FATAWOYIN JAGORA KAN MU'AMALOLI DABAN-DABAN


Zabi Maudhu'in Da Kake So, Don Ganin Abin Dake Cikinsa












Sanao'iDa Kasuwancin Da Bai Halatta Ba Karban Ladan Aiki Kan Abin Da Yake Wajibi
Hukumcin Kide-Kide Da Wake-Wake Hukumcin Rawa
Hukumcin Yin Tafin HannuHukumcin Hoto Da Fina-Finai
Hukumcin Shirya Wasan Kwaikwayo Da Fina-Finai Na SinimaHukumcin Zane Da Sassaka Hoto
Hukumcin Tsafi, Rufa Ido Da Kiran AljannuHukumcin Shan Magani Don Hana Daukan Ciki
Hukumcin Zubar Da CikiHukumcin Shigar Da Ciki Ta Hanyar Na'ura
Hukumcin Canza Halitta Daga Mace A Koma NamijiHukumcin Fede Mamaci Don Nufin Yin Bincike Ko Cire Wata Gaba Tasa
Hukumce-Hukumcen Da Suka Shafi Ganin Likita Da Yin MaganiHukumcin Yin Kaciya
Hukumcin Neman Ilimi Da Kuma Koyar Da Shi Hukumce-Hukumce Kan Karatun Likitanci
Hukumcin Mu'amala Da Wadanda Ba Musulmi Ba Hukumcin Tufafin Da Abin Da Ake Sa Wa Wanda Yai Fice
Hukumcin Kwaikwayon Kafirai Da Kuma Yaryada Al'adunsu Hukumcin Hijira Da Neman Mafaka Ta Siyasa
Hukumcin Kan Tsegumi Da Leken Asiri Da Bayyanar Da ShiHukumcin Shan Taba Da Kuma Miyagun Kwayoyi
Hukumcin Aske Gemu Da Gashin BakiHukumcin Halartar Wuraren Sabo
Hukumcin Neman Tsari (Kare Kai) Da Neman IstikharaHukumcin Raya Ranaku Muhimmai A Addini
Hukumce Hukumcen CinikiHukumci Kan Riba (Kudin Ruwa)



SANA'OI DA KASUWANCIN DA BAI HALATTA BA:

Shin ya halarta a sai da aladan jeji, wanda hukumar mafarauta ta farauto ko kuma manoma suka farauto shi domin kariya ga wajen kiwo ko kuma gonaki, to ya halarta a sai da shi domin ayi naman gwangwani da namansa a kai shi kasashen da ba na musulmi ba?
Ko kadan bai halarta a yi cinikin naman alade ba a matsayin abincin mutum ko da kuwa ba musulmi ba ne, sai dai da za a ce akwai wani amfani da masu hankali ke iya karba wanda kuma ya halarta wanda kuma ake iya dogaro a kai kamar amfani da shi dan yin abincin dabbobi, ko kuma dan yin man da a ke yin sabulu da shi ko makamancin haka a wannan hali ba abin da zai hana a yi cinikinsa saye ko sayarwa.
Shin ya halarta a yi aiki a maaikatar da ake yin naman gwangwani da alade, ko kuma yin aiki a gidajen disko da wurare na fasadi? Kana mene ne hukuncin kudin shiga da yake tattare da hakan?
Sam bai halarta a sharia ba ya kasance alamura na haram su ne aikin da mutum yake yi a matsayin sana a, irin sai da naman alade ko giya ko gina gidan disko ko kula da shi ko gina dandalin fasadi da alfasha ko caca da shan giya da dai makamantansu.
Duk wadannan abubuwan bai halarta a mai da su sana a ba, kana bai halarta a ci kudin ba a matsayin ladan aiki.
Shin sayar da giya ko naman alade ko kuma wani abin da bai halarta a ci ba, ya inganta ga wanda ke ganin cewa ba haram ba ne ko kuma ya inganta a ba shi kyautarsa?
Kyauta ko sayar da abin da bai halarta a ci, ko a sha ba, in har da nufin ci ne ko kuma da nufin sha, ko kuwa ya san cewa mai sayan zai saya ne domin ya ci ko ya sha to yin haka bai halarta ba, ko da kuwa shi mai sayen yana ganin halaccin abin.
Shin yana halarta a sai da jini ga mutumin da zai yi amfani da shi?
Babu laifi a sai da jini domin yin amfani da shi idan har manufa ce wanda masu hankali suka yarda da ita.
Shin ya halarta aikin mutum ya kasance kone mutanen da suka mutu, wadanda ba musulmi ba, ya kuma karbi Lada a kan wannan aikin?
Babu wata hanya wacce ta haramta kone gawar da ba musulmi ba, dan haka ba abin da zai hana ya zamo sanaar mutum shi kone gawar da ba ta musulmi ba, kuma ya karbi ladan aikin konewar.


KARBAN LADAN AIKI, KAN ABIN DA YAKE WAJIBI:

Mene ne hukuncin albashin malaman da suke koyar da(fikhu) ko usulu a cikin makarantun horar da alkalai?
Wajibcin koyar da wajibi na (kifaya) bai hana halaccin karban albashi ga wanda ya koyar da fikihu ko usulul fikih, musamman idan albashin ya zama a sanadiyyar tahowa wurin koyarwar da kuma kula da ajin.
Shin ya halarta a karbi albashi domin limancin sallah ko kuma wa'azi da shiryaswa na addini a karkashin wata muassasa?
Babu laifi a karbi ladan zuwa da dawowa da kuma wahalhalun da mutun ya yi wanda ba wajibi ba ne ashara'a ya yi shi.
Shin ya halarta mutum ya karbi ladan wankin mamaci?
Bai halarta mutum ya karbi lada ba dan saboda shi wankin mamaci, domin kuwa shi wankin mamaci musulmi aiki ne na ibada wacce ta ke matsayin wajibi na (kifaya).
Ya halatta asharaa a karbi lada domin daura aure da mutum ya yi?
Babu laifi cikin hakan.


KIDE KIDE DA WAKE WAKE:

Mene ne bambancin kida wanda ya halarta da wanda bai halarta ba?
Dukkannin kidan da mutane ke -yi masa kallo irin na batsa da wasan da bai kamata ba ko kuma ake yin sa a wuraren wasanni da suka dace da wuri na wargi da kuma bata to irin wannan kida (waka) shi ne ya haramta kuma babu bambanci tsakanin na da ko kuma na zamani da sauransu- kuma gano wannan yana komawa ne ga shi mukallafin amma duk kidan da bai kasance irin wannan ba to ba haram ba ne.
Menene hukuncin jin kaset Wacce wata kungiya ta musulunci take ganin ba laifi ba ne aji?kana kuma mene ne hukuncin sauraron abubuwan kida Misalin-Jita, ko gurmi, ko kuma fiyano?
Halaccin jin irin wadannan kasa kasen yana dai dai da yanda mai jin nasu ya fahimci abin, idan yana ganin cewa abu ne wanda bai tattare da kide, kide da wake wake na holewa wanda kuma a ke yin su a wuraren wargi da batsa to ba laifi ba ne ya saurari irin wannan, amma dan kawai wata kungiyar watsa abubuwan musulunci tana ganin cewa ba laifi ba ne ta watsa kide kide to bai zamo hujja ga mutum ashara'a ba kana ba ya halatta a yi amfani da kayan kidan cikin kidan batsa wanda ya dace da wuraren wasanni da sabo, da kuwa za'ai amfani na halal da irin wadannan kayan kidan kan manufofi na masu hankali to shara'a ba ta hana ba, gane hakan kuwa yana hannun mukallafi.
Shin kida da kwarya ko kuwa da kwano da wasu ababen da ba na kida ba a yayin kai amarya dakinta ya halatta, mene ne kuma hukuncinsa lokacin da sauti ya fita har zuwa gurin da majaze suke ji?
Halaccin hakan yana dangane da yadda ake amfani da su ne, to idan ya zama irin yadda aka saba ne a bukukuwan aure na alada , to duk abin da ba a kira shi da sunan wargi ba, kana kuma bai kunshi abubuwan barna ba babu laifi cikin jin sa.
Mene ne hukuncin mata su yi mandiri a lokacin bikin aure?
Bai halatta ayi amfani da kayan kide kide domin rera kida na wasa ba, amma babu laifi ayi amfani da shi cikin wakokin da ake yin sa na kai amarya.
shin ya halatta ayi amfani da ababen kidan a dararen angwanci, ldan kuma ya halatta mene ne iyakar halaccin ga mata da maza?
Ba laifi mata su rera waka a wuraren da suka kebanci bikin aure kuma ba laifi ba ne su yi amfani da kayan kide kide a lokacin rera wakar a irin wadannan wurare muddin dai bai ketare yanda aka saba ba, amma idan ba wadannan wurare ba to sam bai halatta ba.
shin ya halatta a saurari wakoki a wurin bikin aure ta hanyar rediyo ko kuma kaset?
Bubu laifi a saurari wakoki a bikin daukan amarya (matsawar babu abu na haram).
Ina aiki a wurin da mai wurin kullun yana sa kaset na kade kade da bai halatta ba don haka sai na ga ba yanda zan yi sai na ji, to shin ya halatta gare ni ko a'a?
In har a cikin kaset din akwai wasu wakoki na batsa da suka dace da guraren wargi ko bata ko sabo to bai halatta kai ka yi shiru domin ji ba sai dai in har ya zan cewar nan ne kadai wajen aikinka ba laifi ka je wajen aikinka kuma ka ci gaba da aikinka, illa kawai bai halatta ba ka yi shiru ka saurara dan jin wannan wakokin, ko da ya zo ga kunnenka ba da nufin saurara ba.
Mene ne hukuncin jin wakoki na wargi na (rakashewa) wanda suka fito daga kasashen yamma? Kana mene ne hukuncin raba shi wa mutane?
Abin da bai halatta a saurare shi ko a yi amfani da shi ba na daga wakoki na wargi wadanda suka dace da guraren wargi da bata, to irin wadannan wakoki babu bambanci cikin haramcinsu shin da wane yare aka yi su kuma ko da daga wane kasa (ko gari) suka fito, saboda haka saye da sayar da su ko kuma yada su ko sauraransu dukkan haka bai halatta ba matsawar dai sun kunshi wakoki na wargi wanda suka haramta.
Menene hukuncin jin sautin mace cikin wake ko makamantansa, tare da rerawa ta yanda yara da manya mata da maza ko wanda ba muharrami ba za su iya ji?
In har sautin macen ba ta karya shi zuwa ga wakar rakashewa ba kana wanda yake jin ba yana nufin jin dadi ko aukawa cikin haram ba ne sannan hakan bai zan abu ne da zai jawo wani barna ba, to babu laifi cikinsa .
Shin wai gaskiya ne da ake cewa kida yana da asali a cikin Musulunci, kana wai ta hanyar kida za'a iya saduwa da falarar Allah (WATO KIDAN SUFANCI)?
Kida bai daga cikin hanyoyin samun saduwa da falarar ubangiji, ko kuma ace da shi ne za' a gano girman halittar ubangiji ko rabauta ta hanyar saninsa mahalicci, hakan ba zai taba yiwuwa ba ta hanyar kida.
Ya halatta a rera wakar rakashewa ba tare da kida ba?
Wakar rakashewa dai haramun ce ko da kuwa an yi ta ba tare da kida ba.
Mene ne hukunci cinikin kayan kida kana kuma a wane wuri ne ake yin amfani da shi?
Ba laifi a yi cinikin kayan kida wacce za'a iya yin amfani da ita ba kawai a bangare na batsa ba, to irin wannan kayan kidan ya halatta a yi cinikinsu dan aiwatar da manufofi na halal, kuma ba laifi a saurare su.
Ya hatatta a karanta alkur ani ko addu'a ko kiran sallah da irin sautin da a ke wakoki na rakashewa da shi?
lrin sautin da aka kebance shi domin wakoki na batsa da rakashewa, bai halatta a karanta Alkur ani, ko kiran sallah, ko Addu'a da shi ba.
A yanzu ana yin amfani da kida don maganin wasu cututtuka na rai kamar bakin ciki da faduwar gaba da abin da ya shafi sha awa ko rashinsa, mene ne hukuncin haka?
Idan har likita kwararre, amintacce ya ce magance ciwon ya tsaya ne kan haka to ba matsala ga hakan amma gwargwadon yadda za a warkar da ciwon.
Menene hukuncin yin amfani da kayan kida wanda daliban makaranta suke yi karkashin hukumar tarbiyya ta makaranta?
Kayan kidan da mutane ke ganin cewar za'a iya yin amfani da su wuraren da ya halatta to yana halatta a yi amfani da su, amma kuwa wanda ake ganin ba za'a iya yin amfani da su ba a wuraren da ya halatta to ba su halatta a yi amfani da su ba.
Ya halatta a karbi ladan yin rukodin din kaset din da bai halatta a ji ba?
Kaset din da bai halatta a ji ba to rikodin dinsa ko ladansa bai halatta ba.


