Hudubar Sallar Juma'a Ta Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci
(Ayatullah al-Uzma Sayyid Aliyu al-Khamene'i)

                               Huduba ta Biyu

  • Maudhu'i: Mamayan Amurka A Iraki da kuma Wahalhalun Mutanen Kasar.
  • Wuri: Sallar Juma'a;
  • Rana: 7/Safar/1424 = 11/Afrilu 2003.
  • Shimfida: A wannan rana ce Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Ayatullah al-Uzma Sayyid Ali Khamene'i (H) ya gabatar da hudubar sallar juma'a inda ya yi bayani kan halin da al'ummar Iraki suke ciki bayan mamayan Amurka da kuma matsayar Iran kan wannan lamari. Abin da ke biye shi ne fassarar wannan huduba ta sallar juma'a.Jagora - Imam Khamene'i HUDUBA TA FARKO

Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai

Dukkan godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai. Tsira da amincin Allah su tabbata ga Shugaba kana kuma Annabinmu Abil Kasim Mustafa Muhammad tare da Alayensa tsarkaka kana kuma zababbu, musamman ma Aliyu Amirul Muminina da Siddikatut tahira (Fatimatuz Zahra) Shugaban matayen duniya da Hasan da Husaini jikokin rahama kana kuma shuwagabannin shiriya da Aliyu bn Husaini Zainul Abidin da Muhammad bn Aliyu Bakirul Ulum da Ja'afar bn Muhammad al-Sadik da Musa bn Ja'afar al-Kazim da Aliyu bn Musa al-Ridha da Muhammad bn Aliyu al-Jawad da Aliyu bn Muhammad al-Hadi da Hasan bn Aliyu al-Zakiy al-Askari da Hujja al-Ka'im al-Mahdi. Ya Allah Ka yi salati a gare su ta har abada da kuma Ka yi salati ga Shuwagabannin Musulmi, masu kare raunana sannan kuma masu shiryar da muminai.

Ina kiran dukkan 'yan'uwana mata da maza masallata da kuma ni kaina zuwa ga tsoron Allah da kuma bauta masa. Ina gargadinku da ku yi hankali da kalmomi da kuma ayyukanku kai hatta ma da tunaninku. A hudubar farko ta yau, zan yi magana ne kan muhimmin al'amarin da yake gudana a halin yanzu wanda shi ne lamarin kasar Iraki da kuma abubuwan da suke gudana a can. A huduba ta biyu kuwa, zan ba kusan dukkan lokacin ne wajen magana da 'yan'uwana larabawa da suke kasar Iraki da sauran kasashen musulmi cikin harshen larabci.

Hakika al'amari mai muhimmancin gaske ya faru a kasar Iraki. An kaddamar da harin soji kana kuma an kwabar da gwamnatin da take ci a kasar. Akwai wata kasa wacce take da bukatunta, ra'ayuyyuka da kuma abin da take son cimmawa, tana da irin karfinta kana kuma wani gungun na masu bukata sun kewaye ta.

Babu shakka, kun riga da kun san cewa kasar Iraki ta fuskanci wahalhalu daban-daban cikin karnin da ya wuce. Yanayi daban-daban na zubar da jini sun faru a kasar. Bayan faduwar daular Usmaniyya, Birtaniyya ta sanya wasu mutane da ba Irakawa ba a matsayin masu kula da kasar, wadanda suka kasance sarakuna. An yi sarakuna har guda uku cikin wadannan shekaru, na farkonsu mutuwa ya yi, na biyu kuwa aka kashe shi cikin mafi munin hatsari, kana na ukun kuma jama'a suka yi yaga-yaga da shi.

Hakika Birtaniyya ce ta nada su, daga baya kuma gwamnati bayan gwamnati suka dinga zuwa, bayan juyace-juyacen mulkin da aka dinga samu. Wadannan gwamnatoci dai sun yi karko har kusan shekaru goma, wato shekarar 1958 zuwa 1968 lokacin da gwamnatin Ba'athawa ta dare karagar mulki, wanda a lokacin Saddam shi ne mutum na biyu a gwamnatin, na farkon (shugaban kasa) shi ne Ahmad Hasan al-Bakr. Haka suma suka yi mulki har na tsawon shekaru goma.- shuwagabanni uku da suka dare kan karagar mulki ta hanyar juyin mulkin soja, na farko aka kashe shi, na biyu kuma aka kashe shi a yanayin na zargi kana na uku kuma aka tube shi daga mulki. To daga shekarar 1347 zuwa sama Ba'athawa ne suka ci gaba da mulki har na tsawon shekaru talatin.

