Imam Khamene'i: Matukar Aka Kai Wa Iran Hari, Zan Sa Kakin Soji In Fito
Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai. Dukkan godiya ta tabbata ga Allah Madaukakin Sarki, tsira da amincin Allah su tabbata ga Shugabanmu kuma Annabinmu Abul Kasim al-Mustafa Muhammad, tare da tsarkakan Mutanen Gidansa zababbu musamman
Hujjan Allah a bayan kasa. Ina gode wa Allah Madaukakin Sarki da Ya ba ni wannan dama ta kasancewa tare da ku Ya ku 'yan'uwa maza da mata, muminai ma'abuta tsoron Allah da kaunar Ahlulbaiti (a.s) a ranar farko ta sabuwar shekara kuma a hubbaren Mai Girma Abul Hasan al-Ridha (a.s) mai tsarki. Kalmata ta
farko ita ce ta girmama ga wannan Imami mai girma ce...
«Ci Gaba»
Jawabin Jagora Ga Mahalarta Taron Hadin Kai
Yau rana ce ta haihuwar Manzon Musulunci Muhammad al-Mustafa (s.a.w.a) da kuma Imam Ja'afar al-Sadik (a.s), a hakikanin gaskiya rana ce mai girman gaske ga al'ummar musulmi. Don haka da farko ina taya al'ummar musulmi, madaukakan al'ummar Iran, mahalarta wannan majalisi musamman bakin da suka zo daga waje murnar zagayowar
wannan rana (mai albarka). Abu na biyu kuma, don girmama matsayin Manzon Allah (s.a.w.a), mu musulmi muna da abubuwan fadi ga junanmu, saboda shi Manzo a wajenmu malami ne na kyawawan dabi'u, adalci, 'yan'Adamataka da 'yan'uwantaka, kamala, ci gaban dan'Adam na har abada da dai sauransu...
«Ci Gaba»
Shawarwarin Jagora Ga Masu Son Aure
Da farko dai yana da kyau a fahimci cewa daura aure yana nufin kulla wata alaka ce da Ubangiji Madaukakin Sarki ya yi umarni da ita. Gaskiya ne cewa (aure) ya kasance daga cikin dabi'u na dan'Adam, to amma duk da hakan Allah Madaukakin Sarki ya tsarkake wannan alaka wacce daga karshe take haifar da abubuwa masu kyau. Don haka bai kamata a dauki wannan alaka a matsayin wani abu maras muhimmanci ba. Daya daga cikin munanan ayyukan da kasashen yammaci suka yi shi ne rikon sakainar
kashin da suke yi wa wannan alaka da rashin ba ta muhimmancin da ya kamace ta. Su dai turawa suna mu'amala ne da wannan muhimmin lamari, wannan karfaffiyar alaka tsakanin mace da namiji, mu'amala tamkar ta cire riga ko kuma shiga wani shago, wato a matsayin wani abu kawai mai sauki kana iya yinsa yanzu ka kuma canza shi duk lokacin da ka ga dama...
«Ci Gaba»
Jawabin Jagora Yayin Bukin Ghadir
A Garin Mashhad(
2002)
Dukkan godiya ta tabbata ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai, tsira da amincin Allah su tabbata ga Shugabanmu kuma Annabinmu masoyin zuciyarmu Abul Kasim al-Mustafa Muhammad
tare da tsarkakan Alayensa shiryayyu masu shiryarwa musamman ma da Bakiyatullah (Imam al-Mahdi).Allah Madaukakin Sarki Yana cewa: "Daga yau wadanda suka kafirta sun debe kauna daga (karya) addininku, saboda haka ka da ku ji tsoronsu, ku ji tsoraNa. A yau na cika muku addininku, Na kuma cika ni'imata a gare ku, Na kuma zaba muku addinin Musulunci a matsayin addini (na gaskiya)". (Suratul Ma'ida; 5:3)...