HUKUNCIN RAWA :

Shin ya halatta a yi rawa ta al'ada a wuraren biki, mene ne kuma hukuncin halartar irin wannan wurin?
Yin rawa ta yanda ba za ta motsa sha'awa ba ko ba za ta janyo fasadi ba ba kuma zai kawo aikata haram ba to ba laifi da irin wannan rawar Amma halartar wuraren rawa in har zai karfafa wasu dan su aikata haram ko kuma ya zan yana tattare da haram to bai halatta ba, idan kuwa ba haka ba ya halatta.
Mene ne hukuncin rawa ta al'ada ga maza a tsakaninsu ko kuma ga mata a tsakaninsu ko kuma namiji a tsakanin mata, ko kuma mace a tsakanin maza?
Idan har ya kasance yadda zai motsa sha'awa ne ko zai janyo aikata haram ko barna ko kuma mace tsakanin mazan da ba maharramanta ba, hakan bai halatta ba, haramun ne.
Shin mace ta yi wa mijinta rawa ko kuma miji ya yi wa matarsa rawa ya halatta?
Mace ta yi wa mijinta rawa ko miji ya yi wa matarsa rawa halas ne muddun dai babu aikin haram a ciki.
Menene hukuncin rawar yaron da bai balaga ba ko yarinyar da ba ta balaga ba cikin maza ko mata?
Duk wanda bai balaga ba ba shi da takalifi sai dai bai kamata ba ga wanda suka balaga su karfafa shi ko ita kan yin rawa.
Mene ne hukuncin gina cibiyar koyar da rawa?
Gina cibiyar koyar da rawa da yada ta abu ne wanda ya saba wa tsarin hukumar Musulunci.


HUKUNCIN YIN TAFIN HANNU :

Shin ya halatta mata su yi tafi wurin taron farin ciki kamar biki, ko suna ldan ya halatta mene ne hukumcin su yi shi da karfi yanda wasu mazan za su ji?
Babu laifi cikin yin tafin da aka yi shi daidai gwargwado ko da kuwa ya kai wasu maza daban su ji shi muddun dai bai kunshi barna ba.
Mene ne hukumcin tafin da'ake yin sa a wuraren maulidi ko kuma tunawa da ranar haihuwar ma'asumai, dan nuna farin ciki wanda ake gabatar da shi a cikin masallatai ko makarantu ko wuraren, ibada?
Babu laifi cikin kowanne irin tafi a kan kansa muddun dai bai wuce hankali ba sai dai abin da ya fi shi ne a kawata wurin da salati ga manzo da kabbara musammam ma wanda ake yi cikin masallatai da wuraren ibada ba dan komai ba sai don samun ladan salati da kabbarar.


HUKUNCIN HOTO DA FINA FINAI :

Mene ne hukuncin kallon hoton wata mace daban mara lullubi? Mene ne kuma hukuncin kallon mace ta telabijin?shin akwai banbanci tsakanin musulma da wadda ba musulma ba? Ko kuma tsakanin wanda aka kalla yayin da ake watsa shirin kai tsaye ko kuma wanda ba na kai tsaye ba.
Kallon hoton wata mace daban bai zamo daidai da kallon zatin ita macen ba, dan haka babu laifi sai dai in da aka kalla da nufin yaudarar rai ko fadawa fitina, ko ya kasance hoton na musulma ce wacce ya san ta, lhtiyadi na wajibi shi ne kar mutum ya kalli hoton wata mace daban ta telabijin wanda ake nunowa kai tsaye lokacin da ake shirin, amma ba laifi a kalle ta ba da nufin wani abu ba idan shirin ba na kai tsaye ba ne matsawar ba tsoron fadawa haram ko fitinuwa.
Shin akwai laifi cikin kallo ko jin shirye shiryen abubuwan dariya ta hanyar rediyo ko telabijin?
: Ba wani abu cikin kallo ko jin shirye shiryen ban dariya, amma kida wanda yake na wargi da ya dace da wuraren wasa da kuma sabo to bai halatta ba.
Na dauki hotuna a wuraren biki ba tare da cikakken hijabi ba kuma wadannan hotunan a yanzu suna hannun abokaina da yan uwana, shin dole ne na karbo su?
: In har zaman hotunan a hannunsu ba zai haifar da barna ba ko kuma ko da ya haifar amma ba ta hanyar ki ne aka ba su ba, ko kuwa dawo da su zai yi wahala to ba wani abu a kanki.
Shin akwai laifi cikin yi wa hoton lmam ko shahidai sumba, bayan kuma ba muharramammu ba ne?
Hotunan ajnabai kowanne iri ne ba su zamo daidai da zatin su mutanen ba dan haka babu wani laifi cikin yi wa hotunan, mazan da ba muharramai ba sumba da nufin girmamawa ko neman albarka ko baiyanar, da kauna ln har hakan bai tare da wata manufa daban da za ta haifar da fitina.
Ya halatta a kalli hotunan matan da suke tsirara ko dab da tsirara wadanda ba'a san su ba ta hanyar fina finan sinima ko wasu daban?
Kallon fina finai ko hotunan wasu daban bai zamo dai dai da kallonsu kai tsaye ba dan haka babu laifi a shara'a muddun dai ba'da nufin sha'awa ba kuma hakan bai janyo wata barna ba, sai dai da yake cewa kallon hoto tsirara mai motsa shaawa bai rabuwa da kallo mai motsa sha'awa mafi yawan lokaci dan haka yana zamowa shimfida ne na daukar zunubi to saboda haka haram ne.
Shin ya halatta mace ta kalli kokawa ta maza?
Idan kallon ya zamo ido- da- ido ne a filin kokawar ko kuma ta talabijin ne a lokacin da ake yin kokawar kai tsaye ko kuma tana kallo da nufin jin dadi, da tsoron fadawa haram ko kuma ana gudun fitina da barna cikin kallon to bai halatta ba, amma in ba haka ba ya halatta.
Mene ne hukuncin mace ta dauki hoto ba da hijabi ba a tsakanin muharramanta bayan kuma cewa wasu daban za su iya ganin hoton a lokacin da ake wanke shi?
Idan har wanda zai dauke ta hoton muharraminta ne to ba laifi ya dauke ta kana kuma idan wanda zai wanke hoton bai san ta ba shi ma ba laifi.
Mene ne hukuncin yin hotuna da sayar da su wadanda ake cewa na Ma'aiki ne ko kuma Imam Ali ko lmam Husain da nufin ajiye su a ofisoshi?
Hakan bai haramta ba a sharia muddun dai ba su kunshi abubuwan da zai janyo wulakanci gare su ba, kana kuma bai saba wa matsayinsu ba.
Mene ne hukuncin karanta littattafai da wakoki na batsa wadanda suke motsa sha'awa?
Wajibi ne a nesance su.
Mene ne hukuncin kallon gashin kai ko kirjin mace ta hanyar talabijin?
Ba laifi in dai har kallo ne kawai wanda bai tattare da gudun fitina ba kuma barna muddun dai ba lokacin da ake shirin kai tsaye ake nuna ta ba.
Shin ya halatta masu aure su kalli fim din da yake motsa sha'awa?
In har za a yi kallon da nufin motsa sha'awa ko kuma zai janyo sha'awa to bai halatta ba.
Mene ne hukuncin ma'aurata su kalli fim din da yake koyar da yadda ake kwanciya?
Bai halatta a kalli irin wannan fim din ba wanda bai rabuwa da kallo mai motsa sha'awa.
Shin ya halatta a motsa sha 'awa ta hanyar kallon bidiyo?
Bai halatta a motsa sha'awa ba ta hanyar kallon bidiyo.