Wadannan shekaru 37 ana lissafa su a matsayin shekaru mafiya wahala ga al'ummar Irakin, musamman ma lokacin da Saddam din ya dare karagar mulki. To a halin yanzu, an kawar da gwamnatin Saddam, kuma ba ma wanda ya san inda Saddam din yake - wanda hakan lamari ne da yake cike da shakku.

Wannan lamari dai ya kasance abu ne da ba a saba ganinsa ba, hakika wannan lamari da ya faru a kasar Iraki ya kumshi abubuwa ne guda hudu. Amurkawa, Birtaniyyawa da kuma 'yan amshin shatansu suna so ne su gaggauta gamawa da lamarin, da kuma mai she shi wani lamari mai sauki da kuma kirkirar wani yanayi na e ko a'a a cikin tunanin al'umma, to sai dai kuma wannan aiki na su ya zama aikin baban giwa. Lalle lamarin ya kumshi abubuwa ne guda hudu ba kawai abu guda ba. Jiya-jiyan nan ne ko kuma shekaran jiya ne, aka yada wasu sakonni na Bush da Blair zuwa ga al'ummar Iraki, to sai dai kuma al'ummar Iraki ma ba su da wutar lantarki, don haka ma ba su ji wannan sako ba. Abin da sakon dai ya kumsa shi ne mu mun zo Iraki ne don mu 'yantar da ku. Sun takaita sakon da cewa: Mun zo ne don mu 'yantar da ku da kuma tsamar da ku daga hannun Saddam. Hakika akwai wasu manyan kura-kurai a cikin wadannan sakonni na wadannan mutane biyu:

Na farko dai shi ne fadinsu cewa: 'Mun zo ne mu 'yantar da ku', wanda yake nufin cewa mutanen Iraki ba su da karfi da kuma ikon aikata hakan, don haka sun zo ne don su yi musu hakan. Hakika wannan babban kuskure ne. Na biyu kuma shi ne cewa wadannan maganganu na su karya ce tsagoronta, don kuwa babu yadda za a yi mutum ya 'yantar da wata kasa ko kuma al'umma ta hanyar ta hanyar kai mata hari da harsasai, bama-bamai da kuma makamai masu linzami. Mutum ba zai lalata garuruwa, kauyuka da kuma unguwanni mutane a irin wannan yanayi da suka yi ba - wanda nan gaba kadan zan yi magana a kansa- da sunan wai yana lalata sansanonin soji ne.

A'a, lamarin dai ba wai 'yantar da kasar Iraki ba ne. Hakika akwai wasu abubuwa guda hudu da ya kamata a yi la'akari da su. Daya daga cikin abubuwan kuwa ya shafi faduwar Saddam ne. Hakika an samu sabani da fahimtar juna tsakanin manufofin Saddam da kuma manufofin masu mulkin Amurka - wanda nan gaba an yi karin bayani a kai- wanda hakan shi ne ya haifar da rikici da kuma fada. To sun fi karfi, don haka sai suka kawar da shi. Wannan dai shi ne abu na farko.

Matsayarmu kan hakan a fili take, kuma zan yi karin bayani kan hakan. Muna da fitattun matsaya kan dukkan wadannan abubuwa guda hudu. Mun zabi wadannan abubuwa don bayyanar da matsayar Jamhuriyar Musulunci Ta Iran, wanda take gwargwadon tunani da kuma hikima ta Musulunci. Batu na farko dai dangane da faduwar Saddam ne.

Abu na biyu kuma wanda ya faru a Irakin, kuma ya ke ci gaba da faruwa, shi ne dangane da irin bala'i da kuma cutarwar da aka yi wa al'ummar Iraki. Wannan ya saba wa faduwar Saddam, don haka yana da nasa hukumcin na daban, kuma za mu bayyanar da matsayarmu kan hakan.

Abu na uku kuma shi ne cewa wata kasa ta daban ta kaddamar da wuce gona da irin soji akan wata kasa mai cin gashin kanta - mamayan soji - suna masu fakewa da wasu abubuwa, sun ce Irakin tana da makaman kare dangi, ko kuma suna goyon bayan ayyukan ta'addanci. To, babu shakka, mutum yana iya fadin hakan a duk lokacin da ya ga dama, to sai dai hakan ba hujja ba ce na kaddamar da mamayan soji akan wata kasa da kuma keta mata hurumi. To wannan dai shi ne abu na uku wanda shi ma za mu fadi matsayarmu a kai.

