MAGANGANU DA JAWABAN
AYATULLAH UZMA SAYYID ALIYU KHAMENE'I {H}

(Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci)

A bisa la'akari da cewa dan'Adam mutum ne mai yawan mantuwa da kuma jahilci, don haka nema ya ke bukatuwa da wanda a kullum zai dinga tunasar da shi da kuma yi masa wa'azi don ya kyautata rayuwarsa da duniya da ta lahira.
To a hakikanin gaskiya, kuma babu shakka, cewa daga cikin muminan bayin da Allah Ya arzurtamu da da su a wannan zamani namu, wadanda kusan muna iya cewa dukkan kalamai da ayyukansu babban darasi da hannunka mai sanda ne gare mu, Ayatullah Khamene'i, Jagoran Juyin Juya Hali, yana daga cikinsu, ko kuma ma mu ce yana daga sahun gaba cikin irin wadannan bayin Allah.
Allah dai Ya arzurta wannan Jagora namu da dimbin ilmi, hangen nesa, sanin ya kamata, bugu da kari kuma ga sanin siyasar Musulunci da ma ta yau da kullum, shi yasa ma a duk lokacin da yayi magana, lalle za ka ga hikima da fitar da al'amurra a fili don amfanuwar dukkan al'umma.
To don haka ne, na ware wannan shafi na musamman don kawo jawabai da kuma kalamominsa na hikima don su kasance mana "hannunka mai sanda" a rayuwar ta mu ta yau da kullum.
Don haka mai karatu kana iya biyo mu a sannu a hankali don ganin wadannan jawabai da kuma kalamomi. A sha karatu lafiya.

  • Jawabin Jagora A Bukin Ranar Haihuwar Fatima al-Zahra: 20/Jimada al-Thani/1424 = 19/Augusta/ 2003.
  • Jawabin Jagora A Bukin Mika Makamai ga Dakarun IRGC: 3/Jimada al-Awwal/1424 = 20/Yuli/ 2003.
  • Jawabin Jagora A Garin Waramin Dake Kusa da Tehran: 11/Rabi'al-Thani/1424 = 12/Yuni/ 2003.
  • Jawabin Jagora A Bukin Zagayowar Shekara 14 da Wafatin Imam: 3/Rabi'al-Thani/1424 = 4/Yuni/ 2003.
  • Jawabin Jagora A Yayin Ganawarsa da 'Yan Majalisar Iran a Ranar 'Yan Majalisa: 26/Rabi'ul Awwal/1424 = 28/Mayu 2003.
  • Sakon Jagora ga Maniyyata Aikin Hajjin Bana (2003=1424): Inda Jagora yayi bayani kan abubuwan da suka hau kan maniyyatan.
  • Hudubar sallar Juma'ar Ranar 5 Aprilu 2002: Inda Jagora yayi bayani kan matakan da ya kamata a dauka wajen magance matsalar da Palastinawa suke ciki.
  • Rana guda cikin rayuwar Jagoran Juyin Juya Hali:Tattaunawa da jaridar Ittila'at ta yi da Hujjatul Islam Muhammadi Golpaygani, shugaban ofishin Jagoran kan halayensa.
  • Jawabin Jagora ga Iyalan Shahidai Ranar 26 Satumba 2001:Inda yayi Allah wadai da Amurka dangane da mummunan amfani da harin 11 Satumba wajen cin mutumcin masu adawa da bakar siyasarta.