HUKUNCIN SHIRYA WASAN KWAIKWAYO DA FINA FINAI NA SINIMA :

Shin ya halatta ayi amfani da kayan malamai ko Alkalai cikin finafinan sinima? Kuma ya halatta a kwaikwayi fina finan addini da na manyan bayin Allah wanda suka wuce da kuma wadanda ake zamani da su tare da kiyaye matsayinsu da matsayin addini da nufin fito da martabar addini ko ci gabansa ko bayanin irin abin da ake nufi, da karantarwa da kuma kyawawan dabi'u da kuma halaye na addinin musulunci da kuma yin raddi kan gurbataccen ci gaba, da kuma rashin tarbiyya?
Idan aka yi duba da cewa sinima wani tsari ne na wayar da kai to sai mu ga dukkannin wani shirye shirye ko nuna hoto wanda za'a iya samun amfanin tarbiyyantar da matasa da wasunsu ko watsa ci gaban musulunci ta hanyar nuna sifar wani malami tare da kayan jikinsa ko wasu manyan magabata to duk haka ba laifi, sai dai yana zamowa dole a kare matsayinsu da tufafinsu kada'azo da abin da zai iya janyo musu zubewan mutunci kuma dole ne a lura da cewa ba a yi shiri da ya saba wa musulunci ba.
Mene ne hukuncin namiji ya saka kayan mata ko mace ta saka kayan maza, domin shirya wasa ko fim? Kana kuma mene ne hukunci mace ta kwaikwayi muryar maza, ko kuma maza su kwaikwayi muryar mata?
Sanya kaya ko kwaikwayon murya a matsayin wasa ba laifi ba ne a yayin kamanta yanayin shi wanda ake kwaikwaya idan hakan bai zama yadda zai kawo barna ba.
Mene ne hukuncin mace ta yi amfani da mai ko kayan ado domin yin ado cikin shirya fim wanda wasu mazan daban za su gani?
Idan har mace da kanta ne za ta yi adon ko kuma mata ne za su yi mata ko muharraminta kuma idan babu abin da yake barna a ciki to ya halatta, ln ko ba haka ba haram ne .


HUKUNCIN ZANE DA SASSAKA HOTO :

Mene ne hukuncin yin yar tsana da sassaka ko zanen abu mai rai kamar tsururruka ko dabbobi ko dan adam? Mene ne kuma hukuncin cinikinta, mallakanta da kuma yin wasan kwaikwayo da su?
Babu laifi cikin daukan hoto ko sassaka abu ko zana shi, muddun dai ba abu mai ruhi ba ne, kana ma babu laifi cikin daukan hoto ko sassaka ko zana abu mai ruhi muddun dai ba a yi shi yadda zai zama mai gangan jiki (da inuwa) ba ko kuma ba a yi shi kammalalle ba, amma yin mutum-mutumi na dan Adan ko na dabbobi bisa surarsu kamila tare da gangar jiki to wannan akwai matsala a cikinsa ko da me aka yi shi, to sai dai kuma babu laifi wajen yin ciniki ko mallakar hotuna da mutum-mutumi, kana babu laifi a yi wasan kwaikwayo da su.
Mene ne hukuncin zana wasu wurare na kissoshin Al kur'ani ga yara kamar a nemi su zana kissar Maabuta giwaye, ko yanda kogi ya tsage ga Annabi Musa da wasunsu?
Ba laifi a kan hakan sai dai kuma wajibi ne duk abin da za su kawo shi ya zama gaskiya ne, kana kuma su nesanci yin bayanin abin da babu shi ko kuma abin da zai rage darajarsu.
Mene ne hukuncin yin abubuwan ado bisa sura ta mutum-mutumi? Shin kuma abin da aka yi surar wannan abin da shi shi ma yana da tasiri a haramcin?
Bai halatta ayi mutum-mutumin wani abu mai ruhi ba, kana babu bambanci shin an yi shi da ababen yin mutum-mutumi ne ko kuwa da ababen yin kawa da wasunsu.
Mene ne hukuncin tsage tsage wanda wasu mutane suke yi akan jikinsu ta yanda ba zai bace ba? Shin hakan za a kirga shi cikin garkuwa da yake kare fata ta sadu da ruwan wanka ko Alwala?
Yin tsage tsage ba haram ba ne kana kuma alamarsa wacce take karkashin fata ba ta da wani tasiri na hana saduwar ruwan wanka ko Alwala ga fata, don haka alwala da kuma wanka suna inganta tare da hakan.


HUKUNCIN TSAFI DA RUFA IDO DA KIRAN ALJANU :

Mene ne hukuncin koyo ko koyarwa ko kallon rufa ido ko wasanni da suke da ban mamaki ta hanyar saurin hannu (zafin nama)?
Koyo ko koyar da rufa ido bai halatta ba, amma wasannin ban mamaki wanda ake yi da taimakon zafin nama ko saurin hannu kuma ba' a kidanya ta rufa ido babu laifi.
Shin ya halatta a koyi ilimin Hatimi ko bugun kasa ko makamantansu na daga ilmummukan da suke ba da labarin abubuwan da suke a boye?
Abin da ke hannun mutane na wadannan ilmummuka cikin wannan zamanin galibinsu ba ababen dogaro ba ne, ko kuma abin da rai zai nitsu da su na daga labarurrukan gaibun da suke fade, amma kuma ba laifi a nemi ilimin hatimi ko bugun kasa ta hanya ingantacciya amma da sharadin in barna ba ta shiga ba.
Shin ya halatta a san sihiri a kuma yi aiki da shi, ko kuma a kirawo Aljani ko rauhani ko mala'ika?
Shi dai sihiri haram ne hakanan kuma saninsa, sai dai in ya kasance dan wata bukata ce ta sharia wacce masu hankali suka yarda da ita amma kiran rauhani, ko mala ika, ko aljani, idan mun dauka yana inganta kana kuma gaskiya ne to yana sabawa da sabanin bukatu ko yanayi ko hanyoyi.
Mene ne hukuncin muminai su je wurin mutane masu yin magani ta hanyar yin amfani da rauhanai ko kuma aljanu tare da yakinin cewa aikin alheri kadai suke aikatawa.
Yin haka a kan kansa bai da laifi in har da gaske akwai waraka a cikin hakan amma ta hanyoyin da shari'a ta halatta.
Shin ya halatta a rika buga kasa a matsayin sana'a?
Sam bai halatta ba.


HUKUNCIN DA YA SHAFI SHAN MAGANI DAN HANA DAUKAN CIKI:

1. Ya halatta mace mai lafiya ta yi amfani da magani dan hana daukan ciki zuwa wani lokaci?
2. Mene ne kuma hukuncin yin amfani da maganin nan mai hana daukan ciki mai suna (I.U.D)? Wanda har yanzu kuwa an kasa gane ta yaya ne yake hana daukan ciki, illa kawai an san cewa yana hana shigar maniyi mahaifa?
3. Kana shin matsalolin yau da gobe na tattalin arziki suna halatta a sha maganin da zai hana daukan ciki na har abada?
4. Ko kuwa hakan yana halatta ne saboda cuta wacce ake tsorace wa ran mai cikin?
5. Haka kuma dai shin yana halatta mata su ki daukan ciki na har abada irin mata wadanda haihuwarsu za ta taimaka wajen samar da yaran da suke da cututtuka na gado wanda zai shafi jikinsu ko ruhinsu?
1. Ba abin da zai hana mace ta sha magani dan hana daukan ciki na dan wani lokaci muddun dai da izinin mijinta.
2. Bai halatta ayi amfani da magani ba wanda aikinsa shi ne zubar da ruwan maniyi bayan ya riga ya shiga mahaifa, ko kuma zai janyo a kalli al'aura ko taba ta, irin wanda suka haramta.
3. Rashin abubuwan masarufi na yau da gobe ko yawan 'ya'ya ko abin da ya yi kama da haka bai kamata mutum ya kula da shi ba yanda ta dalilin hakan zai hana wa kansa ciki na har abada.
4. Ba laifi mutum ya hana ciki dan gudun abin da aka ambata, kai yin ciki bai ma halatta ba in har zai janyo hadari cikin rayuwar ita uwar jinjiri, sai dai idan ya faru ne ba da zabi ba.
5. Ba abin da zai hana hakan in har akwai manufa ta masu hankali a ciki kana kuma hakan ba zai jawo cuta sosai ba sa'annan ya kasance da izinin miji.


HUKUNCIN ZUBAR DA CIKI :

Shin ya halatta a zubar da ciki saboda matsalolin yau da gobe na tattalin arziki?
Sam bai halatta a zubar da ciki ba dan matsalolin yau da gobe na abin da za'a ci.
Farkon daukan ciki sai likita ya gaya wa mai ciki bayan bincike da ya yi cewa akwai hatsari a tare da ita muddun ta bar cikin, kana ma za'a haifi yaron da illa, dan haka likitan sai ya sa a zub da cikin shin yin hakan ya halatta? Shin kuma dai yana halatta a zubar da ciki kafin busa masa rai?
Dan gudun haihuwar yaro da illa bai halatta zub da ciki a shari'a ko da kuwa ba'a busa masa rai ba, amma tsoron lafiyar uwa da ci gaban rayuwarta sanadiyyar ciki in har likita ya yi nuni da hakan wanda yake amintacce kuma kwararre to ba laifi a zubar in har ba'a busa masa rai ba.
Shin ya halatta a zub da maniyyin da ya shiga cikin mahaifa kafin ya zama jini, wanda hakan ya kan kai kamar kwana ar'ba'in, kana wane maniyyi ne ya haramta a zubar da shi? Lokacin da ya shiga mahaifa ne? Ko lokacin da ya zama gudan jini ne? Ko lokacin da ya zama tsoka Ko lokacin da ya zama kashi kafin busa rai?
Bai halatta a zubar da maniyyi ba bayan ya shiga mahaifa ko a zubar da ciki cikin dukkan wadannan halaye bai halatta.
Mene ne hukuncin zubar da ciki akan kansa? Kana kuma mene ne hukumcin zubar da shi lokacin da ya zama hadari cikin rayuwar uwa? Idan ya halatta shin akwai bambanci da wanda aka busa wa rai da wanda ba'a busa wa ba.
Zub da ciki haram ne a shara'ance, bai kuma halatta sai in har ya kasance hadari cikin rayuwar uwa to, ba laifi a'irin wannan hali a zubar da shi kafin shigar rai, amma bayan shigar rai bai halatta ba ko da kuwa hadari ne ga rayuwar ita uwa sai dai idan kuma rashin zub da shi din zai kawo rasuwarsu gabaki daya, kuma ba zai yiwu yaron ya rayu ba ko ta kaka sai dai uwar za ta iya rayuwa saboda dalilin zubar da shi.
Mace ce ta zubar da cikinta na zina wanda ya kai wata bakwai da umarnin babanta shin za ta biya diyya? In har za'a biya diyya waye zai biya daga cikinsu? Kana ga waye za a ba da diyyar? Sannan nawa ne abin da za'a biya a daidai wannan lokacin bisa fatawarka?
Haram ne a zubar da ciki ko da kuwa na zina ne, umarnin uba bai kau da laifin zubar da shi dan haka idan ta aikata ko ta taimaka aka aikata dole ne ta biya diyya, amma akwai maganganu kan yawan adadin abin da za'a bayar illa ihtiyat a nan shi ne yin sulhu, kana diyyar tana kasancewa cikin hukuncin dukiyar gadon mutumin da bai da magada.
Nawa ne diyyar cikin wata biyu da rabi wanda aka zubar da gangan? Kuma waye ya kamata a ba wa diyyar?
Idan ciki ya zamo gudan jini aka zub da shi diyyarsa dinari arba'in ne idan kuma har ya zama tsoka dinari sittin ne idan kuma ya yi kashi wanda ba nama dinari tamanin, kana wannan diyya ana ba da ita ne ga wanda zai gaji jinjirin bisa marhalolin gado sai dai wanda ya zubar da cikin bai gadan komai a cikinta.