Abu na hudu kuwa shi ne dangane da makomar kasar Iraki, wanda tuni sun riga da sun tsara tsare-tsare da kuma shirye-shirye tattare da abubuwan da suka riga da suka kulla a cikin zukatansu - wanda hakan wani lamari ne na daban. Akwai hukumci ga dukkan wadannan abubuwa. Iyayengijin Dan Mulkin Kama Karya Saddam ne Suke Rusa Mutum-Mutuminsa, Bayan Ya Gama Biya Musu Bukata
Karshen Alewa Kasa, Karshen Azzalumi kuma Jin Kunya

To dangane da abu na farko, wanda ya shafi faduwar Saddam, to lamarin dai shi ne cewa tun da farko dai, wato tun farkon mulkinsa, Saddam ba shi da wani sabanin manufa da Amurka. Don kuwa su kansu Amurkawan sun bayyana cewa tun farkon mulkin Saddam, kungiyar leken asirin Amurka ta CIA sun taka gagarumar rawa cikin juyin mulkin da 'yan jam'iyyar Ba'athawa suka yi a kasar Iraki a shekarar 1968.

To amma babu shakka bayan hakan, manufofin nasu sun ci gaba da zama tare, musamman ma bayan nasarar Juyin Juya Halin Musulunci da kuma kafa gwamnatin Musulunci (a Iran). Kafin hakan, suna tare da shaidanin dan kama karyar kasar Iran, Muhammad Ridha Pahlawi (Sarki shah), a fili yake cewa manufofinsu suna kusa da juna, kenan bayan samun nasarar Juyin Juya Halin Musulunci suna da manufa guda. Wannan juyi ya canza tsarin kasarmu, ita kuma Amurka tana gaba da kafa gwamnatin Musulunci, ta haka suka samu alaka da juna. To don haka, a shekarar 1980, lokacin da Irakin ta kaddamar da yakinta akan Iran, wato kallafaffen yaki, Saddam ya kai hare-haren soji ta sama a kasar Iran tun ranar farko.

A daidai wannan lokaci kuwa Amurka ba ta ce masa uffan ba, kai face ma dai suka dinga kara irin taimakon da suke ba shi kowace rana. Wannan shi ne hakikanin lamarin, hakan yana nufin akwai wasu tsammace-tsammace, tsammani na farko shi ne cewa tun kafin kai harin ya riga da ya tsara tsarinsa tare da Amurkawan, koda yake ba zan iya yin wani zargi kan hakan ba, saboda kuwa ban san hakikanin abin da ya faru ba. Babu shakka akwai rahotanni kan hakan. Yayin wasu ziyarce-ziyarce da na kai wasu kasashen, lokacin ina shugaban kasa, akwai wasu shuwagabannin kasashen musulmi da suka gaya min hakan. Suka ce min tuni ya riga da ya hada kai da wasu guraren (kan kai harin) tun ma kafin a kai shi, to a halin yanzu dai ba mu da tabbaci kan hakan. Abin da muke da tabbaci akansa shi ne cewa bayan fara yakin dai Amurka ta ba wa Saddam cikakken goyon baya. Sun taimake shi har ma sun ta matsin lamba ga Majalisar Dinkin Duniya wajen tursasa mata ta goyi bayan Saddam ta bangarori daban-daban. Haka muka yi hakuri da wannan yaki har na tsaron shekaru takwas, alhali Saddam yana aikata abin da suke so. Ta hakan ne Saddam ya kara tabbatar da manufar Amurka da kuma ya shagaltar da Jamhuriyar Musulunci Ta Iran har na tsawon shekaru takwas, wato mummunan yanayin zubar da jini na cikin gida, wato yaki kenan.

Hakika da a ce wannan kasa ko kuma wannan Juyin Juya Halin bai shagaltu da wannan mummunan yaki ba, to da hakika akwai dama na ba da himma wajen gina kasa, kuma lalle da an yi ayyuka masu yawan gaske. To amma Saddam ya yi amfani da mafi kyawun lokacin rayuwarmu, wato shekaru takwas, ya shagaltar da mu da aikin da yake tabbatar da kuma kare manufar Amurka. Hakika manufarsu suna da alaka da juna.

