ga mummunan aiki sun samu a gare ku, in kuwa hani da baki bai yi tasiri ba, to wajibi ne ku nesaci sauraron kida da waka na haram, idan kuwa har wannan sauti na haram ya isa gare ku ba tare da son ku ba to babu komai a gare ku.
A wasu lokuta wasu mutane daga gidaje sukan sa wasu kasetoci na kida wanda ba mu san cewa shin halal ne ko haram, ba sannan su kure sautin har ya dami mutane, to mene ne abin da ya hau kan mutane dangane da hakan?
Bai halatta mutum ya shiga gidan mutane (dan yin hani ga mummunan aiki) ba dan kuwa umurni da kyakkyawan aiki da kuma hani da mummuna ya ta'allaka ne da gano kyakkyawan aiki da kuma mummunan kana da kuma mallakan sharuddansa.

YADDA AKE UMURNI DA KYAWAWAN AYYUKA DA KUMA HANI GA MUNANA

Wace hanya ce ya kamata da ya bi dangane da iyayensa da ba sa kula da ayyukan shari'a da suka wajaba kansu saboda rashin cikakken i'itikadinsu ga wajiban?
Wajibi ne ya yi musu umurini da kyakkyawan aiki da kuma hani da mummuna cikin tattausan murya tare da kuma kiyaye girmama su a matsayinsu na iyaye.
Dan uwana ba ya kula da ayyukan shari'a da kuma dabi'un kwarai, duk kuwa da nasihohin da nake masa amma ba su yi tasiri ba, to me ya kamata in aikata yayin da na gan shi yana aikata irin wadannan ayyuka?
Wajibi ne ka nuna rashin amincewarka ga irin wadannan ayyuka da suka sabawa shari'a, da kuma ci gaba da tunasar da shi ta duk wata hanya ta yan uwanataka da kake ga ta dace, to amma kada ka yanke zumuncinka da shi dan kuwa hakan ba ya halatta.
Shin kin amsa sallamar wanda ke aikata mummunan aiki dan tsawata masa ya halatta?
Kin amsa sallamar da nufin hani ga mummunan aiki ya halatta idan har haka din a wajen mutane ana ganin cewa tsawatarwa ne kana hani ne kan mummunan aiki.


MAS'ALOLI DABAN- DABAN:

Idan mu'amalar manyan malamai da azzaluman shugugabanni zai iya sanya su su rage zaluncinsu, shin yin hakan ya halatta a gare su ?
Idan har malami yana da tabbacin cewa mu'amalarsa da azzalumin (shugaba) zai iya hana aikata zalunci kana kuma zai yi tasiri wajen hana shi aikata munkari ko kuma ya ga wani lamari muhimmi da ke bukatar kulawa to babu wata matsala ga hakan.
Na yi aure tun shekarun baya da suka wuce, kuma ni na kasance mutum ne mai kula da addini, to amma abin bakin ciki matata ba ta kula da ayyukan addini sosai, a wasu lokuta kana bayan magana mai tsanani sai ta yi salla kuma ta sake bari, hakan yana damu na, don haka mene ne ya hau kaina a irin wannan hali?
Abin da ya hau kanka shi ne tsara hanyoyin da suka dace wajen gyara ta, da kuma nesantar duk wani aiki da bai dace ba, to amma ka sani cewa zuwa wajen tarurruka na addini da kuma kai ziyara ga gidajen wadanda suka damu da addini yana da tasiri mai girman gaske, wajen gyara.
Idan mutum ta wasu hanyoyi ya gano cewa matarsa -wacce suke da 'ya'yaye da ita-tana wasu ayyuka na boye da suka saba wa kame kai, sai dai ba shi da wata takamammiyar hujjar da zai tabbatar da hakan (kamar samun shaidar da ke shirye ya ba da shaida kan hakan), ta yaya mutum zai yi mu'amala da wannan mace tattare da cewa 'ya'yayensa za su rayu ne karkashin irin wannan mace? Kana yaya mutum zai yi mu'amala da irin wadannan mutane masu aikata wannan mummunan aiki da ya saba wa shari'a, idan har ya san hakan? Tattare kuma da rashin dalilai akansu ballatana ya kai su gaban shara'a?
Wajibi ne a nesanci mummunan zato da kuma dogaro akan dalilan zato, to amma yayin da ya tabbatar da faruwar haramun to wajibi ne ya hana ta ta hanyar tunasarwa da kuma nasiha da kuma hani kan munkari, idan kuwa hakan bai yi amfani ba, to sai a kai al'amarin ga kotuna na kwarai idan har akwai abubuwan da aka tabbatar da su.
Shin ya halatta ga mace budurwa ta taimaki saurayi wajen karatu da sauransu tattare da kula da wajiban shari'an musulunci?
Babu matsala ga hakan, amma ya kamata ayi gagarumin taka tsantsan daga irin waswasin shaidan, kuma wajibi ne a kula da hukumce -hukumcen shari'a yayin hakan kamar rashin kebancewa da mutum ajanabiyi.
Da za'a samu afkuwar almundahana da kuma rub da ciki a cikin Baitul mali, sai aka samu wani mutumin da yake ganin da zai hau wannan matsayi da ya hana faruwar wannan al'amari, to amma yiyuwar hakan ya ta'allaka da ba da cin hanci ga wani mutum dan su zabe shi, to shin yin hakan ya halatta?
Abin da ya wajaba kan mutanen da suka ga faruwar sabawa hukuncin shari'a shi ne hani ga munkari tare da la'akari da sharuddan hakan da kuma dokokin sharia, don haka ba ya halatta a ba da rashawa ko kuma aikata wani aiki da ya saba wa doka wajen hana faruwar fasadi, na'am da hakan zai faru ne a kasar da hukuncin musulunci ke gudana, to a nan wajibin mutane ba kawai ya kare a kan gazawarsu ga yin umurni da kyakkyawan aiki da hani da munkari ba ne, face dai wajibi ne a gare su kai al'amarin ga hukumar da abin ya shafa.
Mene ne abin da ya wajaba kan samari muminai da suke makarantar da take ha?e da mata dangane da irin fasadin da ke faruwa a wajen?
Wajibi ne a gare su tare da kare kansu daga fadawa cikin fasadin su tsaya da umurni da kyakkyawan aiki da kuma hani da munkari, idan har suna da ikon hakan da kuma sharuddan hakan.



MU'AMALA:

SABODA MUHIMMANCI DA KUMA DADA SAUKAKA WA MAI KARATU, MUN RABA WANNAN BANGAREN ZUWA KASHI DABAN-DABAN DON SAUKIN SAMU.
DON HAKA SAI KA MATSA WANNAN ALAMA DON GANIN BANGAREN MU'AMALAR. A SHA KARATU LAFIYA.


Matsa Wannan Alama Don Komawa Sama