HUKUNCIN SHIGAR DA CIKI TA HANYAR NA'URA:

Shin ya halatta a shigar da ciki ta hanyar na'ura in har maniyyin na ma'aurata ne aure kuma na shari'a? In ya halatta to shin wani likita ajanabiy zai iya yin wannan aikin kana yaron da aka haifa'dan ma auran ne, idan bai halatta ba shin in yin hakan shi zai kare auren nasu zai halatta ayi?
Ba abin da zai hana yin wannan aiki akan kansa illa dai kawai a nesaci abubuwan da suke haram dan haka bai halatta ba wani namiji daban ajanabiy ya dau nauyin wannan aikin in har yin aikin zai janyo tabawa ko ganin abin da bai halatta ba kana kuma dai dansu ne muddun dai maniyyin nasu ne.
Da za'a sami maniyyin mutum tun yana raye sai aka zura shi ta hanyar na'ura cikin mahaifar matarsa bayan ya rasu? Tambayar farko a nan ita ce shin yin hakan ya halatta? Tambaya ta biyu shin dan zai zamo dan mijin a shara'a? Tambaya ta uku shin wanda aka haifa zai gaji mai maniyyin?
Yin hakan ba laifi ba ne kana dan kuma na mai maniyyin ne da wacce ta haife shi, sai dai kuma ba zai gaji wanda ya haife shi ba.
Shin ya halatta matar mutumin da ba ya haihuwa a sanya mata maniyyin wani mutum daban a cikin mahaifarta?
Babu hani cikin yin haka in har an nesanci abubuwan da suke haram misalin kallo ko tabawa ko makamantansu, sai dai kuma in an sami da ba na mijinta ba ne dan wanda aka zuba mata maniyyinsa ne, amma yaron dan matar ne, a nan ya kuma kamata a yi ihtiyat domin kubutar da kai cikin harakar gado da kuma nasaba.
Shin ya halatta mace ta zuba ruwan maniyyin mijinta wanda ya rasu cikin mahaifarta?
  • 1- Bayan rasuwarsa kafin gama iddarta.
  • 2- Bayan rasuwarsa da gama iddarta.
  • 3- Bayan ta auri wani namijin daban
  • Shin cikin wadannan halaye ya halatta ta zuba ruwa mijinta wanda ya rasu cikin mahaifarta? Ko kuma bayan mijinta na biyu shi ma ya rasu ya halatta ta zuba ruwan na farkon?
    Ba abin da zai hana dukkannin wadannan abubuwan illa kawai in mijinta na biyu yana da rai lallai ne ta nemi izininsa.


    HUKUNCIN CANZA HALITTA DAGA MACE A KOMA NAMIJI:

    Akwai mutanen da a zahirinsu maza ne, sai dai kuma suna dauke da wasu abubuwa na mata ta bangaren yanayin hankalinsu kana suna da cikakkiyar karkata zuwa ga jinsin mata, ta yanda in har ba'ai saurin canza halittarsu ba za su fada cikin barna shin ya halatta ayi musu jiyya ta hanyar mayar da su mata bisa yi musu (Tiyata)?
    Ba laifi ba ne ayi irin wannan tiyata idan dan gano hakikanin yanayinsu ne da sharadin in har ba za'a afka cikin haram ba kana ba zai jawo barna ba.
    Mene ne hukuncin yin tiyata ga mata maza don a mai da shi mace ko namiji?
    Ba laifi akan kansa muddun dai za a kiyaye abubuwa na haram a tattare da haka.


    HUKUNCIN FEDE MAMACI DAN NUFIN YIN BINCIKE KO CIRE WATA GABA TASA:

    Saboda gano wasu cututtuka na zuciya, ko kananan jijiyoyin da suke hade da ita, ko kuma dan gudanar da wani bincike shin ya halatta a fede jikin mamaci wanda yake musulmi domin gudanar da wadannan abubuwan? Kana in'an gama shin ya halatta a binne zuciyar ko jijiyar a wani wuri daban ba tare da jikin da aka ciro ta ba? Kamar yanda kuma binne zuciya ko kuwa jijiya ita kadai bayan bincike zai wahala to ya halatta a hada ta da wata gawar a binne ta?
    Ba laifi a fede jikin mamaci in har za'a ceto wani ran ne ta hanyarsa ko kuma da nufin yin bincike dan abin da al'umma take da bukatarsa, ko kuma dan nufin gano wata cuta da take barazana ga rayuwar mutane, sai dai in za'a sami wanda ba musulmi ba to a wannan lokacin wajibi ne rashin yi da musulmi, amma kuma gabbai wanda aka ciro su daga jikin musulmi lallai ne a binne su tare da jikin muddin in hakan zai yiwu, in ko ba zai yiwu ba sai a binne ta ita kadai ko tare da wata gawar daban.
    Shin ya halatta a tono kaburburan musulmi da wanda ba na musulmi ba dan a debo kasusuwansu a yi amfani da su kan bincike cikin makarantun horar da likitoci?
    Bai halatta a tono kaburburan musulmi ba, sai dai in ya kasance akwai tsananin bukatar haka ta fuskar magani kana kuma kasusuwan wanda ba musulmi ba ba zai samu ba.
    Shin ya halatta a dasa gashi akan mutumin da gashinsa ya kone ga wanda idan bai yi hakan ba zai rika jin kunya da takura a tsakanin mutane?
    Karin gashi ba haram ba ne da sharadi gashin ya kasance na dabbar da ake ci ne ko kuma gashin mutum ne.
    Ina so in yi kyautar gabobina domin ayi amfani da su bayan na mutu dan haka na ba wa hukumar da abin ya shafa labarin haka sai suka nemi na rubuta hakan cikin wasiyya kana na ba wa magada labari shin ina da hakkin yin haka?
    Ba laifi a yi amfani da gabban mamaci domin a saka a jikin wani da nufin ceto ransa, ko warkar da ciwonsa ba kuma abin da zai hana a yi wasiyya kan haka, sai dai kuma bai halatta a ciri ga?ar da cire ta zai zama alama ce ta cin mutunci ga mamacin ba, bisa yanda al'ada take gani (wato a idon jama'a).
    Mene ne hukuncin gyaran jiki ta hanyar tiyata don kara futo da kyan mutum?
    Yin haka babu laifi akan kansa.
    Shin ya halatta a sai da gabobi ga masu bukata.
    Babu laifi cikin yin haka in har babu cutarwa, wanda ya wajaba a kiyaye musamman ma idan kare wani rai daban ya rataya ne akan hakan to babu laifi.


    HUKUNCE HUKUNCEN DA SUKA SHAFI GANIN LIKITA DA YIN MAGANI:

    Shin ya halatta hukumar da take da nauyin daukan sojoji ta binciki al'aurar wasu don ganin ko suna da kaciya ko don neman yi musu magani? Ya halatta a tilasta su kan a yi musu binciken?
    Bai halatta a bude alaurar wani ba kana bai halatta a kalle ta ba, kana bai halatta a tilasta masa da ya bude alaurarsa gaban mutanen da bai halatta su gani ba, sai da larura, don yin kaciya ko kuma magani, to amma ba aikin mutane ba ne su nemi yi wa mutumin da ya balaga kaciya wannan abu ne wanda ya shafi shi mutumin haka nan ma ba wajibi ba ne a tilasta yi masa magani, sai inda mutanen suka ji tsoron in ba su nemi yi masa ba za ta kai shi ga halaka.
    Budurwar da take hijabi yar shekara goma sha hudu, a ka jarrabe ta da ciwon kai, ta je wajen likita ba sau daya ba ba sau biyu ba suna nuna cewar sai ta cire hijabinta kana za ta samu sauki, kana ita ma kuma akan kanta kamar yadda ta fuskanta in har ta cire hijabin nata kan nata yana samun sauki to shin ya halatta ta cire hijabin nata? Ta ci gaba da fita kanta a waje?
    Ba laifi ba ne ta cire hijabinta daga kanta ta zabi zama alhali babu shi a kanta sai dai kawai bai halatta ta je gaban wasu ba ko ta fito daga gida ba tare da hijabin ba sai a halin lalura.
    Shin ya halatta likita mace ta bude al'aurar mace don nufin yin bincike da gano cuta?
    Ba abin da zai hana yin haka in har larura ta ratsa.
    Shin ya halatta likita namiji ya taba jikin mace ko ya kalle shi domin yin magani?
    In har da larura kan cewa dole sai ta bude jikinta ya taba ko ya kalla, wanda kuma ba mace likita wacce za ta je wajenta, ba laifi ya taba din ko ya gani.
    Shin ya halatta a fitar da maniyyi idan likita ya yi umarni da hakan dan yin wani bincike?
    Ba abin da zai hana yin haka a matsayin magani, ln har maganin ba zai yi ba sai ta wannan hanya.