Sannan kuma a shekarar 1990, Saddam ya mamaye kasar Kuwaiti, to fa a wannan lokacin ne manufofinsu suka fara karo da juna, suka fahimci cewa wannan mutum fa yana da hatsari da kuma hadama ta yadda har ya fara sanya manufofin Amurka a yankin cikin hatsari. Hakan kuwa saboda cewa kai hari a kan kasar Kuwaiti yana daidai ne da kai hari kan manufar Amurka. Idan da ba su kawar da Saddam ba da akwai yiyuwar zai kai hari kan kasar Saudiyya, hakika ya kasance ya kan fadi irin wadannan maganganu. Ya ce: 'Idan na kame Kuwait, to zan matsa gaba har zuwa Hadaddiyar Daular Larabawa, Bahrain, Katar, kuma zan ci gaba iyakacin iyawa na'.

Ina nufin hakan ita ce niyyar Saddam, to hakika anan manufofinsu sun yi karo da juna. Daga nan fa sai Majalisar Dinkin Duniya ta fara matsa lamba ga Saddam, bugu da kari kan farfagandan da suke yi akansa. Saddam dai mutum ne da zai iya jure wa matsin lambar Amurka ba, a shirye yake ya yi sassauci da kuma yin yarjejeniya, to sai dai kuma Amurkawan ba a shirye suke su yi hakan ba. Sai suka fuskanci matsalar ta wata hanya ta daban. Idan da sun yi yarjejeniya da shi to fa sun rasa abokansu a yankin Tekun Fasha, don kuwa shuwagabannin tekun Fasha ba za iya zuba ido su ga Amurka tana karfafa Saddam kamar yadda ta yi a aya ba, don kuwa a tsorace suke. Haka nan kuma idan Amurka ta kara matsa kaimi wajen takura wa Saddam to tana iya rasa manufofinta a kasar Irakin.


(Jami'an Amurkan) Sun tabbatar wa duniya cewa su ne "Kusurwowin Shaidanci" (Axis of Evil) na hakika. Amurka ta tabbatar wa duniya cewa ta cancanci sunan nan da shugabanmu Imam Khumaini (R) ya sanya mata na "Uwar Shaidanu". Hakika Amurka ita ce uwar shaidanu.
To anan Amurka ta fuskanci tsaka mai wuya, Iraki dai kasa ce da take da arzikin man fetur da sauran ma'adinai, tana da al'ummar da adadinsu ya kai miliyan 20, don haka tana da matukar muhimmanci da kuma jawo hankalin Amurkawa a wannan yankin mai matuka muhimmanci a Gabas ta Tsakiya. Tana so ne ta ci gaba da zama a gurin, tana so ta tabbatar da kasantuwanta a gurin don zuba ido kan manufofinta. Tana so ta kwashe irin dimbin arzikin da yankin yake da shi, sai dai kuma ba za ta yi hakan ba. Don kuwa matukar dai ta yi yarjejeniya da Saddam, to za ta fuskanci matsala a yankin, idan kuma ta ki yin wannan yarjejeniya, to dole ne fa ta mance da manufofinta a yankin da kuma binsu. To a nan ne fa sabanin da ke tsakanin Amurka da Saddam Husaini ya fara yin tsami, nan take suka fara tunanin lamarin, so suke su kawar da Saddam don haifar wa kansu da daman shiga kasar Iraki da kuma sawwake lamurra gare su, to daga baya dai hakan ya faru. Don haka idan har Amurka da Birtaniyya suka ce sun shiga kasar Iraki ne da nufin 'yantar da ita to hakan babbar karya da zuki ta malle ne. Hakika ba su yi hakan don amfanuwar al'ummar Iraki ba.

Sun kawar da Saddam ne kawai don manufofinsu da nasa sun fara karo da juna, don kuwa me ya sa lokacin da manufofinsu suke guda, suke taimakonsa, kamar yadda suka taimake shi a yakin da ya yi da Jamhuriyar Musulunci Ta Iran.

To babu shakka, sun zo, sun tursasa masa da karfin soji, daga baya dai Saddam ya gudu. To (abin tambaya a nan shi ne) shin al'ummar Iran suna farin ciki kan hakan ko kuma a 'a? babu shakka suna farin ciki mana, don kuwa tun shekaru 20 din da suka wuce al'ummar Iran suke cewa 'Mutuwa ta Tabbata akan Munafukai da kuma Saddam', to a halin yanzu wannan mutuwar ta zo wa Saddam.