«Ci Gaba»
Hudubar Sallar Juma'a Ta Jagora
(Juma'a 05 Nuwamba
2004)
Yau dai 21 ga watan Ramalana ne, daga dukkan alamu rana ce ta 'al-Kadr' sannan kuma rana ce ta shahadar Amirul Muminina (a.s). Daren jiya ya kasance daya daga cikin darare uku na shekara masu muhimmanci, dararen da ake tsammanin su
ne na 'Lailatul Kadr'. A cikin wannan dare ne Mala'ikun Ubangiji suke sauka, ko kuma Ruhi yake sauka, ko kuma a cikin daya daga cikin dararen nan biyu. Sun ji dadi (sun sami babban rabo) mutanen da suka sami raya ruhinsu da saukowan Mala'ikun Ubangiji....
«Ci Gaban Labarin»
|
Jawabin Jagora Ga Jami'ai A Ranar
Karamar Salla(26 Nuwamba
2003)
Ina taya dukkan al'ummar musulmin duniya, madaukakan al'ummar Iran da kuma ku mahalarta wannan taro, jami'ai, ma'aikatan gwamnati da kuma baki 'yan kasashe daban-daban na musulmi murnar zagayowar ranar Karamar Salla.
Duk da cewa dai watan Ramalana, mai cike da albarka yana karewa ne da idin karamar salla, ...
«Ci Gaban Labarin»
Hudubar Jagora A Ranar Karamar
Salla....
(1424)
Da farko dai abin da na ga ya zama wajibi in yi magana akansa a huduba ta biyu, shi ne cewa a wannan karon ma al'ummarmu a ranar Kudus ta duniya sun sake nuna wa duniya irin karfin da suke da shi. Ranar Kudus dai ba wai kawai rana ce ta al'ummar Iran ba,
rana ce ta duniyar musulmi, don haka ne a dukkan kasashen musulmi al'umma suka fito don nuna goyon bayansu ga 'yan'uwansu Palastinawa. ...
«Ci Gaban Labarin»
Jawabin Jagora Kan Yarjejeniyar Turai Da Iran
Kan Makamashin Nukiliya(02 /11
2003)
Akwai wani abu guda ko kuma wasu abubuwa guda biyu da nake son yin magana akansu (kafin in kawo karshen jawabina). Daya daga cikinsu kuwa shi ne abin da shugaban
kasarmu mai girma Malam Khatami ya yi karin bayani akansa mai zurfi tun da farko (wato batun shirin makamashin nukiliyya na Iran da kuma yarjejeniyar da aka cimma da wasu kasashen Turai). ...
«Ci Gaban Labarin»
Jawabin Jagora A Ganawa Da Mawaka
A Maulidin al-Zahra (a.s) (04 Disamba
2003)
Ina taya dukkan 'yan'uwa abin kauna wadanda suka zo wannan bukin haihuwa da idi mai girma na (haihuwar Fatima al-Zahra) murnar zagayowar wannan rana.
Haka nan kuma ina mika sakon godiyata ga dukkan 'yan'uwan da suka ba da lokacinsu wajen shirya wannan taro mai albarka, musamman 'yan'uwan da suka zo daga wurare masu nisa, haka nan kuma 'yan'uwan da suka tsara da
rera mana wadannan wakoki masu dadi da ma'ana....
«Ci Gaban Labarin»
Imam Khamene'i: Ya Zama Dole Kasashen Musulmi Su Matso Kusa da Juna
Don Tabbatar da Manufofinsu (03 Disamba
2003)
Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Ayatullah al-Uzma
Sayyid Ali Khamene'i (H) ya bayyana cewa: "Duk da kokarin da makiya suke yi wajen haifar da rikici da sabani tsakanin
kasashen musulmi, to sai dai duk da haka ya zama wajibi kasashen musulmi su matso kusa da junansu don al'ummar su
tabbatar da manufofinsu". Jagoran ya bayyana hakan ne a yau din nan Laraba 3 ga watan Disamban 2003 a yayin da yake
ganawa da shugaban kasar Djibouti Ismail Umar Guelleh
...
«Ci Gaban Labarin»
(Matsa Nan Don Ganin Sauran Ayyukan Jagoran)
|