    HUKUNCIN YIN KACIYA:

    Shin yin kaciya wajibi ne?
    Kaciya ga maza wajibi ce, kana ma sharadi ce na karbar dawafi cikin aikin hajji da umara, da mutum zai zauna bai yi ba har bayan balaga. To ya zama wajibi ya yi.
    Mutumin da bai yi kaciya ba sai dai kuma kan kaciyar tasa ya fito gaba daya shin shi ma dole ne ya yi kaciya?
    In har ba wani abu da ya kare kan kaciyar tasa na loba wacce yake zamowa wajibi a yanke to ba lallai ba ne ya yi kaciya.
    Shin wajibi ne a yi wa yara mata kaciya?
    Ba wajibi ba ne.


    HUKUNCIN NEMAN ILIMI DA KUMA KOYAR DA SHI:

    Shin idan mutum ya ki neman sanin masalolin da yake ciki na yau da gobe yana da zunubi?
    Yana da zunubi in har hakan zai jawo barin wajibi, ko kuma aikata haram.
    Mene ne hukuncin cinikin littattafan da suka kunshi bata da ridda kamar littafin Salman Rushdi, kana kuma mene ne hukuncin karanta shi?
    Bai halatta a yi cinikin wadannan littafi ba ko kuma mallakarsa sai dai dan nufin yin raddi da sharadin in har mutum yana da ikon yin raddin a ilmance.
    Mene ne hukuncin karatu a jamia ko makarantar da ba ta kai jami' a ba in har yin karatun zai janyo cudanya da matan da ba sa yin hijabi?
    Babu hani kan shiga jami a' ko wata cibiya ta koyar da ilimi da nufin koyo ko koyarwa, sai dai wajibi ne mata su kare hijabi maza su kuma su kau da kansu daga kallon abin da bai halatta su kalla ba kana su nesanci cudanyar da za ta iya janyo fitina ko kuma barna.
    Shin ya halatta mace ta koyi tukin mota da taimakon namijin da ba muharramin ta ba? A wuraren da aka yi su dan koyar da tuki? Duk da cewa wannan matar tana kare hijabi kana kuma tana kare kanta?
    Ba abin da zai hana ta koyon mota da taimakon wani namiji daban, ln har za ta yi hijabi ta kuma kare kanta, kana kuma akwai amincin rashin afkuwar barna, sai dai kuma duk da haka abin da ya fi shi ne ya zamo akwai muharraminta tare da ita, kai ya zamo muharramun nata shi ne wanda zai koyar da ita tukin shi ya fi.
    Dalibai maza suna gamuwa da yan mata cikin makarantu da jamioi a matsayin abokan karatunsu har ma su kasance suna hira kan darasussuka da wasu abubuwan ma daban, wasu lokutan ma su rika barkwanci da dariya a tsakaninsu, sai dai duk da haka ba fadawa haram a tsakaninsu, kana ba nufin jin dadi, shin yin hakan ya halatta?
    Da hakan zai faru tare da cewa an kare hijabi kana kuma ba da nufin wani haram ba aka kuma aminta da rashin afkuwar barna to ba wani abu, idan kuwa ba haka ba bai halatta ba.
    Mene ne hukuncin sanya yara a makarantun da ake koyar da wasu munanan akidu duk da cewa dai ana ganin hakan ba wani abu da zai jawo a tare da su?
    Idan har ba' a tsoron wani abu zai shafi akidarsu ko kuma su koyi wasu munanan abubuwa, kana kuma suka sami damar nisantar karanta gurbatattun akidu, na bata da barna to ba abin da zai hana, idan kuwa ba haka ba bai halatta ba.


    HUKUNCE HUKUNCE KAN KARATUN LIKITANCI:

    Dole ne dalibai maza ko mata wajen karatun likitanci su shafi ko su kalli wadanda ba muharramansu ba domin koyon wani abu, wanda wannan binciken yana daga cikin tsarin koyarwa na darasussuka, wanda kuma ba makawa sai an yi, domin da hakan ne za' a iya maganin wata cuta mai zuwa na gaba idan har ba' ayi ba yana janyo rashin gano cuta nan gaba, wanda hakan zai janyo mara lafiya ya gaza warkewa da wuri har ma takan kai ga rasuwa a wasu lokutan, to shin irin wannan binciken ya halatta?
    Babu laifi cikin halaccin yin binciken cuta ga wanda ba muharrami ba ln har akwai Larurar yin hakan da nufin gano cuta da saninta da maganinta da kuma tsamo rayuka.
    Shin ya halatta a kalli hotunan mutanen da ba musulmi ba wanda aka yi su kamar tsirara tsirara wanda suke cikin littattafan koyon likitanci domin karatu?
    Ba' abin da zai hana ln har ba' a yi nufin haram ko kuma jin dadi ba, kana ba a ji tsoron afkuwar barna ba.
    Daliban jami' a wadanda suke koyan likitanci a lokacin darasinsu akwai zamanin da suke kallon hotuna ko kuma fina finai daban daban na gabobin jiki da nufin koyon wani abu? Shin hakan ya halatta? Kana kuma mene ne hukuncin kallon al' aura cikin wannan hali ga wanda ba jinsinsa ba ko jinsinta?
    Babu laifi cikin kallon fina finai ko kuma hotuna kawai, muddun dai ba da nufin jin dadi ba ko kuma tsoron fitina domin abin da yake haram shi ne kallon jikin wanda ba jinsinsa ba ko nata da shafarsa, amma kallon fim ko kuma wani hoto na alaurar wani, akwai matsala a cikinsa.
    Mene ne abin da ya kamata mace ta yi lokacin haihuwa, kana kuma mene ne ya halatta ungozoma ta yi dangane da bude al' aura da kallon ta?
    Sam bai halatta ga ungozoma ta kalli al' aurar mace ba lokacin haihuwa sai ln har da larura, haka ma likita dole ne ya nesanci kallon jikin mara lafiya mace ko kuma shafa muddun dai babu larura kan yin hakan, kuma dole ne mace ta rufe jikinta in har tana fadake kuma tana da ikon rufewar ko kuma ta nemi wani ya rufe mata.
    shin ya halatta ungozoma ta kalli al' aura a lokacin da take koyon aikin ungozomanci?
    Kallon al'aura domin koyon wani abu sam bai halatta ba, sai dai idan ya rataya kan maganin wata cuta ce mai hadari da ceto rai wanda maganin yana tattare da a koye shi ta hanyar kallon al' aura.


    HUKUNCIN MU'A'MALA DA WADANDA BA MUSULMI BA:

    Shin ya halatta musulmi su sayi kayan da a ka shigo da shi daga Is'ra'ila wanda ake sayar da su cikin garin musulunci kana idan lalura ce fa?
    Wajibi ne kowanne musulmi ya ki yin muamala da Isra'ila, wanda amfaninsa zai koma hannun yahudawa ne, wanda ba su da wani aiki sai gaba da musulunci da musulmi kana bai halatta ga musulmi ya sayi irin wadannan kayan ba, dan kuwa akwai fasadi da cutarwa cikinsa ga musulunci da musulmai. Hakana bai halatta wani ya shigo da kayan da za su amfana da shi ba ko ya tallata shi.
    Shin ya halatta a bude wuraren sufuri cikin kasashen musulmi zuwa Isra'ila, kana in an bude, ya halatta musulmi su sayi tikiti a' irin wadannan wurare?
    Sam bai halatta ba saboda irin abin da yake kumshe da shi, na cutarwa ga musulunci da musulmi, kana bai halatta wani ya aikata irin wannan aiki ba, dan yin hakan yana zamowa kamar fita ne daga abin da musulmi suka hadu a kansa na yanke alaka da Isra'ila wanda take gaba da musulmi kuma take yakar su.


    HUKUNCIN TUFAFI DA ABIN DA AKE SAWA WANDA YAI FICE:

    Mene ne hukuncin sautin takalmin mace lokacin da take tafiya?
    Sautin takalmi a kan kansa ba komai ba ne dan haka babu laifi, muddun dai ba zai janyo kallo ko kuma barna ba.
    Shin ya halatta mace ta sa kaya mai launin ruwan bula sosai?
    Ba abin da zai hana haka, muddin dai ba zai, janyo a kalle ta ko haddasuwar wani abu na barna ba.
    Shin ya halatta mata su sanya tufafin da zai nuna jikinsu ko wanda bai da fadi, a lokacin biki ko wani lokaci daban?
    Idan har mace ta samu aminta kan cewa ba wani namiji da zai gan ta, kuma hakan ba zai jawo barna ba to ba laifi, in ko ba haka ba to bai halatta ba.
    Shin ya halatta mace mumina ta sanya takalmi baki mai walwali?
    Babu laifi mace ta sa kowane irin launi na takalmi, sai dai in har launin zai karkato da idon mutane ko a rika nunawa da yatsa.
    Shin dole ne mace ta zabi bakin launi kawai cikin kayanta kamar dan kwali da wando da riga?
    Babu laifi mace ta sa kowanne irin launi na kaya, sai dai in har kawai zai karkato da ldon mutane, ko ya janyo ake nunata da yatsa.
    Shin ya halatta namji ya sanya kayan da mata ne ke sawa ko kuma mace ta sanya kayan da maza ne ke sanyawa, ba tare da nufin koyi da daya jinsin ba amma a cikin gida?
    Babu laifi cikin yin haka, muddun dai ba su rike shi shi ne kawai kayansu ba.
    Mene ne hukuncin maza su sayar wa da mata kayan da suka shafi cikin jikinsu?
    Ba laifi muddun ba zai janyo kallo na haramci ba, ko rashin kyakkyawar dabia ko barna cikin alumma.
    Mene ne hukuncin maza su sa sarka?
    In har ta zinare ko kuma sarka ce wacce ta kebanci mata to bai, halatta ba.