Farin cikin al'ummarmu dai kan wannan faduwa ta Saddam tana daidai da irin farin cikin da al'ummar Iraki suka nuna ne, matsayarmu daidai take da irin matsayar al'ummar Iraki. Al'ummar Iraki suna farin ciki ne don faduwar Saddam, mu ma muna farin ciki ne don faduwar Saddam.

Don kuwa ya kasance mai mulkin kama karya, azzalumi, maras kula da nauyin da ya hau kansa, mai baba kere. Haka nan ya kasance, mai mulkin kama karya akan wata al'umma, shi dai ya kasance mummunar halitta ga al'ummar Iraki da kuma mu kanmu a matsayinmu na makwabta.

To sai dai kuma, babu gaskiya cikin ikirarin 'yan mamayan na cewa farin cikin da Irakawan suke nuna ya samo asali ne saboda shigarsu (Amurkawan) kasar, wannan tsagoron karya ce. A'a al'ummar Iraki suna farin ciki ne saboda faduwar Saddam (amma koda wasa ba sa maraba da zuwan Amurkawan).

(A matsayin misali) A 'yan kwanakin da suka wuce, wani gidan Talabijin na Turai ya nuna wani bangare na birnin Bagadada, inda suka yi hira da wani saurayi, wannan saurayi ya daga hannnunsa sama ya ce cikin harshen larabci: Al-Maut li Saddam wal Maut li Bush' (Mutuwa akan Saddam, mutuwa akan Bush) wato ya bukaci mutuwa akan dukkannin mutanen biyu. Sai dai kuma, sun nuna wannan lamari ne kawai sau guda, a takaice dai irin takunkumin da suka sanya wa kafafen watsa labarai ya hana su su sake nuna wannan lamari, to babu shakka idan da za su tambayi mutane dubu daga cikin Irakawa da kuma sun sami kimanin dari tara daga cikinsu sun amsa musu da irin wannan amsa (da wannan saurayi ya ba su).

Hakika farin cikin (da al'ummar Iraki) suke nunawa kan faduwar Saddam ba shi da wata alaka da zuwan 'yan mamaya (Amurka da Birtaniyya); lalle babu yadda za a iya jingina hakan ga shigowar Amurkawan. Babu shakka, ana iya samun wasu 'yan kalilan su yi maraba da zuwan Amurkawan, su kuma nan da nan su ce dukkan al'umma suna maraba da su, a'a ina, lamarin ba haka yake ba.

Ina da wasu bayanai, tabbatattun bayanai, daga bangarori daban-daban kan cewa babu wani gari a cikin kasar Irakin tun daga Basra da Birtaniyyawa suka kame, da kuma sauran garuruwan da Amurkawan suke ciki da al'ummarsu ba su nuna rashin amincewarsu da ganin 'yan mamayan ba.

Hakika im ma mutanen Iraki suna farin ciki da tafiyar Saddam to lalle wannan farin ciki na su ya gushe saboda irin ruwan bama-bamai da sojojin Amurka da Birtaniyyan suke musu. Babu kokwanto cikin 'yan wadannan makonni sojojin Amurka da Birtaniyyan sun dandana wa al'ummar Iraki kuda da sanya su cikin halin wahala da damuwa.

Don haka al'ummar Irakin dai sun kasance 'yan ba ruwanmu ne a yayin wannan yaki da ya gudana tsakanin Saddam da masu mamaya masu wuce gona da iri. Kamar yadda gwamnatin Iran ma ta sanar da rashin tsoma bakinta ('yar ba ruwanmu) cikin wannan yaki, wannan shi ne abin da zama 'yan ba ruwanmu ya ke nufi. Don kuwa dukkan bangarorin biyu azzalumai ne, dukkansu azzalumai ne, Saddam azzalumi ne, kamar yadda su ma 'yan mamayan azzalumai ne.