    HUKUNCIN KWAIKWAYON KAFIRAI DA YARYADA AL'ADUNSU:

    Shin ya halatta a sanya kaya wadanda suke dauke da wasu rubututtuka ko hotuna shin yin hakan watsa al'adun Turawan Yamma ne?
    Ba abin da zai hana a sanya riga saboda hoto ko rubutu sai in har hakan zai kawo barna cikin al'umma, amma kuma maganar cewa haka watsa al'adun Turai ne wanda ya saba na musulunci ko a a, shi kuma wannan ya danganci yanda mutane suke ganinsa ne.
    Mene ne hukuncin yin koyi, da Turawan Yamma wajen aski?
    Abin lura wajen haramci shi ne ya kasance an nemi yin kama da makiyan musulunci ko yada aladunsu dan haka yana sabawa ne da sabawar garurruka da zamani kuma bai takaita a kan (makiya) na yammaci kawai ba.
    Mene ne hukuncin sanya rigar da aka yi ta a Amirka?
    Ba laifi a sanya riga wacce aka yi ta daga kasar yan mulkin mallaka domin kawai suna gaba da musulunci, sai dai in har sanya ta din kuma zai yada al'adunsu, ko kuma zai kara karfafa tattalin arzikinsu, na tatse kasashen musulunci don dalilin sayen ta da sanya ta, ko kuma zai jawo faduwar tattalin arziki ga musulmai, to in har haka zai faru akwai matsala cikin sawa, kana akwai haramci wani sa'in.
    Shin ya halatta mata su halarci bikin tarbar baki wanda wasu hukumomi ke yi kana har ma su ba da furenni wajen tarbar ga bakin masu zuwa? Kuma ko akwai wata hanya da hakan zai halatta yanda mata za su tari baki ba tare da cewa akwai mata da suka taho tare da bakin ba ba dan komai ba sai domin mu bayyana wa kasashen da ba na musulmi ba cewa musulunci addini ne wanda yake ba da 'yanci wa mace da kuma martaba a cikin al'umma?
    Ba wata hanya da za ta sa a gaiyaci mata wajen taron tarbar wasu baki daban, kuma hakan ba ya halatta in har zai kawo barna ko watsa irin al'adun kasashen da ba na musulunci ba wanda suke abokan gabar musulmi.
    Mene ne hukuncin sanya damarar wuya (neck tie)? Idan muka dauka bai halatta ba to shin hukuncin ya shafi kasar Musulunci ce ta Iran ko kuwa a'a ya shafi dukkannin sauran kasashen musulmin duniya?
    Bai halatta a daura "neck tie" ba ko abin da ya yi kama da shi wanda yake tufafi ko ado ne na, wadanda ba musulmi ba, ta yanda daura shin zai tabbatar da watsa al'adun turawan yamma, kuma wannan hukuncin bai kebanci wata daula guda daya ba.
    Saboda irin abin da al'ummar musulmi take ciki a yau na farfaganda don watsa al'adun turai mene ne abin da ya wajaba mace ta yi a yanzu?
    Mafificin wajibin mace a yanzu shi ne ta kare hijabin musulunci, kana ta kare kanta ga sanya tufafin da yake koyi ne da turawan yamma.
    Akwai wasu musulmi wadanda suke taron farin cikin ranar kirsimeti, su ajiye bishiya kamar yanda kiristoci suke yi shin ko akwai wani laifi cikin hakan?
    Idan don kawai yin bikin haihuwar Annabi Isa (amincin Allah ya tabbata a gare shi da Annabinmu da Alayensa) ne ba laifi.
    Shin ya halatta a sanya singileti ko riga wacce take dauke da tambarin giya?
    Bai halatta ba.


    HUKUNCIN HIJIRA DA NEMAN MAFAKA TA SIYASA :

    Menene hukuncin yin hijra da neman mafakar siyasa a garin da ba na musulunci ba? Kana shin ya halatta a kirkiro wani labari na karya a fada domin samun damar wannan mafaka ta siyasa?
    Ba abin da zai hana a nemi mafakar siyasa a kasar da ba ta musulmi ba muddun dai ba zai kawo wata barna ba, sai dai kuma a nemi kaiwa ga hakan ta hanyar karya bai halatta ba.
    Shin dole ne matan da suka musulunta daga kasashen kafirci su yi hijira zuwa ga kasashen musulunci, domin rashin dama da aka ba su ta bayyanar da musulunci a can, da kuma tsoron irin abin da zai faru daga iyayensu ko alummar da suke ciki.
    Ba wajibi ba ne su yi hijira zuwa ga kasashen musulunci in har yin hakan zai janyo musu takura, sai dai kuma wajibi ne agare su su luzumci sallah da azumi da dukkannin abubuwan da suke wajibai.


    HUKUNCI KAN TSEGUMI DA LEKEN ASIRI DA BAYYANAR DA SHI:

    Mun sami rubutaccen labari kan wani awun gaba da wani ya yi da dukiyar gwamanti wanda aka gano hakan bayan gabatar da bincike kan ingancin abin da ake tuhumarsa da shi, ko ingancin sashe. Sai dai kuma a lokacin da aka tambaye shi sai ya musa dukkannin abin da ake tuhumarsa da shi to a nan shin ya halatta mu kai wannan rahoton zuwa kotu? Bayan in an yi hakan mutuncinsa zai zube? Kana in hakan bai halatta ba mene ne ya kamata ga mutanen da suke da irin wannan labarin su aikata?
    Idan mutanen da kare daula ko kuma kare dukiyar baitul mali ke hannunsu suka gano cewa wani ma aikaci ya ci kudi ko kuma wanda ba maaikaci ba, to wajibi ne a kansu a shar'ance su kai shi gaban kotu domin tabbatar da gaskiya, amma maganar tsoron zub da mutuncin mutumin da ake tuhuma, ba hujja ba ce wadda za ta hana a tabbatar da gaskiya dan kare baitul mali.
    Muna gani a cikin jaridu suna buga labari kan kama barayi ko wadanda suka ci hanci a ma'aikatu ko kuma mutanen da suka yi aikin abin kunya ko wadanda suka aikata barna, ko yan kulob na dare, shin buga irin wadannan abubuwa bai daga cikin watsa alfasha?
    Don Jarida kawai ta buga wani abu da ya faru, ba ya zamowa watsa alfasha.
    Shin ya halatta ga daliban cibiyoyin neman ilmi kai rahoto kan abin da suke gani mara kyau wanda ake aikatawa zuwa ga masa'ulai domin su hana?
    Babu laifi cikin yin hakan in har abin da zai kai labarin nasa al amari ne wanda yake a bayyane, ta yanda bai zama leken asiri ko cin nama ba kai yin hakan ma ya kan zama dole in an yi nufi yin hani ga mummunan aiki.
    Shin ya halatta a leki asirin muminai, kana a kai wa hukuma azzuluma labari musamman in yin hakan zai jawo cutar da su?
    Irin wannan aiki a shari'a haram ne kuma wajibi ne kan wanda ya kai labari a mayar musu da asarar da aka janyo musu a sanadiyyar kai labari kin zuwa ga azzalumin shugaba.
    Akwai mutanen da suke surutu gaban wasu kan irin abubuwan da yake faruwa cikin jamhuriyyar musulunci wadanda wasu ke aikatawa da bai kamata ba, mene ne hukuncin jin irin wannan?
    Abu ne wanda yake a sarari cewa yin dukkannin wani aiki wanda zai kawo bata fuskar jamhuriyyar musulunci wanda ke fafatawa da kafuran duniya, masu girman kai sam ba abu ne wanda zai amfani musuluci da musulmi ba, sai dai ma ribar yin hakan tana komawa ne ga makiyan musulunci, wayanda muke addu'a Allah ya wargaza su don haka irin wannan aiki haramun ne ba tare da wani kokwanto ba bai kuma halatta a taimaka wa mai yi ba ko a saurare shi don jin irin wadannan abubuwa.


    HUKUNCIN SHAN TABA DA MIYAGUN KWAYOYI:

    Menene hukumcin shan taba a ma'aikatu ko wuraren taron jama'a?
    Idan har shan ta ya saba wa tsarin wannan ma'aikatar ko taron, ko kuma zai iya janyo cutar da wasu ko takura musu to sam bai halatta ba.
    Ina da dan uwa wanda a ko yaushe cikin shan kwaya da wiwi yake kana ma yana sumogal dinsu, shin dole ne ko kuwa in ce ya halatta na kai kararsa wajen hukuma domin ta hana shi hakan?
    Wajibi ne dan hani ga mummunan aiki ka taimaka masa ya bar shan ta ya kuma daina sumogal dinta, dan haka idan kai kararsa zai taimaka cikin hakan to ba laifi.
    Shin wiwi tana da tsarki? Kana shin shan ta haram ne?
    Wiwi aba ce mai tsarki domin ko da tana sa maye, ba ruwa ba ce a asali dan haka ta tsarkaka, amma shan ta bai halatta ba.
    Shin mutumin da bai shan taba ya fara shan taba haram ne? Ko mutumin da yake sha yai sati ko sama da haka bai sha ba kana ya dawo yana sha haram ne?
    Hukuncin shan taba yana sassabawa daidai da darajar yanda take cutar da mai shan ta.
    Ina rayuwa a wani wuri wanda tattalin arzikin wannan wurin casa'in daga dari cikinsa yana samuwa ne ta hanyar noma muggan kwayoyi, kana Allah ya daukaka mu da bin mazahabar Ahlul baiti shin ya halatta a riki irin wannan noma sana'a ko abin da za a rayu da shi? Kana dukiyar da aka samu ta wannan hanyar halal ce?
    Idan da akwai wani amfani na halas da za a iya yin amfani da abin da aka noma din kamar yin magunguna ko magance cuttuka kana ba' a noma ta da nufin yin amfani da ita ta hanyar haram ba, ba laifi, kana za' a iya cin dukiyar, amma idan ta kasance da nufin amfanin haram ne, to ya haramta a shuka ta, ko kuma a yi cinikinta, kana kudin da aka samu ta hanyarta bai halatta ba.


    HUKUNCIN ASKE GEMU DA GASHIN BAKI:

    Mene ne iyakar gemun da aka so mutum ya bari? Shin saje suna daga ciki?
    Wani daga cikin saje wanda ke biye da gemu yana daga ciki, amma gwargwardon da aka so a bari shi ne daidai yanda a idon mutane za'a iya ganin kana da gemu.
    Mene ne haddin gemu wajen tsayi ko kuwa gajarta, wanda ya zama dole a bar shi?
    Babu wani haddi ga gemu wanda aka aje illa kawai daidai yanda'a idon jama'a za'a ce kana da gemu sai dai kuma karahiya ne abar shi ya wuce kamun hanu.
    Mene ne hukuncin barin dogon gashin baki? Da gajarta gemu?
    Babu laifi cikin yin hakan a kan kansa.
    shin wanda ya aske gemunsa fasiki ne?
    Ya haramta a aske gemu, bisa ihtiyadi kuma hukuncin fasikanci suna tabbata ga wanda ya aske shi.
    Mene ne hukumcin aske gemu in har barin sa zai janyo wulakanci?
    Barin gemu ba abu ne wanda zai janyo wulakanci ga musulmi mai kula da addini ba, dan haka bai halatta a aske shi ba, bisa ihtiyat sai in har zai cutar ko kuma zai janyo kunci.
    Ladan da ma'aski ko wanzami yake karba na yanke gemu shin haram ne? idan kuma haram ne sai ya hadu da dukiyar halas, shin wajibi ne ya ba da khumusinsa kenan sau biyu?
    Bisa ihtiyadi haram ne a karbi ladan aske gemu, amma kuma dukiyar da ta hadu da haram idan an san adadin haram din kana kuma an san mai ita wajibi ne a mayar masa da kayarsa, ko kuma a nemi yaddarsa kan yin amfani da ita, idan ko har ba a san mai ita ba, ko da a cikin wani adadi iyakantacce ya zama wajibi a ba wa mabukata sadakarta, amma da za ace ba'a san yawanta ba sai dai kuma an san mai ita to ya zama wajibi a nemi yardarsa kan dukiyar, idan kuma ba a san mai ita ba kana ba a san yawanta ba, to a nan ya wajaba a fidda khumusinta dan tsarkake ta daga haram kana idan abin da ya rage bayan fitar da khumsi ya karu a kan bukatarsa ta shekara to a nan ya wajaba ya sake fitar da khumusin wannan.
    A wasu lokuta ma aska ko wanzamai suna kawo min gyaran abin askinsu wanda kuma ga shi aske gemu haram ne a shari'a, shin ya halatta na gyara musu?
    Tun da yake wannan abin askin za a iya yin amfani da shi ta wata hanyar daban ba sai aske gemu ba to ba wani laifi a cikin gyaransa, da kuma karban ladan aikin in har ba gemu za'a aske da shi ba.


    HUKUNCIN HALARTAR WURAREN SABO:

    Mene ne hukuncin rayuwa a cikin kasar da take cike da ababen sabo, misalin kide kide da raye raye na batsa, da rashin lullubi kana mene ne hukuncin mutumin da bai dade da balaga ba ya ci gaba da zama a wannan gari?
    Babu abin da zai hana mutum ya ci gaba da rayuwa ko zama cikin garin da yake cike da ababen sabo musamman ma in har ba yanda zai yi, sai dai ya zama wajibi ya nesaci duk wani abu da shara'a ta haramta masa shi, kana kuma babu wani bambanci kan aikata wajibi ko barin haram tsakanin mutumin da bai dade da balaga ba da kuma wadanda suka dade.
    A wasu lokuta ana hada biki na karbar bakin malaman jami'a ko daliban jamiar wani guri daban, kamar yanda kuma aka saba ana kawo abubuwan sha da suke sa maye a irin wannan taron, a nan me shari'a take ganin ya dace ga daliban jami'ar da suke son halartar irin wannan taron su'aikata?
    Bai halatta ga wani ya halarci duk wani wuri da ake shan giya ba, ku bar su su fahimci cewa saboda ku musulmi ne dan haka ba kwa shan giya kuma ba ku halartan wurin shan ta.
    Mene ne hukuncin zuwa wuraren bikin angonci, shin ana iya lissafa wanda ya je wurin da cewa shi ma yana daga cikin wannan jama'a masu irin wannan aiki dan kuwa tilas akwai rawa a wurin, to shin a wannan hali ya wajaba mutum ya bar halartan wurin ko kuwa zai iya zuwa sai dai ya ki yin rawa da kuma abubuwan da ba su dace ba?
    Muddun dai wurin ba za'a kira shi da wurin wasannin wargi da ya haramta ba, ko kuma wurin sabo, kana kuma ba wata barna a cikin halartar wurin to ba laifi a halarta, in har kuma halartar ba za ta kasance a idon jama'a karfafa aikin da bai halatta ba.
    Mene ne hukuncin halartar bukukuwan da maza su su kadai ko kuwa mata su su kadai suke yi tare da kide kide da raye raye?
  • Shin kuma halartar wuraren bikin da ake kide kide da raye raye ya halatta?
  • Shin wajibi ne a irin wannan wurare a yi umarni da kyakkyawan aiki a yi hani ga mummuna idan hakan bai da wani tasiri a gare su?
  • Mene ne kuma hukuncin mata da maza su hadu wuri daya suna rawa?
    Kwatakwata bai halatta a yi rawa ba ta yanda za ta motsa sha'awa, ko kuma rawar da take hade da aikata haram, ko za ta jawo aikata shi, hakan nan kuma idan rawa ta zamo tsakanin mata da maza wadanda ba muharramai ba shi ma bai halatta ba cikin kowanne irin biki na angonci da wanda ba na angonci ba, bai halatta a halarci wuraren sabo ba, idan haka zai janyo a'aikata sabo kamar jin kide kide da suka dace da wuraren wargi ko sabo ko kuma idan haka zai sa a ga cewa an karfafa aikata sabo ne, amma kuma yin umarni da kyakkyawa ko hani da mumuna in har ba zai yi wani tasiri ba, to shi ma ba sai an yi shi ba.
    Idan mutum ya je wajen biki sai ya ga wata mace wacce ba muharramarsa ba ba ta da hijabi kana ya san cewa ko da an hana ta zama ba hijabin ba za ta hanu ba, shin wajibi ne ya bar wannan wurin?
    Fita daga wurin da ake aikata sabo don nuna kin yarda da shi idan har za'a fahimci yin hakan da sunan hani ga mummunan aiki to ya zama wajibi yin hakan.
    Shin ya halatta mutum ya je wuraren taron da ake jin kasa kasai na wakokin holewa, mene ne kuma hukuncin haka in har yana kokwanto kan wakokin na haram ne ko ba na haram ba, kana ya san kuma cewa bai'isa ya hana a sa wakokin ba?
    Bai halatta a halarci wuraren da ake kide kide na wargi da suka dace da wuraren wasa da sabo ba idan in har'anje din zai zamo lallai sai mutum ya ji su ko kuma zuwansa zai janyo karfafa irin wannan aikin, amma kuwa da mutum zai yi kokwanto kan cewa na sabo ne ko kuwa ba na sabo ba ne to babu laifi ya halarta ko kuma ya ji.
    Kana menene hukuncin zuwa wuraren taron da watakil mutum zai ji maganganun da ba su dace ba kamar yi wa shugabannin addini kage ko kuma shugabannin jamhuriyyar musulunci ko wasu bayin Allah muminai.
    Don kawai halartan wurin, muddun dai ba zai janyo mutum ya yi abubuwan haram ba, kamar yi da wani, ko kuma zuwan nasa ya zamo ya karfafi mummunan aiki idan har haka ba za su faru ba, to ba abin da zai hana ya halarta, amma kuma duk da haka yin umarni da kyakkyawa da hani ga mummuna yana nan a matsayinsa na wajibi, a kowane hali.


    HUKUNCIN NEMAN TSARI (KARE KAI) DA NEMAN ISTIKHARA:

    Shin ya halatta a yi taimako na kare kai kana a karbi ladan rubuta shi ko a ba da lada domin a rubuta shi?
    Babu laifi a bayar ko a karbi kudi dan ladan rubuta shi muddun dai wanda aka ruwaito shi a littattafa na hadisai ne (wanda a ka sani).
    Shin wajibi ne a yi aiki da istikhara?
    Ba wani wajibci na shari'a akan yin aiki da istikhara, sai dai kuma abin da ya fi lallai kar ayi aiki sabanin abin da aka gani a istikhara.
    Shin daidai ne a yi istikhara da Alkur'ani kan son sake mace ko rashin sake ta? Kana mene ne hukuncin mutum ya yi isfikhara ya ki yin aiki da ita?
    Halaccin yin istikhara da Alkur'ani ko kuwa carbi ba wai sun kebanci wani wuri ba ne na musamman, kuma mutum yana komawa ga istikhara ne lokacin da yake kai kawo ya kasa fahimtar abin da ya kamata ya yi, dan haka istikhara ba ta da cikakkiyar fa'ida a wurin da mutum yake da yakini a kansa, kana yin aiki da istikhara ba wajibi ba ne, ko da yake kuma abin da ya fi kar ya saba mata.
    Shin ya dace a yi istskhara sama da sau daya a kan abu guda?
    To da yake istikhara dama ana yin ta ne dan kawar da halin rashin sanin abin yi, to idan an sami kawar da irin wannan hali yayin da aka yi istikhara ta farko, to a nan babu ma anar maimaita ta saidai in lamarin ya canza.


    HUKUMCIN RAYA RANAKU MUHIMMAI A ADDINI:

    Mene ne hukuncin buga ganga ko tambari da busar algaita ko dukan sarkar da take a jikinta akwai reza mai kaifi, a ranakun tunawa da ta'aziyyar Imaman musulunci.
    Idan har yin amfani da wasu sarkoki zai kawo a wulakanta mazhaba a idon mutane ko kuma zai cutar da jiki bai halatta ba ayi amfani da su, amma busa algaita da ganga da tambari ta yadda ba'a ketare iyaka ba to babu laifi.
    Shin ya halatta a tara taimakon kudi a cikin kwanakin Ashura, kana a karkasa kudin a ba wa malamin da zai yi karatu da wanda zai yi huduba (lacca) da kuma wanda zai karanto ta'aziyyar Imam Husain (a.s.) kana kuma sauran a yi amfani da su kan sauran shirye shirye na raya wurin?
    Babu laifi ayi, hakan in har wadanda suka ba da taimakon sun yarda kana sun nuna amincewarsu.
    Akan me ya dace a yi amfani da kudin da suka ragu cikin kudin da aka tara dan ayi ashura da su?
    Kudin da suka ragu na ashura za a iya yin amfani da su kan ayyukan alheri, amma tare da neman izini daga wanda ya bayar, ko kuma a ajiye su zuwa wata ashurar mai zuwa sai ayi amfani da su.
    Shin ya halatta ga mata wadanda suke sanye da cikakken hijabi su halarci jerin gwanon Ashura (wurin taro) wanda ake dukan kirji a cikinsa?
    Ba abin da zai hana mata su je irin wadannan wurare na ta'aziyya sai dai bai kamata su rika bugun Jikinsu ko kirjinsu gaban wasu mazaje daban ba.
    Idan mutum ya yi wa kansa mummunan duka a lokacin tunawa da wafatin Imamai (A.S) wanda har ta kai shi ga mutuwa shin za'a lissafa shi ne cikin mutanen da suka kashe kansu da kansu?
    Idan a lokacin da zai aikata hakan ya ji tsoron cewa ransa zai iya fadawa cikin hatsari tun farko wanda kuma sai ga shi, hakan ya janyo mutuwarsa to yana cikin hukuncin wadanda suka kashe kansu da kansu.
    Shin ya halatta a halarci wuraren karatun musulmin da suka kashe kansu da kansu? Kana mene ne hukuncin karanta musu fatiha akan kabarinsu?
    Babu laifi cikin yin hakan a kan kansa.
    Mene ne hukuncin karanta wakokin ta'aziyya da na yabo wadanda suke sa masu jin su kuka, cikin bikin ranar tunawa da haihuwar A'imma (A.S) ko kuma tunawa da bikin ranar aiko Manzo? Kana mene ne hukuncin watsa kudi ga wadanda suka halarci wurin.
    Ba wani laifi cikin karanta wakokin ta'aziyya ko na yabo a ranakun biki masu girma a'addini, kana babu wani laifi cikin raba kudi ga wadanda suka halarci wurin, hakika ma lada ake samu in'an raba, idan har ana nufin nuna farin ciki ne da murna, da sanya annashuwa a zukatan muminai.
    Shin ya halatta mace ta karanta ta'aziyyar lmamai bayan kuma ta san wasu mazan da ba muharramanta ba suna jin muryarta?
    Ba abin da zai hana haka muddun dai karatun nata bai kunshi wani yanayi na wasa ba, kana kuma ba'a ganin cewa sautinta zai janyo fitina kan mazajen.