Al'ummar Iraki dai ba su goyi bayan kowani bangare ba na wannan yakin kamar yadda al'ummar Iran da kuma gwamnatin kasar ba su goyi bayan kowani bangare na wannan yaki ba, wannan dai shi ne ma'anar zama 'yan ba ruwanmu, wato ba mu taimaka wa dukkan bangarorin biyu ba komai kashin taimako. Ba mu taimaka wa Saddam ba don ya tseratar da kansa, kamar yadda kuma ba mu taimaka wa 'yan mamayan ba don su sami nasara cikin lokaci ba. Mu dai mun yi kokarin amfani da dukkan abin da ya sawwaka mana wajen ganin ba mu taimaka wa dukkan bangarorin biyu ba. Hakika wadanda suke leken asiri da tauraron dan'Adam a ko ina sun san hakan, babu wata bukata mu gaya musu hakan. To sai dai kuma ya kamata al'ummar Iran su san cewa gwamnatin Iran da kuma jami'anta sun yi dukkan abin da za su iya- kuma sun yi nasara - wajen hana duk wani taimako zuwa ga dukkan bangarorin biyu.

A fili dai ya ke cewa, idan har 'yan mamayan sun sami nasara cikin sauki, to hakan ya faru ne saboda al'ummar Irakin sun zama 'yan ba ruwanmu ne kan wannan lamari. Babu shakka idan da a ce al'ummar Iraki sun tsaya a bayan Saddam a wannan yaki, to da 'yan mamayan ba su sami irin wannan nasara ba, su ma kansu sun san hakan. Wannan dai shi ne yadda yanayin yake a lokacin da al'umma ba ta yarda da tsarin da ke gudana ba, da kuma jami'an wannan gwamnati. Al'ummar Iraki dai ta fuskanci zalunci, cutarwa da kuma cin mutumci daga jami'an gwamnatin Irakin, shi ya sa suka ki taimaka musu. Wannan lamari shi ne ya ba wa abokan gaban, abokan gaban kasar Irakin, 'yan mamaya, suka sami damar samun wannan nasara da suka samu, akwai abin da zan ce kan hakan nan gaba.

Kamar yadda muka ce, al'ummarmu tana farin ciki da abin da ya faru, gwamnatinmu tana farin ciki, jami'anmu suna murna, duk da cewa suna da shakku cikin zukatansu kan abin da ya faru. Kan cewa me ya sa Bagadada ta gagara jurewa da kuma fuskantar sojojin mamayan kamar yadda garin Basra ta yi. A takaice dai, bayan makon farko na yakin, sai aka ga yanayin yakin ya canza. A makon farkon an ga yaki na hakika, mutane kuma suna cewa asalin yakin ma zai zo nan gaba, to amma, bayan hakan, an dan takura wa abokan gaba na wasu ranaku, daga nan kuma, bayan da 'yan mamayan suka fara matsowa, sai aka ga babu wani cijewa da kuma tsaron da ya dace.

Bagadada dai ta mika wuya cikin kwanaki biyu zuwa uku, wato a takaice ta fadi gaba daya. Babu wani wanda ya kare garin Bagadada da kyau; duk da cewa a Bagadadan kawai, bisa rahoton da muke da shi, akwai kimanin dakarun soji masu makamai 120,000, a cikin Bagadada da kewayensa. Haka nan kuma irin da'irorin tsaro da suka tsara a gefen Bagadadan da suke da tazara ta kilomita 100, wanda akwai wasu dakarun ma na daban, baya ga sansanonin masu tsaron Saddam da suke gefen Bagadadan. Kai idan ma dai muka ajiye wannan a gefe, a Bagadada kawai akwai dakaru kimanin 100,000 zuwa 120, 000. Amma sun gagara jurewa hare-hare na kwanaki biyu zuwa uku. Lamarin dai shi ne ko dai sun gagara jurewar ne da gaske ko kuma dai an umurce su da kada su jure, to sai dai har ya zuwa yanzu lamarin bai fito fili ba tukun, babu shakka tarihi zai kawar da dukkan wannan duhu da ya rufe wannan lamari.

To koma dai mene ne, dangane da lamarin farko dai, wato kawar da gwamnatin Saddam da Amurka da Birtaniyya suka yi, matsayarmu - idan har zan takaita ta - ita ce ba mu taimaka wa dukkan azzalumai biyun ba. Muna farin ciki cewa an kawar da Saddam. Al'ummarmu kuma suna murna kan hakan. Mu dai 'yan ba ruwanmu ne ba mu taimaki kowani bangare ba, kamar yadda al'ummar Iraki ma suka kasance 'yan ba ruwanmu. Muna murna kamar yadda al'ummar Iraki suke murna. Wannan dai dangane da lamari na farko kenan.