    HUKUNCE HUKUNCEN CINIKI:

    shin ya halatta ga masu kamfanoni da shaguna su buga wasu bakin kalmomi daga kasar waje ko hotunan wasu abubuwa daban akan rigunan yara dan su janyo hankulan masu saye?
    Haka ba laifi in har ba'a nufin yaudara ko rudin wanda zai saya.
    Mene ne hukuncin algus, da karya da yaudara a lokacin da ake ma;amala da mutumin da ba musulmi ba, don samun riba mai yawa.
    A kowane hali karya da yaudara da algus ba sa halatta cikin ma'amala ko da kuwa abokin muamalar ba musulmi ba ne.
    Mece ce iyakar ribar da aka yadda a ci a cikin kasuwanci?
    Babu wani haddi ayyananne na riba wacce aka iyakance dan haka babu wani laifi cikin cin ta muddun dai ba zai kai ga haddin cuta ko zalunci ba kuma bai saba da farashin da hukuma ta sa ba, sai dai abin da ya fi wanda kuma shi a ka so a ci riba madaidaiciya wacce za ta biya harkokin mutum na yau da gobe.
    Wani mutum yana sayar da ruwansa ga mutane amma kuma farashi daban daban, yana sayarwa da wani robar ruwan misali naira goma wani kuma daidai da shi a naira goma sha biyar duk da cewa kuma ruwan abu daya ne ba wani banbanci, shin za mu iya nuna rashin yaddarmu Kan bam bancin wannan farashi nasa?
    Idan har wanda yake sayar da ruwan ruwansa ne ko kuma yana da hakki a cikinsa kana ya sayar da shi ga kowanne mutum daidai da yanda suka yi yarjejeniya a tsakaninsu, to bai cancanta ba wasu su nuna kin yardarsu kan farashin.
    Idan na karbo wata dila daga cibiyoyin taimako na kayan masarufin hukuma, kan farashi mai sauki, shin ya halatta na sayar da wannan dilar a cikin kasuwar da take na kowa da kowa bisa farashi mai yawa ninkin yanda na sayo sau uku?
    Idan har hukuma ba ta hana ba kana sayar da ita da wannan farashin ba zai janyo cutarwa ko zalunci ga mai saye ba to babu laifi a ciki.
    Ni ina yin naurori na lantarki shin ya halata na sayar da su da dukkannin farashin da na ga dama muddun dai kasuwa tana da bukatarsu?
    Dukkannin abin da bai da kaiyadadden farashi daga hukuma ba abu da zai hana a sayar da shi, muddun dai an sami yaddar wanda zai saya da wanda zai sayar.
    Mene ne hukuncin jari hujja a cikin musulunci, kana zuwa wani haddi ne aka yarda a mallaka, shin mutum zai iya zamowa cikakken miloniya muddun dai yana ba da taimako wa talakawa da kuma fitar da hakkin musulunci, kana shin fito na fiton da musulunci yake yi da jari hujja ya takaita ne kan dukiyar mutumin da ba ya ba da khumsi da zakka, ko kuwa ya hado dukiyoyin musulmin ma da suke fitar da khumusi da zakka, kana ma wai shin yana yiwuwa mutum ya zamo wanda ya kai tsororuwan arziki muddun dai yana fitar da hakkokin musulunci a cikin dukiyarsa?
    Hakkokin musulunci wadanda suka rataya ga dukiyar masu kudi ba ta tsaya kan zakka ko khumusi ba kadai, kana kuma musulunci ba ya wani fito na fito da tara dukiya idan har za'a tara ta ta hanyar da musuluncin ya yarda kana kuma za a bayar da dukkannin hakkokin da suka rataya ga ita, sannan yawaita ta ya zamo ta hanyar da ta halatta, kuma don amfanin musulunci da musulmi, a wannan irin hali ba abin da zai hana mutum ya kai tsororuwar arziki da wadata.
    Kamar yadda ya zama ruwan dare a yanzu mutum ya kan sanya wani ya sayo masa mota sai ya je ya sayo ta naira miliyan daya a misali amma sai ya ce da shi ya sayo ta ne a miliyan daya da dubu dari yana nufin dubu ?arin ita ce madadin wahalar da ya sha, da zirga zirgar da ya yi ta nema, shin irin wannan ma'amalar ta halatta?
    Da za'ace yana matsayin wakili ne na waninsa sai ya aika shi da kudi na mota ya kai dan ya sayo masa bai da damar da zai kara wani abu akan haka. To sai dai yana da 'yancin da zai nemi ladan wakilcinsa, amma ko da za'a ce shi ya sayo motar da kudinsa kana kuma sai ya so ya sayar da ita ga wani wanda ya ba shi sabon ya sayo masa, to yana da damar da zai sayar masa da ita akan kudin da suka yi yarjejeniya da shi, amma kuma bai halatta ya yi karya ba cikin ba da labarin kudin da ya saye ta, sai dai yin karyar ba zai bata cinikin ba.


    HUKUNCI KAN RIBA (KUDIN RUWA):

    Menene kudin ruwa? Kana kason da bankuna suke bayarwa a matsayin ribar kasuwanci ana kidanya shi kudin ruwa?
    (Kudin ruwa) na riba a fagen bashi shi ne abin da wanda ya karbi bashi yake dada shi akan abin da ya karba, Amma ribar kasuwanci wanda ake samo ta ta hanyar ajiyar da aka yi a bankuna wanda kudin suke a matsayin amana da nufin ayi amfani da ita a madadin mai dukiya domin yin wani kasuwanci da sharia take ganin ingancinsa to babu wani laifi akan wannan, ba kudin ruwa ba ne kana ba wani laifi.
    Da mene ne ake gane kudin ruwa? Shin kuma gaskiya ce da ake cewa babu kudin ruwa sai cikin bashi?
    Kudin ruwa yana kasancewa a cikin ciniki kamar yanda yake kasancewa a cikin bashi, ruwa a cikin bashi tana kasancewa in har an sanya sharadin kara wani abu, abin da za'a kara din kuwa kudi ne ko wani abin amfani ne, a idon jama a amma kudin ruwa a bangaren ciniki yana kasancewa ne lokacin da aka sayar da jinsi iri daya amma waninsu ya fi dayan kudi kamar misalin shinkafa da shinkafa.
    Kamar yadda shari'a ta halatta cin mushe a lokacin tsananin bukata wacce in har ba'a ci mushen ba za'a mutu ba shi kuma da abin da zai ci in ba shi ba to shin ya halatta a ci kudin ruwa a lokacin da mutum ya zama yana da larura ta yanda bai da karfin da zai iya yin aiki don ya sami kudi, amma ya kasance yana da wasu kudi kadan dan haka sai ya ga dole ne idan yana so su ci gaba da karuwa ya yi ma'amala ta kudin ruwa da su domin ya rayu da ribar da suke kawo masa?
    Kudin ruwa haram ne wannan kuma kiyasin da ka yi na cin mushe a lokacin tsananin larura yana da banbanci da shi domin kuwa a wannan lokacin mutum na cin mushe ne dan ba shi da abin da zai ci idan ba mushen ba amma shi wannan yana da ragowar kudi a hannunsa ba su kare ba tukuna wanda shi ma mai cin mushen da akwai ragowar abinci a hannunsa ai da bai halatta ya ci ba.
    Shin haramcin kudin ruwa yana kan kowa da kowa ne, kuma cikin kowanne irin hakki ba tare da wani banbanci ba, ko kuwa akwai wasu wuraren da aka kebance?
    Kudin ruwa haram ne ta kowace fuska banda kudin ruwa na bashi da uba yake ba wa dansa ko kuma kudin ruwa da musulmi yake karbarta daga wanda ba musulmi ba.
    Da za a ce wani mutum yana bukatar bashi sai dai bai sami wanda zai ba shi ta hanya na halas ba to shin ya halatta ya sami bashin ta wannan hanyar. Wato ya sayi kaya sama da kudin da ake sayar da shi da sharadin zai ba da kudin nan gaba, jim kadan bayan haka sai ya sake sayarwa ga wanda ya saya a wurinsa kasa da yanda ya saye shi sai ya karbi kudin to yin hakan ya halatta?
    Irin wannan maamalar wacce ta kunshi wayon gudu daga kudin ruwa na bashi haram ce a shara'a kana batacciya ce.
    Shin ya halatta a sayi wata dila sama da yanda ake sayar da ita saboda bashi ne aka yi cinikin, kana ana kidanya yin hakan ruwa ko kuwa a'a?
    Babu laifi a sayar da dila ko makamanciyarta sama da yanda ake sayar da ita in har ba take za' a ba da kudin ba kana kuma ba' a kidanya wannan banbancin farashin (wanda ake ba da kudin take da wanda ake bayarwa bayan an kwana biyu) a matsayin kudin ruwa.



    KU BIYO MU A HANKALI DON GANIN SAURAN FATAWOYIN


    Matsa Wannan Alama Don Komawa Sama